Showing 198001 words to 201000 words out of 332344 words

Chapter 67 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

30870

suka fara kokawa, ya kaiwa Tk sara ya kauce, ya sake kai masa sara ya sake kaucewa.

Jijiyar wuyansa Tk ya daka da ?arfi, take ya tafi luuu ya zube a ?asa a wajan. Tk ya Wauki waya tare da Waukar hoton fuskarsa ya kai kallonsa ga Nayla da take yashe a wajan numfashin tana yana sama da ?asa. Da sauri ya ?ara kusa da Nayla ganin yadda jini yake tsiyaya daga hannunta ya ce, "Antyn mu, taso na kai ki asibiti."

Nayla jin maganar take yi a sama, ?irjinta yana bugawa tsoro ya gama dabaibaiye mata zuciya. Jikinta rawa yake yi, ga azabar da hannunta yake mata ga tsoro da tashin hankali.

Tk ganin bata cikin hankalin ta ya kalli hanyar, har lokacin babu kowa sannan ga wanda ya sumar a sheme a wajan. Ya du?a ya ce, "Antyn mu ki taso mu tafi, kina zubar da jini sosai, kina bu?atar ganin likita."
"Wayyo Allah! Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Na shiga uku, hannuna, jini ne yake zuba" ta faWa a firgice dan maganar Tk kamar farkar da ita tayi daga mafarki.

Tk a gigice yake, so yake ya kaita asibiti saboda jinin da take zubarwa, in wani abun ya same ta ya san mai gidansa bazai Waga masa ?afa ba. Ganin haka sai ya ce, "Antyn mu Didi bata nan, ki zo na kai ki asibiti, zaman ki a nan babu tsaro, komai zai iya faruwa dake a wajan nan. Ki nutsu mu tafi asibiti don Allah." Nayla kuka take yi cikin azabar ciwon da take ji, ta nuna masa hanya ta ce. "sun ?wace min wayata, wu?a ya Wauko yana nuna min. Sun....sun....cire min hannu."

Tk ya runtse ido, ya Wuka ya ri?o hannunta duka biyun zuciyarsa na bugawa, ji yake kamar yaci amanar Tiger da ya ri?e hannun matarsa, amma babu yadda zai yi, taimaka mata yake so ya yi, ri?e ta Win yafi barinta a wajan. Ya ce, "Antyn mu ki nutsu don Allah, ki zo mu tafi asibiti" ya faWa yana buWe mata motar. Kasa tashi tayi, sai da ya Wagota sannan ta iya tsayawa tana jiri, kamar mai taSin hankali haka ta shiga motar ya ja da sauri suka bar unguwar.

?? Yana so ya bata waya tayi blocking bank account Winta amma ya san bata cikin nutsuwarta. Kuka kawai take yi tana ri?e hannunta da yake zubar da jini dan ba ?aramin yanka suka yi mata ba. Asibitin da Didi ta haihu ya kai ta, ganin yadda aka ji mata ciwo sai yace masu ?wacen waya ne suka ji mata ciwo. A take aka karSe ta aka yi mata allurar TT. Ana dressing wajan tana kuka mai sauti saboda azaba, bata cikin hankalin ta gabaWaya, azaba ce take ratsa jijiyoyin jikinta. A lokacin Omar ya shigo wajan, suna haWa ido da ita ya sakar mata banzar harara wacce ta saka ta sake fashewa da kuka.

Nurse Win da yake mata dressing Win ya ce, "Ciwon ya yi zurfi, dole ayi mata Winki." Omar ya sauke numfashi yana kallon yadda take hawaye, hijjab Win ta duk ya lalace da jini dan sai yanke hannun hijjab Win aka yi aka fito da ciwon. ?auke kai yayi daga kallon ta, yana jin zuciyarsa kamar zata fito saboda tashin hankali da tausayinta.

Zama ya yi a kusa da ita fuskarsa a Waure ya ri?e ta a jikinsa, ta kwanta a jikinsa tana kuka mai sauti. Kanta yaji da zafi sosai alamun ciwon kai, ya sauke numfashi bai ce komai ba saboda bazai iya magana. A haka aka yi mata Winki tana kuka, kwantar da ita aka yi a asibitin saboda zazzaSin jikinta aka saka mata ruwa. Yana zaune a gefenta yana kallon ta tana sauke ajiyar zuciya cikin rashin nutsuwa, allurar da aka yi mata ya rage mata raWaWin da hannunta yake mata.

Tk ne ya shigo Wakin cikin sanyin jiki ya kalli Omar ya ce, "tuba nake Tiger, na gaza bata kariyar da ya kamata." Omar ya kalle shi da jajayen idonsa ya Wauke kai. Bai ce komai ba, kai ya girgiza yana haWWiye yawu mai Waci, ya Waga masa hannu kawai dole Tk ya fita.

A haka baccin ya Wauke Nayla, ya yi ajiyar zuciya ya mi?e ya dafa goshinta zuciyarsa cike da jin haushinta da kuma tausayinta. Tausayinta yake ji dan ya san bata taSa tsintar kanta a wannan yanayin ba, sannan haushinta yake ji akan laifin da ta yi masa. Ba jimawa Didi ta zo asibitin, ganin yanayin yadda hijjab Win Nayla ya lalace da jini ya saka ta kuka, ya kalle ta da idanunsa da suka ?an?ance saboda Sacin rai ya ce, "ki daina kuka kar ta tashi, ki zauna da ita zan je na dawo" ya faWa muryarsa a dashe saboda damuwa.

Didi ta goge ido ta ce, "me ya faru haka Omar? Waye ya ji mata ciwo haka?."
"Ki zauna, zan je na dawo" ya faWa yana sake dafa goshin Nayla. Hijjab Win jikinta ya cire mata ganin tana gumi, ya kalli inda aka ji mata ciwon yaga tsahon yankan tun daga guiwar hannunta har tsintsiyar hannunta. Ya sauke numfashi ya fita bai kula Didi ba.

Ya jima bai dawo ba, sai goma na dare sannan ya dawo ya ce Didi ta wuce gida zai kwana da ita. Didi suka wuce da mijinta bayan ya saka Bashir ya yi musu rakiya, dan a yanayin da ake ciki komai zai iya faruwa.

A haka suka zauna shi da ita, sai cikin dare ta farka suka haWa ido taga irin kallon da yake mata sai ta Wauke kai dan ita wallahi tsoronsa take ji ba kaWan ba. Sauka tayi daga kan gadon ta shiga banWaki. Alwala tayi tana so tayi sallah amma babu mayafi, shi kuma babu fuskar da zata yi masa magana. Ganin haka sai ya fita dan ya je gidan Didi tunda babu nisa, yana fita suka haWu da mijin Didi ya kawo masa abinci da kuma kaya a leda. Komawa ya yi ya ajjiye mata bai ce mata komai ba. A tsorace ta Wauka ta saka hijjabin tayi sallah.

Wayarsa ya mi?a mata ta kalle shi suka haWa ido, ya Waure fuska ya ce, "ki yi blocking bank account Winki." A sanyaye ta karSa da hannunta da babu ciwo ta yi ta ajjiye masa wayar. Bai sake ce mata komai ba sai abinci da ya nuna mata. A yanayin da yake ciki babu damar yi masa musu, dole ta Wauka taci kaWan ta ajjiye. A haka suka kwana shi da ita, washe gari ba a sallame su da wuri saboda zazzaSin da ya rufe ta, sai gab da magrib suka wuce gida bayan an bata magani.

Tana zaune a falo tana kallon hannunta, abinda ya faru ya dinga dawo mata cikin kanta tsoro ya sake mamaye mata zuciya. Jin ta take yi kamar ba ita ba, ji take kamar ta gudu Kaduna ta huta da tashin hankali. GabaWaya zaman Kano ya fita daga ranta, zama da Omar ya fita daga zuciyarta gida take so ta koma ko hankalinta zai kwanta.

Omar ne ya shigo da sallama, ta amsa a ciki tana Wago kanta. Kallo Waya tayi masa gabanta ya faWi, abinda ya faru a daren shekaran jiya ya faWo mata a rai musamman yadda yanayinsa ya canja mata ya koma mata na wancan Omar Win da ta sani.

?? A hankali ya tako ya zo inda take, ya bita da kallo cike sa tausayi ganin yadda ta rame lokaci Waya, duk ta firgice kamar ba ita ba. Ya Wauke kai daga kallon ta, ya daure ya kawar da tausayin ya ce, "Dan baki da hankali, baki da tunani zaki fita ki bar gidan nan ba tare da na sani ba? Ba sai da na ce miki kar ki je ko ina ba?." Nayla bata san ta mi?e tsaye ba, jikinta ya cigaba da rawa tana jan numfashi da?yar ta ce, "tsoron gidan nake....." wata irin zabura ya yi ya Waga hannu kamar zai mare ta ya ce, "wallahi Allah ki ka ?arasa sai na mare ki!." ?uf tayi, numfashinta yana neman Waukewa tana kallonsa a tsorace.

"Uban meye a gidan da zai baki tsoro? Dah ba a cikin sa ki ke zama ba?. Dan kin raina min hankali sai ki Wauki ?afa ki bar gidan nan ba tare da na sani ba, a irin wannan yanayin da ake ciki da an kashe ki fa!?. Kalli ciwon da aka ji miki, da sun same ki a inda zasu kashe ki fa!?" Ya faWa cikin faWa yana nuna mata ciwon hannunta. Tsoronsa ne yake tsirga mata, jinin shekaran jiya kawai take gani a jikinsa, ga wanda ya nuna mata wu?a ya ?wace mata waya, ga wanda ya sare ta har jini ya dinga zuba, sai abin yayi mata yawa.

"Dan kinga ina sakar miki fuska shine raini zai shigo ko? In ba dan kin samu dama ba har kin isa ki bar gidan nan ba tare da na sani ba?. Kuma dan tsabar rashin hankali ki hau abin hawa na haya ki bar gidan nan ba tare da nace ki je ba. Yaushe ki ka raina ni haka?." Bakinta yana rawa tana kallonsa ganin ya canja mata gabaWaya, soyayya da tausayin da take gani a idanunsa yanzu duk ya gushe. ?are masa kallo take yi tana tabbatar da wannan ba Rouhii ta bane, Omar Tiger ne na gidan Didi. Ganin ta?i magana ya saka ya ce, "ba magana nake miki ba!."

"Ni ban....rai....na.....ka......ba" ta faWa a rarrabe tana kallonsa
"Iskanci ne kenan? Iskanci ne ya saka ki ka fita daga gidan nan ba tare da izinina ba ko?."
"Na yi maka....text..." ta sake faWa murya na rawa.

"Da ki ka yi min text na baki amsa?." Ta girgiza kai alamun a'a ya ce, "raina ni ki ka yi kenan?." Ta fashe da kukan da yake cin ranta ta ce, "A'aaaaaa!" Ta ja kalmar da ?arfi tana kuka mai sauti.

Ya girgiza kai yana nuna ta da yatsa cikin jin haushin ciwon da aka ji mata ya ce, "in kika sake wannan gangancin mai raba ni dake sai Allah, wallahi duk ranar da ki ka kuma aikata wannan ganganganci sai na saSa miki kammani ta yadda babu wanda zai iya gane ki." Ya bita da harara sannan ya ce, "ki wuce ki Wauki abinci ki ci." A zabure ta nufi inda ya nuna mata ta Wauki robar abincin da ya yi order daga Leemars_delicious tana ci tana kuka. Yana tsaye a kanta dole ta dinga tura abincin ba dan tana jin daWi ba, ya bi ciwon hannunta da kallo tausayinta yana sake shiga jikinsa. Bai nuna mata ba, sai da ta ci rabi sannan ya sake jan tsaki ya bar wajan.

Yana barin wajan ta Wora hannu a kai ta fashe da kuka ta ce, "Na shiga uku ni Nayla, na auri Wan daba!" Ta faWa cikin fitar hayyaci.
KRB3P073
Nanahaleema.


? ? ? Nayla bata san lokacin da ta Wauka a wajan ba ta ji an taSa ta, wata irin zabura tayi ta mi?e sai taji an ri?e kafaWarta Didi ta ce, "Nayla ni ce, nutsu." Nayla da take a gigice ta ce, "Didi!."
"Na'am Nayla, ki nutsu. Kar ki fama ciwon hannun ki." FaWawa jikin Didi tayi ta rungumeta tana sake faahewa da kuka.

Cikin tausayinta Didi take shafa bayanta ta ce, "Ki daina kuka Nayla, ki nutsu kin ji?.." cikin kuka ta ce, "Didi jini ne a jikinsa, da daddare aka zo aka dinga buga gidan nan ana cewa in ya isa ya fito" ta Wago daga jikin Didi ta ce, "Shine....shine.....ya Wauki wu?a ya fita. Ina zaune ya dawo jikinsa duk jini, Didi jini ne a jikinsa da alamun ya yi faWa da wani. Tsoro nake ji Didi, ki Wauke ni daga gidan nan, tsoronsa nake ji. GabaWaya ya canja, baya jin tausayina, sai faWa yake yi min, har ya Waga hannu zai mare ni" ta faWa tana sake komawa jikin Didi tana kuka.

A sanyaye Didi ta ce, "Ya isa, ki nutsu ki daina kuka. Kinga baki jima da dawowa daga asibiti ba." Zaunar da ita Didi tayi ta bata ruwa ta sha tana ri?e da hannunta tana kallon ciwon da aka Winke. Sai da ta nutsu sannan ta ce, "ki yi ha?uri, ki dawo hankalinki." Nayla ta ce, "da naje gidan ki shine aka ?wace min waya, aka ji min ciwo a hannuna."
"Ki yi ha?uri, ki daina kuka" ta faWa tana dafa kafaWarta cikin rarrashi. Nayla ta koma sauke ajiyar zuciya zuciyarta tana bugawa sosai.

"Didi!" Omar ya furta cikin dashewar yana shigowa falon. Wani irin tsalle Nayla tayi ta faWa jikin Didi ta ?an?ame ta. Omar ya bita da kallon takaici, ganin yadda take rawar jiki in ta ganshi kamar ta ga abun tsoro yana bashi haushi sosai, ita bata san haushinta yake ji ba take sake tsiro da abinda take tunzura shi. Ya tako ya finciko hannunta mai lafiya, ya rabata daga jikin Didi yana girgiza ta ya ce, "Ke ni Dodo ne? Meye a jikina da yake baki tsoro!" Ya faWa yana jijjigata. Luuuu Nayla ta tafi ta kife a ?irjinsa, ya Wago ta a gigice yana bubbuga fuskarta ya ce, "Jidda!."

Didi cikin faWa da fusata akam halinsa ta ce, "ka sumar da ita hankalin ka ya kwanta. Wai me yake damun ka ne? Ciwo aka jiwa yarinyar nan fa, wannan faWan da ka ke yi mata na meye?." Bai kula Didi ba hankalinsa yana kan Nayla, ya kwantar da ita a kan kujera ya Wauko ruwa aka yayyafa mata. Ya kalli Didi a sanyaye ya ce, "Didi ta suma fa, mu je asibiti."
"Ba dole ta suma ba, wannan Waga mata murya da ka ke yi kamar ba matar ka ba. Ka san ba lafiya ce da ita ba, ka duba ciwon hannunta mana. Sai ihu ka ke mata kamar ba kai ba." Tsaki Didi tayi ta ?arbi ruwan hannunsa ta sake shafawa Nayla a fuska. Nayla ta ja numfashi a hankali, a hankali ta buWe ido tana kallon Didi.

Didi ta ri?e hannunta ta ce, "Ki nutsu Nayla, ina tare dake." A hankali take jan numfashi tana kwance a jikin Didi. Ya bita da kallo yana sauke numfashi cikin yanayin da yake nu?ur?usar zuciyarsa. Tausayinta yake ji sosai, amma haushin ta fita bai sani ba har tsautsayi ya same ta ya danne tausayin, gani yake da bata fita ba da hakan bai faru ba.

Shiru suka yi babu mai magana, Didi tana shafa kan Nayla a hankali, Omar ya jawo stand fan ya kunna mata iska tana kaWata. Sun kwashe mintina talatin a haka har bacci ya kwashe Nayla.

Sai da baccin nata ya yi nisa sannan Didi ta zame jikinta ta saka mata pillow, ta ri?e hannunsa suka dawo babban falon ta bishi da kallo ta ce, "Omar faWa ka yi shekaran jiya? Jinin wa take magana ta gani a jikinka?." Omar ya Wan yi tsaki ya ce, "ni ban yi faWa da kowa ba."
"To jinin wa ta gani a jikinka? Meyasa ka Wauki wu?a ka fita? Me wu?a take yi a gidan nan Omar?. Sannan waye ya jiwa Nayla wannan ciwon? Ya akayi waWannan abubuwan suka faru?" Ta faWa a sanyaye tana kallon sa.

Ya Waga mata hannu ya ce, "Kinga Didi, kar ki sake tunzura zuciyata na aikata abinda zan yi dana sani, ki ?yale ni naji da abinda yake raina."
"Bazan ?yaleka ba wallahi. Wanne irin faWa kayi da har matarka ta firgita da kai haka Omar? Meyasa ka ke son dawo da abinda ya wuce? Meyasa ka ke son lalata hanyar da aka jima ana gyaranta sai yanzu gyaran ya kammala?. Omar meyasa zaka biyewa zuciya?."

"Mtsww! Na faWa miki ba faWa nayi ba, ni ban yi faWa da kowa ba, ki yarda mana!" Ya faWa cikin masifa yana kallon ta. Didi ta ce, "me ya kawo jini jikinka in ba faWa kayi ba? Me ka yi da wu?a Omar?."

"To Didi faWan nayi, nayi faWan sai me?. Har gida aka zo ana yi min wula?anci, ni ake Wagawa murya har ana cewa in ban fito ba naji tsoro, ni ake cewa in ban fito ba na ja da baya. Bana taSa ja baya, bana taSa jin tsoron ko wacce halitta a duniyar nan!. Tunda da salon da suka dawo kenan mu je zuwa, ina nan yadda nake ban canja ba!. Tunda suka yi kuskuren taSa lafiyar matata babu wanda zan bari, zasu san ja da baya ba tsoro bane" Sai ya yi ?asa da murya ya ce, "Ko kura ta rame ta wuce rainin karnuka wallahi! Akan a taSa min ku zan iya salwantar da rayuwar ko waye!."

Didi ta fara hawaye ganin Omar Win shekarun baya yana ?o?arin dawowa, dan har maganarsa ta canja ta koma ta Omar Tiger da ta Wauka ya jima da mutuwa, sai gashi ya dawo yana tsaye a gabanta. Kafin ta yi magana ya ce, "Jidda suka tura a kashe, Jidda suka yi ?o?arin kashewa shine silar ciwon hannunta. Tunda aka taSa min lafiyar matata har ta zubar da jini babu wanda zan ?yale wallahi!."

Didi cikin kuka ta ce, "Omar ka rufa mana asiri, don Allah ka yi ha?uri kar ka koma rayuwar da ka bari don girman Allah!" Ta faWa cikin kuka mai sauti. Ya bita da kallo kafin ya ja tsaki ya ce, "kina nufin na bar wanda suka taSa min Jidda kenan? Sun yiwa banza ko Didi..?" Ya yi ?wafa yana girgiza kai yana binta da kallo kafin ya ce, "kin cika min kunne, bana son kuka" ya faWa yana bata waje.

Didi ta zube a wajan tayi kuka son ranta, ba kowa ne yake bata tausayi ba sai Nayla, bata san hawa da sauka ba an fara ?o?arin kashe ta a karo na biyu. Sai da ta gaji da kukan sannan ta koma wajan Nayla taga har lokacin bacci take yi. Ta kira mijinta a waya suka wuce gida dan ta san bazai saurareta a yanzu ba, zuciyarta cike da tsoro da fargaba dawowar Wabi'ar Omar.

Shima da ya koma wajan Nayla ya koma, ya zauna a gefenta ya Wora kanta a cinyarsa yana shafa kanta. Hannunta mai ciwon ya kalla yan jin wani irin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login