Showing 42001 words to 45000 words out of 332344 words

Chapter 15 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14438

jifanta da shi a jikinta, tana jin kaifin idanunsa a jikinta kamar shigar allura cikin tsokar naman jikinta. Wannan yanayi da take ji ya saka ta ce,  Babu kowa.
 Na ce miki ina da bu?ata ne?.
 Baka ce ba.
 Meyasa ki ka yi?.
 Haka kawai ta bashi amsa a hankali dan wallahi a tsorace take, bata jurewa zama a inda yake ko kaWan, yanzu sai ta fita daga nutsuwarta.

 Ba a yin abu haka kawai dole akwai dalili, meye dalilin?. Nayla kamar zata yi kuka ta ce,  na faWa maka babu komai.
 Karya ki ke! Ya faWa kai tsaye ba tare da ya kalle ta ba. Nayla ta ji babu daWi a zuciyarta musamman yadda ya ?aryata ta lokaci Waya, ta kawar da kai a raunane ta ce,  Nayi ne dan na taimakawa kasuwancinka ya sake zuwa inda ba a yi tunani ba, bayan wannan babu komai.

Gira ya Waga zuwa sama yana taSe baki ya ce,  a matsayinki na wa kenan?. ?ago ido tayi a lokacin da suka fara tara hawaye ta kalle shi ta ga ba ita yake kallo ba, kafin ta janye idanunta ya kalle ta suka haWa ido ta sake mayar da kanta gefe. Hawayen ya sakko kan kuncinta ta goge ta ce,  A matsayina na ?ar uwarka musulma. Kuma kana matsayin Yayana, tunda ?anin Didi ne kai ta faWa a sanyaye.

 A a ni bani da ?anwa a duniya, iyayenmu mu biyu kawai suka haifa daga ita sai ni, ba a lissafo ki a cikin wanda suka haifa ba balle ki zama ?anwata. Gwara ki barshi matsayin ?ar uwa ta musuluncin, amma ba wai Yayanki ba. Ya faWa da wata irin murya mai nuni da gaskiyar sa yake faWa mata.

Nayla ta yi murmushin takaici bata ce komai ba, amma jin zuciyarta take tana bugawa sosai. Omar ya share ta kamar bazai yi magana ba kafin ya sauke ajiyar zuciya ya ce,  ko ita Didin baki san sai da izinina take shiga abinda ya shafe ni ba, balle ke mai kalen ?ar uwarta ce?. Zuwa lokacin hawayen da take ri?ewa ya fara sakkowa kan kuncinta. Omar ganin tana hawaye ya zuba mata ido yana kallonta cikin mamaki, to me yayi mata da zata yi masa kuka? Duka ko zagi ko cin fuska? Raini ne ko kuma wula?anci?.

Murya ya na rawa ta ce,  Allah ya baka ha?uri.
 Ke in ina magana dake kina yi min kuka wallahi wata ran sai na saka kin haWWiye ha?orin ki, sa an ki ne ni?!. Yadda ya yi maganar a kausashe ya saka ta kuma tsorata sosai ta tuna lokacin haWuwar su a gidan Didi.

 Ni dai ka yi ha?uri kawai ta sake faWa murya na rawa sosai. Ya kalle ta ya ce,  Ko nan gaba ba a shiga lamarina in ba ni na saka mutum ba, ki kuma faWa min kuWin da kika kashe na biya ki. Nayla ta Waga kai alamun gamsuwa ta ce,  ni ba sai ka biya& & 
 Ki faWa min kuWin! Ya faWa a tsawace yana zare idanu. Nayla ta ce,  To& .zan faWa. Sai nayi lissafi na manta.
 Bar nan!. Ai da sauri ta mike tazo wucewa ta inda yake zaune yana facing Winta, tsabar tsoro ?afar center table Win wajan ta jata tayi gaba ta faWa kansa da yake zaune akan kujera.

Babu zato yaji faWuwar ta jikinsa, ya rutse ido da sauri tare da jan numfashi jin lafiyayyen ?hamshin da ya kai masa ziyara hancinsa ya kuma zagaya ko wanne sashi na jikinsa. Nayla kuwa bata banbance a ina take ba sai bayan ta faWo kansa Win sannan ta gane halin da take ciki, da sauri ta mi?e bata iya magana ba ta wuce ciki a guje. Lumshe idanu ya yi bayan ta bar wajan, sai kuma ya ja tsaki tunawa da rainin hankalin da tayi masa kafin ta bar wajan, da kuma daren da ta kai a waje ba tare da ya san inda taje ba.

Nayla da tana shiga ciki ta dinga mita ita kaWai a zuciyarta, shayin da ta haWa ma ta barshi a falon kuma ba iya komawa zata yi ta sha ba. In ta tuna kalmarsa ta meye ma sunan ki yana sakawa taji babu daWi, amma bata bar damuwar tayi mata tasiri ba ta yi kwanciyar ta duk da tana ta tuna abinda ya faru.

Mamakin sa take yi sosai dan yanzu yana iya yi mata magana mai tsaho, duk da ba alkhairi ne yake haWa su ba amma yana yi mata magana har ya amsa gaisuwarta. Sannan bai cika yi mata magana a kausashe ba sai dai ya yi kamar yadda yake magana da Didi ba kamar farkon zamansu ba.

Washe gari ma da ta tashi daga aiki saloon Win jiya ta wuce aka yi mata black henna sannan ta shiga store tayi siyayya dan akwai abinda take so tayi. Tun daga wannan maganar bata sake ganin sa ba ma gabaWaya, sai dai taji motsin buWe ?ofa da rufewa amma bata sake jin koda muryarsa ba. Tana mamakin rashin amfani da kayan gidan da ba baya yi, hana rantsuwa ta san yana shan ruwa bayan wannan ko lemo bata taSa gani ya Wauka ba duk akwai a fridge sosai har da yourgut amma baya sha.

Ranar ashirin da tara ga watan ramadan ana e gobe sallah kenan kasancewar lahadi ce tana gida a kitchen ta shiga tana ta aiki tun safe. Tayi abubuwa da yawa wanda hakan ya kawo mata gajiya matu?a. Da yake da wuri ta fara zuwa biyar ta gama duk abinda take so. Bashir ta kira a waya ta ce ya zo gida zata bashi sa?o.

Bata san tare suka shigo da Omar ba ta fito da hijjabi tana cewa,  Bashir ance min an kai sa?o Kaduna jiya, ashe& . Maganar ta tsaya ganin sa tare da Omar da leda a hannun Omar Win. Wani irin dumm ta ji a zuciyarta, dan tun ranar ashirin da bakwai bata sake ganin sa ba kwana biyu kenan yau. Tana so tayi masa sannu da shigowa tana tsoron kar ya yarfa ta a gaban Bashir, ta daure ta basar ta ce,  Sannu da shigowa, Bashir Ina zuwa ta faWa a haWe tana komawa ciki ba tare da ta bashi damar amsawa ba.

Kallon sa Omar ya yi alamun ?arun bayani, da sauri Bashir ya ce,  Ta yi min waya ne ta ce na zo.
 Ta yi maka waya!? Ya maimaita zahiri ba tare da ya sani ba dan abin haka kawai ya daki zuciyarsa, wai tayi masa waya. Bashir ya amsa da,  Eh, ita ta kira ni ta ce na zo.

Bai sake magana ba ya share Bashir ya zauna ya buWe masa ledar da ya shigo da ita. Kaya yake sakawa yana haWawa waje Waya yana ware takalma. Omar ya ce,  Ku Wauki wanda ki ke so gida biyu ko wanne. Bashir ya murmusa ya ce,  Godiya mu ke yi Damisa, bayan kayan sallah da kuWin Winki harda takalmi? Allah ya ja da rai ya ji?an su Mama.

A iya baki ya amsa da amin a lokacin ta fito ta ce,  Bashir gashi. Tasowa ya yi ya karSi manya-manyan foil packs har gida biyar. ?aya doya da ?wai ce mai yawa a ciki da wata lafiyayyar liver sauce, Waya irsh potatoes ne aka soya, sai ?wai a kai da aka soya shima, Waya tosted bread ne mai yawa wanda ya sha butter sai ?hamshi yake yi. Daya kuma milk cincin ?anannu mai yawa, na biyar Win kuma lafiyayyar fried rice ce da gasashhiyar kaza guda a kai.

Ta ce,  Ku yi iftar kai da sauran. Murmushi ya yi y ce,  Godiya mu ke Antyn mu, Allah ya biya. Wannan kayan daWi haka? Godiya mu ke yi. Murmushi ta yi ta koma ta zuba lemo da yawa a leda ta kawo ta ce,  ga drink. Ya karSa yana ta godiya kafin ya kalli Omar da kamar bai san me ake yi ba. Bash ya ce,  Damisa Antyn mu ta yi mana kyauta, yau mu ka zan samu yi iftar dan da shan ruwa mu ke yi. Sautin murmushin ta ya ji hakan ya saka ya juyo kamar zai yi magana sai ya fasa ya sake Wauke kai.

Bashir ya sake kallon ta ya ce,  Antyn mu Boss ya yi mana kyauta, an yi mana Winkin sallah kowa guda biyu da kuWin Winki, sannan ga takalma an bamu. Kuma tsakiyar ramadan ya bada kuWi ya ce kowa ya kai gidan su, sannan ga sallamar azumi da aka yi mana mai kauri, a taya mu godiya, Boss ya yi mana komai a rayuwar nan. Nayla ta Wan yi murmushi tana aiyyana baka san ka fini daraja a wajansa ba shiyasa ka ke faWa min haka. Ta daure ta ce,  Kun gode.

 Kuma Antyn mu baki san wani abu ba ba, Boss fa mutane ne suke ganin sa haka, amma bala in sau?in kai gare shi, sannan& ..
 Kai!! Omar ya faWa cikin tswar da ta saka Bashir yin shiru yana kallonsa. Hannunsa ya juya alamun tambaya sannan ya ce,  Meye na maganar!? Ya sake faWa cikin tsawa sosai.

Bash ya ce,  Tuba nake.
 Fita! Ya faWa yana nuna amsa ?ofa Bashir ya mi?e sum sum sum ya fice.

Nayla zata bar wajan ta ji ya ce,  meye na biye masa kuna surutu? Bakya ganin Ina wajan? Sai an saka min ciwon kai?. Nayla jin yadda yake maganar a fusace sai ta kalle shi tana mamaki abinda ya fusata shi a cikin maganarta ko ta Bashir. Nayka ta ce,  ka yi ha?uri. Ta faWa ta koma ciki tana cewa,  masifaffe kawai.

Bata sake ganinsa ba sai gab da shan ruwa ta fito dining dan ranar a kai ta jera abinci saboda ta ci son ranta. Ta kuma yi aniyar yi masa tayi koda zai dizgata sai tayi, tana so ta samu lada tunda ramadan Win ya ?are, babu tabbacin zata kai mai zuwa da rai. Shigowarsa ta gani yana waya kamar ko yaushe, sai da ya gama wayar sannan ta ce,  Sannu da zuwa YaMar, Ga abincin shan ruwa na ajjiye maka, don Allah kar ka ce baka ci, kaga daga yau an gama azumi, don Allah! ta ?arasa faWa tana karyar da murya cikin shagwaSa. Yadda ta ce YaMar Win a haWe sai sunan ya bada wani salo mai dadi, ta cire harafin farko ta faWi na ?arshe, sannan ta haWe shi waje Waya da Yaya.

Omar abubuwa ne masu yawa suka haWar masa a lokaci guda suka daki zuciyarsa, sai da ya runtse ido jin abun da ?arfi kamar an saka abu mai nauyi an daki ?irjinsa. Na farko bai san meyasa indai zata ce masa Yaya Omar ba sai ya ji sunan har cikin ?ahon zuciyarsa, bai sani ba ko dan bashi da mai faWa masa Yaya ne sai ita Win shiyasa yake jin haka oho. Na biyu kuma yadda take yiwa sunan iyayi wajan faWa yana yi masa daWi, duk da ta bashi dariya dan gabaWaya bata iya furta harafin R ba, da ta ce Mar Win sai harafin R Win ya tashi kamar wani harafin daban ta faWa. Na uku yadda ta ke yi maaa shagwaSa tana wani kwaSe fuska ya dake shi sosai.

Kallon ta yayi ya ga ta sunkuyar da kai tana jiran amsarsa ya dake ya kawar da abinda yake ji ya ce,  baki faWa min kuWinki ba. Nayla ta Wago dan wallahi ta manta da batun kuWin, ta sake mayar da kai ?asa tana wasa da hannunta ta ce,  Na manta wallahi, amma zan yi lisaafin.
_Ji ta harda wallahi, ko meye na rantsuwar oho._ ya faWa a zuciyarsa ba tare da ya furta komai a fili ba.

Nayla ta ce,  Don Allah YaMar ka ci abinci yau. ?o?arin wucewa yake yi ya ce,  na ce ina so ne? Ba na ce babu ruwanki da lamarina ba?.
 Baka ce kana so ba, kyautatawa ce nake so nayi maka. Kuma kaga yau azumin ?arshe daga yau sai wata shekarar ga masu yawan rai. Wata?ila kafin shekarar ta dawo na mutu bana duniya, ka ga ko babu komai zaka tuna ka ce ranar azumin ?arshe na last year ni na baka abinci, kaga zan samu lada a cikin kabarina. Don Allah YaMar ta faWa a sanyaye.

TaSe baki ya yi ya wuce ciki Nayla ta yi ajiyar zuciya cike da mamakin sa da bai yi mata masifa ba,  ki cigaba da shige masa Hauwa, in ya make ki wata ran ke kika jiyo. Sai tayi dariya ta zauna akan dining din ta lumshe ido tana addu ar gab da shan ruwa.

Hawaye ya sakko mata tunawa da shikenan ramadan ya ?are, babu tabbacin zaka kai wata shekarar gashi ka yi azumin baka da tabbacin an karSi wanda ka yi. Rauni taji a zuciyarta ta dinga hawaye tana addu a har aka yi kiran sallar magriba. Ido ta goge ta sha ruwa ta yi ajiyar zuciya ta furta,  Allah ya maimaita mana. Cincin Win da tayi ta Wauka ta saka a baki tana ci kafin ta shiga ciki da niyar yin sallah.

(Addu ar gab da shan ruwa, addu a yayin shan ruwa mustajaba ce bata da hijjabi a wajan Allah. Ba sai axumin farilla ba ko azumin nafila ne in aka kai a daure a yi addu a ko ya take. Akwai falala mai tarin yawa a cikin wannan lokaci, sannan addu a bata da hijjabi da ka yi da Allah ya amsa. Allah yasa mu dace ya amsa mana dukkan addu ar mu amin.)

Shima ruwan ya sha sannan ya fito ganin bata falon bai neme ta ba ya fita dan yin sallah. Tana zaune tana shan tea ya dawo sai ta ga kamar bashi da lafiya dan gabaWaya kamar ba shi ba, fuskarsa ta Wan yi ja kuma jijiyar kansa ta tashi, idanun sa sun Wan yi ja kaWan, ga yanayinsa babu ?arfi sosai kamar mai zazzaSi. Rauni taji ya sake mamaye zuciyarta ganin ya zauna a falon ya jingina da kujera ya kulle ido.

Nayla zuciyarta umarni take bata ta je ta kai masa abinci, wani Sangaren na zuciyarta kuma yana hanata aikata hakan. ?arfin guiwa ta samu ta fara haWa tea, ta tuna Didi ta ce mata yana da shan madara sosai kuma yana shan sugar. Ta haWa tea Win da tosted bread ta haWa komai a tray ta tako a hankali ta ajjiye akan table Win da yake kusa dashi. Yana jinta amma bai motsa ba dan kansa ciwo yake yi sosai.

 YaMar ga abincin. Bai motsa ba balle ya kalle ta, ta koma ta zauna tana cigaba da cin nata amma gabaWaya hankalinta yana kansa har lokacin bai motsa ba. Sai ta ji abincin ya fita daga ranta ta taso tazo nesa dashi ta tsaya ta ce,  YaMar baka da lafiya? Ka ci abinci sai ka sha magani. Idanunsa a kulle bai ce komai ba amma yayi mamakin yadda ta fahimci bashi da lafiya lokaci Waya.

 YaMar! Ta sake faWa a hankali a tausashe. Idanu ya buWe ya kalle ta ganin yadda idanunsa suka yi ja sai gabanta ya faWi a rikice ta ce,  YaMar baka da lafiya ko? Idanun ka sun yi ja sosai, Ciwon kai ka ke yi?. A hankali ya janye idanun sa daga kallonta ya mayar da ido ya rufe. Sallama ta ji ana yi ta kalli wanda ya shigo da alama aiken shi ya yi shiyasa ya bar ?ofar a buWe, ta amsa sallamar. Tk ya shigo ya ce,  Sannu Damisa, ga maganin ya faWa yana ajjiye masa a kusa dashi.

Kallon Nayla ya yi ya ce,  Antyn mu mun ga sa?o, Allah ya saka da Alkahiri. Da amin akwai ta amsa dan gabaWaya hankalinta yana gare shi. Ajjiye wata ledar ya yi ya ce,  Ba a samo ayaba, amma ga apple Win nan. Daga haka ya fita daga falon.

Maganin ya Wauka zai sha da sauri ta dakatar dashi ta ce,  Don Allah ka sha koda tea ne in yaso sai ka sha maganin, babu abinda magani zai maka bayan tun jiya baka ci komai ba ta faWa kamar zata yi kuka tana kallonsa.

_Ya Allahu! Me yarinyar nan take son mayar dani ne? GabaWaya ta shiga rayuwarta na rasa meyasa nake jin maganarta har cikin kaina._ ya faWa a zuciyarsa jin maganar Nayla har cikin zciyarsa. Nayla ta Wauki tea Win ganin bai ce komai ba ta mi?a masa ta ce,  Ka sha don Allah. Ji yake kamar ya karSa ya watsa mata a jikinta, tabbas da Omar Win da ne abinda zai aikata kenan, amma yanzu ya rasa meyasa yake jin abinda yake ji akan yarinyar.

 Don Allah YaMar ka karSa! Ta sake faWa a sanyaye tana sake mi?a masa. Kamar wanda aka bawa umarni ya mi?a hannu ya karSa kamar yadda take bashi. Da yake babu zafi sosai tunda ta Wan jima da haWawa ya kai bakinsa ya sha a hankali. Duk da bashi da lafiya amma tea Win ya yi masa yadda yake so, ya yi mamakin yadda ta iya haWawa daidai da ra ayinsa.

Nayla ganin ya shaa sai taji farin ciki ya mamaye mata zuciya, rana ta farko da ya ci sha wani abun na cikin gidan bayan ruwa. Zata iya cewa abu na farko kenan ma da ya fara amfani dashi a gidan shine mug Win hannunsa.

Ri?e tea Win ya yi bai sake sha ba, ya rufe ido ya jinginar da kansa a jikun kujera. Nayla ji take kamar tayi kuka saboda rauni, ta zuba masa ido tana kallonsa kamar ta cire ciwon ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login