Showing 1 words to 3000 words out of 332344 words

Chapter 1 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14350

??ࡱ?>?? 8?????????????? ?
?
? ?
?
???????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????<

 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Root Entry???????? ?F?WordDocument????1470Table????????8Data
???????????????????? P?92KSKS?147????????rr????w??D?? ??$w?)*r??????S??S?S??? ?^`????^Normal d??,CJmH sH nHtH_HOJPJQJ^JaJTA`????TDefault Paragraph FontOJPJQJ^Jfi`????f Table Normal :V ?4?
l4?a? OJPJQJ^J(k`????(No List ?=T| Arewabooks@nanahaleema11.

Didi ta yi saurin katse Omar ta hanyar hana shi magana ta ce, "Omar!." Yadda ta yi maganar ya saka ya dakata ya kalleta ita kuma ta kalli Hajja ta ce, "Hajja don Allah ku bani dama nayi magana dashi a keSance, Ina so nayi masa bayani akan wacece Nayla sosai da alama bai gane wace ba. Don Allah Daddy" ta faWa tana kallon Daddy. Daddy ya ce, "An baki dama Aisha, amma karku jima kin ga dukkan mu jira mu ke yi" ya kalli agogon hannunsa ya ce, "gashi har dare ya yi."

Didi ta ce, "in sha Allah." Ta ?araso kusa da Omar ya ri?o hannunsa ta ce, "taso mu yi magana."
"Maganar me zamu yi? In maganar ce ma a nan ya kamata ayi a gaban kowa."
"Na sani, ka taso mu je" ta faWa tana jan hannunsa dole ya mi?e ya bi bayan ta ba dan yana so ba.

Sai da suka yi nesa da falon dan ta san muryarsa da shegen amon yanzu sai su jiyo abinda yake cewa. ?wance hannunsa ya yi ya ce, "Didi ki bari komai ya ?are mana, ki bari a warware komai tun a yau." Didi ta kalle shi gabanta ya faWi ganin Sacin rai a kwance akan fuskarsa, har jijiyoyiin kansa sun tashi saboda yadda ransa ya Saci. Ta san in ransa ya Saci bazai saurarenta, kuma za a kai ruwa rana kafin ya tsaya ya ji abinda zata ce ma kafin ya saurareta.

"Omar!." Bai kalle ba hakan ya saka ta ce, "Kar ka furta kalmar saki a kan Nayla, koda a zuciyarka ne bana so ka furta ka saketa balle kuma kalmar tazo kan harshenka. Ka karSeta a matsayin matarka ta sunna don Allah." Kawai zubawa Didi ido ya yi yana kallonta dan bai ma san me zai ce ba. ?are mata kallo yake yana tunanin anya itace kuwa? In kuwa itace Win kamar yadda idanunsa sauke gani tabbas Didi ta sha ?waya.

"Don Allah kar karSi auren nan, kar ka saketa a yanzu ko nan gaba. Abinda nake so dakai koda mahaifinta ne da kansa ya kiraka ya ce maka ka saketa kar ka saketa, ka karSi aurenta, in yaso komai sai ya jiyo baya."

"Anya Didi kin san abinda ki ke faWa kuwa?."
"Na sani Omar, cewa nayi ka karSi auren nan kar ka saketa." Sake zuba mata idanu ya yi kafin ya ce, "Nidai nasan bakya shan ?warya balle nace ko itace ta taSa miki hankalinki, ban sani ba ko zama da mijinki ya Wan saka kin rasa kaWan daga cikin hankalinki, dan kalaman ki basu yi kama da na wacce take cikin nutsuwarta ba."

Didi ta ce, "kome zaka ce ka ce, nidai ka yi min wannan alfarmar don Allah." Bai ce komai ba sai yawo yake yi da idonsa akan fuskarta. Didi ta kuma cewa, "Alfarma nake nema a matsayina na Yayarka, jininka, ?ar uwarka Waya tal a duniya, kar ka juya min baya don Allah, kar ka bani kunya." Kai ya girgiza yana taSe baki ya ce, "bazan karSa ba Didi, gwara na faWa miki gaskiya bazan yaudareki ba. Kin san bana Soye-Soye, dan haka bazan Soye abinda yake raina ba."

"Omar saboda ni zaka yi."
"Bazan yi saboda ke Win ba! Didi bazan yi ba. Bazan karSi auren da bana so ba, bazan karSi auren da ban san yarinyar ba, bazan karSi auren da ban san ma anyi shi ba. Da me zan kira wannan auren in na karSa? Na dole ko na sadaka!?." Jin yadda ya fara yin mata magana cikin muryarsa mai shegen amon tsiya ya saka ta sassauta murya ta ce, "ka saurare ni, duk wannan zai biyo baya amma a yanzu kar ka ce baza ka karSi aurenta ba. Yarinyar nan bata da laifi, Allah kaWai ya san dalilin mahaifinta na aurawa maka ita, ransa ne ya Saci a lokacin har ya aikata haka, da alama akwai abinda ya Sata masa rai har ya yanke wannan hukuncin."

Ya bita da wani irin kallon up and down cike da harara kafin ya ce, "Dan kawai ran mahaifinta ya Saci sai ya Wauko ?afa daga wani gari yazo har garin nan, ya kuma rasa inda zai sauke Sacin ransa sai a kaina?. Munin halayena ne ya saka ya yanke hukuncin bani aurenta ko kuma meye?."

Didi ta ce, "ni dai koma meye kar ka ce baza ka karSi auren nan ba, ka zo mu koma" ta faWa tana niyar komawa, ya dakatar da ita ya ce, "ba fa zan karSa ba, bana son auren ban ce ina bu?ata ba. Su ri?e ?arsu, ban ce a Waura min aure da ko wacce yarinya ba."

Didi ta juyo a sanyaye ta ce, "Omar Didi ce fa take maka magana, ro?onka nake yi akan ka amince."
"Sanin ke Win ce ma ya saka na ke saurarenki, in ba dan ke Win bace da yanzu na sumar da ko wacece a wajan nan. Aure ne bazan karSa ba."
"Omar alfarma fa nake nema a gareka, baza ka iya yi min ba?."

"Bazan iya ba! Bazan yi ba Didi!. Zan iya yi miki ko wacce alfarma amma ban da wannan, ki canja tunaninki bazan karSi auren nan ba. Dan ma an raina min hankali a rasa da wanda za a yi mata auren sadaka sai ni? Kawai dan ni aka raina kaf cikin garin nan, ko kuma dan ni ne kawai mai mutum halin da za a yi mata hukunci ta hanyar aurar dani?."

Ganin yadda ya birkice lokaci Waya yana zazzaga mata masifa ya saka ta ri?e hannunsa ta girgiza shi,ta wara ido akan idanunsa ta ce, "Omaar kamar uwa nake a wajan ka, baza ka yi min abinda nake so ba?." Shima ya wara nasa idanun a cikin nata ya ce, "kamar uwa ki ka ce Didi, ai ba uwar ba ce. Bazan yi miki biyayya akan abinda baka so ba!."

Didi ta runtse ido ta buWe ta buWe, ta sauke numfashi ta kalle shi tare da kakkausa murya ta ce, "shikenan Omar ka yi abinda ka ke so, ka je ka aikata abinda zuciyarka take faWa maka. Amma ina so ka san abu Waya, na rantse da Allah in ka sake ka furta kalmar saki akan Nayla ka warware auren da yake tsakanin ku, ina so ka sani ka kuma shaida babu ni babu kai Omar!" Ta faWa tana nuna shi da yatsa cikin fusata.

Sak ya yi yana kallonta kafin ya samu damar magana ta sake cewa, "Eh! Ka ji abinda nace ai ko? To ina sake tabbatar maka in ka ?i karSar auren nan kar ka sake tunanin kana da wata ?ar uwa mai suna Aysha a rayuwarka, ka je can ka yi rayuwarka nima ka barni na yi tawa rayuwar. Ban sanka ba, kaima baka sanni ba, baka da ala?a dani, bani da alaqa dakai!."

"Didi akan auren da ban san shi ba, akan auren da bana so, akan auren da ban ma san yarinyar ba ki ke faWa min haka?. Babu ni babu ke fa ki ke cewa?" ya faWa yana kallonta da mamaki da ?unar zuciya.

"Eh Omar! Ba kuma iya yanzu ba, ko nan gaba in ka warwarwe aurenta da yake kan ka babu ni babu kai. In kana son farin cikina da cigaba da kasancewa matsayin ?ar uwa a wajanka kar ka furta komai a falon nan, in aka tambaye ka akan kana son zama da ita matsayin matarka ka amince, in ba haka ba wallahi babu ni babu kai, ka ji na sake maimaitawa!." Omar kallonta yake yi kawai ya rasa abinda zai yi, inda wata ce ba Didi ba tabbas da yanzu sai dai ko tana asibiti ko kuma a Wauki gawarta ta a wajan, amma Didi ce, Didinsa ce wacce yafi ?auna sama da komai a duniya, ya zai yi mata?.

Runtse iso ya yi gashin jikinsa gabaWaya ya mi?e saboda Sacin rai, fuskarsa ta koma ja sosai jikinsa har rawa ya ke yi. Didi ganin ya yi shiru sai ta ce, "Mun bar mutane suna zaman jiran mu, in tafiya zaka yi ka tafi Omar sai wata rana, Allah ya haWa fuskokin mu a aljanna. In kuma zaka biyo ni ka biyo ni."

Yawun Sacin rai ya haWWiye murya a ?asa ya ce, "Didi in na karSi auren nan bayan kin san bana so bazata taSa zama lafiya tare dani ba, kuma ke kanki kin san bana yin ?arya dan wani ya ji daWi balle nayi ?aryar zan ?arbeta matsayin matata a gaban iyayenta, in na karSi auren nan na ?arya ne domin kuwa bana so."

Didi ta kalle shi ta ce, "Omar ai ban hana ka ba, ga hanya nan. Ko ka biyo ni mu koma ciki, ko kaje a sauka lafiya, Allah ya haWa fuskokin mu inda rabon zamu sake haWuwa" ta faWa tana fara takawa zuwa cikin gidan cike da tsoro da zullumi. Zulluminta Omar zai biyo bayanta ko kuma zai zaSi ya rabu da ita?. Bata ji motsin ya biyo ta ba, hakan ya saka ta lumshe ido hawaye yana sakkowa daga idanunta ta yi sauri ta goge sannan ta shiga ciki.

Duk suka bita da kallo, ta yi murmushi ?arfin hali ta ce, "Ku yi ha?uri, mun tsayar da ku." Waje ta samu ta zauna a sanyaye tana tunanin abinda zai biyo baya. Ajiyar zuciya tayi ganin ya shigo yana takawa kamar baya so ya zauna a inda ya tashi. Murmushi da hawaye ya suSuce mata, ta san Omar bazai taSa zaSar rabuwa da ita ba, zai iya ha?ura da komai dan ya zauna da ita.

Daddy ya ce, "To Omar me ka yanke? Ka karSi auren nan ko kuma baka karSa ba?." Runtse ido ya yi cikin ?unar rai da Sakin ciki haWi da zallar Sacin rai. Wai shi Oamar aka saka a gaba ana yi masa zancen auren da bai ma san dashi ba, ko matar da ake i?irarin matarsa ce bai santa ba.

Daddy ya ce, "Kai mu ke saurare Omar dere yana yi, ka karSi auren nan ko a'a? Ka karSi Nayla a matsayin matarka ko a'a?." Hannu ya saka ya shafa fuskarsa ya kawar da kai gefe, idanunsa har ruwa ya tara saboda Sacin rai da rashin mafita. HaWWiye yawu ya yi da?yar ya Waga kai alamun eh.

Mama Sa'adatu tayi ?aramin tsaki dan ba haka taso ba, gabaWaya halayen da yake nunawa ya saka ta ji bata son ya amince da auren, bata son inda Nayla zata sha wahala. Hajja ta saki murmushi ta ce, "Omar kana nufin ka karSeta a matsayin matarka?." Kamar ya kwashe Hajja da mari haka ya ji, shi fa ya tsani ya wuce a dawo dashi baya, tunda har ya Waga kai ai ya amsa lallai sai an sake tambayarsa?. Da?yar ya jure ya sake Waga kai alamun eh.

Daddy ya ce, "magana zaka yi mana Malam Omar, baza mu fahimce ka ta hanyar Waga kai ba." Wallahi ba dan girman Daddy da yake ji a zuciyarsa ba babu abinda zai hana bai yi ashar ba, amma ya danne Sacin ransa ya ce, "Eh." Abba ne ya ce, "eh me? Eh ka karSa kenan?." siririn tsaki Omar ya yi dan kuwa wallahi bazai sake magana ba sai dai ayi abinda za a yi.

Didi da ta san halin kayanta tana kuma lura da duk motsinsa sai ta ce, "Ya amince Abba, daman a rashin sanin wacece wacce ake kira da matarsa ne ya saka ya furta abinda ce Wazu, Amma da nayi masa bayani ya gane." Kowa na falon yana ganin yadda ya Wago ido yana kallon Didi, kana ganin kallon da yake mata kasan kallo ne na ji ?aryar da ki ke faWe. Ta kula da kallon da yake mata kawai ta Wauke kai bata sake kallonsa ba.

Daddy ya ce, "To Alhamdu lillah! Tunda wannan aure ya tabbata a yanzu sai magana ta gaba. Maganar gwajin jini da ake yi kafin aure saboda a tantance ciwon da yake cikin jinin su duka su biyun. Yanzu gashi dare yayi ba za a samu damar yin gwajin a yanzu ba, amma gobe in Allah ya kaimu za a kawo likita har g1da da zai gwada jinin Nayla da Omar domin tantance su."

Omar ya kalli Daddy da jajayen idanunsa sai dai ba shi Daddyn yake kallo ba, yana maimaita gwajin jini a zuciyarsa. Ah lallai zasu ga gwajin jini ganin idanunsu, dan babu wanda ya isa ya Webi jininsa sai dai kar ayi.

Daddy ya ce, "Omaar!." Ya Wago idanu ya kalle shi ta ?asan idanu ya ce, "Nayla tana aiki, duk da a Kaduna take aikinta amma za a yi mata transfer zuwa nan Kano, muna neman alfarmar ta cigaba da aikin ta a ?ar?ashin inuwar aurenka." Bai ma yi motsi ba balle ya masa, a zuciyarsa yana ta masifa ko ina ruwansa da aikin ta oho, in ma duniyar zata bari shi meye ya dame shi balle wani aiki?.

Daddy ya ce, "Kana da magana?." Omar ya yi shiru bai ce komai ba, to wacce magana yake da ita bayan Didi ta kulle masa baki? Me zai ce? Gwara ya yi shiru hakan zai fi masa alkhairi.

"Babu komai" ya furta a ta?aice cikin wata irin murya mai nuni da zallar Sacin ran da yake ciki. Didi ce kawai take fahimtarsa, amma dukkan su babu wanda ya san halin da yake ciki daga ita sai shi kawai, shiyasa motsi kaWan sai ta kalle shi dan ta san a wajan Omar dan ya watsa taron nan abu mai sau?i ne a wajansa.

Abba ya ce, "To ma sha Allah. Yadda aka Waura auren nan zuciya babu daWi Allah ya sa auren nan ya zama silar wanke ko wacce zuciya a nan wajan." Aka amsa da amin.

Ita Mama Sa'adatu abin sam bai mata ba, so tayi a raba auren kawai a huta ba a zauna ana jajjada aurensa da ita ba. Ita a kuwa Maman su Jidda ban da murna babu abinda take yi, tafi kowa shiga fargaba da ake tambayar Omar akan auren, da ace ya ce baya so sannan ya saki Nayla da bata san halin da zata shiga ba saboda ba?in ciki. Yanzu kam zuciyarta fess, yadda yake misbehaving a gaban mutane ya tabbatar mata da Nayla zata sha matu?ar wahala a zaman auren su.

Nayla tana zaune kamar mai bacci amma duk abinda ake yi tana ji, tana jin duk abinda Omaar yake faWa, da yadda yake magana kai tsaye ya furta baya son auren. Ido take runtsewa tana buWewa saboda ?unar da take ji a zuciyarta. Babu abinda ya fi tsaya mata a rai irin in ya furta wacece Nayla? Shi bai ma san wacce aka aura amsa ba. Abin yana tsaya mata a rai, sai tayi tunanin ita kuwa wanne laifi ta yiwa Abiy ya aura mata wanda baya ?aunarta?.

Mama Sa'adatu ce ta katse shirun ta ce, "Omar kar ka ga ta yadda auren nan yazo ka ga kamar sadaka aka baka Nayla, wallahi Nayla tafi ?arfin auren sadaka, da gatanta gaba da baya, ?addararta ce ta zo a haka ta kuma amsa kiran rabonta. Kar ka yi amfani da hakan wajan Sata mata don Allah, ka ri?eta hannu biyu marainiya ce mahaifiyarta ta jima da rasuwa. Ka martaba ta kamar wacce ka sha wahala a yayin neman aurenta."

_to auren meye in ba na sadakar ba? Ni na ce ina so ne? Sadakarta kawai aka bani kuma sadakar ma cikin tursasawa. Da ki ke zancen marainiya ce bata da uwa ni bani da uwa da uban ma._ Omar ya faWa a zuciya yana yiwa Mama Sa'adatu wani kallo da har sai da ta ce, "eh ka ke kallona, ka ri?eta hannu biyu don Allah." Idanu ya Wauke daga kanta, ita bata san haushin su yake ji bane shiyasa take wannan zubar.

Hajja ta yi murmushi ta ce, "Omar zo nan, kema Hauwa'u ku zo kusa sani." Omar banza ya yi kamar bai ji ba yana kallo Nayla ta koma kusa da Hajja ta zauna ya bita da kallo a ransa yana ko itace matar oho. Dan motsawa ya yi kaWan amma bai tashi ba. Hajja tayi dariya ta ce, "Omar mazan fama, mai hali baya fasa halinsa. Yi zaman ka kunnen ka kawai make so ka bani."

Hajja ta ce, "Ummaru ga Hauwa nan ka ri?eta hannu biyu, duk a yanayin da auren na ku ya zo amma na tabbatar da za ku ji daWin auren a nan gaba daga kai har ita. Ko kusa a raina bana kawowa auren nan naku rabuwa a yanzu ko nan gaba, domin babu wanda san abinda Allah ya Soye har hakan ya faru. Ka ri?eta da amana don Allah, ka bata duk kulawar da miji yake bawa matarsa.

 Hauwa! Kema ki yiwa mijinki baiyyya, kar ki yi tunanin a yadda auren ya riske ki, aure dai sunan sa aure, ko ya ki ka yi wani abun ba daidai ba mala'ikun Allah zasu rubuta miki zunubi ne. Kin fito daga gidan tarbiyya, kin kuma samu tarbiyayya da ilimi na addini, don Allah kar ki ba da kunya, ki ri?e aurenki da kyau kin ji?" Ta faWa tana shafa kanta.

Siraran hawaye ne suka sakko daga idanun Nayla, ko ta ya zata iya zama da Omar a matsayin miji oho. Bata san wanne karanbani ne ya kai zuciyarta fara sonsa ba, da bata fara sonsa ba da wata?ila hakan bai faru ba, da wata?ila tana nan hankali kwance bata da wata damuwa makamanciyar wannan. Hajja ta ce, "Allah ya ba da zaman lafiya, ya kawar da idanun ma?iya daga kan ku." Aka amsa da amin kafin Abba ya rufe taron da addu'a kowa ya shafa.

Daddy ya ce, "To ango, tare da kai zamu kai amaryar?." Wani irin dummm Omar ya ji a zuciyarsa, wai fa kenan ana nufin a gida Waya zasu zauna ko? TaS lallai da sake wai an saci zanin mahaukaciya.

Didi ce tayi caraf ta ce, "Daddy da kaina zan kawo shi in sha Allah." Daddy ya murmusa ya ce, "wato yadda ya kai ki kema zaki kai shi." Tayi dariya kamar yadda Hajja ma take dariya.

Tsam Omar ya mi?e ya fita ba tare da ya kalli


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login