Showing 54001 words to 57000 words out of 322641 words

Chapter 19 - DEEN Complete Hausa Novels By Arewa Novels.txt

27 Nov 2025

4333



Haka taita saqa da warwara daga baya dole Deen ta nema don yabata shawarar yadda zatayi kuma kamar yadda yasaba samo mata mafita a matsalolinta wannan karon ma haka yayi

Tare dashi sukaje parking space din malamai inda mottocinsu ne a parke a wajen

Wajen motar mr ibrahim suka nufa cikin sa'a kuma sukaga daya daga cikin glass din windown motar be ida rufewa ruf ba

Tanan suka lalla6a suka zura takardar tafada seat din mai zaman banza

Suna ganin haka sukabar wajen da sauri kowanne zuciyarsu fall murna

Mr ibrahim betashi ganin takardar ba saida ya isa gida, dauka yayi yana jujjuyata sannan ya warwareta

Ganin rubutun dayawa yasashi maida wa ya ninke akan saiya nutsu sannan ya karanto


Sosai yasha mammaki bayan yagama karance takardar kodayake dama yaga alamu daga gareta tun lokacin data fara zama class dinshi Saidai beyi tunanin yadda take nuna jinkai dinnan zata iya bashi haquri akan abubbuwan da duk tayimashi

Maida takardar yayi ya ninke ya adanata

Zee tayi tunanin zai nemeta amma Shiru takeji, data gayawa Deen yace mata ta kyaleshi kawai yanzu dama ba lallai bane yayi saurin haqura kawai tabari atafi hutu adawo saita sameshi a mutum taqara bashi haqurin

Sosai ta gamsu da wannan shawarar Hakan yasa tayi amfani daita ta kyaleshi


A bangaren su sumee kau sosai yanzu suke hadewa da zee don Mafi yawancin lokuta suna tare musanmman yanzu da ba komai take ba ga Deen yana busy don basu gama tasu Jarabawar ba hakan yasa suka koma suka jone kamar da dukda suna yawan hadewa da Deen din shima anytime he's free




*BAQAR RANA*


Yau laraba kuma yau su Deen ke qarasa paper dinsu ta qarshe

Sosai ake kwala rana yau ga zafi harna innanaha Hakan yasa duk inda zaka gitta a school din Saidai kaga students qarqashin bishiyoyi suna shan iska don idan ba dole ba babu abinda zai saka zaman class


Dayake duk yawancin departments sun gama Jarabawarsu sai school din yarage jama'a sosai don sai tsirarun masu Jarabawa saikuma ire irensu zee wadanda dalili kawosu

Tare suke da Deen har saida lokacin shiga final paper dinsu yayi sannan suka rabu bayan yafada mata inda zasu hadu idan yafito


Ta dan jima nan zaune ita kadai tana yan danne dannenta a waya

Zaman kadaicinne ya dameta Hakan yasata miqewa ta sa6i jakkarta da niyyar zuwa wajensu sumee koba komai sunyi fira to whine time away


Koda taje mazauninsu saita iske wajen wayam, tana niyyar juyawa taji muryar sumee a bayanta

Juyawa tayi ta hangota ta taho tana daga mata hannu Hakan yasata yimata guntun murmushi ta tsaya don jiran qarasowarta

Qarasowa tayi wajen tana dan sauke numfashi

"keda wa kiketa sauke numfashi kamar wanda aka biyo?" inji zee

Tsaki sumee taja tace
"kede bari, wlh saqo naje amsowa na tararda mai kawowan ma bai isoba shiyasa na dawo har zan wuce naga wata kamar ke shine fa na biyo ki"

"to? To where are others? Naga wurin wayam ko yau basu zo bane?" inji zee

"sunzo mana, wazai zauna anan kina ganin yadda ray din rana ke reflecting ta koina? Wani cool waje muka samu daga bayan school, bakiji wurin ba so cool kamar karka tashi, nima dan iskan saqonnan danaje amsowa ne ya tadoni abin ban haushi kuma ashe be qaraso ba" tafada cikin nuna jin haushi

Ta6e baki zee tayi tace
"yanzu dai muje wajen dan allah, na gaji ga rana na kwalata i need some breeze"

"ai dole, gaskiya yau ana rana, qila ruwa xa'ayimana dama andan daga mana qafa kwanan nan" inji sumee suna tafiya


Tafiya suke suna firarsu suka nufi bayan school inda tunda zee take a school din bata ta6a zuwa wajen ba Saidai bata kawo komai a ranta ba don babu wata alama da zai janyo ta zargi wani abu


Suna cikin Tafiya wayar sumee tayi ringing

Cirota tayi ta kara a kunne bayan ta tsaya Hakan yasa itama zee tsayawa tana kallonta

"wai fatima wannan wanne irin wulaqanci ne? Kince min kinzo naje na tararda bakya nan, naita jira Shiru kin shanyani cikin rana kamar yar iska" tafada a masifance

Jimm tadanyi alamun magana akeyi acan bangaren can kuma taja Tsaki tace
"haba wannan ai wulaqanci ne wlh, kawai saiki sani zuwa da dawowa kamar marar aikinyi bayan kinga yadda ake kwala wannan ranar? Mtcheew! Ganinan zuwa idan kuma kinga dama karki tsaya inda zanyi saurin ganinki, Mtcheew!" ta katse kiran a fusace

Dagowa tayi ta kalli zee dake sauraronta Tundazu
"wai kinji don wulaqanci sai yanzu taga damar zuwa, ni wlh badon saqonnan nada muhinmmaci ba da babu abinda zai sani wannan wahalar" tafada cikin fushi


Dan Ta6e baki zee tayi tace
"to ya kika iya? Tunda yanada muhinmmaci dolenki kau kije ki amso, ehe!" ta qarashe tana mata Dariya ganin yadda take cika tana batsewa

Tsaki sumee taja tana girgiza kai tace
"ko zaki rakani please" tafada tana narke fuska


Harara ta gallamata tace
"ca6! Wazai qara wannan uwar tafiyar yadawo? Nikam saikin dawo, ni wlh ma bansan abinda yasa kukazo nan ba, zafi kanku farau zaku shigo nan inda babu wulgin kowa? Ni tunda nake a school dinnan ban ta6a zuwa nan arear ba" inji zee tana qarewa environment din kallo

"hmm wlh duk aikin su deeya ne, nima dafarko nayi wannan mitan amma danaje naji coolness din wajen kamar naita barci donma wannan yar banzar fatiman ta kofsa min"

"haba wajen yayi nisa sosai, ga wurin so quiet ku bakwa tsoro?" inji zee

"kede ke ganin haka, sai kinje wurin zakiga acike yake don duk can students suka ruga shiyasa kikaga basuda yawa acan cikin school din" tafada cikin son convincing dinta


"to nidai bari na qarasa ranar nan tafara gasamin forehead, kije ki amshi saqon kin shanyata itama"

"kyaleta itama ta dandana ai" tafada tana Dariya

Wucewa zee tayi tana cewa
"badai kyau mugunta"

Dariya sumee tayi tajuya itama tana cewa
"saina iso" ta wuce



Cigaba da tafiya zee tayi hoping ta hango su deeya din amma sai qara nausawa take babu su babu alamun su don ko wulgin mutum bata ganiba

Gajiya tayi ta ja ta tsaya tana riqe kugu

Izuwa yanzu wani iska iska akeyi mai shige da na hadari don dama kamar yadda sumee tace wannan zafin na yau da walakin

Tsaki zee taja cikin quluwa, in banda ma hauka mezai kawoka nan duk da sunan shan iska?


Wayarta ta ciro daga cikin jakka tashiga lalubar number su Saidai babu ta wanda ke shiga, Hakan ba qaramin qara quleta ba yayi Hakan yasa tayi kwafa ta kashe wayar tajuyo da niyyar tafiya sai jitayi ta bangaji abu har wayar hannunta na faduwa

Baya2 tayi tasamu dakyar tayi regaining din balance dinta sannan ta dago don ganin menene ta bangaje


Gabanta ne ya yanke ya fadi ganin wani tsaye agabanta ciggarete a hannunshi yana aikamata wani dan iskan kallo da jajjayen idanunta


Dan jada baya tayi Saidai motsin dataji a bayanta yasata saurin Juyawa nanma taga wani

Da guda guda taga sunata fitowa har suka gama fitowa suka zagayeta ya zamana tana tsakiyarsu


Da guda guda tafara binsu da kallo gabanta na faduwa, gabanta ne yayi wani mummunan bugawa datayi tozali da master dayayi pocketing din hannunshi yana kallonta da jajjayen idanunshi dan guntun murmushi dauke a gefe bakinshi

Cigaba tayi da kallonsu da daidaya zuciyarta na mugun bugawa, dakyar ta tattaro yawun bakinta ta hadiye sannan tayi qoqarin aro nutsuwa ta yafa ta duqa da niyyar daukar Wayarta sai gani tayi na kusada ita ya taketa har saida tayi qarar fashewa sannan yayi ball daita tafada can cikin wasu ciyayi


Dagowa tayi gabanta na cigaba da racing tana kallon wadda ya take wayar, cikin qarfin hali tace

"wai malamai lfy? Ku su waye?" tafada cikin muryar dataji kamar ba nata ba

Wata mahaukaciyar Dariya suka kece daita wanda Hakan yaqara farashin tsoronta don wannan Dariyar daga jinta ta tsantsar mugunta ce

"baa baa! Kaji wai qarin bayyani takeso" inji gandu yana qara fashewa da Dariya

"wai dagaske kike baki ganemu ba? Harda nima" inji T.J yana nuna kanshi yana Dariya


"haba baby? Kin iya mari amma baki iya tantance mutane ba?" inji Alex dake gefen damarta shima yana Dariya


Gabanta ne yayi mummunan bugawa da jin haka

_ya ilahi! What am I into_ tafada a cikin zuciyarta


"ya isa!!" inji master yana daga hannu wanda hakan yayi daidai da daukewar dariyarsu


"baby bata ganeku ba, qilama bata sanku ba tana neman qarin bayani, koba haka ba baby?" yafada yana kallonta tareda kashe mata ido daya

Kasa magantuwa tayi sai kallonshi datake speechless

"karki damu, ni zan fahimtar dake, ai ke ranki shi dade ce dole sai ana hadawa da tuni" yafada yana tunkarota


Bugun zuciyarta ne yaqara qaruwa tafara ja da baya cikin tsananin tsoro shikuma yana tunkarota haryanzu dauke da wannan murmushin


Duk takunshi daya na tunkararta daidai yake da nata daya na ja da baya, haka sukaitayi har tajita gab da bash dake bayanta, saurin Juyawa tayi tana kalleshi ta kuma kalli master dake daff daita, cikin kidima tasa hannu da niyyar ture master daya kusan Hade jiki da ita ta gudu Saidai caraff ya cafke hannun, kafin ta tantance komai taji an dauketa da wani giggitaccen mari... âœï¸



Ummin fasihu 🧚ðŸ»â€â™€ï¸?
8/2/21, 9:34 PM - BuhainatðŸ˜: *ðŸ™ðŸ»â€â™‚ï¸DEEN ðŸ™ðŸ»â€â™‚ï¸?*






*022*





*DEEN*



Yana fitowa daga exam hall yanufi inda sukayi da zee zasu hadu

Be tarar daita ba wajen Hakan yasashi zama don jiranta yasan qila wani abu tajeyi ko taje saye

Fiddo wata takarda yayi yana sake dubata

Form ne da wani maqocinsu ya samo mashi na aiki a wani company

Ga yadda maqocin nasu ya gayamashi yace suna daukar mutum da kowanne mataki na karatu kai hatta wanda iyakar shi primary suna dauka Saidai kawai banbancin albashi da za'a samu tsakaninsu


Tun jiya yabashi akan zai amsa yau idan ya cike, sosai shima Deen din yaji yana son aikin don dama yanzu hutu zasuyi gashi aikin furniture dinsu yanzu ba'a cika samu ba kasancewar yanzu damuna ce kowa ta kanshi yake duk ba'a fara fitar da amfanin gona ba bare kudi su yawaita har afara maganar aure2, dakuma ya zauna hakanan ai gwara ya jaraba wannan din ko allah zaisa a dace


Ciro pen yayi yashiga cike takarda cikin nutsuwa making extra sure beyi mistake ba ko guda


Saida yagama cikewa tsaf sannan yatsaya yana sake dubawa don tabbatar da beyi kuskure ba ko daya, Ganin komai daidai ne yasashi bude tsakiyar wani Littafi ya saqa takardar ciki ya maida ya rufe


Daga kai yayi yana kallon sararin samaniya ya hangi yadda hadari ke neman haduwa ga iska iskar daketa kadawa yanzu


Duba wristwatch dinshi yayi yaga 3 saura, yanzu aqalla yafi 30mins da zama

_to ina ta shiga ne haka?_ tambayar dayayiwa kanshi kenan


Komawa yayi jikin kujerar ya harde hamnayenshi a qirji ya cigaba da jiran tsanmmani




*ZEE*


Wani dum taji kanta yayi tayi baya baya ta zube qasa

Dafe kumatunta da takeji kamar ba nataba tayi tana jan numfashi cikin fitar hayyaci


Rankwafowa Master yayi gabanta yana cigaba da wannan dan iskan murmushin

"da kika wani yunquro, nima marina zakiyi? Eh?" yafada yana leqa fuskarta data farayin jajajaja

Dagowa tayi ta kalleshi da idanunta dasuka farayin ja hannunta still Dafe da inda ya mareta tana jan numfashi haryanzu

"gayamin, nace nima marina zakiyi?" yafada yana kai hannunshi saitin qirjinta

Bige hannun tayi tana ja da baya dakyar

Kamo hannunta yaso qarayi taqara Bige hannun tana qara ja baya tana nishi

"Go away, you brat!" tafada tana dibar qasa ta watsamashi still tana ja da baya

Saurin kauda kai yayi ganin qasar ta nufo fuskarshi Hakan yasa ta sauka a jikinshi

Sake juyowa yayi ya kalleta
"brat? Nine brat? Wato bakinki bai mutuwa ko? Dont worry, zan kashe maki shi ayau, now and forever!" yafada yana nufota

Ganin Hakan yasata saurin miqewa a gigice tayi niyyar guduwa sai kawai taji bash dake bayanta ya cafketa

Qara tasaki tashiga qoqarin kwace kanta a hannunshi amma takasa, batayi wata wataba tasa kafarta atsakiyar kaffafunshi ta dago gwiwarta


Wani mahaukacin qara bash yasaki tareda sakinta ba shiri, ya fadi yana billayi

Faduwa tayi itama daya saketa amma ko second daya batayi ba ta miqe tafara gudu cikin son ku6uta daga garesu

"kubita! Karku sake ta gudu!" inji master cikin qaraji


Da gudu su alex suka bita yayinda shikuma master din ya zube gaban bash daketa ihu haryanzu hannayenshi damqe da gabanshi ya dagoshi yana kallo


Gudu take cikin fitar hayyaci batareda tasan hanyar da takebi ba, ga wani iska mai qarfi daya taso mai tafeda duhun hadari


Iya gigicewa ta gigice don kawai jefa kafarta take inda tasamu gashi bata ganin gabanta sosai saboda iska, qarin tashin hankalinta kuma shine sautin gudunsu dataji yana qara kusantota sosai

Kafin ma tayi wani nisa suka cimmata gandu yasamata kafa tayi tuntu6e ta fadi

Jan kugu tashigayi da baya baya tana numfarfashi

Nufota suka ta cigaba da jan kugu tana girgiza kai cikin tsantsar tashin hankali, tsabar rudewa ma takasa jawo kowacce addu'a sai 6ari da duk ilahirin jikinta keyi


Take kafarta T.J yayi wanda hakan yasata sakin qarar azaba, bata gama tantance zafin wannan ba taji an damqi gashinta anfara janta qiiiii!


Ihu ta cigaba da kwallawa tana Iya qoqarinta na ganin ta qwace amma takasa, be tsayar da ita koina ba sai a gabansu master dake duqe still gaban bash daya galabaita Iya galabaita don ba qarya ya bugu

Jefar daita yayi ta zube gabansu master tana haqi

Afusace master ya damqi gashinta har saida tayi qara ya dago kanta saitin fuskarshi yana kallonta da jajjayen idanunshi

Qalato yawu tayi ta tofamashi a fuska cikin qarfin hali

Kauda kai yayi yana rintse ido saboda yawun daya sauka akan fuskarshi, Afusace yasake juyowa ya dauketa da marin dayafi na dazu ratsa jiki


Wata wahallaliyar qara tasake fasawa ta zube awajen tana numfashi sama2

Jitayi kunnenta nayimata dumm dumm ga idanuwanta da suka fara ganin dishi2

Bayan hannu yasa ya goge yawun fuskarshi yana huci sannan ya qara nufarta ya sake damqo gashinta ya tadota zaune

Rintse idanuwanta tayi gamm, tsabagen damqa har jijjiyoyin gashinta ana gani

"ni zaki tofawa yawu a fuska? Eh?" yafada yana qara dauketa da wani marin wanda yaqara sata zubewa

Cusa fuskarta tayi cikin ciyayin wajen tana jan numfashi dakyar

Qara damqo gashinta yayi ya dagota again yana saita fuskarta saitin fuskarshi ya nufi bakinta da niyyar sumbata

Datse bakinta tayi gamm ta hanyar maida la66anta ciki ta danne tana numfarfashi masu nauyi

Cikeda mugunta yasa dayan hannun ya Kamo kumatunta ya lotsa yatsunshi a kowanne gefe cikin mugunta har saida bakin ya bude

Qara nufar bakin yayi da niyyar kiss ta dago hannunta daya dakyar ta rufe mashi fuska tana turashi

Kauda kai yake cikin son kaucema ture fuskarshi datakeyi amma taqi bari Hakan yasa ya saki gashinta da haryanzu ke a damqe a hannunshi ya Kamo hannun nata data tare mashi fuska dashi dago dayan hannun tayi shima ya cafkeshi ya hadesu a baya ya riqesu da hannu guda yasake dago fuskar da tsiya yasake nufar bakin





*DEEN*


Qara duba agogon hannunshi yayi a karo na ba adadi, wai ina ta tsaya haka? Koko ta tafi ne? Amma ai basuyi daita cewa tafiya zatayi ba, gashi kuma beson tafiya kuma ace tananan tazo ta nemeshi batanan


Kallon sama da hadari keta qara haduwa yayi ga iska daya fara qarfi

Miqewa tsaye yayi yana rungume littatafanshi a qirji yana qara kallon yadda hadarin ke qara haduwa

Ina ta shiga to? Sai yanzu yake jin haushin rashin number wayarta da bedashi daba yanzu yakira yaji ko ta tafi ba?

Ga hadari sai qara haduwa yake, yasan rufin asirinshi shine yabar school dinnan Tun yanzu kafin ruwa ya 6alle saboda yanayinshi don yanzu haka ma iskar dake kadawa yafara affecting dinshi

_maybe ta tafi gida itama_
_yes na tabbata ta tafi_ yafada ma kanshi cikin qwarin gwiwa


Da wannan tunanin yasa ya fito daga inda yake yana qara qanqame littatafanshi a qirji ya fara tafiya don barin school din.


Wani iska mai qarfin gaske yaqara tasowa wanda saida Deen yaqara qanqame jikinshi, gashi dama daga shi sai wata yar farar t-shirt mai gajeran hannu, kasancewar yau da zafi aka tashi yasashi sanyota don ko kadan be ta6a kawoma kanshi za'ayi ruwa ba


Qara saurin tafiyarshi yayi cikin zuciyarshi yana addu'ar allah ya daga ruwan nan harya kai gida don bazai manta da gargadin Dr ba a wancan attack din na ciwonshi inda ya gargadeshi sosai akan ya kiyayi shiga ruwa saboda condition dinshi don koyaya ya shiga ruwa matsala za'a samu


Wani iska mai hadeda gugguwa yasake tasowa wanda saida yakai hannunshi yakare fuskarshi ganin yadda gugguwar qasar ta nufoshi


Yanajin zubewar wasu daga cikin littatafan hannunshi amma be bude idanunshi ba saima addu'o'i daya shiga karantowa a zuciyarshi har gugguwar tawuce


Sauke hamnayenshi yayi Bayan ta wuce yayi saurin duqawa don tattare littatafanshi

Iska ake sosai wanda Hakan yasa littatafan suka bashi wuya wajen tattarosu don iskan sosai yake kadawa har littatafan na bubbudewa da kansu

Cikin hakane wani Littafi ya bude iska yashiga bubbude pages din da sauri sauri har yakai page din daya saka takardar shi na form din daya cike


Fitt! Iska ya figeta tayi sama tafara shawagi acikin iskan


"O'O!" yafada yana kallon yadda takardar ke sama ke qasa acikin iskan

Saurin ida tattara kingin littatafan yayi sannan ya miqe yafara bin takardar don kamota

Saidai kwata2 yakasa don the more yake tunkarar takardar the more iska ke qara yin gaba daita

Haka yaita binta da gudu2 sauri2 trying all his best na ganin ya kamota amma a banza



*ZEE*


Duk yadda taso qwatar hannayenta daya riqe a bayanta kasawa tayi don ba qaramin riqo yayimusu ba gashi qarfi ba daya ba

Duk yadda yaso ya lallubo bakinta kasawa yayi don sosai take amfani da iyakar qarfinta na ganin ta kwace wanda Hakan yasa taqi tsayawa wuri guda bare yasamu damar lallubo bakin


Su alex na nan still tsaye kansu suna kallon artabun da sukeyi Tundazu, suna son su shiga suma a faffata dasu amma sanin halin master yasa suka jinkirta don ga dukkan alamu shi da kanshi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login