Showing 54001 words to 57000 words out of 332344 words

Chapter 19 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14394

ita kuma ta shiga cikin gidan da sallama. Abinda bata saba gani ba ta gani, shine a zaune a falo amma lissafi ya ke da alama kuma lissafin ya sha kansa sosai. Sallamar da ya amsa ma bai Wago ba lissafi yake bugawa da wayarsa yana sake duba littafin da take tunanin a ciki yake rubuta komai. ?arasowa ta yi ta kalle shi ta ce,  Ina yini. Bai kalle ta ba ya ce,  lafiya. Daga nan ya Wauka zata ?yale shi ganin abinda yake yi sai bai sake cewa komai ba.

Nayla ta ce,  Na je gidan Hajja na yi mata barka da zuwa. Yayi mata banza bai ce komai ba, Nayla ta ce,  ga sa?o ta ce a baka.
 Bakya ganin abinda nake yi ne!? Lallai sai kin yi magana!? Ya faWa a faWace yana kallonta. Nayla da ta firgita a sanyaye ta ce,  yi ha?uri, Hajja ce ta ce na baka ta faWa tana ajjiye masa ledar ta tashi ta koma ciki.

Tsaki ya yi ko kallon ledar bai yi ba ya cigaba da abinda yake yi yana mita a zuciyarsa. Sai da ya gama ya lissafa ribar da aka samu daga fara aikin zuwa yanzu, da abubuwan da aka kashe, da wanda aka siya ya ga an samu riba fiye da tunaninsa. KuWin sun ninka sun sake ninkawa, domin kuwa tabbas sai ya fitar musu da zakka, babu abinda zai cewa Allah sai godiya domin kuwa lokaci kaWai ya kai inda bai yi tunanin zuwa ba.

 Ya kamata na samu Didi na ji abinda ya kamata ayi ya faWa a bayyane cikin tsananin jin daWi, ko a mafarki bai Wauka zai mallaki abinda ya mallaka yanzu ba. Shiyasa yake ?o?arin kyautatawa ma aikatansa ko yaushe, shiyasa suke son aiki dashi dan bayan albashi haka kawai zai yi musu kyauta. A bayyane ya sake cewa,  Zan tambaya naji kuWin sun kai tsahon lokacin da za a fitar da zakka. Kallon abinda ta ajjiye ya yi kamar bazai Wauka ba sai kuma ya Wauka bai buWe ba ya tashi ya shiga Waki zuciyarsa cike da farin ciki.

Bayan Kwana biyu.

Ranar ta kama rana asabar, Nayla tana gida babu aiki tana kwance a Waki ciwon kai ya dameta. Mai aikinta ce tayi mata komai har tea ita ta dafa mata sannan ta tafi tunda ba kwana take yi ba.

Bata san yana gidan ba har azahar ashe ranar bai fita ba yana cikin gida yana hutawa. Ta fito falo tana shan tea ta ganshi ya fito daga Waki suka haWa ido. Tunda ya yi mata tsawa ranar da ra dawo daga gidan Hajja basu sake haWuwa ba sai yanzu. Nayla ta ce,  Ina yini. A iya lallaSansa ya amsa, ba dan kallon sa take yi ba baza ta fahimci ya amsa ba.

Fita ya yi bakin gate, lokacin rana ta buWe sosai har sai da ya kare fuskarsa da hannunsa saboda ranar, hango Didi yayi a cikin adaidaita sahu a zaune tana jiransa, ya ?araso inda take ya ce,  wai baza ki shigo ba?. Didi ta ce,  sauri nake yi, bani key Win gidan mu

 Me zaki yi a ciki?. Didi ta ce,  YallaSai ne ya yi tafiya, ka san kuma yanayin unguwar ta mu bazan iya zama ni kaWai ba, shine ya ce na taho cikin gari in ya dawo sai na koma. Bani key Win na tafi na tsayar da mai mota. Ai su Bashir ba a nan suke kwana ba ko? Na ji kwnaaki ka ce min sun daina zama a gidan.

Wani irin kallo yake yi mata na ta ma raina masa hankali ya ce,  wai kina nufin a can zaki dinga kwana?. Didi ta ce,  eh mana.
Omar ya harare ta ya ce,  Meye amfanin nan da baza ki zo ba?. Didi ta wara ido da mamaki ta ce,  Omar ni fa Yayarka ce ba ?anwa ba, kawai sai nazo gidan ka da ka ke zaune da matarka na zauna? Haba wannan ai bai dace ba. Ka bani key Win naje na gide na zauna, in kuma baza ka bani ba na tafi gidan Hajja.

Ya girgiza kai cike da jin haushi jin amsar da ta bashi ya ce,  Oh! zaki iya zama a gidan Hajja, Hajjan da babu dangin uwa da uba amma baza ki iya zama a gidan da nake biyan kuWin hayarsa ba ko?. Dariya Didi ta yi tana tunanin wannan wacce irin Wabi a Omar yake da ita, wato bazai ce gidansa ba sai dai gidan da yake biya kuWin haya zai ce.

Didi ta ce,  Gaskiya bazan zauna ba, tunda muna da na mu gidan zan je can na zauna. Omar ya Waure fuska yana girgiza kai ya ce,  wallahi indai baki shiga gidan nan kin zauna ba bazan sake kwana a cikin sa ba har abada. Kin ji kuma na ce wallahi, babu wata halitta da ta taSa karya min rantsuwa a duniya. Kin san kuma zan iya yin abinda na ce, amma in kina ganin bazan iya ba ki tafi Didi ya faWa yana bar wajan.

Didi ta ce,  Innalillahi wa inna ilahir raji un! Wannan wanne irin yaro Allah ya haWa ni dashi?.

 Hajiya sauri nake yi ki sallame ni mai adaidiata sahun ya faWa yana kallonta. Didi ta ce,  yi ha?uri ta faWa tana Wauko kuWi ta bashi ta fito daga ciki ta rasa mafita.

Allah ya sani bata son kwana a gidan dan gani take yi zata takurawa Nayla ita kuma bata son faruwar hakan. Matsayin uwa take a wajansa, haka kawai sai ta shiga gidansa ta ce zata kwana bayan tana da inda zata iya kwana?. In kuma bata shiga ba tunda ya ce ya daina kwana a gidan wallahi ya daina, ta san halin kayanta in and out, ita kuma so take aurensa da Nayla ya daidaita, in bata shiga ba yadda ya rantse ya kenan?.

Ajiyar zuciya tayi ta Wauki ?aramar jakarta ta ?arasa bakin gate Win. Ashe yana tsaye daga ciki yana kallonta, ?iris yake jira ta tafi ya shiga ya tattaro kayansa dan bazata karya masa rantsuwa ba. Kafin ta ?arasa sai gani tayi ya buWe mata gate Win tare da karSar jakar hannunta dan cikin jikinta ya fito sosai.

Harararsa ta yi ta ce,  Wallahi ka cika rigima, ina ni ina zama a gidan nan don girman Allah? Wannan ?arfa-?arfa da me tayi kama?. Wato a nan ka ja tunga kana jiran tsammani ko?. Shi dai bai kula ta har cikin falon. Nayla tana tsaye a Inda take har lokacin tana goge dining glass Win.

Jin muryar Didi ya saka ta juyo ta ce,  Didi! sannu da zuwa ta faWa da fara a tana takowa tazo inda Didin take. Didi ta bi ta da kallo ta ce,  Nayla baki da lafiya ne?. Nayla ta yi murmushi ta ce,  Eh Didi, ciwon kai ne yake damuna sosai.
 Ga fuskarki nan har ta Wan kumbura kamar wacce ta yi kuka. To ki je asibiti mana wannan ciwon kai yan damun ki.
 Ranar Monday kafin na tafi aiki zan biya in sha Allah. Sannu da zuwa.

Didi ta ce,  Yauwa Nayla, Zauna kar jiri ya Wauke ki. Nayla ta zauna kusa da Didi ta ce,  Sannu da zuwa Didi. Didi ta amsa ta kalli Omar da yake tsaye ta ce,  Bata da lafiya shine baka faWa min ba?. Kallon Didin ya yi ba tare da tunanin komai ba ya ce,  ban sani ba.

Didi ta ce,  ta ya zaka sani tunda baka so ka sani ba?. Ta sake kallon Nayla da take murmushi ta ce,  Wai fa YallaSai ne ya yi tafiya zai yi kwana biyu baya cikin gari, shine nazo ya bani key Win gidan mu naje na zauna. Nayla ta Wan buWe ido ta ce,  ke kaWai a gidan? Meyasa baza ki zauna a nan ba?.

Didi ta kalli Omar da yake tsaye har lokacin, ta kalli Nayla ta ce,  Nayla Omar fa ?anina ne, ke ma ?anwata ce, ta ya ina matsayin uwa a wajan ku zan Wauko ?afa na zo gidan nan na ce zan kwana don Allah?.

Nayla tayi dariya ta ce,  Didi to meye a ciki? Mahaifiyar Mama tana kwana gidan mu na Kaduna kafin ta rasu. Kuma ni ai ba ba?uwa ba ce ba Didi, zaman ki a nan zai yi min daWi fiye da yadda ki ke tunani, na tabbatar in ki ka zauna a ranar zan fara jin daWin zaman gidan nan. Don girman Allah ki kwana a nan Win, in kuma ba haka ba mu koma can gidan sai mu kwana tare.

Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce,  Ubana ma ai ya yi min dole, harda rantsuwa kuma yana faWa min baya karya masa rantsuwa, dole na amince ko bana so. Nayla tayi dariya jin daWi ta ce,  YaMar ya kyauta, ya yi daidai. Yanzu me zaki ci?. Didi da murmushi ta ce,  haWe min kai zaku yi kenan? Shi yana tsaye ?i?am kamar soja. Nayla ta ce,  ni dai yanzu ki faWa min me zaki ci?.

 Keda baki da lafiya ina ke ina girki? Ki bari in zan ci zan girka da kaina. Nayla ta zaro idanu ta ce,  ki yi girki a gidan nan? Ai bazai yu ba Didi. Yanzu ki ka ce matsayin uwa kike a gare mu, kuma sai na bari ki yi girki? Lallai bani da kunya ta faWa tana dariya kafin ta ce,  Ni fa ganin ki har ya saka na daina jin ciwon kan ta faWa tana tashi ta shiga ciki.

Didi ta bita da kallo tana murmushi kafin ta kalle shi ta ce,  yarinya bata da lafiya baka damu ka sani ba ko Omar? Yanzu in wani babban ciwon ne fa? In wani abun ya same ta wallahi kai kanka baza ka ji daWi ba. Ka gyara zaman nan naku don Allah, ba dan komai ba ko dan saboda lafiyarta. Bai ce komai ba amma shi kansa bai ji daWi ba a ransa, in ya tuna yadda ta dinga lallaSa shi tana bashi tea hakan yana yi masa daWi a lokacin, shima zai so ya kula da lafiyarta kamar yadda ta kula da tashi.

Basarwa ya yi yana kallon Didin ya ce,  nima ai bani da lafiyar yana gama faWar hakan ya wuce zuwa Waki.

Didi tashi tayi ta bi Nayla kitchen ta same ta a tsaye kamar mai nazari, ganin Didin sai ta ce,  Yauwa Didi, me zan girka miki?. Didi tayi murmushi ta ce,  duk abinda ya yi miki.
 A a, ina so na san abinda ki ke so, meye favorite Win ki?.
 Ki dafa Omar s favorite, nima Ina so. Nayla tayi ?ar dariya ta ce,  har na tuna lokaci da ki ke faWa min yana son jellof rice, pasta, indomie and awara. Yanzu ni me zan dafa?.

Kafin Didi tayi magana ta ce,  okay, let me prepare some delicious jellof rice for my Didi ta faWa tana Waukar waya tana danne-danne. Ba jimawa ta ajjiye ta ce,  kin ce jellof dWin mai kifi ko?. Didi ta yi murmushi ta ce,  ba sai kin saka ba, a ina za a samu yanzu?.

 Akwai inda nake order, yanzu zaki ga an kawo min. Didi ta bi kitchen Win da kallo cikin burgewa, yana nan tsaf dashi sai ?hamshin turaren wuta yake yi ta ce,  kitchen Winki very neat Nayla. Murmushi tayi bata ce komai ba ta fara haWa kayan girki.

Gyaran kayan miya ne bata ?auna, ta Wan yamutsa fuska ta ce,  I hate this wallahi, a gida ko me zan dafa bana gyarawa sai dai a yi min. In ba haka ba sai dai na ha?ura da cin ko meye. Sai ta bawa Didi tausayi, ta san Nayla ?ar gata ce ajin ?arshe, komai yi mata ake yi a gidansu amma gashi ta ?are rayuwarta a haka. A sanyaye Didi ta ce,  kawo na gyara miki. Nayla ta wara ido ta ce,  So ki ke unborn ya fara jin haushina tun yana ciki? A a bari zan yi da kaina. Waya aka yi mata sai ta kalli Didi ta ce,  Kin gani, rider Win ne yake kira yanzu zasu kawo.

?aukar wayar tayi tana bashi address, ba jimawa ya sake yi mata waya ta fita ta je ta karSa ta dawo. Didi ta kalle ta bayan ta ajjiye tana buWewa ta ce,  meyasa ki ke siya da kuWin ki? Ai ha??in Omar ne ya siya ba ke ba.

Nayla ta ce,  Didi ni ba siya nake yi ba fa, dan ni bai dame ni ba gabaWaya. Kuma ni bana siyan abu sosai, da azumi ne akwai na siya kaji shima sai gab da azumin zai ?are sannan na siya.
 Duk da haka dai Nayla. Nayla tayi mumurshi bata ce komai ba, Didi ta karSi gyaran kifin ta dole ta ta bata ba dan ta so ba.

Viniger ta bawa Didi ta karSa ta gyara kifin su na ta hira cikin nishaWi. ?an ri?e kai Nayla tayi alamun ciwo Didi ta ce,  ciwo ko? Sannu Nayla. Na ce ki ji ki huta amma kin ?i, gaskiya ya kamata ki je asibiti a duba aga meye yake kawo miki wannan ciwon kan, kina yawan yinsa. Nayla ta ce,  Ranar Mondy zan je in sha Allah, Ko ma azumi bazan Wauka ba ranar.

 Ai gwara haka, Allah ya ?ara Lafiya.
 Amin Didi.
 Kina da ?o?arin azumi Nayla, kina burge ni sosai saboda kina da ri?o da ibada sosai.
 Bana jin wahalar azumi, na riga na saba in ba ban yi ba bana jin daWi. Yanzu haka na gama sitta shawwal kuma har wanda ake bina na yi.

Didi ta ce,  kin yi ?o?ari sosai. Allah ya kar nan gaba Omar ya hana ki azumin litinin da Alhamis Win nan, ko da yake ma ai kina wajan aiki ba yini ki ke a gida ba. Nayla da mamaki ta ce,  Kawai sai ya hana ni ibada Didi?.
 Eh mana, baki san maza suna hana mata yin azumi ba?.
 Na sani, akwai cousin Wina itama haka take kamar ni, amma da tayi aure ta daina. Har ta kan cemin tana so ta cigaba amma mijinta ya hanata
 Ashe ma kin sani Didi ta faWa tana ajjiye abinda yake hannunta.

Nayla ta ce,  To wai Didi meyasa suke hana azumi? Ba sa so ana yin ibadar ne ko me?. Didi tayi ?ar dariya ta ce,  ba haka bane, kawai saboda shiga ha??in su ne. Nayla ta Wan yi jim kafin ta ce,  Kamar ya shiga ha??i? Kawai dan mutum yana azumi sai ya shiga ha??in wani?.

Didi ta sake yin dariya ta ce,  Zamu jira mu gani, in har Omar ya hana ki yi zaki fahimci me nake nufi, in ma bai hana ki Win ba ma zaki gane.

Nayla ta ce,  no, ina so na sani yanzu.
 Zaki sani Nayla, faatana da burina Allah ya daidaita zaman ku. Nayla tayi ajiyar zuciya Didi ta cigaba da taya ta aiki tana murmushi. Zata so ganin ranar da Nayla da Omar zasu zama ma aurata kamar kowa, zata so ta ga irin so da ?aunar da Omar zai nuna mata, zata so ta ga tattali da riritawar da Omar zai gwadawa Nayla. Kuma zata iya rantsewa Omar yana daga cikin mazan da zasu iya hana Nayla yin azumi, ba dan komai ba sai dan za a shiga ha??insu. Haka kawai take ji a ranta hakan zai faru, ba dan Omar Win ya faWa mata ko wani dalili ba, haka kawai ta san da?yar hakan bai faru ba.

Nayla ta kalli Didi ganin tana murmushi ta ce,  Didi wallahi you re so beautiful. Didi tayi dariya ta ce,  Nayla ban da tsokana.
 Allah kuwa, Da na ga Anties Win ku sai na tabbatar da gadon kyau ku ka yi dan dukkan su ma sha Allah. Ashe ma halfcast ne ku
tunda dangin Mama ?an Chad ne, Shiyasa ku ke da kyau. Kin san anyi analysis babu wanda ya kai halfcast kyau a duniya.

Diid tayi dariya ta ce,  Omar dai yana da kyau amma ba ni ba.
 Ai kuna kama dashi sosai, ana ganin ki a san ke jinin shi ce.
 Kama ta jini ba, amma Omar da mahaifiyar mu yake kama completely. Manyan idanu kawai ya fita, idanunta na da girma sosai itama kawai na shi ya fi nata ne sosai. Tana da kyau sosai, tana da kyaun da ake kira kyau shiyasa Omar da ya gadota ake kallonsa in ya shiga waje. Zan nuna miki hotonta zaki gani.

Nayla tayi murmushi ta ce,  Allah ya gafarta musu. Didi ta amsa da amin suka cigaba da hira har suka gama girkin tsaf suka wanke kayan.

Didi ta kalle ta ta ce,  Tunda naga har wata apron ki ke sakawa a kitchen Win, cire ta mu je mu ci abincin. Nayla tayi murmushi tana kwance igiyar apron Win ta ce,  bana son Sata kayana ne.

Didi ta ce,  jeki ki shafa turare a jikinki da hannunki ki dawo. Nayla bata musa ba ta fita taje ta dawo. Tana dawowa ?hamshin turaren ya shiga hancin Didi tayi murmushi ta ce,  turaren kam akwai ?hamshi, kin san kifi yanzu sai ya ma?ale miki a jiki. Na kai abincin falo na ajjiye, na ji dawowar Omar daga


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login