Showing 78001 words to 81000 words out of 322641 words
Chapter 27 - DEEN Complete Hausa Novels By Arewa Novels.txt
aiko na rana daban na dare daban? Allah dai yasaka da alhairi ya jiqan mahaifa" tafada muryarta na rauni tana jawo ha6ar zani tana rufe fuska
Ganin Hakan yasa tayi saurin kallon Deen dake kallon ta itama
Hade rai tayi tana zaromashi idanu tareda cije haqoranta 😬
Ganin Hakan yasa ya 6ata fuska yana kallonta gira ahade
Ganin kaka ta dago daga kukan kicihinta yasa tayi saurin gyara yanayin fuskarta tana qaqaro murmushi
"zauna mana aminiya, kinyita tsayuwa?"
Sai a lokacin ta tuna da zama Hakan yasa tayi saurin jawo kujerar dake gefe ta zauna tana qara fadada yaqen fuskarta
Don dole zee taita jan kaka da fira don kawar da hankalinta daga kan Deen daketa 6ata 6atan rai don atambayeshi wanda she's very sure idan aka tambayeshin abinda take gudun zai fada Hakan yasa ta dage suna fira da kakar tama mance dawata kunyarta datake ji
A bangaren kaka kau abin nema ne yasamu nan sukayita firarsu abinsu
Deen kau sosai Dariya ke cinshi ganin yadda zee ta dage sai zubo zance take wai duk don karya fadi Hakan ba qaramin Dariya yake bashi ba Saidai yana qoqarin dannewa yana sauraronsu, dayaga tafara relaxing irin tana tunanin ya mance dinnan saiya 6ata fuska yana ta6a kafarshi yayi kamar zaiyi magana Hakan sai yasa taqara saurin jawo wata firar
Sai gashi harda labarin akun gidansu dasuke kiwatawa take bata bayan labarin school dinsu kala2 databata, dama labarin abinda yafaru a kotu jiya shine farko farko da labaran suka qare ne tafara bada duk wanda yazo kanta kawai muddin dai Hakan zai kawar da wancan zancen
Haka Deen yakoma yayi relaxing yana sauraronsu yana ta kyalkyala Dariya cikin zuciyarshi
(kai Deen muna maka kallon ustaz🤭)
Saida ya wajigata son ranshi sannan yaqara 6ata fuska yace
"ouch!!"
Duk juyowa sukayi suka kalleshi, kaka na saurin miqewa tana tambayarshi menene yayinda zee tashiga fargaba sosai
Hade gira yayi yace
"ni kaffafuwana sunyi dayi, nidai zan dan fita na dan yawata"
"yawo kuma? Idan ka kamu da sanyi fa?"
"bafa iska ba ake kaka, bakiga zafi ba ake? Danaji iskan yafara isata saina dawo"
"to kai ina kasani a asibitin nan da zaka yawata? Idan ka 6ace fa?" inji kaka kamar irin allurar nan, wai zai 6ace 🙄
"ai ga Zainab, ita tasan hospital din sosai, nidai wlh nagaji da zama wuri guda" yafada yana narke fuska
Shiru tayi kamar mai nazari sai kuma tace
"to yan dubiya fa? Idan sukazo bakanan fa?" tafada da alamu dai batason yatafi
Shiru yayi kawai amma kana ganin yadda ya maida fuskar baby face kasan kawai haqura yayi ba don yaso ba
Ganin Hakan yasa kaka cewa
"to ai shikenan, amma fa karku dade... Aminiya ai kina iya rakashi ko?" tafada tana maida akalar tambayar ga zee dake sauraronsu Tundazu
Murmushi zee tayi tace
"sosai ma kaka" tafada tana niyyar tashi
Ganin Hakan yasa shima Deen saukowa daga kan gadon cikin jindadi
Saida kaka ta gargadesu akan karfa su dade sannan suka fice
Fitowa sukayi daga dakin zee agaba Deen biye daita sukaita tafiya har suka sha wata kwana da babu mutane sosai Hakan yasata juyowa ta tsaya tana kallonshi hannuwa riqeda kugu fuska a Hade
Jan burki shima yayi yana kallonta trying so hard wajen controlling dariyarshi
"menene?" ya tambaya innocently
"menene? Menene ma zaka tambayeni?" tafada cikin tada jijjiyoyin wuya
"O'O!"
"O'O! Nabi O'O da gudu, kai kenan ba'a sirri dakai, daka bude baki, da nufinka gayamata komai zakayi? Ansamu ta manta amma saboda shegen naci saika tuna mata?"
Yadda ta haqiqice tanata bala'in yasa dariyar dayake dannewa Tundazu taqi dannuwa yashiga kyalkyala abinshi
Sakin baki tayi tana kallonshi saikuma ta jinjina kai ta juya tafara tafiya
Ganin Hakan yasashi saurin binta yana cigaba da dariyar
"look, it's not what you're thinking.. Listen" yafada cikin Dariya yana cigaba da binta
Banza tayi dashi ta cigaba da tafiyarta kamar zata tashi sama don haushi
"hey... Listen mana, please" yasaka fada cikin Dariya yana Binta cikin qoqarin ganin ya taddota
Ganin taqi sauraronshi yasashi yi kamar yayi tuntu6e ya duqe yana Sakin yar qara
Zee dake gaba tana tafiya cikin fushi tayi saurin juyowa ta kalleshi
Ganin shi a duqe ya riqe qafa yana runtse idanunshi yasata waro nata tareda komowa wajenshi da sauri
"hey, are you ok?" Ta tambaya tana tayashi duba qafar
"wash! Zafi" yafada yana yarfe hannu
"a ina? Ina ne wajen?" tafada tana qara duba qafan tana son gano inda ya bige din
Jin shiru yasata dagowa sai gani tayi kallonta yake fuska dauke da murmushi
Tsuke fuska tayi ta tashi cike da jin haushi tawuce, Ganin Hakan yasa shima saurin miqewa yabita yanata mata magana amma taqi sauraronshi saida suka zo wani wuri inda ba jama'a sosai tasamu karkashin wata bishiya ta zauna
Shima zama yayi dan nesa da ita yana maida numfashin biyo tan dayayi
Dagowa yayi ya kalleta yaga danne danne ma take a wayarta
"O'O! Ni menayi to? Why are you strong-headed?"
Ganin yadda ta dago tana gallomashi harara yasashi dan daga hannuwa in surrender yace
"ok, ok. Am sorry, shikenan?"
Bata kalleshi ba kuma bata tankamashi ba
"O'O! Banace sorry ba? What did you want me to do again?"
Harararshi tasake yi bata ce komai ba
"honestly, niba gayamata fa zanyi ba, ke kike ganin haka, i was just kidding you"
Sai a lokacin ta kalloshi tace
"kidding? Ka kusan sa zuciyata ta buga saboda fargaba shine zaka kira Hakan da wasa? Sai gashi nazama ru66a6iyar redio ta qarfi da yaji"
Dariya Deen keyi tunda tafara har takai aya
"but why? Are you that scared of her?"
"fiyeda tunaninka, yadda batason komai ya sameka dinnan idan tasan takeka nayi ai babu kanta"
Murmushi yayi yace
"kibar tsoro babu abinda zatamaki, kakata nada kirki"
"dama aiba kirki nace batadashi ba, Saidai cikin few days dinnan na karanci yadda take sonka kuma bata qaunar abinda zai ta6aka"
"meyasa kikace haka?"
"saboda haka ne, just imagine idan tasan nice na watsamaka coke kwanakin baya, me kake tunanin zai faru?"
Murmushi yayi yace
"babu komai, ai tsautsayi ne kuma kowa yasan tsautsayi"
"no ba tsausayi bane ganganci ne, ni dakai munsan Hakan, ya kake ganin zatayi reacting? Ga kalamanta na ranan nasan reaction dinta won't be good"
"shine dalilin dayasa kikayi fushi?"
"fushi? Cema akayi nayi fushi?"
"A'a kawai ni nasani"
"to baka canka daidai ba" tafada tana harararshi
"to amma meyasa baki zoba ranar da daddare kamar yadda kika saba?"
"saboda banajin dadi ko ba Haka mummy tace ba"
"haka tace kuma tace Hakan ne don haka kika gayamata amma kuma a zahirin Gaskiya ba Haka bane, kinqi zuwa ne saboda abinda kaka tace"
"eh naqi zuwa ne saboda abinda kaka tace amma ba a sigar daka fahimta ba, ni banyi fushi ba, why on earth ma zanyi fushi? Me zaisa inyi Hakan bayan ni keda laifi? Kawai jinkaina nayi very guilty a lokacin naji kamar duk nice silar wahalhallun dakuke sha daga kai har kaka a sanadiyar ciwon nan naka daya tashi Sau biyu duk ta dalili na, abinda yasa nace wahalhallun dakukasha bance da kasha ba don itama kakar zan iya cewa banbancinka daita alokacin shine kai kana kwance unconcious ita kuma she's concious Saidai physically ba emotionally ba
Tinawa nayi da yadda ta damu matuqa, ta yini kuka, every now and then tana dauke hawayen dake sakkomata, a fuskarta naga tsoro, tsoron rasaka wanda kallo daya zaka mata kasan idan wani abu yasameka akwai matsala, ban ta6a sanin tanada surutu ba don da farko ko magana sai takama dole takeyi ko fira ake bata cika sa baki ba Amma kana samun lfy tazama talkative, labari harna saidawa
A lokacin nakama tunanin qila yadda tayi a lokacin dakake a kwance haka tayi wancan karon da na tadomaka ciwon, nasan ga lokacin ma tayi dararen dabata rintsaba
Tunanin halin dazata shiga da wanda kaima yashiga yasa naji guiltiness atattare dani, idan kuma na tuna silar faruwan komai sai inji narasa inda zan saka kaina don guiltiness, shiyasa... Shiyasa ranar naji bana iya zuwa, bana iya zuwa naganta ko naganka don zuciyata tayi nauyi sosai, i can't face you guys"
Deen dake Sauraronta keenly Tundazu yayi murmushi yace
"kibar wannan tunanin, kibar jin guiltiness akan abinda yafaru a ranar, rashin sanine, gashi kina cikin fushi, fushin kuma mai dalili don honestly ko nine akayiwa haka I'll get mad
In 6ata lokaci na inyi important assignment irin wannan wanda shizai zame mani tsani wajen hayewata a wannan subject din, in baje kwalwata inzuba komai wato inyi maqurar qoqari akanshi sannan wani wanda ban tabbatar da ya iyaba yazo ya yaga ya chanza dawani nashi without my permission? Konine zan fusata matuqa kuma komai na iya faruwa, so ni banga laifinki ba kuma koda kaka zataji bazataga laifinki ba don koba komai akwai rashin sani aciki don am perfect sure da kinsan inada pneumonia bazakiyi Hakan ba, so kibar tsangwamar kanki akan Hakan don bakida laifi koda kaka taji barema bazata jiba Saidai idan ke zaki fadamata"
Murmushi zee dake kallonshi Tundazu tayi, wani lokacin idan yana magana kamar bashi ba, idan yaga dama ya dinga abu maturely idan yaga dama ya dinga abin yara, ta rasa gane kanshi
"wa? Rufamin asiri, Saidai ko kai zaka fadamata, yadda take nuna sonka dinnan bana fatan na 6atamata rai ta wannan bangaren"
Dariya sosai yayi ganin yadda tayi da fuska
"waya gayamiki? Kaka nasona kamar yadda kowa keson nashi"
"A'a, na kaka ya zarta"
"be zarta ba"
"ya zarta!"
Murmushi yayi yace
"how? You know, bake kadai bace ke ganin haka ba, dayawa mutane na ganin haka, wasu ma sai suga soyyayar datake nunamin yayi yawa tana overpampering dina
Abinda mutane basu ganeba shine, ita qauna daya ce Saidai kowa da yadda yake nuna tashi
Akwai masu iya 6oyewa ma'ana masu kawaici akan nasu
Akwai masu bayyana nasu afili kamar dai kaka
To irin haka ne sai aga kamar yayi yawa bayan da za'a gwada wannan soyyayar tasu data wannan mai kawaicin da wata qila aga ko kama qafar ta mai kawaicin batayi ba
Kakata bata nuna kawaici akaina, she loves me openly batareda damuwa da abinda mutane zasuce ba
Bana mantawa lokacin da nake qarami kusan kullum sai kaka tayi hayaniya da mace akaina
Bawai jawo magana ba nake, A'a ni ake ja itakuma bata iya kyalewa most especially idan tasan ni keda Gaskiya, kaka bata ta6a kawaici idan taga za'a kwareni saita tsaya mun batareda damuwa da abinda mutane zasu ce akan Hakan, Hakan yasa mutane ke ganin soyyayar datake nunamin tayi yawa bayan ba Haka bane
Idan ma Hakan ne banga laifinta ba don tana taking role din mutane uku ne agareni
Uwa, uba da kaka. Shiyasa soyyayar tayi yawa don tana min soyyayar dazan buqata a wajen wadannan mutanen wato mahaifiyata, mahaifi na da kaka ta
Shiyasa bana missing iyayena ta fannin nuna qauna da kulawa don kaka tayimin komai, tana sona kuma nine komai nata kamar yadda nima nake sonta kuma itace komai nawa
Duk duniya banida babbar masoyiya kamar kaka daga ita sai mai sonta sai mai son mai sonta sai mai son wadda taso wanda ke sonta"
Dariya sukayi atare saboda yadda hausarshi ta qarshe take so confusing
"to aku mai bakin magana, wai mai son wadda taso mai sonta, wannan love chain din fa?" inji zee tana Dariya
Murmushi yayi yace
"wai don ki gane"
"tayaya za'ayi ingane wannan doguwar hausar? Gaka ba bahaushe ba sai fihili"
6ata rai yayi
"nine ba bahaushe ba?"
Dan bude idanu tayi tace
"oh ashe bahaushe ne, mantawa nayi" tafada tana ta6e baki don ita haryanzu bata yarda shi bahaushe bane Akwai dai abinda yake 6oyemata
"yanzu ai kin tuna" yafada yana harararta
Qara ta6e baki tayi tace
"aikau dai na tuna bawai don na yarda ba"
Ta6e baki shima yayi yana daga kafadu sannan yace
"dazu naji kina ba kaka labarin yadda akayi da qawayenki jiya"
Mood dinta ne ya chanza, Ganin Hakan yasa yace
"Allah ya tsare gaba, allah yasa kuma Hakan yazama silar shiryuwarsu, 2yrs kamar 2days ne insha allah"
Kada kai tayi sai kuma ta dago ta kalleshi tana tuna abinda sukace shine dalilinsu na juyamata baya
_*son Deen*_
Jitayi zuciyarta ta buga da qarfi Hakan yasa tayi saurin kauda kai daga kallonshi zuciyarta na beating fast
Tasan kwata2 maganarsu ba Gaskiya bace amma tarasa dalilin dayasa daga jiya zuwa yau data tuna Da wannan kalmar sai zuciyarta taqara gudu musanmman ma yanzu datake tare dashi
Haka ta danne abinda zuciyarta keyimata ta cigaba da sauraronshi suka cigaba da firarsu
Basu qara jimawa ba suka tashi don komawa don kar kaka taita jira shiru
Daga nesa daka hango yadda suke tafe suna hira kowanne da murmushi a fuskarshi sai sun burgeka don sosai sukayi matching dajuna ta kowanne fanni... ✍️
Tofa, munfara tsunduma cikin main labarin, muje zuwa 💃 yanzu ma za'a fara wasan😍
Ummin fasihu 🧚🏻♀?
8/2/21, 9:35 PM - Buhainat😝: *🙍🏻♂️DEEN 🙍🏻♂?*
*029*
Saida tadan qara jimawa hospital din sannan tawuce gida
Tun daga ranar abin nema yasamu, duk lokacin dasu zee suka zo saisun fita da ita dashi wai miqe kafa wanda Dr ne yaqara qarfafa abin don acewarshi ya dinga yawatawa din Hakan na cikin abinda zai ida sawa yaji sauqi sosai
Haka kullum zasu fita susamu quiet wuri inda ba'a cika zirga zirga ba suyi zamansu susha firarsu, sai sun gaji sannan zasu koma
Acikin yan kwanakinnan wata muguwar shaquwace ta shiga tsakaninsu wacce tafi ta da
Har takai idan basa tare sai sudinga jinsu empty kamar akwai abinda ke missing a rayuwarsu
Sosai Deen yake samun sauqi don ba qarya yana samun kulawa na sosai da sosai, abinka da private hospital inda ake tarairayar patients sosai da sosai
Gashi kuma patient din Alhaji farouq ne wanda yana daya daga cikin wadanda suke darrajawa sosai saboda gudunmawar dasuke ba asibitin shiyasa yake samun special treatment
Ranar daren da za'a sallamesu ake amsar result a school Hakan yasa zee bata samu zuwa hospital din ba
Koda ta isa school din saitaji komai na ranar nan na komamata sabo
Duk inda tawuce sai an bita da kallo wanda tasan Hakan baya rasa nasaba da abinda yafaru dakuma makomarsu master
Kamar yadda tasaba kallon be dameta ba harkar gabanta kawai take
Wucewa tayi wurin da aka liqa nasu ta duba, babu abinda tafara nema sai subject din mr ibrahim
Wani farinciki ya ziyarceta lokacin dataga abinda tasamu
*57/100%*
Hakan na nufin a exams taci 40% idan kuma aka jona da score dinta 17% na assignment dinnan saiya bada 57%
Sosai taji dadi kuma ta godewa allah akan Hakan sannan tabi sauran subjects din wanda suma duk tayi qoqari acikinsu
Koda tagama kamar ta tafi saikuma wata zuciyar tace mata ta dub a nasu nurr mana
Dubawa tayi Saidai results dinsu ba kyan gani don duk tarin carryover(s) ne, bataji dadi ba sam don haryanzu suna ranta dukda kuwa abinda sukayimata don ita idan zata so mutum to da dukkan zuciya takesonshi babu algus
Daga nan wucewa tayi department dinsu Deen don ta dubomashi shima
As expected, shima yayi passing in flying colours don result dinshi is so amazing
Ciro wayarta tayi tashiga snapping din daidai nashi murmushi a fuskarta
Saida tagama komai sannan tawuce cafteria ta siya snacks da drink ta wuce wurin zamansu don jiran qarasowar bala
Ga mammakinta tana zama wajen sai jitayi tana kewarsu sumee, sai tafara tunanin ko me sukeyi a yanzu?
Da sunanan da yanzu suna tare ana maida yadda akayi
Kawar da tunaninsu tayi tafara cin snacks dinta silently
Tunanin Deen ne yafadomata, ko me yakeyi yanzu shima? Tambayar da tayiwa kanta kenan, tasan da yau ta tafi asibitin da yanzu suna tare suna firarsu mai dadi mai sa nishadi
Sai jitayi tayi missing dinshi shima, murmushi kawai tayi ta cigaba da cin abin hannunta tana saqa da warwara ita kadai har bala ya qaraso
Babu 6ata lokaci ta tashi tawuce parking space din tashiga mota suka fice daga harabar school din
*WASHEGARI*
Yau ce ranar sallamar Deen daga hospital, ya warke garau kamar be ta6a kwanciya jinya ba saima wani qara fresh dayayi da kyau
Kaka yau baki be rufuwa, sai kai kawo take wajen ganin ta kammala kayyayakinsu waje guda
Wajajen 12 su zee da mummy suka duro asibitin suma daddy kau dama yayi tafiya tun washegarin ranar da akayi zaman kotu, dama abinda ya tsaidashi kenan
Koda suka iso sai tarar da kaka sukayi tagama kammala komai wuri guda jira kawai take a sallamesu su qara gaba don zaman asibitin ya isheta, sati biyu ba wasa ba
Mummy ce tashiga tsokanar kaka akan zumudin datake wai kodai don taje ta cigaba da samun yan anninnan ta yasa take wannan zumudin?
Dariya sukayi baki daya kaka nacewa ashe dai ta gano
Kallon Deen zee tayi taga ya sakarmata murmushi
Itama maida mashi martani tayi tana kauda kai tashiga gsida kaka itama
Cikin fara'arta kaka ke amsawa tana tambayar ta ya sakamakon dataje dubowa jiya
Murmushi tayi tace
"Alhamdullilah kaka, sakamako yayi kyau sosai"
"masha allah, ai haka akeso. Ai ina ganinki nasan zakiyi qwanya kamar dai kyakyawa na, allah sarki, kowa zaije ya dubomashi shi? Inajin nizanje in dubomashi bari dai komai ya lafa"
Dariya duk sukayi jin abinda tace, Deen yace
"to kaka ke ya za'a yi ki iya? Tayaya zaki iya gano sunana cikin jerin sunayen dake manne a wajen? Kuma ma Dariya zasuyi miki wlh, suga tsohuwa tazo duba result" yafada yana Dariya
Daquwa ta watsamashi tace
"ungo nan don qaniyarka, nice tsohuwa?"
Dariya duk suka sake dauka
"Ato, maganar shi dai na kan hanya" inji mummy tana Dariya
"ba wata kan hanyar datake zaki wani goyi bayan shi, kubar ganin na haka to tsohuwa ce mai ran qarfe don abinda mai ji da quruciya bata iyayi ina iyawa, ko aminiya?"
Murmushi zee tayi tace
"kyalesu kaka, ai fadi ma 6ata baki kuma bama sai kin wahalar da kanki ba na dubomashi, bari kigani" tafada tana zaro wayarta ta lalubo result din ta nuna ma kaka, aikau ta amshe wayar tana dubawa baki washe kamar irin tasan abinda ke ciki dinnan
"kai masha allah! Bana gayamaku ba, dan jikallen nawa ba dai qwanya ba, kalli wani dan abu abu nan nasan na masu qoqarine ko?" tafada tana nunama zee dake Dariya bama itaba duk mutanen dakin
"eh kaka ai yayi qoqari sosai" inji zee tana kallon wayar
"snapping