Showing 174001 words to 177000 words out of 322641 words

Chapter 59 - DEEN Complete Hausa Novels By Arewa Novels.txt

27 Nov 2025

4335

abin ya tsaya mashi arai.

Ga wani gizo da fuskarta keyi mashi duk lokacin daya motsa.

Tunawa yayi jiya a wajen dinner

Kasa concentrating yayi akan abincinshi banda satar kallonta every now and then babu abinda yakeyi


Itakau batama san yana yi ba don bayan Gaisawar dasukayi sama sama ko gefen shi bata qara kallo.


Koda ya dawo sallar asuba shirin fita asibiti ya hau yi don yau aikin safe garesu.


Qarfe 8:00am yafito daga dakinshi cikin shigarshi ta qanannun kaya, baqin dogon wando da farar shirt yaci zanzaro ga lapcoat dinshi dake sagale da hannunshi sai briefcase riqe da dayan hannun.

Yayi kyau sosai a shigar ga wani irin cool qamshi dake tashi a jikinshi


Fara saukowa yayi daga stairs din Waya kare a kunnenshi yana amsa kira har ya ida sauka.


Dago idanunshi yayi sai suka sauka akan zee dake jejjera flask akan dining table


Kafeta da idanu yayi yana kallon every movement dinta Yayinda can qasan zuciyarshi yake jin wani feeling da bazai tantance kona menene ba


Zee dake aikinta hankali kwance tadan dakata jin kamar ana kallonta

Ahankali ta dago sai caraff suka hada ido dashi tsaye a inda yake yana kallonta itama


Ahankali yadan sakarmata wani cool murmushi

Dauke kai tayi kawai ta cigaba da abinda takeyi

Hakan yasa ya qara fadada murmushin shi sannan ya nufo dining area din


Jan kujera dake facing dinta yayi bayan Qarasowarshi ya zauna still yana kallonta


Bata dago ba ta kalleshi haka kuma bata dakatar da abinda takeyi ba

"sabahal khair ukhtie" yafada jovially


Sai a sannan ta dan dago ta kalleshi, kamar bazata yi magana ba sai kuma ta motsa bakinta ahankali tace
"sabahan-nurr"



Dan Wara idanunshi yayi jin ta maido mashi da larabcin

"dama kinajin arabic?" ya tambaya yana kallonta

"No" tafada tareda Juyawa tabar wajen


Binta da kallo yayi harta shige kitchen din, daga girarenshi yayi sannan ya danyi murmushi ya kada kai sannan ya sa hannu yajawo abubbuwan kan table din yana bubbudewa don serving kanshi.



Yana cikin cin abincin ne suka sake fitowa daga kitchen din da zee da batool


Dagowa yayi daga shayin dayake sipping yana kallonsu har suka qaraso

"sabahal khair Akhie" inji batool cikin fara'a

"sabahan-nurr" yafada yana dan satar kallon zee dake dora tray din hannunta kan table din

"yau kuma tunda safe zaka fita?" inji batool tana taya zee jejjera abubbuwan dasuka kawo

"ga zahiri?" yafada a taqaice yana sipping shayinshi ahankali yana satar kallon zee ta saman kofin

"da ace yau lecture din safe gareni da kayi dropping dina"


Dagowa yayi ya gallamata harara yace
"ke da wa?"

Dariya tayi

"Don't even try that, rannan ma dakikaga na kaiki don ummy tayi magana ne shiyasa amma wlh kika qara yimin Hakan zan daukeki ne naje na watsar gefen titi babu ruwana"


Dariya batool tasakeyi tace
"babu komai saina tashi na nemi cab ya qarasa dani school din, what matters shine kadai tuqani"

Dagowa yayi ya gallamata harara Hakan yasa ta koma bayan zee datayi kamar batasan sunayi ba tana Dariya

Kwafa yayi sannan ya turama zee plate dinshi
"zubamin wannan kadan ukhtie"

Kallon plate din tayi saikuma ta dan jawoshi tashiga zubamashi

Saida yaga yakai daidai yadda yakeso yace
"yauwa ukhtie, shukran. Ke kuma ki koyi yadda ake girmama na gaba kamar dai ita" yafada yana nuna zee

Ta6e baki batool tayi tace
"nima ai inayi, Ganine ba'ayi"


"a ina kike yi? Kin maidani abokin wasanki, shi yaya girmama shi akeyi sosai, don babban wa uba ne, koba haka ake cewa ba ukhtie?" yafada yana maida kallonshi kan zee

"yes" tafada simply sannan tajuya ta bar dining din ta nufi stairs


Binta da kallo duk sukayi sannan suka kalli juna

Qumshe Dariya batool tayi tana rufe bakinta da tafin hannunta

Wani kallo ya watsamata yace
"bar nan"

Da sauri tabar wajen tana cigaba da qumshe dariyarta tabi bayan zee


Kwafa yayi sannan ya maida hankalinshi akan abincin gabanshi ya cigaba da ci


Bai qara 6ata lokaci ba ya tashi ya fice daga gidan.


Tunda yashigo hospital din aketa gaidashi, duk inda ya gitta sai an gaidashi shikuma yana amsawa cikin fara'a


Aymaan kenan, kyakyawan namiji mai cikar haiba da kamala, mutum ne faran faran ga yawan wasa da sakewa wanda Hakan yasa yakeda farinjinin mutane sosai

Aymaan ba fari bane haka zalika ba baqi bane, he's chocolate in complexion, chocolate dinma irin mai sheqin nan.


Dr Aymaan qwararren likitan mata ne wanda ake jidashi a daya daga cikin manyan asibitocin dubai saboda qwarewarshi da hazaqa da allah yayi mashi


Yayi suna sosai a asibitin dama sauran asibitocin qasar don sosai kingin asibitocin ke kwadayin samunshi a asibitinsu suma kuma sunsha kawo mashi tayin yadawo asibitin su akan farashi mai tsoka amma yayi turning down request dinshi politely don idan akwai abinda ya tsana to cin amana ne?


Ko patients sunfi son Dr Aymaan ya dubasu saboda qwarewarshi wajen aiki dakuma iya mu'amallantar patients dayayi, gashi qwaro ne a fannin aikinshi don wani lokacin idan wasu likitocin suka kakare to shi ake kira kuma cikin ikon allah da yazo komai zai warware. Shiyasa mafi yawancin lokuta ma bayada timetable na kanshi na aiki don ko lokacin aikinshi bane ana iya kiranshi at anytime kuma yatafi batareda gardama ba



Aymaan allah yayishi da tausayi musanmman akan mata.

Yana matuqar tausaya masu kuma beson abinda zai ta6asu don idan akwai abinda beso to kukan mace ne idan kuma akwai wanda ya tsana to mai sa mace kuka ne, duk wanda yasan Aymaan yasanshi da wannan tausayin na mata ko don shi likitansu ne kuma yasan matsalolin da suke fama dasu?


Akwai lokacin daya ta6a yiwa wata mata aiki dazata haihu don takasa haihuwar da kanta, haihuwar matar tabiyu kenan


Cikin sa'a akayi aikin lafiya aka gama lafiya don har Saida ya gwadama matar diyar daya Ciro yana Tambayarta me tasamu dayake aikin na ido biyu akayi.

Lafiya lau ta amsa mashi da mace aka samu Hakan yasa yabada diyar akaje wajen gyarata shikuma yafita yima ahalin matar albishir din yin aikin successfully.


Sosai ahalin sukaita murna suna godewa allah shikuma suna sanya mashi albarka.

Da farinciki ya dawo dakin da take Saidai me? Sai ya tarar matar nata kokowa da numfashi nurses nata qoqarin bata taimakon gaggawa.

A rude shima ya shiga iya qoqarin shi wajen ganin numfashinta ya daidaita Saidai kana naka allah na nashi don ko minti biyar bata qara ba a duniya ta rasu


Sosai mutuwar ta girgiza Aymaan a lokacin.

Sunfi Mintuna 10 ahaka dashi da nurses din dakin dasukayi cirko cirko cikin rashin sanin abin yi


Daga baya Dakyar ya iya summoning courage yafita Domin sanar da ahalin nata

Saidai ganinsu sunata daukar jaririyar anata murnar qaruwa

Sosai gwiwarshi ta sage yaji zuciyarshi ta karye

Koda sukaga Hakan sai suka fara Tambayar shi lfy?

Dakyar ya iya danne abinda yakeji yayi breaking din labarin mutuwar matar garesu

Dayake ba masu qarfin imani bane sai suka hau koke2 da iface iface har wata ma ta sha qwalarshi tana cewa qarya yakeyi ba yanzu yazo ya sanar dasu lafiyarta lau ba

Nan fa akazo aka taru mutane nata rarrashin ahalin mamaciyar suna yimusu tuni da qaddara.

Aymaan kau be cewa komai sai hawayen dayake wanda ba komai ya jawo Hakan ba sai kukan da jaririyar keta tsanyarawa.

Sosai jaririyar tabashi tausayi don bilhaqqi da Gaskiya take kukan kamar tasan abinda yafaru

Ganin Dr Aymaan na hawaye yasa duk jikin mutanen wajen yin sanyi suna kallon yadda ya dauki jinjirar yana kallo yana hawaye.


Saida ya dauki kwanaki sosai kafin abin yasakeshi kamar yadda yasaba dik lokacin da patient ya mutu a hannunshi.


Babu wanda besan wannan halin nashi na tausayi ba a fadin asibitin



Hakan yasa Koda yaji labarin zee sai yaji ta mugun bashi tausayi kuma yaji ya tsani wanda yaudareta don shi aganinshi mata hallitu ne na musanmman wanda ya kamata ayi treating dinsu specially don a gurinshi mata sune gift of life.



Aymaan yanada abokai wadanda shi kansa besan iyakarsu ba Amma acikinsu akwai babban amininshi wanda alaqarsu tawuce abota kadai ta koma kamar ta yan uwantaka.

Sunan aminin nashi AHMAD JUNAID, dan kasuwa kuma P.A a companin babanshi

Tare suka taso tun suna yara kuma tare sukayi karatu a makaranta daya sai course dinsu kawai daya banbanta


Sosai suke abota mai tsafta wanda Hakan yasa tun suna qananu suka qulla zuminci tsakanin iyayensu suma don sosai iyayen Aymaan da Ahmed ke zuminci

Zuminci yaqara karko ne lokacin da Ahmad da batool suka fara soyayya.

Babu wanda beyi farinciki ba da Hakan don ko babu komai Hakan zai qara qarfafa zumuncinsu kuma zai qara girmama abotar dake tsakanin Aymaan din dashi Ahmad din, Wannan kenan.



Sai da marece sosai sannan yabaro asibitin

Akan hanya ya tsaya yasayi kayan maqulashe da fruits sannan ya wuce gida.


Parking yayi a parking space sannan ya bude motar yafito

Kamar kullum lapcoat din na sagale a hannunshi ya riqo briefcase dinshi da dayan hannun

Rufe kofar yayi sannan ya zagaya ta dayan bangaren ya bude back seat ya Fiddo ledar tsarabar daya siyo yasake maida kofar ya rufe ya kulle motar gabadaya da key din hannunshi sannan ya juya ya nufi cikin gida


Da sallama yashiga falon, babu kowa aciki Hakan yasashi nufar stairs kawai yanufi sama

Yana qarasa hawa saman itakuma ta fito daga dakin

Turus tayi ganinshi haka unexpected

Murmushi yayi mata, bata mayar mashi da martani ba Haka kuma batayi magana ba sai kauda kai datayi.

"hyy, slm alaiki" yafada cikin murmushi


Qara Dagowa tayi tadan kalleshi saikuma ta dauke kai

"wa'alaika sallam" ta amsa tana shirin wucewa

"here" yafada yana miqa mata ledar hannunshi

Kallon ledar tayi takuma kalleshi da alamun tambaya

Murmushi yasake yimata
"tsarabarku ce, ke da batool"

Kamar bazata amsa ba sai kuma ta miqa hannu ta amsa
"thanks"

"afwan, haza wajibi" yafada yana mata murmushi

Juyawa tayi batareda taqara cemashi komai ba takoma dakin

Murmushi yasake yi ya dan shafa lallausar sumarshi sannan shima ya wuce dakinshi.


A dinner ma yau haka yabi ya takura mata da kallo donma kallo bemata komai Tariga ta saba dashi shiyasa bata maida hankaliba kanshi.

Duk abinda yasan zai jawo suyi musayar magana shi yakeyi don ko yaya ne sai yayi yadda yayi ya sanyota cikin Maganarshi


Haka ya cigaba dayi acikin kwanakin dasuka biyo baya.


Sosai yake qoqarin janta ajiki by behaving freely around her amma kwata2 taqi bashi hadin kai, magana ce idan yayi mata ta amsa a taqaice daga haka kuma zataja bakinta tayi gumm

Saidai Hakan be sanyaya mashi gwiwa ba ko kadan kuma besa yafasa janta ajiki ba, everyday idan zai dawo saiya dawo masu da tsaraba, wani sa'in kuma ya kwashesu da ita da batool sufita outing ko shopping wanda acewar batool albarkacin zee take ci don da don ta itace Saidai ta ru6e bata fita shopping ba Indai shi zai kaita

Ahankali ahankali tadan fara sabawa dashi don Aymaan mutum ne matuqar iya zama da mutum komai baudadden halinshi, idan ya lura da yadda kake to baya damuwa da duk abinda zakayi zai bika ne a yadda kake har ku fahimci juna.

Ahankali zee tafara dan Sakin jiki dashi don wani sa'in suna dan fira sama sama.

Ga packs packs daya saba mata da zuwa duk lokacin da yake free

Sosai Aymaan yasan takan gari kuma yasan wuraren shaqatawa masu sanya nishadi wanda duk idan ya kaisu sai zee ta nemi damuwarta tarasa.

Hakan yasa har qagara take taji yayi masu magana akan su shirya suje yawo.


Kasancewar lokacin da zee tazo dubai duk higher institution sunyi nisa a semester dinsu don gab ake da zana exams Hakan yasa aka bari sai anyi hutu an koma sannan a sama mata replacement itama.


Cikin yan kwanakinnan zee ta dan warware, yanzu lafiya lau za'a zauna ayi fira da ita harda dariyarta, tasaba da wannan ahalin sosai musanmman batool data koma mata kamar wata bestie don bata jin komai wajen sharing damuwar ta da ita


Aymaan kuma haryanzu dai bata ida Sakin jiki dashi ba don basu yan tsokane tsokane yadda yakeyi da batool don koya tsokaneta Saidai tayi murmushi kawai ta kauda kai


Shikau Aymaan Hakan baya damunshi don ko gwasaleshi tayi baya nuna yaji haushi haka zai bita yadda takeso don a zauna lfy


Ahmed ma yasan da zaman zee a gidan don gidan Wurin zuwanshi ne sosai kamar yadda shima Aymaan ke zuwa gidansu Ahmad din sosai

Sau biyu suka ta6a ganin juna amma kusa kullum da kalar labarinta da Aymaan zai bashi

Shidai nashi saurare idan kuma yagama yaita yimashi Dariya yana tsokanarshi akan koya afka ne, duk lokacin dayace Hakan Saidai Aymaan yayi mashi kallon uku saura kwabo ya watsar batareda yace mashi uffan ba.





*1 MONTH LATER*





"nifa zan tafi Allah" inji zee dake bakin kofa tana kallon batool fuska a tsuke

"haba habibty, don Allah Kiyi hqr saura kadan fa, idan kika fita wlh tafiyarshi zaiyi bazai tsayani ba" tafada tana cigaba da kiciniyar daure igiyoyin takalminta


"kema mugun nawa gareki wlh, tun yaushe kike abu guda kin kasa gamawa anbar bawan allah yanata jira"

Tashi batool tayi bayan ta ida gyara takalmin tace
"kice dai kawai zumudi kike mutafi bawani an tsaida bawan allah mu mukace muna zuwa? Shi yace muje mu shirya mutafi"

Kwafa zee tayi ta juya ta bude kofar ta fita.


Saurin feffesama jikinta turaren hannunta batool tayi ta ajiye ta maramata baya da sauri



Qara duba agogon hannunshi Aymaan yayi a karo na ba adadi yana wondering wane irin shiri ne Hakan sukeyi haryanzu basu fitoba

Sanye yake cikin farin wando da sky blue din riga mai ratsin fari sai takalma farare, yar sumar kanshi tasha gyara sai salqi take


Jin taku a stairs yasashi Dagowa ya kalli wajen


Lumshe idanu yayi akanta yasake budewa cikin zuciyarshi yana fadin "masha allah"


Sanye take cikin dark blue arabian gown da duk jikinta stones ne sai gaban rigar da stones din yafi yin da6a da6a, rigar mai irin faffaden hannun nan ne mai jela sai gyalen rigar data yana akai irin na larabawa wanda sukeyi harda saman ha6a


Purse fara ce a hannunta sai takalmi suma farare wanda bakama hangensu sosai sai idan tana tafiya saboda tsawon rigar


Besan kallonta yakeyi ba har Saida yaji muryar batool na cewa
"Akhie!! Ko mun fasa fitar ne"

Da sauri ya dawo duniyar kallonta daya shiga ya juyo ya kalli batool dake tsaye riqeda qugu tana kallonshi

Harararta yayi sannan ya miqe tsaye yana cewa
"ni tsaranki ne? Kin gama tsaida mutane kuma shine yanzu zaki ishesu da ihu?"

Dan Wara idanu batool tayi
"na tsaida mutane ko ta tsaida mutane, Tundazu ita nake jira tagama Tambayarta kaji"

Juyowa zee tayi tana kallonta a mammakince jin yadda ta laftamata qarya qiri qiri

Ganin Hakan yasa Aymaan yayi kamar zai maketa yana cewa
"munafuka, sharri zakiyi mata ko? To wlh kibi ahankali kar nace banda ke a tafiyar nan"


Turo baki batool tayi
"nidai dama nasan ba'a sona"


"gwara da kika san Hakan, ukhtie mutafi kinji?" yafadawa zee

Saida zee ta danyi mata gwalo a fakaice sannan ta taho suka wuce da Aymaan

Binsu da kallo batool data cika famm tayi saikuma tayi Kwafa tabi bayansu, da tana iya zuciya da tayi tafasa binsu amma tasan ko tayi ita keda asara ba suba


Awaje ta taddasu zee harta shiga bangaren mai zaman banza Aymaan ya maida kofar ya rufe gently

Qara kumbura fuska tayi sannan tazo sumi sumi ta bude back seat ta shiga

Ta6e baki Aymaan yayi shima ya zagaya mazaunin driver ya shiga ya tada motar sannan suka fice daga gidan.



Tafiya suke babu mai cewa komai a motan daman batool itace aku mai bakin magana cikinsu to yau kuma fushi akeyi shiyasa Aymaan ya kunna wani disc na waqar maheer zain jin yadda motar ta dauki shiru.


Basu jima ba suka iso wani babban pack

Tun daga waje zaka gane pack din ya hadu kuma bana qanannun mutane bane.

Parking space Aymaan ya nufa ya nemar ma motarshi Wurin parking ya pakata sannan duk suka firfito


Sosai zee taji farinciki ya lullu6eta don ko ba'a fadaba tasan pack din ya hadu.


Wajen siyan tickets suka nufa ya siya masu sannan suka wuce ciki

Saida suka babbada tickets din sannan suka wuce ciki.


Sosai farinciki yasake lullu6e zee don suna shiga taji Wurin yayi bala'in yimata

Har mammaki take na yadda Aymaan yasan wuraren shaqatawa masu qayatarwa irin haka.

Batool dake fushi tuni itama ta warsaqe suka shiga yawonsu.


Sosai sukayi enjoying lokacinsu don sun yayyawata sosai don pack din babba ne yana Hade da zoo da restaurant ma, ga beach daga can qarshen Wurin.


Saida suka sha yawo suka gaji sannan suka samu wuri kusada beach din suka zauna shikuma Aymaan yawuce don samarmasu ice cream da sukace suna so.


Labari zee da batool suka cigaba dayi cikin nishadi suna kallon ruwan gabansu suna jiran dawowarshi

Dan shiru zee tayi kamar mai tunani

Ganin Hakan yasa batool cewa
"ya dai?"

"wlh dazu dazamu shigo daidai wajen wasan yarannan naga ana siyarda burger, ina son burger sosai wlh, kallo daya nayimata ta biya raina don rabona daita tun a Nigeria"


"shine kuma bakiyi magana ba muka tsaya muka siya?"

Dan yatsina fuska tayi
"banson tsaidamu ne amma bari kigani kafin yadawo zanje nasiyomana" tafada tana yunqurin tashi

"A'a kibari yadawo saiki fadamashi saiya siyamana" inji batool

Harararta zee tayi tace
"tunda gashi bawa ko? Nidai natafi I'll be back in a jiffy" tafada tana wucewa

"ok saikin dawo" batool ta amsa sannan ta maida hankalinta kan ruwan gabanta ta cigaba da kallo.




Dakyar zee ta iya gano inda taga burger dazu saboda girman wajen donma tana bin signboard suna nuna mata hanya


Burger manya biyar tasa akayi mata wrapping sannan taciro kudi tabiya aka bata



Chanjinta aka bata ta amsa tajuyo tana zura kudin a cikin purse dinta

Batayi auneba taji tayi qaro da abu wanda Hakan yasa ledar burger dinta faduwa

"ya sallam!" tafada ahankali tana kallon burger dasuka watse a qasa

Juyawa tayi ta kalli mutumin da sukayi karo dashi wanda yaqara gaba kamar ba mutum ya buge ba.

Ganin yayi nisa yasa ta buga Tsaki cikin jin haushi ta duqa tafara tattara burgern


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login