Showing 3001 words to 6000 words out of 322641 words

Chapter 2 - DEEN Complete Hausa Novels By Arewa Novels.txt

27 Nov 2025

6128

alamu dai suma chewing gum din sukeci

"Muje ko?" Tafada tana fara tafiya suma sai suka motsa suka jero su biyar suna tafe suna Yar firarsu da classic girls


Duk binsu da na mujiya akayi, masu Allah wadai nayi masu kushewa nayi masu yabawa nayi, masu ji dama su nayi.




"Kaiiii! Baabaa kalli can" inji wani yana qara kafesu da dissashin idanunshi

Wanda aka kira da baabaa din dake zaune kan booth din wata baqar mota wanda kallo daya xaka Mashi kasan tattacen dan iskane shima, yace

"Manta kawai, Ai na rigaka ganinsu yafada yana jan sigarin hannunshi idanunshi still akansu

"Kai baabaa alqur'an babes dinnan akwai kayan ruwa, kullum saisun sa dau sautina ya dau sauti" inji wani mai qaton baki, le6en duk sun dafe don zuqe2

Na ukun yace
"Ba doleba? Kajinne dagani zasuyi romo, wlh nima kullum sai sun kunnani"

Na hudun yace
"Babu kamar wancan mai yellow da red din, duk tafisu komai, Oga dakai kadai ta dace yasin"

Wani kafirin murmushin gefen baki nakan motar yayi yana qara jan cigarette dinshi batareda yace komaiba saima kafama kugun Zainab idanu dayayi kasancewar harsun gittasu

Na farkon yace
"Oga nidai yau abani izini in tashi yanmatan nan hakanan, kwalelen yayi yawa"

"Kana haukane Alex? Ka manta yadda take yaga duk wanda ya taremata gaba?" Inji na ukun

"Ai gaba kuma da gabanta gandu, mu munfi qarfin yaga"

Na biyun yace
"Ga yamashi dai Alex yaga Ai mune nan zamu yagasu kai bama yagawa ba saidai mu farka mutum dan kaza kazanshi" yafada yana gatsine irinna qaurayen nan

Alex ya kalli nakan motar wanda da alamu dai ogansu ne yace
"Oga kabani izini na kawoma ita har makwancinka"

Sai a sannan ogan ya dauke idanunshi daga Kansu zee dasukayi nisa ya kalli alex din sannan yadanyi wannan dan iskan murmushin na dazu da alamu dai shima miskilin kanshi ne sannan ya motsa baki dakyar yace
"Nabaka"

Kamar kau jira yake sai kawai ya nufesu cikin tafiyarshi ta bouncing suka bishi da idanu


Su Zee basusan sunayiba suna tafe ne suna firarsu sai gani sukai ansha gabansu

Hakan yasasu dakatawa suna kallonshi a dage

Ganin abinda ke shirin faruwa yasa mutane fara dan matsowa most especially wadanda suke acan nesa don sunsan wani show din za'ayi yau don anma dan jima ba'ayi show ba don kowa tsoron tunkararta yake don sunsan hakan ba riba

Gashi sunga daya daga cikin yaran MASTER ne wanda shima yayi qaurin suna a makarantar hakan yasasu qara matsowa don kashe kwalkwatar idanunsu


"Yane chicks? Ya yau?" Yafada yana pocketing din hannayen shi tareda karkacewa gefe daya

Anan ma babu wanda ya amsa mashi saidai da alama su qawayen zee sun dan sha jinin jikinsu sanin wanda ke gabansu itakau zee hankalinta nakan wayar hannunta tana taunar chewing gum tana qas qas dashi

"So batareda 6atamuku lokaci ba kuma na 6ata nau, dama big boss ne dama yagani kuma ya kyasa, yakuma bani kwangilar kawo muku wannan gara6asar wanda ba kowa keda sa'ar samunta ba, hasalima yanmata ke kawo Kansu gareshi badai ya nema ba amma dayake Ku sipeshial (special) ne shiyasa ya turoni da kanshi don tashin Ku musanmman wannan sarauniyar kyau din" yafada yana kallon zee da da alamu bata Masan me yake cewa ba yana dan lasar bussashen lower lip dinshi

"Ya? Mutafi ko? Gayacan yana jira, kunsan boss baya jira" yasake fada yana dake babbakewa yana dan jujjuyawa

Har yanzu babu wanda yace komai, saima basarwa da suma qawayen sukayi ganin yadda itama boss dinsu tayi kamar batasan da wanzuwarshi ba

Mutanen dake kallonsu sun dan qara yawa kasancewar wasu sun fito daga lecture ga gulmar daketa yawo hakan yasa wasu wadanda ma ba harabar makarantar suke ba garzayowa wajen don ganin qwam

Ganin sunki motsawa bare suyi magana yasashi dan riqe tip din phone din hannun zee wanda tundazu idanunta na kai

Hakan yasata dagowa tana kallonshi tacikin sunglasses dinta

"Magana akemiki fa" yafada yana karkace baki

Gira daya ta daga alamun me yake cewa?

"Nace boss ne...."
Maganar maqalewa tayi sanaddiyar wutar data kiftamashi a idanu

Dagowa yayi agigice yana kallonta hannunshi dafe da kumatu yana kallonta baki bude

Kingin yaran *Master* kamar yadda suke kiranshi sunyi yunkurin motsawa, Master din da har yanzu yana kan booth din motar ya daga masu hannu yana yima cigarette din hannunshi wawan zuqa idanunshi kansu zee din

Suma yan ganin qwam sakin baki sukayi cikin mammaki suna ganin qarfin hali da tsantsar wautar da zee ta tafka

"Kan bujinnan kayyasa! Ni kika mara?" Yafada unbelievably still dafe da kumatu

Zare glasses din idanunta tayi tana aikamashi matsiyacin kallo tace
"An mareka! Me zakayi?!"

Cikin wani irin huci yayi kanta kamar zai maketa yaji Master ya kwalamashi kira wanda hakan yasashi tsayawa cak daga yunkurin dayayi

Bata damuba ta nunashi da yatsa tacigaba dacewa
"Kai waye dazakazo ka tareni a hanya? Waye kai? Waye ubanka a Katsina? Nace waye ubanka a Nigeria?!" Tafada cikin tsiwa

"To bari kaji, nafi qarfin cakuri cici irinku, nafi qarfin jagaliyancinku, kaje ka gayawa wanda ya aikoka cewa mai wankemin toilet dinna ma tafi qarfinshi bare ni gabadaya, wutsiyar raqumi tayi Nisan nisa da qasa, yayi kadan don ko matsayin mai bawa flowers dinmu ruwa be kaiba and also ka gayamashi I don't mingle with riff-raffs don qaddara mace tasani attending din makarantar nan at the first place and duk randa wani dan iska yasake yunkurin tsallake limit dinshi I'll help him take him back to the lowest limitation"

Tsaki taja tana bude murfin wayar hannunta a fusace, zare sim cards dinta tayi sannan tayi wurgi da wayar taja hannun na kusa da ita suka wuce bayan tasake jan wani dogon tsakin


Duk binsu akayi da kallo yayinda qannanun murmurings keta tashi acikin mutanen yan kallo

Daya daga cikin yaran Master din yazo inda Alex ke tsaye haryanzu yana hucin 6acin rai

Bubbuga kafadarshi ta dama yayi sannan ya kama hannunshi suka nufi motar

Tun kafin su iso Master ya diro daga saman motar ya kafa facing cap dinshi yana jefar da kingin tabar hannunshi tareda murjeta da qafa

Daidai nan suka qaraso wajenshi, kallon Alex da fuskarshi haryanzu ke bayyana 6acin ran dayake ciki yayi sannan shima ya bubbuga kafadarshi alamun ya share kawai sannan ya zagaya yashiga motar suma suka shishiga aka rufe qoffofin sannan suka bata wuta suka fice daga makarantar aguje suna bade yan gulma da qura




"Zee kin kau san suwaye wadannan mutanen?" Inji daya daga cikin friends dinta mai suna Nadeeya

Ta6e baki tayi sannan tace
"Ke Ai kin Sani ko?"

"Honestly speaking abinda kikayi be dace ba, wannan ganganci ne, kinkau San hadarin gayun nan?" Inji Nadeeyar

Tsaki zee taja cikin qosawa tace
"Look, bansan suba bansan hadarinsuba, kamar yadda suma basu sanniba basusan hadarina ba, don haka ki kyaleni da maganar su karki qaramin 6acin rai akan wanda nake ciki ayanzu" tafada cikin Isa da tsiwa kamar yadda tasaba yimusu

Shiru duk sukayi yayinda kusan dukansu maganarta tayimusu zafi, suna jin haushin yadda take treating dinsu tana nunamusu Isa saidai kwadayi ya hana suyi zuciya su kyaleta shiyasa kodayaushe basu iya musamata duk abinda tayi daidai ne koda beyimusuba, gwara gwara nadeeya ita tana dan magantuwa wani sa'in


"Kema deeya ki kyaleta mana, mutanen nan fa su suka tsokalota sukazo har inda take, banda ma daqiqanci ma irin nasu ina sukaga munyi Kama da irinsu? Kwata kwata ba class dinmu bane su kinga kau duk abinda akayi musu su suka ja, ni wlh zee kinmin daidai don ko nice haka zanyi" inji wata mai suna Sumayya suna cemata sumee

"Ai gwara Ku, suna iya tunkararku tunda dama zani ce ta tadda muje, meye banbancinku dasu? Amma tsabar ya rainama kanshi hankali yarasa wanda zai tunkara saini?" Taqarashe zancen tana nuna kanta a qasaice

"Kodayake ba laifinsu bane, da ina UK da duk haka bata faruba, na yanzu ina can living a free and classic life, ina mingling da classic friends turawa ba irinku ba don Ku kam wlh managing nake daku don dai ba yadda zanyi ne" tafada tana yatsine face

Dukkansu sunji haushin kalamanta sosai amma babu wacce ta gwada don idan da sabo sun saba da cin mutuncin datake musu akaikaice saidai sunkasa yin zuciya subarta saboda d'an abinda suke samu a wajenta don babu laifi zee badai bushasha ba

"Yanzu dai komai yawuce, topic close. Ba girmanmu bane mu zauna muna discussing akan wadancan garorinba, muyi abinda zai fishemu kawai" inji ta ukun mai suna Nuratu suna cemata Nurr

Tsaki kawai zee taja tana maida miqewa tsaye tareda sagale jakkarta tace
"6acin rai upon 6acin rai, nagudo school saboda 6acin ran gida Ashe ban tsiraba, mtcheew! Muje please in chanza waya bana iya zaman diff"

Duk tashi suma sukayi suna gyara zaman jakkarsu sumee nacewa
"Aikaudai, Ai gwara da kika barmashi wancan, kiyi me daita baya ya ta6ata da dirty stained hannunshi? Muje mudawo dawuri don mudafa lecture"

"Wane lecture?" Inji zee datayi gaba

"Na mutuminki" inji sumee tana dariya

Tsaki taja tace
"Na manta ma, shiyasa fa yau nace ban zuwa mummy ta chaza min kai tasa dole nafito"

Nurr dake dayan gefenta don tsakiya suka sata, sumee a gefen haggu nurr a na dama sai deeya da rukky dake bayansu

Nurr tace "Ai naga bakwa shiri da mutuminnan"

"Bashida mutunci Ai, shiyasa babu ruwana da lecture dinshi, text da exams dinshi kawai nakeyi shima don yazama wajibi"

Su nadeeya dake baya kau kallon bayanta suke cikeda haushi sunajin kamar su maketa, sosai hassada ke dawainiya da zuciyarsu, komai ta hada ga kyau ga iya gayu ga kudi

Badan abinda suke samuba awajenta da tuni anyi uwar watsi atsakanin su

"Mtcheew, how I hate this girl" inji nadeeya

"Hmm ke ke fadi anaji" inji rukky

"Mtcheew ni wlh sumee tamafi bani haushi, sai wani zaqalqalewa take, cusa kai ba qwarjini kawai" inji deeya

"Hmm Ai shiyasa kikaji ban tankaba, don wani abin takaicin hanaka magana yake amma ke naga alamun wulaqancin ta be damun ki don da kanki kike saye" inji rukky tana yin qas qas da chewing gum din bakinta

Duk maganar dasuke ahankali sukeyi suna biyeda su zee din abaya

"Hmm Ai wani abin kasa yin shiru nake saboda haushi, who did she think she is dazata mari yaron Master kamar Alex!"

Wani makirin murmushi rukky tasaki na gefen lips tace
"Nikuma dadi naji, gwara tafara ta6a wadanda zasuci ubanta, su maidota hayyacinta, wlh kinji na rantse kuma bazanyi kaffaraba, bazasu ta6a kyaleta ba, badai rawar kai da girida ba, zata gani, zata gane mummunar qaddararta yasata schooling a school dinnan ba UK din datake cikamana kunne dashiba, wlh Master saiya dauki mummunan mataki akanta don shirunsa ba alhairi bane kuma bazai ta6a zama alhairi ba, zatasan ta jangwaloma kanta"

Itama deeya murmushin jindadi ya bayyana a face dinta tace
"Kumafa hakane, Allah yasadai karya shafemu muma"

Yar dariya rukky tayi daidai sun iso motar nurr kasancewar itama tanada ita don ba laifi suma sunada hali, tace
"Karki damu, we're free"

Dukda su zee sunji wannan Kalmar saidai basusan inda ta dosaba hakan yasa basu maida kai ba suka bude murfin motar, nurr a mazaunin driver zee a gefenta sai kingin dasuka shige baya.

Tada motar nurr tayi sannan suka fice daga school din...✍️


Ummin fasihu🧚🏻‍♀?
8/2/21, 9:31 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂DEEN🙍🏻‍♂?*



*003*



Miqamashi ruwan gora mai sanyi Gandu yayi ya amsa ya 6alle murfin yashiga kwankwada

Saida yakusan shanyewa sannan ya janye baki yana kwarama kanshi kingin ruwan

"Hmm Ai na gayamaka, yarinyarnan idonta tsakar kai yake kaqi yarda, ga irinta nan ka zubarwa kanka mutunci a bainar jama'a" inji gandu

Furzar da huci Alex yayi mai zafi kana yace
"Wlh baxan bari taci bulus ba, sainayi gunduwa² daita, wlh saina sauyamata kammani yadda ko uwarta data haifeta bazata shedeta ba" yaqarashe zancen yana huci

Dariya wani da ake kira t.j yayi yace
"Daga baya kenan Ai, wannan Ai ihu bayan hari kakeyi, lokacin data wankeka yakamata kayi wannan burgar"

Cikin jin haushi Alex yace
"Wlh ba don Master ya dakatar daniba babu abinda zai hanani lallasa Yar iska, Kutt! Ni wlh sai yanzu abin ke qara bani haushi" yafada yana cizon yatsa

Duk dariya suka fashe daita harda Master din wanda hakan yaqara qular da Alex din

"Kai amma fa yarinyar nan tasha dakai, kawai sai gani nayi tayima fyal! Ta falleka da mari, yasin sautin Marin har inda muke tsaye" inji wani wai shi Bash

Dariya suka qara saki wanda hakan ba qaramin kaishi bango yayiba

"Wlh tlh na rantse da wanda ya busan numfashi saina rama, a tsakiyar school zanci mutuncin ta al-qur'an, wlh tajama kanta bala'i"

"Kasan ko diyar waye?" Inji t.j cikin dariya

"Ko diyar uban waye be shafeniba don ubanka, wlh sainajawa iyayenta asara" yafada cikin tada jijjiyoyin wuya

Master ne ya tashi yaje ya zauna kusadashi yana murmushi ya dafa kafadarshi guda yace
"Ya kakeji a zuciyarka yanzu?"

Jin tambayar yayi kamar ma ta rainin hankali, ko makaho ya lalluba ai yasan ranshi a matuqar 6ace yake

Hakan yasashi yin banza ya kyaleshi yacigaba da hucinshi

"Karka damu, zaka rama. Da ace na barka a lokacin ka rama da tuni an wuce wurin ka sauke fushinka saidai Kaine da faduwa don bakasanta ba bakasan ubantaba, wlh ubanta na iyasawa a daureka har igiya tayi rara, yana iya sa a 6atar dakai amance da babinka kaga wa gari ya waya?"

"Bayan wannan ma yanzu waya cemaka ana dukan mace? Wawa ke dukan mace, mace dakeda hanyoyi birjik na ramuwa marar gogewa a kwakwalwa? Duka abune mai zafi ga duka mutane biyun da abin yashafa Wato mai duka da wanda ake dukan, ta mareka, kai datayiwa Marin kaji zafi hakama itama datayi taji zafi amma a zuciya kaima idan ka rama haka zakaji, why not kayi ramuwar da ita zataji zafi, zafi marar misaltuwa, zafin gangar jiki da ruhi. Abangarenka kuma dadi zakaji, dadi marar misaltuwa, dadin gangar jiki da ruhi, ya kaji kafcen?"

Alex da tunda master yafara magana ya kafeshi da mini minin idanunshi, bama shikadaiba harda sauran mutanen dakin suma sun bada hankalinsu kacokam gareshi suna saurarenshi

"hakanma chakwai ne boss, wlh abinda ya dace daita kenan, kutt! Amma fah za'a kwashi kayan dadi anan" inji t.j yana kada kai


Dan kama le6en qasa Alex yayi ya cije yana kada kai shima yana hasaso abin a qwalwarshi

"amma fa bashi kadai ba yakamata ya ramaba master, yakamata mu tayashi ramuwar don nuna kishin ta6amana Dan uwa da akayi" ya qarashe cikin dariya ganin yadda Alex yadago yana watsamashi harara


"ji Dan iska, wa aka mara wa ke kukan zafi? To kwalelenka, tawace ni kadai, wlh saita yabawa aya zaqin ta, b***a uba! Wlh ketata zanyi inyi yaga yaga daita, wlh saitafi wata bata iya zamaba, ca6! Zan tattakura inmata eh yane" yafada yana dunqula hannu yana wani wawwanashi


Dariya duk suka sa gandu yace
"kaji dan air, To wlh bakai kadaiba, muma saimun kwashi romonta mu shar6e mai gangarowa" yafada yana lasan lips

Bash yace
"ato gwara daka gayamashi, donmu ba itace bane dazamu barka da ita kai dayaba, harda mu wajen ramuwar yadda nan gaba bazata qara qaunar ganin namijiba, koya kace boss?"


Murmushi master yayi yace "kwaret! Don nine nan zanfara shigewa sannan ku ku biyoni abaya, na dade ina tarata dama, tunda na dora idona kanta naji ko ana menene saina danata, saina jagula abinda take taqama dashi, dama kawai nake jira kuma tana gab da zuwa, zan kashe qishirwar da nadade ina tarawa akanta" yafada yana cizon baqin lower lip dinshi daya dusashe don zuqe2


"To yanzu master yaushe zamu far mata?" inji Alex cikin zaquwa

"very soon, kawai dama zamu jira ta bayyana kanta saimuyi amfani daita, bawai gaggawa zamusa ba don aikin gaggawa na tareda danasani, ahankali zamu lalla6a harmu samu yadda mukeso, mu dasa mata mikin da baxai ta6a gogewaba a zuciyarta"

Duk shewa sukayi irinna yan tashan nan sunama master din kirari yayunda shikuma ya jingina da kujera yana sakin wani munafikin Murmushi

"Allah yakai damo ga harawa!" inji Alex da yanzu yake jinshi wasai duk wani fushin shi ya yaye

Ameen dukkansu suka amsa dashi sannan suka cigaba da firarsu wanda duk na zainab ne



*TUSHEN LABARI*


Zainab diyace tallin kwal ga attajirin dan kasuwa Wato *Alhaji Farouq Dan faranshi*

Alhaji Farouq mai kudi ne sosai kuma sannane ne a jahar katsina dama kewayenta.

Matarshi daya mai suna *Maimuna Abdullahi* barumiya kyakyawa

Diyarsu daya a duniya itama dakyar da sudin goshi suka sameta kasancewar tanada fragile womb duk cikin data dauka be kaiwa koina yake 6arewa, Dakyar suka samu cikin zainab ya tsaya shima sosai tasha wahalarshi don yasha yunqurin zubewa amma dayake Allah ya qaddarta zayazo duniya sai ta tsallake amma fa dakyar.

Bayan haihuwar Zainab ma tayi 6ari sau uku, ganin haka yasa suka yanke shawarar suje ajuya mahaifar don Maimuna ta huta da wahalar hakanan


Haka kau akayi, aka juya mahaifarta suka dawo suka maida hankalinsu kacokam akan gudan jininsu daya da Allah yabasu

Soyyaya sosai suka dauka suka dorama zainab, riritata suke suna tattalinta kamar gwal, basa qaunar abinda zai ta6amasu sanyin idaniyarsu

Zainab ta taso cikin gata da kulawa ta munsanman, tana samun gata ta kowane bangare, iyayenta basuda wani buri aduniya daya wuce su farantamata amatsayinta na diyarsu daya jall


Ahaka tafara girma aka sata private school din boko dama islamiyya

Makarantar datake zuwa na masu dashi ne sosai don idan kaji school fees din saika riqe baki

Ahaka akaita rarrafawa tun zainab bata fahimtar gatar da ake mata har abin yafara shiga kanta

Ahankali ahankali tafara tsiro halaye daban2, tafara sangarcewa tana yin abinda taga dama

Tun abin be damun mummy(Maimuna) harya fara damun ta don sosai ta tsiro da halin wulaqanci ga na qasa dasu kai harma daidai dasu

Tun mummy na kauda kai har abin yafara isarta tafara tsawatar mata

Sosai take mata jan ido idan tayi abu ba daidai ba wani sa'in har ta hada da duka saidai daddy kwata2 beson haka don shi aganinshi yarinyace qarama quruciyace

Hakan yasa suke yawan samun sa6ani dashi don ita acewarta bazata zuba ido yarinya ta sangarce ba


Zainab kau duk da yadda mummy ke qoqarin tsawatar mata taga ta saitu ina? Yadda kasan tirata ake don abin sai qara gaba2 yake wanda Hakan yasamo asaline asanaddiyar goyon baya da daddy ke bata

Wulaqanci har na saidawa take dashi, yan aikin gidansu sukafi tantance hakan don bata ragamasu ko kadan dukda ga lokacin bata wani girma ba

Kuskure kadan mutum zaiyi ta wankeshi tass baruwanta da yawan shekarunka

Akwai ranar da tasa wata yar aikinsu ta kawomata ruwa, garin miqamata hannunta ya kwa6e yazubarmata ajiki

Batayi wata wata ba ta dauke mai aikin da mari wanda hakan yayi daidai da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login