Showing 210001 words to 213000 words out of 332344 words

Chapter 71 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14364

Win da zai tafi da ita.

Tare suka fito falo, Didi ta mi?e tana kallonsu tana murmushi cikin burgewa ta ce, "Ka fito?." Kai ya Waga ya kalle ta ya ce, "Na fito Didi, ki taya ni da addu'a." Didi ta ce, "Allah ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya, ya baka abinda ka je nema."

Murmushi ya yi yana kallon ta, ya saki hannun Nayla ya ri????? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?e na Didi duka biyun ya ce, "Amin Yaya Aisha, Duk abinda ki ke so ki faWa min kar ki ce bana nan baza ki faWa min ba, in wani abun ya taso na Marmerh ki sanar dani. Sannan ban da yawo ko ina musamman da daddare, bana so wani abu ya same ki. Didi tayi dariya jin sunan da ya kira ta dashi ta ce, "To Yaya Omar, in sha Allah." Ya kalli Nayla ya kalli Didi ya ce, "ki kular min da amanata Didi, da ke kaWai na yarda na bar ta a hannunki, kar ki bari ta dinga wannan kukan kin ji?."

Didi ta ce, "in sha Allah Omar, zan yi duk abinda zan yi wajan tayata farin ciki."
"Na san zaki yi Didi." Ya shafa fuskar Marmerh da take bacci, ya kalli Nayla da take hawaye ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Yaushe zaki tafi gidan Daddy Win?." Cikin dauriya ta ce, "In anjima" ta faWa murya na rawa sosai. A tausashe ya ce, "Don Allah ina ro?onki kar ki dinga fita ke kaWai, duk inda zaki je in dare ya yi kar ki ce zaki yi driving ki bari a kai ki. Ina so naje na dawo na same ki lafiya, bana so wani abun ya same ki kin ji?.

Nayla ta Waga kai alamun to, ya tako ya zo inda take ya ce, "in kina kukan nan sai na ji kamar na fasa tafiyar nan, gabaWaya tafiyar ta fita daga raina wallahi, a haka kike so nayi farin ciki in kina kuka?. Baki ga Didi bata kuka ba?." Sake shiga jikinsa tayi tana sauke ajiyar zuciya, ya yi murmushi tare da rungumeta idanunsa a kulle kafin ya sake ta ya Wagota daga jikinsa ya ri?e hannunta ya ce, "Zan tafi."

Ta goge hawayen idanunta ta ce, "Allah ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya."
"Amin Ashiq, Ki yi min alqawarin baza ki cigaba da kuka ba."
"Ban yi alqawari ba, ni kaWai? na san me nake ji a zuciyata."
"nima ni kaWai na san abinda nake ji, amma na yi ha?uri kema ki yi kin ji?."
"Bazan iya ba."

Murmushi ya yi ya kai bakinsa kusa da kunnenta ya ce, "Aljanun da suka tashi jiya a wannan yanayin na baki ajiya Allah yasa ki karSa, so nake kafin na dawo na ji an ce ajiyata ta yi ?wari, har Didi ta san na baki ajiya Wanta." Murmushi tayi mai sauti ta rufe ido ya ja hancinta ya ce, "kunyar ce ko?." Murmushi take yi ta ce, "in dai ka bada ajiyar da kyau na karSa, in kuma baka bayar yadda ya kamata ba laifina ba ne."

"Bara na faWawa Didi a ji laifin waye." Ta wara ido ta ce, "Rufa min asiri, kar ka faWa mata don Allah."
"To na rufa miki, amma sai kin yi dariya na gani." Sai kuwa ta yi dariyar ya juyo inda Didi ta ke ya ga bata wajan ya kalli Nayla ya ce, "kin ga kin saka na za?e da yawa a gaban Didi, gashi ta gudu."

Nayla ta ce, "Allah babu ruwana, laifin ka ne."
"Laifin ki dai." Ta kalli agogo ta ce, "Mu je na san su Bashir suna jiranka." ?aukar jakar ya yi ya ri?o hannunta sai ta turje ta tsaya ta ce, "Rouhii!." Ya juyo ya kalle ta ya ce, "Na'am Ashiq! Me ki ke so?." Ta matso kusa dashi ta ce, "to ka Wan rage tsaho ka yi min tsahi da yawa."

Bai ce komai ba ya Wagota jikinsa ya rabata da ?asa, ta yi kissing Winsa kamar yadda ya yi mata Wazu. Idanunsa a lumshe ta kalle shi ta ce, "Ina sonka Rouhii." Ya lumshe ido ya ce, "Ina sonki Ashiq!." Murmushi ta yi ya direta a ?asa suka fito tare, a nan suka tarar da Didi suna hira Bashir ganin fitowa su ya saka suka karSi jakar aka saka a mota.

Didi ya kalla ya yi murmushi itama murmushi tayi, ya kalli Nayla ya girgiza mata kai alamun kar ta yi kuka. Bata yi kukan ba sai ya Wauke kai daga kallon ta, ya kalli manyan yaransa da suka zo yi masa sallama duk suka gaisa sannan ya shiga gaban motar Goje da Tk da sabon yaronsa Mustapha suka shiga baya suka fita daga gidan.

Nayla tare suka koma da Didi, ta yi ?o?ari ta ware suna ta hira da Didi har ya kira ta a waya ya shaida nata sun shiga jirgi zasu tashi. Suka yi masa fatan sauka lafiya daga nan ya kashe suka cigaba da hira da Didi. Amma zuciyar Nayla babu daWi, kewar mijinta take ji amma babu yadda zata yi.
KRB3P078
Nana haleema.

? ? A daren Nayla ta Wauki motarta a gidan Hajja ta haWa kaya ta tafi gidan Daddy dan Salma ma ta koma har Hajja tana can ana ta shirin biki. Suna zaune gabaWaya a falo ana ta shirye-shirye Mummy ta ce, "Nayla ai na Wauka Kaduna zaki gudu."

Nayla ta kalli Salma tana dariya ta ce, "Ai Mummy ina nan, ni ce babbar ?awar amarya ina zan tafi Kaduna?." Mummy ta yi dariya ta ce, "Gaskiya ne. Kuma kin san da yake ma duk events Win a nan ne ba damuwa za a yi da zuwa can ba." Nayla ta ce, "shiyasa ban saka a raina zan je ba, ina za a kai amarya ma tafi" ta faWa tana dafa Salma tana dariya.

Mummy ta ce, "na Wauka baza ki je ba ai."
"Zuwa kai Mummy." Suka cigaba da hirar biki tana yi tana kallon waya dan ta san har lokacin mijinta yana sama suna tafiya.

Haka aka cigaba da hirar biki kamar baza su yi bacci ba, sai dare sosai suka yi bacci. Nayla tana tashi da asuba waya ta duba ta shiga WhatsApp tana tura masa sa?on kewa da sauran su kafin ta cigaba da harkokinta.

Sai da ya kwana biyu da tafiya da yamma tana zaune an gama yi mata gyaran jiki, dan duk abinda aka yiwa Salma sai an yi mata kawai ta ga kiransa ta whatsApp call. Hannunta har rawa yake yi ta Wauka ta saka a kunne ta kasa cewa komai. Daga nasa Sangaren shima bai ce komai ba sai daga baya ya yi murmushi tare da ajiyar zuciya ya ce, "Ashiq!."

Nayla a kasalance ta ce, "Rouhii!." Omar ya ce, "uhum kina lafiya? Ina fatan kin daina kuka ko?."
"Rouhi bazan daina kuka ba har sai ka dawo."
"Ki fara lissafi, har an ci kwana biyu ko?."
"Ka sauka lafiya?."
"Lafiya lau, shigata hotel kenan na kiraki, Na damu na ji muryarki, zuciyata tana faWa min matata tana nigeria tana kuka."

Nayla cikin shagwaSa ta ce, "Baka huta ba?."
"Ban huta ba Jidda, sai yanzu da na ji maganarki zan huta. Na gaji sosai, ina ma kina tare dani da kin yi min tausar nan taki mai saka ni bacci." Nayla ta lumshe ido ta ce, "Ka je ka huta Rouhi, na san in ka gaji sai ka fara ciwon kai, bana so kanka ya yi ciwo."
"Zan huta Ashiq!. Kina lafiya? Kin fara jin alamun ajiyata?." Nayla tayi dariya kaWan ta ce, "Rouhii haka ka ke son yara ban sani ba?."

"Nima ban san ina so ba sai da aka haifi Marmerh, ina so na ga an nuna yarinya kyakyawa kamar ki an ce wannan ?ar Omar ce wacce Jiddan shi ta haifa." Murmushi ta yi ta ce, "Yanzu ka huta tukunna, bana so ka yi ciwon kai."
"Yanzu kuwa Ashiq! Dare ya yi sosai a nan, asuba ta kusa."

"Mu kuma ko sallar magriba ba mu yi ba."
"zan kira ki video call in anjima, ki kasance ciki shiri zan ga abinda na yi kewa, ina nan ina tunani da kewar rashin jinsu a jikina da bacci tare dasu, kin gane ai." Dariya tayi shima haka ya kashe wayar.

Nayla bayan sun gama waya sai walwalarta ta ?aru ko babu komai ta san yana lafiya. Ta cigaba da harkokinta bai kira ta ba sai bayan sallar i'sha ta shiga Waki har da rufe ?ofa ta saka lock ta zauna sannan ta Wauki kiran.

?? Fuskarsa ta bayyana akan screen Win sai ta ga ya sake yi mata kyau yayi haske gashin kansa ya kwanta kamar ba shekaran jiya suka rabu ba. Omar ya ce, "Ya dai ki ke kallona, na yi miki kyau ne?." Nayla ta ce, "sosai ma kuwa, ka yi bacci kuwa?."
"Ban yi ba, yanzu aka idar da sallar asuba da zan kwanta sai naji bazan iya ba sai na ga fuskarki. Ga ki nan kin yi kyau sosai, daga tafiya kwana biyu naga an sake canja min ke."

Nayla ta ce, "mu kuma a nan an yi sallar 'isha, ka je ka huta in ka farka daga baccin sai ka kira ni."
"Lokacin ai kin yi bacci."
"Zan katse baccin na amsa kiranka Rouhii."
"To Ashiq zan huta." Kiss ta yi masa sannan ta ce, "Bye Rouhi." Katse kiran ta yi dan tana so ya huta ta biye masa bazai huta ba.

? ? ? ? Kwanakin biki yana ta tahowa ana ta shiri Nayla na ta shan soyayya da mijin ta a waya, duk inda ya je sai ya faWa mata, haka duk abinda ya siya sai ya tura mata. Haka take zama ta lalace a video call dashi ko gajiya da wayar basa yi, kewar junan su na sake damun zuciyarsu.

A cikin garin Kano aka fara events na bikin Salma, Nayla itace kan gaba komai tare ake yi da ita sai Jidda da ta shigo ciki, Sune ?annen Ango kuma ?awayen amarya. Tun daga kan masu henna, da masu kwalliya duk tare ake yi musu, Nayla dai iya ba?in henna tayi iya hannu ta ce baza ta yi ba sai mijin ta zai dawo suka dinga tsokanarta.

An yi kamu, an yi dinner aka Waura aure ranar Friday, ranar Saturday aka tafi da amarya garin Kaduna. A can Kaduna ma wani bikin aka sake yi, Nayla sai zirga-zirga take itace wajan ango itace wajan amarya. Kowa in ya ganta sai ya yi dariya ya jinjina mata ana tsokanarta ?anwar ango ?awar amaryar, gashi ta yi kyau ta sake yin haske sai aka dinga tunanin ciki ne da ita. Mama ma ta Wauka ciki ne da ita, shiyasa take hanata wani yawo, sai da ta tambayeta ta ce ita bata da komai sannan ta ?yaleta. Amarya bata je gidanta ba sai ranar lahadi da daddare, su Nayla ne yan rakiyar amarya ita da Jidda da Ummimi.

A tsakiya suka saka Salma suna ta tsokanarta tun tana ?yale su har ta fara basu amsa, sai da ango ya shigo sannan suka dawo gida ita da Jidda cikin farin ciki. Biki ya watse kowa ya koma gida ana huta gajiya, Nayla ma ta sha baccin gajiya, kiran wayar mijinta ne ya tashe ta a firgice ta duba ta ga video call ne.

?auka ta yi ta kalle shi ta ce, "good morning Rouhii!." ?are mata kallo yake yi dan kayan bacci ne a jikinta, rigar mai ?aramin hannu kuma bata da kauri sosai sannan bata saka komai ba sai rigar kawai dan haka ana iya ganin jikinta. Ganin ya yi shiru yana kallon ta sai ta kalli abinda yake kallo ta kalle shi sannan ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Na yi kewarki Ashiq, ni kaWai na san halin da nake ciki da bakya tare dani, Kin san dai halin mijinki, mayenki ne."

Nayla ta yi kasalalliyar dariya da ta saka Omar ya lumshe ido ya ce, "Kina sake kashe min jiki Jidda, kar ki saka ni kuka mana." Ta wara ido ta ce, "wace ni na saka YaMar tiger kuka? Sai daina saka shi farin ciki." Murmushi ya yi ya ce, "kuka na nawa kuma? An ce da kare ya sunanka ya ce na nawa kuma?." Dariya ta yi sosai shima dariyar ya yi ya ce, "ko ba haka ba ne?."
"Ni dai babu ruwa."

?? "Yanzu rufe jikinki in ya so sai mu yi magana, in ina kallonki a haka akwai matsala." ?i tayi ta shagwaSe fuska tana kallonsa ya Wauke ido ya ce, "Jidda ki yi abinda na ce, Allah zan rasa nutsuwata, ki taimaka min. Kar ki saka aljanuna su tashi gashi bakya kusa balle ki yi min ru?iya." Dariya tayi sosai sannan ta ja bargo ta rufe jikinta ya kalle ta ya ce, "Wai waye ya saka ki yi wannan shigar?."

"Gajiya na yi sosai, wannan Win ma a cikin kayana na nemo ta."
"Amma wannan kayan da zaki saka a gida ba ne, akwai ?an biki, ko wata ce ta ganki a haka ai ta cuce ni." Nayla tayi dariya ta ce, "yanzu zan yi wanka."
"Ya gajiyan biki?."
"Bari kawai Rouhi, na gaji sosai."
"sannu, ai dole ki gaji, ?awar amarya ?anwar ango."

Dariya ta yi kaWan tana kallonsa ta ce, "ni ko ina dani a wannan bikin. Yau baka je kasuwar ba?." Ya Waga mata gira ya ce, "zan je sai anjima, akwai da wanda mu ke zuwa tare."
"Allah ya taimaka ya dawo min da kai lafiya."
"Amin. Na ?agu na dawo nima wallahi, duk na gaji da zaman."
"Nima na gaji da zama baka nan."
"Hmmm Kamar gaske."
"Da gaske mana, in ka dawo zan tabbatar maka da na yi matukar ?ewar ka." Murmushi ya yi bai ce komai ba ta ce, "kasan meye?." Ya girgiza kai alamun a'a ta ce, "yau na tashi da azumi, rabona da azumi har na manta, tun dai wanda muka yi tare guda uku nida kai."

Omar ya ce, "ki yi abinda ki ke so kafin na dawo."
"Don Allah meyasa baka so na yi azumi?."
"Akan me zance bana so ki yi ibada? Kawai bana so a shigar min lokacina ne. Ina so na kasance dake kuma ga azumi, kinga akwai shiga ha??i, maimakon ki samu lada sai ki kwashi zunubi tunda ba azumin farilla bane. Ina taSa ki zaki ce azumi ki ke yi, to akan me nida ha??ina kuma matata mallakina? Shiyasa gwara ki ha?ura kawai."

Dariya tayi zata rufe fuska ya ce, "kina rufe fuska zan kashe wayata, a wayar ma kunya ki ke ji?." Dariya ta yi sosai har ya shagala da kallon ta kafin ta ce, "Daman Didi sai da ta faWa min, ta ce da?yar in baka hana ni azumin litinin da alhamis ba, nayi-nayi ta faWa min dalili ta?i, ta ce na jira na gani in har ka hana Win zan fahimta, gashi kuwa na gane."

"Ta san ?aninta bai yi kama da mai ha?uri ba, ta san ?aninta yana da ?ulafuci akan abinda yake so. Inda zan iya zan barki kiyi ai lada zaki samu, babbar matsalar indai zan barki kiyi sai dai in na fita tun safe baza ki ganni ba sai kin sha ruwa. Dan in muka haWu, in idanuna ya faWa cikin naki ke kan ki baza ki san kin karya azumin ba. To me ya yi zafi? A dinga karya azumi da gangan? Maganin kar a yi kar a fara. Baazan iya ba, ji zanyi kamar za a zare min rai daga jikina. Ya za a yi na iya tsallake daddaWan yanayin nan na bayan sallar asuba?."

Dariya tayi sosai tana rufe ido ta ce, "kana bani kunya Rouhii."
"to ?arya nayi? Ke kan ki lokacin baya burge ki don Allah? Ki faWi gaskiya banda ?arya, aljanun da suke tashi a lokacin na san baza ki so a shiga ha??insu su ?i tashi ba." Bata ce komai ba sai fuska da ta rufe ya yi ?aramin tsaki ya ce, "komai kunya, zan kashe wayata in baza ki buWe fuska ba." Nayla ta ce, "Kana adawa da wannan kunyar tawa, ni kuma ba ni nayi kaina ba."

"Kunyar ta gulma ce ai, inda ya kamata tazo bata zuwa. Ki tuna daren za zan yi tafiyar nan mana, mantawa ki ke yi da kunyar, sai daga baya ki fara rufe min fuska." Ido ta rufe tana dariya suka cigaba da hira cikin nishaWi da soyayya.
KRB3P079
Nana haleema

Narma ta kammala idda amma har lokacin bata walwala kamar da, iyayenta sun Wauka tunda ta gama idda zata dawo kamar baya amma sai suka ga akasin haka har lokacin ware kanta take yi a cikin su.

Suna zaune a falo gabaWaya har da Yayansu Dad ya kalle ta ya ce, "Narma wai meye matsalarki ne? Na Wauka da kika gama idda zaki dawo kamar dah kina walwalarki sai na ga akasin haka. Me ki ke so ne?."

Narma ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Abinda nake so ba samu zan yi ba shiyasa gwara na yi shiru kawai." Mum ta ce, "Wan daban nan ko?." Narma ta ce, "Mum sunansa Omar, Omar sunansa ba Wan daba ba." Mum ta ce, "na rasa me ya shiga kanki, ina ke ina wannan yaron?."

"A haka nake sonsa! A haka nake so na rayuwa dashi Mum. Shekara Waya kenan da ku ka raba ni dashi, amma zuciyata har yanzu tana tare dashi. Matu?ar baku amince min da aurensa ba baza ku taSa samuna a yadda ku ke so ba. Yadda na bi abinda ku ke so na auri Ashraf, ku ma ku yi min adalci na aure shi!."

Dad ya ri?o hannunta cikin rarrashi ya ce, "yi a hankali my love, ke yanzu kin san inda Tiger Win yake? Kuma kina da tabbacin zai karSe ki?."
"Indai zaku amince na aure shi zan nemo shi a duk inda yake, kuma zan tabbatar da na dawo da soyayyata a cikin zuciyarsa. In kuma ba ku amince ba zan iya barin gidan nan na koma Kano na rayu dashi."

Jin abinda ta ce Nabil Yayanta ya ce, "Baki da hankali." Dad ya dakatar dashi ya kalle ta ya ce, "Narma yaron nan ba type Winki bane, na rasa abinda ya shiga kanki kika kasa fahimtar matsayin da ki ke dashi. Mahaifinki fa takarar governor yake yi, meyasa zaki dinga cewa kina


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login