Showing 81001 words to 84000 words out of 322641 words
Chapter 28 - DEEN Complete Hausa Novels By Arewa Novels.txt
dinshi kikayi?" inji Deen yana kallon zee
Kada mashi kai kawai tayi alamun eh
"mugani kaka" yafada yana miqa hannunshi
Janyewa tayi tana cewa
"tsaya mugani, meye wannan abin shikuma?"
"ko an fadamaki ba ganewa ba zakiyi kaka, kidai bani ingani"
Harararshi tayi tasake gwadawa zee Saida tagayamata ko menene sannan ta bashi tana jinjina kai alamun ta fahimta amma a zahiri babu abinda ta fahimta
Amsa Deen yayi cikin zumudi yana dubawa
Wani kyakyawan murmushi yayi yana maida pink lip dinshi na qasa ciki yana taunawa
Batasan itama shi take kalloba tana murmushin da Batasan tanayi ba Saida ya dago suka hada ido
Saurin janye idanun ta tayi cikin basarwa still murmushin a fuskarta
"mugani son" inji mummy
Miqamata yayi ta amsa itama tana dubawa
"kai masha allah! Gaskiya result yayi kyau sosai"
Cikin jindadin abinda tace kaka tace
"kede bari, ai dan naki badai qwanya ba. Yo to Allah na tuba yadda yake raba dare yana karatunnan ai dole ma yaci, ko lokacin dayake firamari shi ke dauko na daya, duk lokacin hutu saiya dawo da kyauta, abashi a makaranta abashi a hanyar dawowa gida, duk wanda ya gamu dashi a hanya ya amshi takardar ya duba saiya bashi wani abu, tun sannan nasan yaron naki dan baiwa ne ba irin wasu ba masu kwalwar dusa, kullum Saidai a matse jakka a hammata azo amsar kudin tara, ja'irai dama kudin ke kaisu sudai abasu sutafi sukul din sukasosu sudawo suna zare idanu, ranar hutu kuma sunfi uban kowa kukan an kaddasu a jarabawa
Haka kyakyawana yaita fama dasu, duk lokacin da aka bashi takardarshi sukaji yayo na daya sai suyita jin haushinshi wani sa'in ma su tareshi a hanya suyimashi duka su yaga takardar, dayake raggo ne babu abinda ya iya shiyasa suka bi suka rainashi
Haka zai dawomin hurtutu idanu jajjaye ga yagaggiyar takarda, Saida na tashi tsaye sosai suka shafamashi lfy don bana jin kunyar kowa idan danki ya daki jikana har gida zan biyoshi na rama mashi, babu ruwana
Sunyi surutun sunyi surutun amma ban fasaba don ko qarqashin gado yashuge saina zaquloshi na rama mashi saigashi sun daina ko kallon Banza ma basa mashi
Ato idan kace ka nuna sanya sai a raina maka hankali..."
Haka kaka taita zuba Sukau sai sauraronta suke suna murmushi, wani wurin kuma mummy tasa baki
Suna haka akafara kiraye kirayen sallar azahar
Duk tashi sukayi suka gabatar daita
Basu dade da gamawa ba Dr yashigo
Saida yaqara duba shi yaga komai normal sannan ya rubuta masu sallama bayan ya basu maggungunan Deen dazai cigaba dasha yakuma gargadesu su dinga kulawa abar barin sanyi na bugunshi
Babu 6ata lokaci suka gama kimtse kimtsensu suka fito
Motarsu mummy suka shiga mummy ce ke tuqi sai zee gefenta, abaya kuma Deen ne da kaka suka fice daga asibitin suka shilla
Da kwatancen kaka suka qaraso unguwarsu Deen
Zee sai kallon unguwar take tana ganin yadda aketa kai kawo jefi jefi
A gaban wani dan gida kaka tasasu tsayawa
Fitowa duk sukayi gabadaya suna maida koffofin suna rufewa
Bïñ arear zee take da kallo tana kallon yadda yanayin gidajen unguwar suke
Wucewa tayi wajensu kaka daketa qoqarin lalubo makullin gidan shikuma Deen rungume da qullin komatsansu
Bude kofar kaka tayi tana cewa
"to bismillah, kuyi hqr gidan dai gashi nan dan kuqut"
Deen ne ke bayanta sai zee dake riqe da nad'ad'iyar tabarmarsu wanda kaka ke amfani daita a asibitin sai mummy
Da sallama duk suka shiga gidan dake tass yasha shara don dama tun jiya matar mallam Nasiru taje ta amshi makulli tasa yaranta suka gyara gidan fess don tasan agajiye zasu dawo gashi dama gidan ya dade bega gyara ba
"maraba damu, kai yaushe rabo? Nasan gidannan ma yayi kewarmu" inji kaka tana qarasawa kofar dakinta
Murmushi duk sukayi sai mummy tace
"ai dole, sati biyu fa?"
Kaka data shige dakin tace
"sati biyu amma jinshi nake kamar shekara biyu"
Tafito hannunta da wata tabarmar ta shinfida masu tana cewa
"bismillah, ku xauna munshawo rana, kamal tashi kasamomana pure water mai sanyi ko ma jiqa maqoshi"
Tashi Deen da dama zamanshi kenan yayi ya amsa yawuce
Binshi da kallo zee da mummy sukayi cikin sha'awa
Sai ji mummy tayi yaqara kwanta mata don a duniya tana bala ' in son d'a ko 'ya mai biyyaya kuma a yan kwanakinnan datayi dasu kaka ta lura Deen akwai biyyaya ga sanyi bayada hayaniya ko kadan abinda take buri ga diyarta amma Saidai ba Haka take ba ko dayake taga acikin kwanakinnan kamar tafara dan hankali hankali
Suna zaune suna dan fira Deen yadawo da rabin ledar pure water masu sanyi yawuce dasu kitchen can kuma yafito dasu bisa unbreakable plate mai dan fadi kamar yadda suka saba yiwa baqi yazo ya ajiye tsakiyarsu dan murmushi a fuskarshi
Kaka da kejin kishi sosai tafara dauka tana cemasu ga ruwa su dauka
Babu musu suka dauka zee na raka Deen daya nufi wani daki da kallon qasan ido
Mummy ce tafasa tadan sha ba laifi itakau zee dauka kawai tayi badon tasha ba don bata iya shan wannan ruwan inba sotake cikinta ya rikice ba hakan yasa ta riqeshi a hannu kawai
Saida suka qara dan jimawa sannan suka tashi da niyyar tafiya
Tashi itama kaka tayi tanata kwarara masu Godiya da samasu albarka da addu'o'i suna amsawa, kiran Deen tayi don suyi bankwana
Saida suka rakasu har kofar gida suka tsaya suna jiran ganin wucewarsu sai gani sukayi mummy ta tafi bayan booth ta bude sannan ta yafito Deen da hannu alamun yazo
Babu musu ya qaraso wajen cikin nutsuwa
Gwadamashi booth din tayi tace
"ya za'ayi a sauko dasu ko wasu za'a samu su taimaka?"
Dan wara idanu Deen yayi ganin abinda take gwadamashi
"na menene wadannan din?"
"naku ne and banason wani qorafi, maza samo masu dauka"
Ganin yadda ta Hade rai yasashi kasa musawa sai kawai ya fara nade hannun shirt dinshi yace
"bari na dauka zan iya ai"
Zee na gefe tana kallonsu har suka gama fidda kayayyakin daga booth din
Kaka tariga takoma ciki so Batasan wainar da ake toyawa ba
Rufe booth din mummy tayi tana cewa
"to mu zamu tafi amma insha allah zamu dinga dan leqowa tunda munga gidan, allah yaqara sauki" tafada tana kallon smiling face dinshi
"to mummy mun gode qwarai, jazakillah bil-jannah" yafada cikin ladabi
Wani kayattacen murmushi tasaki tana cewa amin sannan tawuce bangaren driver
Kallon zee dake tsaye gefen kofar mai zaman Banza yayi yaga itama shi take kallo
Murmushi yayi mata itama ta maida mashi martani slightly sannan tajuya ta bude kofar tashiga ta zauna maida ta rufe, mummy ma rufe nata tayi bayan tashiga tana daura seat belt
Juyowa zee tayi ta kalleshi ta window taga shima still yana tsaye yana kallonta itama
Tsayawa sukayi suna kallon juna kamar suna karanta wani abu a fuskar junansu
Tada motar mummy tayi tafara reversing ahankali
Ahankali Deen yaga zee ta dago hannunta sannan tayimashi waving murmushi nadan forming a fuskarta
Shima dago hannun yayi yafara daga masu hannu fuska dauke da murmushi har suka bar layin
Bïñ motar datayi nisa yayi da kallo yanajinshi awani yanayi dabazai iya pointing finger akai ba
Saida ta 6acema ganinshi sannan ya sauke ajiyar zuciya yadawo da kallonshi akan kayayyakin dake gefe ajiye
Wani yaro dan babba2 yazo wucewa ya kirashi yace ya taimaka mashi shigar da kayan ciki
Tare sukaita shiga da kayan ciki har suka qare sannan Deen yaba yaron naira 20 yanamashi Godiya sannan yadawo cikin gidan inda kaka ta tisa kayan gaba tana binsu da kallon mammaki
Shigowar Deen din yasa ta maida kallonta akanshi cikin ayar tambaya Hakan yasa yadan 6ata fuska yace
"wlh kaka Saida nace a'a saita fara fushi wai saina amsa"
"ita wa?"
"mummy mana, zanyi magana ta hanani wai Batason qorafi"
Shiru kaka tayi tana kallon kayan wanda duk kayan abinci ne, su cartons din taliya, macaroni, couscous, gallon din mai da manja, packs din maggigika sai wasu abbubuwa a leda wanda ahaka bazasu iya gane meke ciki ba saisun buda
Ajiyar zuciya kaka tayi tace
"kuma shine kabari ta tafi ko Godiya?"
"ina gama saukewa ta tafi ai"
Ajiyar zuciya kaka tasake yi tace
"to allah yasaka masu da alhairi, allah ya biyamasu dukkan buqatunsu na alhairi, gashi ko unguwarsu bamu saniba bare muje Godiya, allah dai yaqara budi, sun taimaka sosai wlh kaga zasu riqe mu nawasu lokaci kafin mu maro, allah dai ya biya"
Da amin Deen ya amsa, cemashi tayi yakama su shiga dasu ciki kafin afara Shigowa
Da taimakon shi suka kwashesu duka suka kai dakin kaka suka adana sannan suka daura alwalar sallar asr don har anfara kiraye kiraye
Wucewa masjid yayi ita kuma kaka tawuce d'aka
***
Tunda suka kamo hanya take kallonshi ta side mirror din motar harya 6acema ganinta, sai jitayi kamar ta taho tabar wani abu nata acan
Lumshe idanu tayi ta koma ta lafe a kujera tayi shiru tanajin yadda suke tafiya akan titi
Basu wani dade ba suka qaraso gida
Horn biyu mummy tayi aka wangalemasu gate din gidan suka shige
Saida tayi parking sannan duk suka fito zee na jinta very empty
Wucewa sukayi ciki suka haye sama kowa yayi sashenshi don gabatar da sallar asr da aketa kira
***
Koda aka gama sallah gagaisawa Deen yashiga yi da mutanen cikin massalacin kamar yadda yasaba sunata tayashi murnar sauqin dayaji
Koda yafito ma zai tafi gida haka yaita gamuwa da mutane sunata mashi barka yana amsawa da murmushi harya samu ya qaraso gida
A gidan ma yan tsirarun mata ya iske wadanda suka shigo yima kaka barka
Gaidasu yayi a ladabce duk suka amsa suna mashi ya jiki ya amsa masu sannan yatashi yashiga dakinshi
Be dade ba ya fito yazo wajensu yaqara gaida wadannan suka sake Shigowa bayan shigarshi daki sannan yace ma kaka zai dan fita wajen aikinsu
Fatan dawowa lfy tayimashi tana cewa kar yakai magrib
Da to ya amsa ya tashi yayi sallama da mutanen yafita
Direct wajen workshop dinsu yawuce inda ya ishesu suna dan ta6a aiki don yanzu sai ahankali abunka da damuna
Duk sunyi murnar ganinshi Hakan yasa suka shiga gagaisawa cikin fara'a Suna tambayar shi ya jiki yana amsa masu da ya warware
Haka ya zauna cikinsu anata fira wanda becika sa baki ba Saidai da anyi abin Dariya yayi murmushi kawai
Be baro wajen ba sai wajajen magrib
Saida yafara gabatar daita sannan yashiga gida inda ya iske duk matan sun tafi sai kaka dake daki bisa sallaya ita kadai
Saida yayi mata barka da gida sannan yawuce dakinshi Be sake fitowa ba sai lokacin isha'i yawuce massalaci don dama da alwalarshi
Koda aka gama ya dan jima awaje sannan ya dawo gida
Abinci kawai sukaci suka kwanta saboda dama a matuqar gajiye suke shiyasa suna kwanciya barci yayi awon gaba da kowanne
A bangaren zee kau yau Dakyar tayi barci, wani irin kewa takeji sosai musanmman da lokacin Zuwansu asibiti na dare yayi
Haka taita juyi a gado don kwata2 babu barci a idanunta
Ganin Hakan yasa tajawo wayar ta tana yan danne danne amma a Banza don Hakan bewani hanata jin abinda takeji ba
Haka taita fama har tasamu Dakyar barci yayi gaba daita can wajajen 12 dare... ✍️
Ummin fasihu 🧚🏻♀?
8/2/21, 9:35 PM - Buhainat😝: *🙍🏻♂️DEEN 🙍🏻♂?*
*031*
"Are you ok?" yafada yana tsareta da ido
Kauda kai tadanyi gefe tana hadiye qululun takaicin daya tokaremata maqoshi
Kallonshi tayi tadanyi murmushi irin na takaici tace
"am fine, kawo nasa maka"
Amsa tayi tana jin kamar ta kwalata da qasa amma tayi qoqarin controlling emotion dinta
Saboda tsabar yadda takeji har wani dishi dishi take ganin screen din wayar
Dakyar tasamu ta daddana nambobin mummy data riga ta riqe ta offhand sannan ta miqamashi
Ganin be amsa ba yasa ta dago ta kalleshi taga ita shima yake kallo
Sake miqamashi wayar tayi batareda tace komai ba
Amsa yayi ahankali sannan yace
"Are you sure you're ok?"
"more than you are" tabashi amsar tana juyawa kwalin wayar a hannunta
Kafin yasake wata maganar harta fice daga zauren ta nufi Motarsu
Dayake a fusace take ko jira a bude mata motar batayi ba ta bude abinta dakanta tashige
Tsayawa Deen daya biyo ta shima yayi a bakin kofar gidan yana kallon motar dukda baya iya hangota taciki saboda tinted glass dinta
Da sauri bala ya zatayi ta bangaren mai tuqi yashiga shima yarufo qofa
Yana tsaye yaji qarar tashin motar sannan tafara yin reverse tana barin layin
Bin motar yayi da kallo abubbuwa da dama na kai kawo a zuciyarshi
Tabbas she's not ok, ya hangi wani abu a fuskarta dukda 6oyemashi datayi qoqarin yi, kamar fushi kamar takaici bazai dai iya pointing finger akai ba
To idan ma fushin ne meye silar? Tunda yashigo gidan ya lura da wannan expression din a fuskarta
Duk sai yaji ba dadi, satinsu daya rabonsu da juna and he's longing and waiting for the day they'll meet, a tunaninshi bayan wannan lokacin da sukayi basu ga juna ba haduwarsu zaya zama very memo ranar one, zasu dade suna firar yaushe gamo amma yaga akasin haka saima qin Sakin jiki da fuska data sabayi
Ya dade nan tsaye sannan ya juya ya koma ciki a sanyaye
Idan ran zee ya kai dubu to duk sun 6aci
Tama kasa fasalta abinda takeji a ranta wannan lokacin
She's totally and totally dissapointed with him
Tayi sati tana kewarshi tana begen ganinshi tana looking forward to ranar haduwarsu cikin zumudi amma sai gashi babu abinda ta kwasa a ranar datake zumudin sai kayan haushi da takaici
It hurts idan kadamu da mutum harya kasance koyaya ka motsa saiya fadomaka a rai amma at the end of the day ka gano cewa bakai ke gabanshi ba
Koda bala yayi parking bata tsaya ya budemata kofa ba kamar dazu ta bude ya fita tayi gaba
Zagayowa bala yayi ya rufe kofar data bari bude cikin ranshi yana gulmarta wai dama idan tafito mota dakanta to ranta a 6ace yake
Da sallama ciki2 tashiga falon, babu kowa falon hakan yasa tayi sama direct
Kamar tashiga dakin mummy sai kuma tafara bude dakinta ta tilla ledar wayar hannunta saman gadonta sannan ta rufe tawuce kofar mummy tashiga knocking
Saida aka bata izinin shiga sannan ta tura kofar tashiga tana kokarin saita fuskarta
Mummy daketa lissafe2 ta dago tana kallon zee data shigo dakin
Qarasawa zee tayi ta samu wuri ta zauna tana yiwa mummy sannu da aiki
"yauwa, harkun dawo?"
Kada mata kai tayi tace
"eh mummy, tana gaidaki sosai tamace zata kiraki nabata number ki"
"masha allah, me jiki fa? Hope ya warware"
Wani abu taji ya tsayamata a qasan maqoshi jin anyi maganar Deen
"eh da sauqi" ta amsa non-chalantly
"to allah ya kyauta gaba dama haka muke fatan ji"
Shiru yadan ratsa dakin can zee ta tashi da niyyar tafiya
"kunyi waya da daddy?" inji mummy tana dakatar daita
"A'a, duk yau bamuyi ba Saidai jiya munyi da daddare" ta amsa
"wani abu yafaru ne mummy?" tafada cikin curiosity
Murmushi tadanyi tace
"ohon muku, ai kunfi kusa, cemin yayi yana kiranki bata shiga wai idan kin dawo ki kirashi"
Murmushi tayi tana jin kaso kadan daga cikin 6acin ranta na tafiya
"ok zan kirashi yanzu insha allah"
Daga haka tayi mata sallama tafita
Dakinta tawuce direct
Gyallen kanta tafara warwarewa ta cire sannan ta zauna gefen gado tana scrolling din wayar ta
Foreign number daddy ta lalubo ta antayamashi kira
Bugu biyu ya daga ya dauka yana sallama
Shagwa6e fuska tayi lokacin dataji muryar daddynta
"daddy na"
Murmushi mai sauti daddy yayi daga can bangaren yana cewa
"my jewel! Har kun dawo"
Komawa tayi da baya ta kwanta tana lumshe ido tana jin sanyi na ratsa zuciyarta
"eh daddy na, nidai daddy na yaushe zaka dawo, i missed you sooo muchhhh"
Dariya daddy yayi daga dayan bangaren yace
"missed you more and more darling, wannan satin naso dawowa amma allah beyiba inajin sai kuma next week qila"
"kai daddy, next week is too far, i can't wait" tafada a Shagwa6e
Dariya yasakeyi yace
"then bari nabaro komai nadawo tunda sweetheart dina bata iya jira"
"but daddy kingin aikin fa?"
"that can wait i guess"
Murmushi tayi tace
"kai daddy"
"yes, ina iya barin komai nazo na ganki inhar Hakan zai farantamiki"
"no daddy tunda ka kusa kabari saika gama sannan kadawo"
"no, bayan kin tadomun tsumin son ganinki? Gobe zaku ganin daga sama, don't tell your mummy about this"
Tashi tayi zaune tana dan wara idanu tace
"wai dad da gaske kake? Daddy am joking please karka taho saika gama abinda yakai ka"
"Sai kiyi, am done talking"
Sai gashi ita takoma bashi haquri yabari saiya kammala abinda yakaishi sannan ya dawo don tasan qaramin aikinshi ne ya taho din muddin Hakan zai sata farinciki
Dama haka yake koda yaushe farincikinta shine nashi, yasha yin abu don farincikinta koda kuwa Hakan na nufin sadaukar da nashi farincikin ne, that's daddy for you
Dakyar tasamu ya yarda zai zauna din yana mitan zata hanashi ganinta, nan tace indai don ganinta ne suyi video call ba shikenan ba?
Haka kau akayi, nan take sukayi switching din kiran zuwa video call
Sun jima sosai suna wayar sannan sukayi sallama kowanne murmushi a fuskarshi
Izuwa yanzu kaso mafi rinjaye cikin 6acin ranta yabi iska tareda firarsu da daddy
Tashi tayi ta shiga toilet can ta fito hannunta da fuskarta Duk ajiqe
Idanuwanta ne suka sauka akan ledar wayar dake a tsakiyar gadon
Yarfe hannunta tayi ta dawo gefen gadon ta zauna tajawo ledar ta bude ta Fiddo kwalin tana jin ranta na qara 6aci
Bude kwalin tayi taga wayar gatanan kamar ma ba'a ta6a ta6ata ba
Cirota tayi tana jujjuyata a hannunta cikin zuciyarta tana tambayar kanta kodai ya raina wayar ne? Inba haka ba wa za'a ba this kind of kyauta ya mayar? Kodai besan ko nawa take ba? Ko ba kalarta yakeso ba? Ko... Ko... Ko..
Tama rasa abinda zata hasaso again
Danna power din wayar yayi tafara booting
Saida tajira ta bude dakanta sannan tayi swiping
"wow!" tafada ganin tana preparing apps din wanda Hakan ke nufin ko ta6a kunnata beyi ba
Kada kai tayi cikin qunar rai tana dan murmushin takaici
Tarasa dalilin dayasa abin yake 6ata mata rai har haka
Ko don bata ta6a yiwa wani kyauta ba