Showing 87001 words to 90000 words out of 322641 words
Chapter 30 - DEEN Complete Hausa Novels By Arewa Novels.txt
lumshe idanu
_ya sallam! Meke damuna ne? Meyasa zuciyata ke bugawa da sauri_
Tambayar da tayiwa kanta kenan
Anya zuwan nan nata bazai jamata raini ba? Ta bashi waya da number ta aciki da tsanmmanin jin kira daga gareshi amma beyiba gashi kuma ta biyoshi har gida?
Wannan ba zubda class bane?
_ai ba zuwanshi kikayi ba, mummy ce ta aiko ki wajen kaka_
Wata zuciyar ta gayamata Hakan
Kada kai tayi, yes mummy ce ta aikota kuma ba wajenshi tazo ba sai kuma ta furzar da iska takoma ta lafe a kujerar
Bude kofar mazaunin drivern akayi Hakan yasa tadan dago idanu ta kalli bala dake qoqarin Shigowa
"madam na gano, ashe ma mun dan wuto layin amma yanzu zamu koma"
Bata ce komai ba sai maida idanunta datayi ta rufe tana jin yana sake tada motar
Basuyi wata tafiya mai nisa ba taji motar ta tsaya Hakan yasa taji zuciyarta ta tsinke ta fadi
Fita bala yayi daga motar ya zagaya ya bude mata kofar
Saida ta hadiye wasu yawu dasuka taru a maqoshinta sannan ta zuro kafarta tafara fitowa
Wani sanyayar iska ce ta bigi fuskarta Hakan yasa ta lumshe idanu ta sake budesu
Kallon kofar gidan take, tabbass gidan ne don bazai iya 6acemata ba dukda Zuwansu daya
"ina jin nan ne gidan, amma bari mu tambaya" inji bala
Dakatar dashi tayi da
"eh nan ne basai ka tambaya ba"
Dan kallon wasu samari biyu masu wucewa sun wani sakarmata na mujiya tayi sannan ta dauke kai ta nufi kofar gidan bala na binta a baya da ledar kayan da suka siyo
Da sallama suka shiga gidan amma shiru Hakan yasa suka qarasa ciki zee na qara sallama
Jitayi ana amsawa daga cikin daki kuma ta shaida muryar kaka ce
Shiru tayi zuciyarta na cigaba da gudu tana jiran taga ta inda za'a bullo
"maraba!!" suka sake jin muryar kaka tana daga labule ta fito
Jan burki kaka tayi tana qwalalo idanu ganin Hakan yasa zee maida nata qasa tana dan murmushi
"wa zan gani kamar Zainabu?" tafada mammaki a fuskarta
Murmushi zee tasakeyi tace
"mune kaka"
"lale lale da baqin ogas, yaushe rabo? Gaskiya yau muna da manyan baqi" tafada tana shigewa daki can kuma ta fito hannunta riqe da tabarma ta baza masu tana cewa
"daki zafi nima sallah takaini ciki kunsan yanzu sirkawa akeyi ga zafi ga ruwa"
Zama zee data cire takalminta tayi tana murmushi tace
"ai ana zafi sosai... Ina wuni kaka"
"lfy qalau lumi aminiya, kwana dayawa"
Murmushi kawai tayi bata ce komai ba
Shima bala gaidata yayi sannan ya ajiye ledar hannunshi kusada zee yace bari yaje ya jirata waje, Kada mashi kai kawai tayi ya juya ya fice
Tashi kaka tayi tana cigaba dayi mata maraba tashiga kitchen can tafito da kofin silba mai murfi ta ajiye mata agaba tace
"ga ruwa Zainabu abu mai tagwayen suna, kun shawo hanya dole maqoshi ya bushe"
Murmushi tayi tadan ja kofin gabanta Saidai bata bude ba tace
"Kaka mun sameku lfy? Ya mai jiki?"
"wlh duk lfy qalau yar nan. Ya bayan rabuwa kuma? Mu bamu san inda kuke ba gashi baku sake zuwaba, munga kaya rannan amma ba hanyar Godiya tunda cikinmu babu wanda yasan ta inda zamu sameku"
_shi jikan naki ya sani ai_ tafada a zuciyarta amma a zahiri murmushi kawai tayi
"yasu mamar taki?"
"wlh lafiya lau kaka, tana gaida ki tama so zuwa amma allah beyi ba"
"ai ba komai wlh, kunga Deen kwarai mace mai kirki, kai allah dai yasaka da alhairi, bari na zubomiki abinci" tafada tana niyyar tashi
Saurin Dakatar da ita zee tayi da
"A'a kaka, alhamdullilah azumi ma nake"
Dan waro idanu kaka tayi tana komawa ta zauna tace
"azumi? Ca6 shiyasa baki sha ruwan ba ashe, amma duk mai azumi yau sai yaji a jikinshi wannan kwala rana haka masha allahu"
Murmushi tasakeyi
Firarsu suka cigaba dayi wanda kaka ce keyin kusan rabi da kwata zee sai murmushi take don sosai takejin dadin firar tata
Suna ahaka sukaji sallamarshi wanda ke daidai da bugawar zuciyar zee
Saurin kauda kai tayi daga kofar Shigowa ta maida kan jakkarta dake gabanta ajiye tana jin kaka na amsa mashi
Jimm aka dan yi sai kuma taji kaka na cewa
"qaraso mana, ita ce din dai"
Sai a lokacin ta dago bata sauke idanun a koina ba sai cikin nashi
Saurin Janye nata tayi tana runtse su gam
_ya sallam!_ ta fada a zuciya
Bata ta6a sanin tayi missing dinshi har haka ba sai yanzu, jitake zuciyarta na kumbura tana sacewa don shauqi
Qarasowa Deen daya kafeta da idanu yayi kamar meson gasgata abinda idanunshi ke gani
"wlh itace, ina sallame sallah naji sallamarsu bama su dade da zuwa ba" inji kaka
Ida Qarasowa yayi ya cire takalminshi ya zauna kan tabarmar still idanunshi kanta
Be ta6a jin ya ta6a missing wata hallita ba kamar ita, ganinta kuma yau ba qaramin tado mashi tsumin kewar yayi ba
Dukda bashi take kallo ba tasan ita yake kallo don tana jin idanuwanshi akanta Hakan yasa taqi dagowa ta cigaba da kallon qasa tana wasa da zoben yatsarta
Cool voice dinshi taji yana cewa
"Kaka yaushe tazo?"
Lumshe idanu tayi ta bude, ya Allah! Tayi missing komai gameda gayen nan, har muryar
"basu jimaba wlh, nima abin yazo mun a bazata wlh kuma naji dadi sosai"
Maida kallonshi yayi akan zee din dataqi sake kallonshi can kuma yace
"yasu mummy?"
Dan dagowa tayi ta kalleshi saikuma ta kauda kai tana dan murmushi
"tana lfy, ya qarfin jiki?" tafada trying so hard wajen controlling muryarta
"Alhamdullilah, longest time"
Dan kallonshi kawai tayi sai kuma ta kauda kai tana jin takaicin maganar shi
Wai longest time, da yaso da ya kirata ko gaisawa sunayi amma ya share amma har yanada bakin cewa longest time
Haka kawai taji rashin kiran nashi na cimata rai, batama san tun ranar daya ajiye wayar be qara waiwayarta ba
"to kaka bari mutafi" inji zee din tana kallon kaka avoiding Deen's gaze
"haba badai tun yanzu ba Zainabu"
Qoqarin miqewa tsaye zee keyi tana cewa
"wlh kaka, mummy tace karmu dade ne"
Tashi itama kakan tayi da zee da Tundazu yakasa janye idanunta akanshi
"to ai mungode qwarai ma wlh, gashi dama azumi kike, to allah yasa asha ruwa lfy, kice ina gaida mamar taku sosai da sosai, ya kamata kyakyawana ka amshi lambar su yadda zamu dinga gaisawa" inji kaka
Kada kai Deen yayi alamun to saikuma yajuya yashige dakin kaka
Da kallon qasan ido ta rakashi sannan ta dauke kai ta duqa ta dauko ledar dasuka shigo daita ta ajiye gaban kaka tace
"gashinan kaka ba yawa"
"meye din? A'a wlh abin ai saiyayi yawa ga wancan ga wannan?"
"Kaka dan allah ki amsa ba yawa kawai kayan marmari ne"
Da farko qiyawa tayi amma daga baya saboda nacin zee ta amsa tana Godiya
"dan allah ki miqamin godiyata gareta idan kin koma, insha allah zan kira ma da kaina mu gaisa kibashi lambar ki"
Da to ta amsa kawai tana murmushi sannan tayi mata sallama ta nufi hanyar fita
Daidai nan Deen yafito daga dakin kaka yaga ta danyi nisa ma
"Kaka ina zuwa"
Da to kaka tabishi tana kallonshi ganin ya nufeta
Dukda tanajin alamun binta dayake Hakan besa ta nuna tasani ba bare ta tsaya
Daidai tashiga zaurensu taji muryar shi na cewa
"Zainab!.."
Cak ta tsaya ba don ta shirya ba sai don tasirin da kiran yayi agareta sosai
Qarasowa yayi ya tsaya bayanta yana dan basu tazara
"Tafiya zakuyi?" yafada yana kallon bayanta don bata juyoba
Ahankali ta juyo ta kalleshi suka kafe junansu da idanu without saying anything
Ahankali zee ta motsa baki tace
"eh, ko kanada matsala da Hakan ne?"
Murmushi ya dan saki yace
"A'a... Ga wannan" yafada yana miqamata wata baqar leda
Kallon ledar tayi saikuma ta kalleshi da ayar tambaya
Qara miqo mata yayi murmushi a fuskarshi Hakan yasa ta amsa ta bude tana leqawa
Kanta ne ya sara ganin kwalin wayar data siyomashi ce
Dagowa tayi ahankali tana kallonshi still da ayar tambaya
"ki maidama mummy kice mun gode qwarai amma bazan iya amsa ba, dawainiyar da kukayi akanmu ta isa, muna Godiya. Dama tun ranar dana ganta na maidata na adana akan idan kuka zo kamar yadda mummy tace ko muka hade a school inbaki, mun gode qwarai amma bazan iya amfani da wannan ba, yanzu haka ma nayi wata so no need na damuwa, kinga saiki samin number mummyn don su dinga gaisawa kamar yadda tace and also na warware please ku daina mana dawainiya haka nan, the one you did is appreciated and we'll continue to appreciate it..."
Saka hannu yayi a aljihu don lalubo wayarshi batareda ya lura da irin kallon da zee ta kafeshi dashi ba
Zaro yar qaramar wayarshi keypad qirar itel yayi ya miqamata yana cewa
"here, samun number"
Kallon nata ne ta janye daga kanshi ta maida akan yar ficikar wayar hannunshi tana feelings din da bata ta6a jin irin shi ba kuma ta rasa taqamaimai me takeji
Haushi? Takaici? Dana sani ko embarassment?
Ashe duk haukan ma datakeyi na jiran kiran shi ita kadai keyi?
Ko ta6a budewa beyi ba, wai ya adana ta don ya maida mata? And qarin gishiri a ciwo wai tabashi number mummy don su dinga gaisawa da kaka bama tabashi tata ba A'a ta mummy wato ita kadai ke haukanta he Don't care a bit about her
Wani abu mai daci2 taji ya ziyarci maqoshinta tana jin kamar ta dora hannu aka taita ihu
Ganin tayi tsaye tana kallonshi dakuma irin kallon datake mashi yasashi dan wara mata oily eyes dinshi yana cewa
"are you ok?".... âœï¸
Ummin fasihu 🧚ðŸ»â€â™€ï¸?
8/2/21, 9:35 PM - BuhainatðŸ˜: *ðŸ™ðŸ»â€â™‚ï¸DEEN ðŸ™ðŸ»â€â™‚ï¸?*
*032*
*BAYAN KWANA BIYU*
Shiru zee tayi takasa cewa komai sai ma wasa datake da zoben hannunta
"am talking to you Zainab"
"mummy babu komai fa"
"babu komai kika koma haka? Just look at yourself amma kice babu komai? Ke kanki kinsan you're lying"
Sauke idanunta tayi tana kallon yatsun hannunta cikin rashin ta cewa
Dawowa mummy tayi ta zauna kusada ita tana kallonta
"Zainab..."
Dagowa zee tayi ta kalleta da idanunta dasuka fara salqin hawaye
"meke damunki? Are you sick?"
Girgiza kai tayi ahankali tana maida kanta kasa, ita kanta da tasan abinda ke damunta datafi kowa murna
"Zainab am your mother kuma bakida kamar ni.. Bakida wanda zaki fadawa matsalar ki kamar ni don haka karki 6oyemin komai, ki gayamin komai I can understand"
Yadda mummyn tayi magana tenderly yasa zuciyarta qara tsuma kan kace me sai hawaye
Kamo hannunta guda mummy tayi tana murzawa ahankali cikin sigar rarrashi wanda ta rabu dayi mata Hakan yasa zee kwantowa a kafadarta tana cigaba da hawayen
Hannu mummy tasa around her tayi mata side hug wanda Hakan yasa taqara narke mata
"tell me" inji mummy
Sniffing tayi sannan tace
"mummy am bored, am lonely. Banajin dadin komai, ina kadaici sosai"
Shiru mummy tayi can kuma tace
"shiyasa kika takurawa kanki har haka? Duka yanzu kwana nawa ya rage kuyi resuming school?"
"dukda haka mummy, am very lonely banida wanda zamu dinga hira, am always bored"
Ajiyar zuciya mummy tayi sai kuma tace
"ok, yanzu ya za'ayi? Kina son insamo miki training class, kona girki ko kwalliya or something like that?"
_no i want to see Deen_
Abinda tafada a zuciyarta kenan amma azahiri tace
"no mummy, I want to travel"
"travel? Ina?"
Dagowa zee tayi daga jikin mummyn sannan ta marairaice fuska
"Ruma, don Allah mummy kibari intafi"
Sakin baki mummy tayi tana kallonta
"ke kecewa zaki Ruma da kanki yau? Wonder shall never end"
Dan tura baki zee tayi tace
"mummy nafa rabu da zuwa"
"kin rabu da zuwa amma wancan zuwan qarshen ya kikace? Cewa fa kika yi baki qara zuwa kuma ma bazan bari kije ki takurawa mutane da daukar maganarki ba, never"
Sake marairaicewa tayi don sosai takeson tafiyar ko zata manta da wannan annoying fring din
"mummy please, nafa shiryu baki gani ba"
Sosai maganar zee taba mummy Dariya amma sai tayi dan murmushi tace
"kin dai shiryu and also duka yanzu saura kwana nawa kuyi resuming? Da zuwan ne ai da tun farkon hutun ya kamata kije amma yanzu kije hutu be kai sati biyu zai qare ba wannan zuwa hutu ne?"
"mummy ko sati daya ba sai nayi ba na dawo? I promised mum baxanyi komai ba nafa shiryu mummy na daina abubbuwa marar kyau"
Harararta mummy tayi ta tashi ta nufi closet dinta
"kinji mummy? Please.."
Batareda mummy ta juyo ba tace
"kije zan gayawa daddy duk yadda yace shikenan"
Dadi ne ya ziyarci zuciyarta taji kamar tayi ihun murna don tasan idan daddy ne batada case dashi amma sanin halin mummy abu kadan zaisa ta chanza ra'ayi yasa ta danne tace
"to mummy, allah yasa ya yarda"
Juyowa mummy tayi ta gallamata harara
"kamar duka kenan, salan kije ki kallalameshi kafin na gayamashi kiga idan ban soke tafiyar ba"
Daga hannu zee tayi tace
"A'a ni bazan kirashi ba, how dare me"
Ta6e baki mummy tayi ta cigaba da abinda take
Tashi zee tayi taimata sallama ta fita cikin zumidin tafiyar tanajin atlast zata rabu da kadaici bare har tunanin Deen ya samu gurbi a zuciyarta don ita duk tunaninta kadaici ke jawo tunanin nashi
Tana shiga daki ta murza key ta nufi bedside locker dinta ta dauki phone dinta ta zauna can qarshen gado ta lalubo number daddy ta dannamashi kira
Ba'a daga ba har Saida ta yanke tana qoqarin sake kira kiranshi yashigo
Cikin zumudi ta dauka ta kara akunne
"daddy na!"tafada cikin tsananin murna
Dariya daddy yayi daga can 6angaren yace
"na'am daughter din daddynta"
Murmushi tayi tace
"daddy I missed you!"
"missed you more and more jewel, amma alhamdullilah am coming back soon, me zan miki tsaraba?"
"komai ma daddy don kafini sanin abinda zai sani farinciki"
"really? To angama I'll make you happy insha allah"
"Allah ya yarda daddy"
Sai kuma tadanyi Jimm sannan cikin shagwa6e murya tace
"daddy?"
"yes? Daddy's pet"
"daddy am lonely, banajin dadin komai kullum kasa barci nake har kuka nake yi ma" tafada cikin narke fuska
"subhanallilah, but why?"
"am lonely, every thing seems boring gashi babu school kullum zaman gida na gaji" tafada kamar zatayi kuka
"oh please kar Kiyi kuka kinji? Ba gashi na kusan dawowa ba? Idan nadawo kullum saimun fita shaqatawa, idan bazaki iya jira bama gobe balarabe ya fita dake duk inda kikeso Kiyi shopping and every other thing that will make you happy uhm? Nakusan dawowa everything will be ok"
6ata fuska tayi don ba abinda takeso ba kenan
"Nidai daddy duk wadannan baxasuyi ba, na gaji ne da komai da garin, I want to go to Ruma, please"
"Ruma kuma daughter?"
"yes dad, please! Kaga na rabu dazuwa"
"to yaushe zaki dawo idan kika tafi yanzu, and kun kusa resuming ai"
"daddy yanzu saura kwana 12 muyi resuming, Kaga sai inyi 1 week acan kuma dama naji ance aunty Feenah tadawo kaga zamu ga juna dama rabona da ita tun kafin ta tafi a waya ma bamu cika magana ba, please kabarni naje daddy just 1 week zanyi nadawo, zanji dadi sosai zanyi farinciki" inji zee don tasan idan akwai abinda yakeso to farincikin ta ne
Ajiyar zuciya taji ya sauke daga can 6angaren yace
"Alright then, kin gayawa mummyn ki?"
Cikin zumudi tace
"eh daddy, tace ma zata kira ka ta gayamaka"
"ok idan takira zance mata tabarki kawai, yaushe kikeson zuwa?"
Ihun murnar da batayi ba dazu tayi tana cewa
"yes! Thank you my sweet daddy"
Murmushi mai sauti daddy yayi yace
"you're welcome, nace yaushe kikeson zuwa?"
"dad ko zuwa gobe haka, please kace tabarni natafi gobe"
"to shikenan an gama princess"
"yauwa daddy kuma fa karka cemata munyi maganar dakai don Saida tayimin warning akan Hakan, kawai kayi pretending bakasan da maganar ba if not she'll slaughter me"
Dariya daddy yayi sosai a dayan 6angaren sannan yace
"to angama dear, sai kuma me?"
"shikenan sweet daddy"
"to shikenan, I'll pretend bansan da maganar ba and also zanmiki transferring din sum amount sai ayiwa mutanen Ruma tsaraba"
Cikin jindadi sosai tace
"thank you so much daddy, muah! I love you"
Cikin Dariya yace
"love you more sweetie"
Da haka sukayi sallama ta koma ta jingina da gado beaming with smiles tanajin atlast zata rabu da qaya
Duk a tunaninta zama lonely ke kawo tunaninshi shiyasa ta yanke wannan shawarar na tafiya Ruma tasan ko yaya ne she'll feel better from what she's feeling now
Da wannan tunanin ta kwana ta tashi, haka taita baza kunnuwa taji me mummy zatace gameda tafiyar amma shiru
Tun tana jira harta sire don har magrib shiru batace mata komai ba
Sai bayan isha'i suna tsaka da dinner mummy tace mata ta shirya gobe zasu wuce Ruman
Dukda da farko fushin sharetan da mummy tayi take Hakan be hanata yin murna ba
A cikin daren ta harhada kayanta wadanda zasu isheta na zaman sati da tarkacen kayan amfani na yau da kullum
Medium trolley guda tacika ta ajiye gefe sannan ta kwanta tana Allah Allah gobe tayi ta shilla
*WASHEGARI*
Sai wajajen 12 rana suka bar gidan a motar da bala ke ja suka nufi garin Ruma dake qaramar hukumar batsari bayan mummy ta gama cikasu da tsarabobi da zata kaiwa yan uwanta mutanen Ruma
Tunda suka kamo hanya zee keta sauke Ajiyar zuciya tana fatan Hakan zai ragemata abinda takeji acan din
Bluetooth ta maqalawa kunnenta wanda cool music ke tashi a cikinshi ta dawo kusada window ta jingina tana kallon yadda suke wuce dajika da gudu, sosai abin ya nishadantar da ita don koina luff yake da ciyawu sunyi green abin sha'awa abunka da damuna wannan scene din ya mantar da ita abubbuwan dake damunta a zuciya ta kama jinta wasai
Anata sallar azahar suka isa cikin garin.
Direct gidansu mummy suka wuce wanda keda girma ba laifi kallo daya zakayi mashi kasan na masu rufin asirine sosai
Saida yayi horn sau uku sannan aka bude qaramar kofar gate din aka leqo sai kuma aka koma can aka shiga bude dan madaidaicin gate din
Shigar da motar bala yayi, yayi parking a parking space din wajen da beda girma sosai sannan ya fito ya zagayo ya budemata
Saka bluetooth din data ciro daga kunnenta tayi cikin jakka sannan ta zuro kafarta tafito daga cikin motar
Shaqar iskar garin tayi sannan ta fesar tana jin wani dadi har cikin zuciyarta
Rataya jakkarta tayi a kafada ta saka siririn spec dinta sannan