Showing 45001 words to 48000 words out of 322641 words

Chapter 16 - DEEN Complete Hausa Novels By Arewa Novels.txt

27 Nov 2025

4336

nace I don't like you ne kuma saboda lokacin you're harsh ne amma yanzu.." Sai kuma ya daga kafadu

"amma yanzu me?" tafada kamar zata makeshi

Dan gaucewa yayi yana Dariya sannan yace
"amma yanzu you're nice"

Daga gira daya tayi tace
"really?"

"yes, amma kadan fa, you're a little bit nice, kamar haka" yafada yana nunamata daidai saman qaramin yatsunshi

"ba haka ba?" tafada tana wara hannu tana mai nuni da tsayin tsakankanin hannun nata

"A'a, bekai hakaba tukkuna" yafada yana Dariya ganin yadda ta 6ata fuska

Ta6e baki tayi tace
"well, me I don't care idan mutane basasona, mutane baka iya musu gwara kayi living life dinka ka sharesu"

"yes, sometimes gwara hakan amma kuma shaidar mutane akanka ba qaramin tasiri ke gareta ba, yes karka biye akan saika iyawa mutane amma kuma kar hakan yasa kuma kasa su dinga yimaka wani kallo daban, care about what people say about you sai ka tsinta aciki, idan akwai inda ake buqatar gyara saika gyara idan kuma babu saika share amma nuna halin ko in kula ga abubbuwan da mutane ke tunani akanmu yanada illa ko babu komai bamusan sadda zamu mutu ba and idan ka mutu, the same mutanen da baka damu dasu ba su zasu fara fadin abinda suka sani gameda kai, for instant idan na kirki ne kuma mutumin is nice to them sai kiji anfara yabonshi ana jimamin rashi da akayi amma idan sa6anin haka ne saikiji ana magangannu marassa kyau gameda mamacin kuma ana nan ana daukar record amma they dont care wasu ma don aqara maka kan abinda zaka tarar zasu dinga yi dakai din kinga ai that's not proper bayan haka kuma mutane ganin su kike amma bakisan baiwar da Allah yayi musuba, wani kambun baka gareshi duk abinda ya fada akanki yana iya binki, akwai masu haka dayawa Batareda suma sunsan sunada shiba, kinga gwara ka kiyaye kuma kabi a sannu don ko ba haka ba ma, kasancewar mutumin mutane yafi dadi akan mutum yazamana kowa baya sonshi only few does"


Tunda yafara maganar ta kafeshi da idanu harya kai aya, mammaki ne sosai aranta, ina duk yasan Wannan? Mutumin datake yiwa kallon sha uku sha hudu shi yasan duk wadannan?

Ganin batace komaiba sai yacigaba dacewa
"and also rashin kunya ga nagaba dakai babu kyau, komai abinda zaiyimaka kau, Koda yayi maka wani abu marar kyau to yaci albarkacin girme maka dayayi kayi hqr ka kyaleshi shi da Kanshi idan ya nutsu daga baya zaigane yayi ba daidai ba kuma koba komai yasan kanada issashiyar tarbiya bazai kuka dakai akan hakan ba

Yanzu misali mr ibrahim, idan kika duba babban mutum ne, yanada 'ya'ya qilama yakusan haihuwar ki, he's well respected man, mutane na yabonshi saboda kyawawan hallayenshi, yes ke yana nuna miki baya sonki amma kin ta6a tambayar kanki meyasa? Kin ta6a lura da yanayin mu'amallarshi da sauran dallibai sannan ki duba da naki? Meyasa yake son kingin dalliban ke yake nuna maki akasin haka? Ke zaki bawa kanki amsa
And also ki dinga dora kanki a mizanin wasu, idan kece yaro dan 10yrs yayi maki rashin kunya Koda kuwa laifinki ne ya zakiji? Am sure idan bakiyi mashi duka ba saikin mareshi, so goes with mr ibrahim, shi bazai dakeki ba don kin wuce duka a wajenshi amma abinda kikeyi dake qonamashi rai zaisa ya dauki mataki ta wata hanyar kamar yadda yake shirin yi yanzu don ko kece hakan zakiyi saboda abinda zakiyi tunani akai shine yaya zakiji idan mutum tsaranki ya yarfaki agaban wadanda ke ganin mutuncin ki? To bare ace kin girmeshi nesa ba kusaba

Bayan haka kuma mallamai sunada matuqar muhinmmanci agaremu don Allah ma na amsar addu'ar su akanmu, To idan hakane sai kiyi tunani tsinuwarsu agaremu baxaiyi tasiri akanmu ba kuwa? Ni aganina mr ibrahim bashida laifi a Wannan gabar taku idan ma yanadashi kiyimashi uzuri da shekarunsa ku shirya, am telling you zakiji dadin subject dinshi fiyeda yadda kike zato... Amma fa shawara ce" yafada yana daga kafadu yana kallonta da innocent eyes dinshi


Zee da tundazu ta maida shi t.v takasa cewa komai ta Kauda kai tana jan numfashi

Hakan yasashi tsarguwa sai yace
"sorry idan magangannuna sun 6ata miki rai, am just trying to.."

Ringing din wayarta ta katseshi hakan yasa yayi shiru yana kallonta


Cirota tayi daga jakkarta ta daga ta kara a kunne tana kallonshi

Shiru tadanyi sannan can tace
"am around the school, menene?"

Bamuji abinda akace ba sai cewa tayi
"ok ganinan, am coming"

Daga haka ta katse kiran sannan ta dago ta kalleshi taga shima ita yake kallo

Murmushi tayimashi shima ya maida nata martani

"bari naje Deen" tafada tana maida wayarta a jakka

Kamar zai tambayeta ina? Saikuma yayi shiru

Ganin hakan yasata yin Murmushi ta miqe tsaye tana rataye jakkar tace
"wajen mr ibrahim, guess result din zan amsa, sumee tabugo wai yana nemana"

Murmushi yayi mata yace
"ok good luck"

"thanks, zan dawo in tardaka anan?"

"no, library zan koma, iskar nan wajen yafara yawa, idan kuma 1 tayi zan wuce class"

"ok see ya, ai bazan kai 1 dinba tunda nasan result din kawai zai bani, saina dawo"

"To, adawo lfy"

Batace komaiba ta juya ta wuce shikuma yabita da kallo harta 6ace mashi

Ajiyar zuciya ya sauke yana daga kafadu sannan shima ya tashi ya tattara littatafan shi yanufi library don iskar dake kadawa harya fara mashi yawa gashi dama mura yake dukda da sauqi sosai... âœï¸




Ummin fasihu 🧚ðŸ»â€â™€ï¸?
8/2/21, 9:33 PM - BuhainatðŸ˜: *ðŸ™ðŸ»â€â™‚ï¸DEEN ðŸ™ðŸ»â€â™‚ï¸?*







*018*





Tafiya take amma magangganun Deen ne keta dawomata a kwanya

Tarasa dalilin dayasa magangganun suka tsaya mata sosai a rai har tanajin tasirinsu ajikinta


Da Wannan tunanin ta qarasa kofar office din mr ibrahim


Knocking yayi, saida yabata izinin shigowa sannan ta tura qofar tashiga

Abin mammaki sai jitayi ta tsargu ga wata uwar kunya data lullu6eta kamar ta nitse lokacin da yadago suka hada ido hakan yasata janye nata da sauri ta ida Qarasowa cikin office din

"good afrernoon sir.." tafada a hamgame Batareda ta kalleshi ba

"afternoon" ya amsa a taqaice shima Batareda ya kalleta ba

Saida yagama abinda yakeyi sannan ya dago yasake kallonta saikuma ya Kauda kai yana zaro wata takarda


"here.."

Dagowa tayi taga miqomata yake, hakan yasata qarasawa sai samun kanta tayi da amsa hannu biyu

Dan kallonta yayi saikuma ya Kauda kai yajawo wani aikin

Ganin still tana atsaye yasashi cewa
"zaki iya tafiya"

Kada kai tayi sannan tajuya tabar office din

Binta da kallo mr ibrahim yayi harta fita sannan yakoma ya jingina da kujera yana cije lip din qasa

Sosai scores din dataci yabashi mammaki, tunma yana marking yake mammakin yanayin aikin nata, da ba agabanshi tayi ba da saiyace ba ita tayi aikinnan da kanta ba

Hakan ba qaramin 6ata mashi rai yayi ba don yaga alamun duk inda ya 6ullomata saita sha, yarasa hanyar dazaibi ya rama wulaqancin datake mashi, yarasa yadda zaiyi daita.



Koda zee tafito saikuma taji batason komawa wajen Deen

Wucewa tayi inda tasan su sumee suke

As usual, fira ta tadda sunayi ana shewa

Ganinta yasa duk suka maida hankalinsu kanta

"hey guys!" tafada tana Qarasowa wajensu

"hey!!!" Duk suka amsa mata dashi

"yane?" tafada tana zama cikinsu


"normal, ya? Kin kau je kiran mr ibrahim kuwa?" inji sumee

Kada kai kawai tayi alamun eh tana komawa ta jingina da bishiyar bayanta

"To ya kuka qare? Hope dai kina tafe da good news" inji deeya cikin zaquwa


"well, ban saniba nima don ban ma bude ba" tafada tana nunamasu takardar a hannunta


Har rige rigen fizgewa suke a hannunta suka shiga warwarewa cikin doqi

Shiru tayi kawai tana kallonsu Batareda tace uffan ba

Sosai score dinta ya Girgiza zuciyarsu don ba haka sukayi expecting ba

Saida suka dan ja lokaci suna Bin takardar da kallo sannan sumee tayi qarfin halin cewa
"wow! Masha Allah, gaskiya abu yayi kyau"


Sai a sannan kingin ma suka hau yaqe suna yaba score din nata

Itadai batace komaiba sai dan Murmushin datayi kawai

"kai amma abu yayi, gaskiya mungodewa Allah dayasa mr ibrahim ya tausaya yabarki kikayi wani, kinga yanzu no more fargabar carryover" inji rukky wanda da zaka bibbiya yadda zuciyarta take akan hakan dakasha mammaki

"aikau dai Allah ya sanya alhairi, ya taimaka kam" inji nurr tana maida mata takardar

Amsa tayi tana cewa
"thanks" ta maida a jakka Batareda ta duba ba

Firar tasu yanzu ta rage armashi don kowa da abinda yakeji a zuciya na rashin Jindadin abinda yafaru ga zee

Sai anan kowacce tafara fargabar carryover din wa kanta don da su bata tasu suke ba, itan dai data tsaremasu wuri suka sama ido

Ganin zaman ya isheta wajen yasa ta tashi tace masu bari taje library tayi karatu

Duk da to suka amsamata don dama suna buqatar space su tattauna akan Wannan mummunan abin da yafaru agaresu



Duba agogo tayi taga 1 tadan wuce, tasan baya library din yanzu, yana class

Illai kuwa data shiga bata tardashi ba, bata damuba ta wuce ta zauna ta dora jakkarta saman desk din ta buga tagumi da hannu bibbiyu

Shiru tayi yayinda tashiga yiwa magangganun Deen na dazu fashin baqi

Tabbas idan bazata sanyo san zuciya a lamarinnan ba tasan Deen nada gaskiya a Wannan fannin

Itace cause din gabarsu da mr ibrahim, don tun farko ita ta taqaleshi

Ta shigo class Batareda izininshi ba yayimata magana maimakon tayi apologizing tazo tawuceshi ta fice

Tabbas kowa akayiwa haka saiyaji haushi kuma saiya dauki mataki akai wataqila shiyasa ya addabeta a lokacin tazama abin dizgawarshi a class inda daga baya dataga bazata iya cigaba da dauka ba tabar attending lecture din nashi

Tabbas idan za'a bibiyi gaskiya ita keda laifi saidai ga lokacin, tunanin cewa tafi qarfin kowa dakuma qiyayyar datakema school din yasata take gaskiya ta cigaba a hakan

Ciro takardar tayi ta warwareta itama tana kallo

*17%*

Saidai abin mammaki bata tsinci kanta cikin farin cikin da take tunanin zata tsinci kanta ba

Haka kawai takejin zuciyarta a cinkushe tun bayan maganarsu da Deen.


Tunda take dasu sumee basu ta6a nunamata abubbuwan datake ba daidai bane saima turata dasukeyi, duk abinda tayi daidai ne a wajensu saigashi yau tasamu wanda ya nusar daita abubbuwan datakeyi ba daidai bane dakuma hujjoji wanda ta gamsu dasu

Tunanin dayafi tsayamata a qwalwa shine, yau idan ta fadi tamutu me yan school dinnan zasuce akanta? Me mr ibrahim zaice? Wa zaiyi jimami akan haka? Bayan qwatarta (su sumee) wazaiyi jimamin rashin ta har ya bude baki da sunan yimata addu'ar jin qai awajen Allah?

_babu_ dayan zuciyar tabata amsa
_dadi ma zasuji sun rabu da alaqaqai_ dayar zuciyar ta fada mata

Cukwikwiye takardar tayi ta damqeta a hannu sannan ta kifa kanta a desk din gabanta tana lumshe idanu, ita kanta Batasan yadda zata misalta yadda takeji a zuciya ba, kawai jin ranta take a matuqar jagule, jagulewa marar misaltuwa.



Batasan iya lokacin data dauka ba ahakan sai jin cool voice dinshi tayi sama2

Jitayi an bubbuga desk din ana cewa
"hey, get up!"

Sai alokacin ta bude idonta sannan ta dago ahankali

Tsaye taganshi akanta da dan guntun Murmushi a fuskarshi

Zama yayi yana cewa
"sleepy skull, kin karya dokar library"

Murmushi tayi tana zama daidai tace
"harkun gama?"

"yes, dazu nayita jira shiru, saura kadan nayi missing lecture"

Murmushi tadanyi wanda yafi kama da na yaqe tace
"be sallameniba da wuri ne"

"ok, hope dai an dace" yafada yana dan wara idanu

Ganin kallon dayake mata yasata Murmushi sannan ta bude hannunta dake damqe da takardar still tabashi

Qara wara idanu yayi yace
"O'O! Wannan ce takardar kuma kikayi squeezing dinta haka"

Daga kafadu kawai tayi ta koma ta jingina da kujera

"pheew! You're careless" yafada yana zaro mata idanu

"whatever!" itama ta fada tana maida kanta akan desk kamar dai dazu

Harararta yayi sannan ya warware takarda zuciyarshi na gayamashi ko She failed ne shiyasa duk tayi haka


Ganin score dinta yasashi waro idanu
"wow! You passed!" taji yafada, hakan yasata danyin Murmushi daga kwance

"look you scored 17" yafada yana nunamata cikin murna

"I know' tafada a taqaice

"amma meyasa bakya murna?" yafada murnanshi na dan komawa ciki

"just" taqara amsawa a taqaice

Tsayawa yayi yana kallonta
"are you ok?" yafada asanyaye

Hakan yasata dan dago idanu ta kalleshi daga kwancen

"yes, kawai banajin dadine" ta amsa tana tashi zaune

Bata fuska yayi kamar zaiyi kuka yace
"sorry"

Kada mashi kai kawai tayi tana dan Murmushi

"ko muje school clinic abaki magani?" inji Deen cikin damuwa


"no, dont worry dana je gida zansha nawa"

Daga haka basu qara cewa komaiba, ita ta maida kanta a jikin kujera tareda lumshe idanu shikuma ya fiddo littafi yana dubawa yana yi yana Dagowa ya kalleta akai2


Kiran sallah ya fiddasu library din, ita tawuce masjid din mata shi yawuce na maza

Koda suka fito bankwana sukayi don wucewa Deen zaiyi gida ita kuma sunada lecture yanzu, hakan yasa suka rabu anan akan sai gobe idan Allah yakaisu inda yake qara jaddadamata tafa sha magani idan taje gida.


Lecture din dai rabi da rabi ta fuskanta don mind dinta baya wajen

Saida sukayi 30mins sannan suka fito

Direct parking space ta nufa don bala yariga yazo

Babu 6ata lokaci tashiga yaja suka fice



***


Ranar haka ta qarashe yinin cikin rashin kuzari.

Magangganun Deen sun kasa barin ta ta sarara, duk motsin da zatayi saita tunasu kuma saitayi zurfi atunani akansu


*WASHEGARI*




Daga takardar yayi don hanata gani yace
"kibar kallo haan?"

Dariya tayi tana qara tantado dan gani tana cewa
"To menene idan na kalla haan?"

Maida takardar yayi bayanshi yace
"idan teacher na marking dama student na zuwa ya kalla ne?" yafada yana hade gira

"Sai afara akanka" tafada tana Dariya

Saka takardar yayi a aljihu yace
"To shikenan, nafasa marking din sai naje gida sai nabaki gobe"

Wara manyan idanunta tayi tace
"gobe kuma? To shikenan yi abinka nabar leqowa"

Kauda kai yayi yana hade rai yace
"no, sai naje gida"

6ata fuska tayi tace
"O'O! Sokake in kasa barci yau?"

"me zai hanaki barcin"


"zullumin marks da zanci mana"

"To ba ke ke leqowa ba?"

"To nabari, kaga ma ba kallonka ba nake" tafada tana kallon gefe

Saida ya gallamata harara sannan yaciro takardar yacigaba da marking yana yi yana satar kallonta yaga ko zata juyo


Bata juyo dinba amma tana satan kallonshi shima ta wutsiyar ido har yayi ya gama.

"To juyo" inji shi

Juyowa tayi ta gallamashi harara
"mutum da abinshi a hanashi kallo ai gashi yanzu zaka gwadamin duk 6oyon.."

Ganin yana linkewa alamun yayi zuciya be bada wa yasata Saurin Wara idanu tana cewa
"laa, wasa fa nake maka kai bakasan wasaba?" ta qarashe tana fizge takardar ta tashi tsaye tana warwareta da sauri

Ganin abinda taci yasata dan yin qarar murna
"yeeee!" saikuma tayi mashi gwalo 🤪

Kwafa yayi kawai yana jinjina kai


Komawa tayi ta zauna tana cewa
"dama dan kaga naci duka shiyasa kake jamin rai ko"

Harararta yayi yace
"stop talking to me ni babu ruwana dake"


"Sai nayi, sai nayi!!!" ta qarashe da qarfi

Saurin dode kunnuwa yayi yace
"O'O! Why are you shouting?"

"I'll keep shouting indai bakace da ruwanka dani ba" tafada tana yin ready din yin wani qarar


"To, ok naji! Da ruwana dake, shikenan!" yafada da dan qarfi sannan ya juya mata qeya


Dariya tayi tana cewa
"Allah ya taimakeka to" tafada tana qara duba takardar aikin daya bata yanzu ta cinye duka


Sosai haduwa da Deen ya chanzata cikin yan kwanakinnan, yanzu she's more happy and lively

A kullum idan tazo school burinta ayi agama ta Kama gabanta ta koma inda tafito amma yanzu har qagara take gari yawaye taje school duk don su hade dashi

Tunda take bata ta6a sakin jiki da namiji kamar yadda tayi da Deen yanzu ba, kai ko mace babu wacce ta ta6a sakin jiki daita kamar yadda tayiwa Deen, lafiya lau suke wasa da dariyarsu, idan tana gabanshi itama komawa take mashiririciya kamar shi, daga abokin fada yakoma aboki yanzu kuma bestie duk acikin yan kwanaki. Sosai takeson tarraya dashi don he's fun to be with


Kallonshi tayi taga yana gyara setting agogon hannunshi

Shiru tadanyi tana taunar qasan bironta sannan ta janye tace
"Deen?"


Dagowa yayi ya kalleta

"inaso muyi magana dakai ne"

Jin haka yasashi maida dukkan hankalinshi akanta

Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace
"akan maganar damukayi jiya ne... You know, nima banason gabar dake tsakanina da mr ibrahim but.. Bazaka ganeba, mr ibrahim mugun dan dizgi ne, dama abinda yafara hadamu kenan, duzga mutane, yanzu ina iya zuwa inbashi hqr ya yarfani, I know him very well" tafada tana 6ata rai


Shiru Deen yadanyi sannan yace
"kinaso ku shirya ne?"

Itama shiru tayi kamar mai nazari can kuma ta daga kafadu tace
"maybe"

Murmushi yayi yace
"bazai duzga ki ba, I bet you"

"no ni kadai nasan halinshi, bana sone wajen gyara a 6ata gabadaya don idan ya dizgani zuciya na iya dibana nayi mashi rashin kunya and I don't want that to happen"

Shiru Deen yasakeyi na wani lokaci kamar mai nazari sannan ya kalleta yace
"To, why not muyi haka? Karki tareshi directly kibashi hqr, kibi indirectly"

"how?" tafada cikin yanayin rashin fahimta

"first step shine kifara attending class dinshi ma'ana daga yanzu no more missing din lecture dinshi"

"tayaya hakan zai taimaka?" ta tambaya cikin rashin fahimta

"ta hanyoyi da dama, kinga na farko abin zai bashi mammaki, he'll be like anya kuwa kece? Na biyu hakan zai dan sauko dashi daga fushin dayake dake, idan kika tunkareshi daga baya baxaiyi bursting ba zaiyi considering dinki"


"hmm idan ya koreni daga class din fa?"

"bazai koraki ba, da farko zaiyi mammakin ganinki a class dinshi, sai kuma ya kyaleki yaga dame kikazo dashi, ke kuma alokacin sai kiyita neman kusanci dashi ta hanyoyi daban2 kamar amsa tambaya idan yajefo, tambayarshi abinda baki ganeba, kodama kin gane ki dinga tambaya, yadai kasance kuna communicating ko yaya ne, da haka da haka har muga perfect time daya kamata kibashi hqr"

Shiru tayi tana nazarin maganganunshi can tace
"To students fa? Me zasu ce gameda hakan? Baka ganin class dina zai zube?" saikuma tayi Saurin matse bakinta don zancen zuci ne yafito fili

Murmushi yayi yace
"kefa kikace bakya damuwa da abinda mutane ke cewa akanki, you see mutane baka iya musu, so far kinsan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login