Showing 306001 words to 309000 words out of 322641 words

Chapter 103 - DEEN Complete Hausa Novels By Arewa Novels.txt

27 Nov 2025

6232

sosai sai kai komo suke

kaka sai bin mutane masu wucewa take da kallo kamar don ganin ko zataga mai fuskar Deen, duk tawani yi yaushi kamar ba itama

fitowa sukayi daga entrance din airport din inda adaidai lokacin idanun Lailah suka sauka akanshi


still tayi da numfashinta tana sake wara ido tana kallonshi sannan tasake kyafkyafta idanunta cikin son gasgata abinda tagani

hannun kaka dake gefenta ta damqe cikin sauri tana cewa
"gashi can kaka, ga yaya balaraben can kalla kigani!" tafada da qarfi tana nuna Deen din dake tsaye jikin budaddiyar kofar motarshi yana kallonsu tacikin baqin shade din idanunshi

bata tsaya bi takan kaka data sandare atsaye ba tayi wurinshi aguje tana kwala kiran sunanshi cikin kuka

tana zuwa batayi wata wata ba tafada jikinshi tana kuka sosai

qamewa yayi a tsayen dayake don ita kanta Lailah saida taji sanda ya dauke numfashi don be ta6a expecting hakan ba, hakan yasa itama saurin dawowa hayyacinta ta sakeshi tana dan ja baya

"y..yaya, am sorry amma nakasa yarda kaine" tafada muryarta nadan rawa saikuma tajuya ta kalli su Abba dake can tsaye basu qaraso ba sannan tajuyo ta kalli Deen dahar lokacin beyi motsi ba

"yaya kalli kaka.. ga kaka can, tareda ita mukazo.. kullum saitayi kuka saboda rashinka zoka gani" tafada tana jan hannunshi suka qarasa gabansu kaka Deen nabinta kamar sakarai

"kaka ga yaya! kingani ko dama nace yana lafiya" tafada cikin tsananin murna batama lura da tashin hankalin dake fuskokinsu Abba ba


"kaka..." taji anfada ahankali cikin raunin murya

juyawa Lailah tayi ta kalli Deen din kusada ita don tabbas muryarshi taji amma kamar ba daga kusada ita ba gashi Deen din akusada ita yake

kallon Deen din da Kamar bashi yayi maganar ba tayi kafin tace komai taji ansake cewa
"kakata"


still tayi jin muryar abayanta gakuma Deen agabanta da baiko motsa bakinshi ba

wara idanu tayi gabanta na faduwa hakan yasa mussadiq dake gabanta dan sakin murmushinnan nashi nagefen baki yana kallonta tacikin glass din idanunshi

saurin juyawa tayi daidai lokacin da Deen na ainahin ya rungume kaka dake tsaye kamar an dasata yana qara kiran sunanta yanajin wani irin kewarta na tasomashi daga qasan zuciya kamar sunyi shekaru basu hadu ba

sosai Lailah ta girgiza ganin Deen biyu agabanta, bama ita kadai ba kowama na wajen saida ya girgiza don ko Alhajin Deen be gayamashi batun twin dinshi ba


hakan yasa duk sukayi still kamar wanda aka dasa suna binsu da kallo inshock sunma kasa magana

Habeeb dake tareda su Deen murmushi Kawai yakeyi don yasan za'a rina, that's the same shock he recieve lokacin dayaga Deen da mussadiq at the same time

"kaka nayi kewarki.. nayi kewarki kakata" inji Deen yana cupping fuskar kaka data qurawa mussadiq din bayan Deen idanubabu kyaftawa

"ky..kyakyawana.. k..kalli bayanka, nashiga uku.. kalli bayanka" tafada cikin rawar murya tana riqe hannayen Deen dake fuskarta gamm idanunta har lokacin akan mussadiq

juyawa deen yayi yakalli mussadiq saikuma yajuyo ya kalli kaka yana murmushi

"eh nagani kaka"

"w...wani ne mai kama dakai" tafada har lokacin muryarta na rawa

"eh kaka dan uwana ne" yafada ahankali yana murmushi

"d..dan uwanka?"

"kaka muje gida muzauna saina fadamaku komai.. karki damu kinji?"

itadai batace komai ba sai riqe hannunshi datayi gamm tana kallon mussadiq kamar a tsorace, jikinta sai rawa rawa.yake

sai a lokacin yajuya kansu Abba da Habeeb ke gefensu yanata murmushi ya tsugunna yana gaidasu suka amsa suna kallonshi saikuma su kalli mussadiq wanda hakan yasa shima mussadiq qarasowa ya cire glass din idanunshi yana yimasu sallama

duk amsawa sukayi dakyar suna kallonshi don dukkansu arude suke they can't understand what's going on

ganin dai haryanzu kamar suna cikin shock yasa Deen yimasu iso zuwa mota wanda girmanta yasa zata iya kwashesu tsaf

duk wucewa sukayi wurin motar Habeeb na budemasu duk suka shiga

"Lailah come and get in" inji Deen ganin taqi motsawa a inda take

saida ta kalli Deen sannan ta kalli mussadiq daya daga gira daya yana mata wani kallon qasa qasa hakan yasata saurin kauda kai tawuce tanajin kamar zata harde kafaffu

duk shishiga sukayi cikin motar inda mussadiq yashiga mazaunin driver yatada suka fice daga wajen








------





A gidansu mussadiq suka taka sauka


tunda akafara tafiyar babu mai magana acikinsu kowa tunanin dake zuciyarshi ya isheshi


jin motar ta tsaya ankuma bubbude kofofi yasa suka fara yunkurawa suna saukowa


kowannensu sake wara idanu yayi yana kallon kantamemen gidan da aka kawosu

sai bin koina da kallo suke cikin mammaki kansu na dad'a kullewa

"Abba bismillah mushiga daga ciki" inji Deen da farinciki yakasa 6oyuwa a fuskarshi, he was just extra happy na ganin kaka ayau, jiyake kamar ya goyata don murna, he can't wait ya gwadama kaka umminshi datake yawan gayamashi tarasu


kasancewar daidai entrance motar takawosu yasa basusha wahalar fallo hanya don ba laifi ko daga parking space akwai tafiya kafin azo entrance


bisa jagorancin Deen da fuskarshi ke washe kamar gonar auduga suka shiga entrance din yabude masu kofar yashiga yana musu iso

sudai binshi Kawai suke babu mai iya magana saboda yadda kansu yayi mugun qullewa


wani katafaren qayattacen falo suka tsinci kansu aciki wanda tunda suke basu ta6a ganin mai irin haduwarshi ba

daga can cikin falon suka hango wata mata fara qall mai mugun kama dasu Deen tayi shigarta cikin shigar larabawa daya qara fiddo kwarjininta da haiba

"ummie! ummie! gasu Abba! ga kakata!" inji Deen cikin dan larabcin dayake ji yana jayeda hannun kaka da tunda taga ummie jikinta yadau rawa sosai

ummie datun shigowarsu tamiqe ta karaso gabansu cikin murna da fara'a tana masu lale marhabin cikin harshen larabci Aysha kuma na wucewa wurin kaka da Deen ke riqeda hannunta har lokacin tana kallonta fuskarta fall murmushi


iso ummie keta yimasutana cewa su zazzauna inda dakyar mutanen suka iya yin yadda tace don banda kallonta babu abinda sukeyi kamar sunsamu t.v


kan kace me? maids sunfara kai kawo inda cikin qanqanin lokaci aka cikamasu gaba da abubbuwa iri iri


babu wanda ya iya ta6a komai aciki dukkansu sai kallon ummie da Aysha daketa qara yimasu marhabin suke kansu na qara mugun kullewa

Gaisawa suka farayi inda duk cikinsu Abba ne mai dan tauri taurin dayake amsawa lafiya lau, hajiya kaka kau jikinta banda rawa babu abinda yakeyi

nan ummie take tambayarsu sunzo lafiya? duk suka amsa cikin qarfin halil banda kak da ha lokacin bata dawo nutsuwarta ba


Aysha ummie ta kalla tace taje ta gwadama su mamy da kaka masaukinsu su huta sai tawuce da Lailah dakinta shikuma Deen yakaisu Abba suma masauki

haka kau akayi, Deen yawuce dasu Abba Aysha tawuce dasu mamy da har lokacin zuciyarsu cinkushe take da tambayoyi kala kala


adakin da Deen yakai Abba Abba yahau fadan wai duk meke faruwa ne, yazai kawosu wuri without any explanation yasa sukoma kamar wasu sakarkaru


ganin kamar Abba yadan hau yasa Deen yashiga bashi haquri yana cewa ai zaiyi musu bayani

"waye wancan matar balarabe? kaga yadda.kuke kama kuwa?"

murmushi Deen yayi
"Abba ummie na ce"

"umminka? ba cewa kayi umminka da abbanka basa raye ba?"

"nima haka nayi tunani amma a wannan tafiyar allah ya bayyana minsu, allah ya hadani da ainahin family dina"

cikin mammaki sosai Abba yace
"yanzu dagaske wannan ce ta haifeka? but how come? ya akayi kaka tace bakada iyaye? wacece kaka?"

"wannan amsar kaka ce Kawai zata iya badata, itace Kawai zata warware mana komai"

"hasbunallahu wani'imal waqeel, allah mai iko, wannan fa me kama dakai din?"

murmushi Deen yayi
"he's my twin brother"

"you're a twin?" inji Abba cikin tsantsar mammaki

murmushi Deen yayi yana kadamashi kai


sosai Alhaji Shamsu yaita mammakin wannan al'amari inda abin yaqara kullemashi kai, miliyoyin tambayoyine ke kai kawo akanshi amma shima yasan babu mai bada amsarsu sai kaka


ahaka Deen yafita yakoma bangaren da aka sauke su kaka inda yaje ya tadda kaka nata kuka kamar ranta zai fita su mamy suna zagayeta suna rarrashi amma taqi shiru

cikin tashin hankali Deen ya qarasa wajensu yana tambayar kaka lafiya

ganin Deen yasa kaka tashi tafada jikin Deen da qarfi ta rungumeshi qaqam kamar za'a kwacemata shi tacigaba da kuka sosai

sosai Deen yarude jin irin kukan datakeyi hakan yasa yahau rarrashinta shima kamar zaiyi kukan

"ka gafarceni Kamal, ka gafarceni" tafada cikin kuka sosai


"kaka don allah kibar wannan kukan, don allah kibari"


"dole nayi kuka Deen dolene nayi, na rabaka da kowa naka na tsawon shekaru, naita guje guje duk don kar arabamu dakai ashe dai zamu rabu din, nayimaka qaryar komai ma, nasa kayi tunanin bakada kowa gashi duk dubarata da wayau na yau sirrina ya tonu, Ka gafarceni Deen don allah"

"kaka don allah kiyi shiru kibar fadin haka, ni haryanzu kece komai tawa kuma babu mai rabamu insha allah"

"wlh nasan rabamu zasuyi Kamal, shikenan baxan qara ganinka ba, shikenan narasa Ka dama kai kadai nake gani naji dadi, kai kadai nake iya kira nawa, shikenan banida kowa kuma"

haka kaka tadinga kuka tana surutai wanda dole tabaka tausayi gashi taqi sakin Deen don gani take rabasu za'ayi

kowa na dakin saida jikinshi yayi sanyi Aysha kau dabatasan me suke cewa ba saboda hausar dasuke sai kallonsu take tana hawaye don sosai tsohuwar tabata tausayi


dakyar Deen yasamu ya rarrashi kaka har tadan kwantar da hankalinta inda yasa Aysha ta hadamasu ruwan wanka sudanyi freshen up


dakyar kaka tabar Deen yafita daga dakin mamy na cigaba da kwantar ma kaka hankali





*RANAR WANKA....*




Zaune suke a babban falon kowa idanunshi akan kaka dake hawaye har lokacin


qarewa yan falon kallo nayi naga hardasu mummy da daddy da ummy da abbu agefe daya kuma babban Ahmad da ummanshi duk zazzaune akan kujerun falon


aqasa kan carpet kuma zee ce Zaune jikin qafaffun ummy sai batool akusada ita sai Aysha sai Lailah adayan bangaren kuma Deen ne kusada kafar kaka dake kan kujera itama sai mussadiq kusadashi sai Habeeb sai Ahmad daga qarshe kuma Aymaan


kowannensu kansu aqasa suna sauraron kaka da dakyar ta iya bude bakinta tafara magana....✍?




Ummin fasihu🧚🏻‍♀?
8/10/21, 8:09 AM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?*









*097*









*WAIWAYE*





"Asalin sunana Asma'u Mamman, ni marainiyace banida uwa banida uba don agidan marayu natashi na tsinci kaina a garin komasi dake qasar ghana.


Acikin gidan marayu natashi kamar sauran yan uwana marayu damuke rayuwa a cikin gidan

baza'a kira rayuwarmu da ingantacciyar rayuwa ba don gaskiya bama samun kulawa yadda ya kamata, abinci ma kanshi bama samun ingantacce saidai kame2


ga rashin ilimi daga na bokon har na arabi bama samu (gwara gwara na arabin tunda munsan wasu abubbuwan kamar yadda akeyin sallah da yan gajerun surori) ga rashin suturun kirki


gidan marayun kasancewar anyi yawa sosai aciki yasa babu kulawa sosai gashi da dan tallafin da gomnati ke badawa duk wata aka dogara saidai idan allah ya taimakemu yajefo mana taimako daga ire iren mutane masu sadaka dasuke tunawa da yara marayu irinmu


zama gidan marayunmu zama ne marar dadi don kowa burinshi allah ya rabashi da gidan ko ta hanyar adoption (daukar yara don rainonsu) kokuma aikatau

don har taya wadanda xasu bar gidan murna mukeyi munaji dama mu


Haka nataso nima kamar sauran yaran babu ilimin arabi ba na boko sai qwarewa a iya aikace aikace da rainon yara don yawanci marayun dasuka tasa suke komawa masu kula da qanannu qanannun cikinsu


haka muka tashi cikin wata irin rayuwa marar alqibla, kullum a aiki da raino muke qarewa bamu fita daga gidan ko nan da wajen gidan, duk wanda kaga ta fita to ko ansamu masu daukarta ne ko tasamu aikin aikatau kokuma tayi aure don babu laifi akwai masu zuwa neman aurenmu agidan wani lokacin kuma marayu yan uwanmu maza ke auranmu


haka natashi agidan kullum inama kaina fatan fita daga gidan watarana nima nasamu ingantacciyar rayuwa koyaya ne

rayuwa awajen gidan na matuqar bani sha'awa musanmman idan ina ganin mutanen dakan shigo gidan marayun namu don daukarmu sai inji sunbani sha'awa ina kuma qara jin kwadayin son fita daga gidan inason jin yadda wajen yake


saboda kwadayin son fita daga gidan yasa duk lokacin da akazo dauka har addu'a nake aza6eni nima, bandamu ba ko aikatau xanje inyi burina Kawai nafita daga gidan

duk lokacin da akazo akayi dauka ba'a daukeni ba kwana nakeyi kuka bama ni kadai ba harda wasu acikinmu saboda yadda zaman gidan ya ishemu, burinmu Kawai mufita aganinmu rayuwarmu awaje saitafi tacikin gidan inganci



ahaka harna girma naxama budurwa, ina shekara 20 wani mutum yazo neman aure na agidan


da gudun tsiya na amince dashi batareda duba yanayin shekarunshi ba don babbane sosai don a haife ya haifeni gashi yanada mata biyu da 'ya'ya kusan goma sha

ban damu da duk wannan ba alokacin na amince nan da nan aka daura aurenmu bayan anyi dan bincike dasukeyi na sanin mazaunin mutum da sana'arshi inda aka gano sana'arshi qera tukane na qasa da tulu dadai sauran kayan qerawa na qasa


bayan daurin aurenmu aka damqani ahannun mijina daga ni sai yan kayana sai dan ihsani da manyan gidan suka hadamin wanda betaka kara ya karya ba nabi mijina bakina har kunne don tsabar murna muka bar gidan da tun haihuwata banta6a fitowa ba


abin hawa muka hau dani da mijina har gidanshi wanda yakasance na qasa ne duk ya tsufa ya zaizaye

gidan zagaye yake da yar gajeriyar katanga ta qasa inda idan kashiga ciki saika fara cinkaro da wani washeshen fili mai girma sosai inda daga nesa xaga hangi yan qanannu qanannun dakunnan dake gidan


dakuna hudu ne gidan masu yan qanannun taga (window) daga can sama

daki nafarko na maigidan ne sai biyu na kowanne matarshi daya kuma na yara inda na qarshen wanda da alamu saida akayimashi kwaskwarima saboda qamshin sabon shafen qasan dayakeyi nawane ni amarya

babu kitchen gidan don a tsakar filin gidan suke girki sai makewayi dake daga can qarshen gidan.


ahaka nashiga gidan ina kalle kalle inda yarane sosai tsakar gidan duk yan kuya kuya kusan duk kai daya kowa na,binmu da na mujiya, daga tagar dakunnan matan gidan kuma ina iya hango kawunnan mutane ana leqomu

ahaka muka shiga dakina wanda yasha gyara ga tabarmi anbaza takoina sai dan tulu dake daga can kusurwar dakin

ataqaice nan yazama dakina kuma ranar nazama cikkakiyar mace ta hanyar raya sunnar aure da mukayi da mijina


da farko farkon zamana gidan komai na tafiya min lafiya lau don sosai.mijina kesona don yamafi fifitani akan kingin matan

baya yarda inyi wahala don ko girkin gidan da sai andora qatuwar tukunya baya bari nayi kullum abinci na shi ke kawomin wanda duk yawanci kayan dadi ne

hakan yaqara sani jindadin auren don ina samun kulawa sosai fiyeda wanda nake samu agidan marayunmu hakan yasa kan kace me nayi 6ul 6ul naqara kyau


haka naita rayuwa mai dadi agidan mijina inda nalura kamar mijina bayason kingin matanshi saboda yadda baya shiga harkansu don becika shiga dakunnansu ba kuma maganar arziqi bata hadasu kullum sai fada ga yaranshi suma banga yana wani kula dasuba don suma rayuwarsu suke kara zube


ina mammakin abubbuwan dake faruwa agidan dakuma yadda yake watsar da sauran iyalenshi saidai ganin ni bayamin haka yasa Kawai nashare na cigaba da more rayuwata


acikin wata na hudu dayin aurenmu nasamu ciki

inda sai anan nagane waye ainahin mijina

tun lokacin dayaji batun cikina ya chanzamin kwata2 inda yafara tsiromin da wulaqanci iri iri inda tun bangane dalilin hakan ba harna gane ashe haihuwace bayaso

lokacin nasha wahala sosai saboda cikin yazomin irin mai shegen laulayinnan ne gashi mijina yajuyamin baya abinci kanshi yabar bani sai alokacin nagane ashe matan gidan suke ciyar da kansu ma

gashi matan gidan dama duk haushina sukeji saboda yadda mijinmu ke nuna kulawa agareni abaya hakan yasa alokacin babu mai tausayamin saima allah qara dasuke yimin da qannanun habaice habaice



ahaka naita kashe yan kudadden hannuna a lokacin inasamu inci abinci don ko shekara zanyi banci abinci ba babu wanda zai damu da hakan agidan

haka naita wahala ga laulayi ga rashin kula har na qulla wata biyu sai alokacin na yanke shawarar fara sana'a ganin idan nazauna hakanan yunwa zata kasheni ne abanza gashi duk na cinye yan kudaddena

ahaka nafara aikin wankau dukda yadda banida lafiya haka nake daurewa nayi wanki don samun abinda zansaka aciki

ahaka har cikina yayi wata biyar inda lokacin muka wayi gari mukaga ana tada daki daya a gidan

cikin qanqanin lokaci aka gama ginin yaji shafen qasa kamar nawa inda sai anan nakejin labarin ashe aure zaiyi


naji baqinciki sosai a lokacin don sai a lokacin nakejin ashe mutum ne shi daya saba da aure2

cikin sati biyu aka daura aurenshi dawata ta tare inda itama yakoma yimata duk abubbuwa na kyautata dayake yimin abaya

ahaka naita rainon cikina nikadai yau fari gobe baqi inda har lokacin babu wani jituwa atsakaninmu da matan gidan don kowaharkar gabanta takeyi, kowa kanshi yasani da 'yayanshi

ahaka naita rainon cikina da tun kafin na haifeshi allah ya dasamin qaunarshi sosai a zuciyata don koyaya nake cikin baqinciki na dan cikina ya motsa sainaji sauqi sauqi, kullum burina na haifeshi lafiya nima inga wanda zan kira nawa

cikina na shiga wata takwas mijinmu ya6ata da amaryarshi kasancewar itama ta dauki ciki

wulaqanci yafara mata itama kala kala hardamu ma yana cewa bamu iya komai ba sai haihuwa

ahaka ya watsar daita itama tafara dandana abinda muke dandanawa

ana hakan watarana yashigo dakina daya rabu dazuwa don har saida nayi mammakin ganinshi don rabonda yashigo dakina tun ina amarya

ashe shigowar ma bata alhairi bace don yana shigowa babu cass bare ass ya sakeni saki irinna jahilci wato uku gabadaya yakuma ce na tattara nafitarmashi agida aure zai qara


sosai naji ciwon abin sosai don abin nashi babu ko tausayawa, ga tsohon ciki ga saki sakin ma na wulaqanci

ahaka nabaro gidan bayan kwana biyu saboda budemin wutar dayayi na nabarmashi gidanshi

sanin babu inda zani don babu wanda nasani yasa ban zarce koina ba sai gidan marayunmu

koda naje nafadama manyan wajen yadda komai yafaru sai Kawai suka bani hqr don dama sunsaba irin wannan case din don yawanci ana sako wadanda sukai aure sukuma dawo gidan marayun su cigaba da rayuwa

haka nakoma cikin gidan da rayuwa har lokacin da allah ya saukeni na haihu lafiya inda na haifi d'a namiji saidai ko kwana beyiba yakoma


sosai naji rashin d'ana don na kwallafa rai akanshi sosai kuma inasonshi sosai tunma kafin na haifeshi

hakan yasa har ciwo saida na kwanta kafin daga baya na hqr na cigaba da rayuwata dukda har lokacin d'ana na maqale a zuciyata


haka na cigaba da rayuwa a gidan har tsawon shekaru takwas inda ana tara nasamu wata tazo daukar yan aikatau aka hada dani

matar munsanta sosai don tana yawan zuwa dibar yara agidan inda take rarrabawa aikatau kamar dai wata dillaliyace ta masu kudi mai kaimasu yan aiki

kasancewar angaji dani a gidan yasa aka hada dani dukda na girma don lokacin shekaruna talatin aka samu akatafi dani don dama yawanci abinda


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login