Showing 69001 words to 72000 words out of 332344 words

Chapter 24 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14390

kanta cikin ciwon da yake damunta. A hankali ya mi?e ya ?arasa ya kunna hasken Wakin yana kallonta, kuka take yi bilha??i tana zaune ta ri?e kai.

Mamaki abin ya bashi, mai neman maganin ciwon kai ina shi ina kuka kuma?. A hankali ya ?araso inda take ya zauna a gefenta a karo na farko a zamansa da ita. Sai da yaji wani irin yarrr dan kafaWarsa ta taSa ta ta kaWan, ya ji wani abu kamar jan wutar lantarki kafin ya dawo daidai. Duk da ciwo yana damunta sai da ta ji wani iri a jikinta da mamaki mai matu?ar yawa.

"Cire hannun ki" ya furta gab da ita hakan ya saka taji maganar a kunnenta. A hankali ta sauke hannun daga goshinta shi kuma ya kai hannunsa goshinta ya ri?e jiijiyoyin kan nata. Yadda suke bugawa da gudu zai baka tabbacin ba ?aramin ciwo kanta yake yi mata ba, sai ta sake bashi tausayi dan ya san azabar ciwon kai tunda yana yi, ga kan nata ya yi zafi.

Addu'a ya fara yi mata wacce annabi Muhammad S.A.W ya koyar damu yayin jin ciwo. A online school Win da yake attending aka sanar dasu addu'ar, kasancewar bata da tsaho karantawa uku ya haddaceta a kansa. Sannan ya ji sheikh Isah Ali ibrahim Pantami ya koyar da ita a wani tafsir Winsa wanda ake Worawa a whatsapp status ko tiktok. Bai taSa gwadawa ba, amma yana ji a jikinsa in ya gwada mata zata samu lafiya. A zuciya yake karantawa hannunsa na ri?e da kanta kusan mintina uku kafin ya zare hannun ya tofa a hannunsa ya shafa mata a goshin a hankali.

(Za a ri?e inda yake ciwo, ko ina ne yake maka ciwo zaka ri?e wajan sannan ka yi Bismillah sau uku, sai ace #9OHR0O (P'DDGP HNBO/R1N*PGP EPFR 4N1PQ EN' #N,P/O H#N-N'0P1A'uzu billahi wa ?udratihi min sharri ma ajidu wa uhadir. Ina neman tsari da Allah da kuma Ikonsa daga sharrin abin da nake ji (na ciwo) kuma nake jin tsoransa. Za a karanta ?afa bakwai. Addu'a ya?ini ce, sai ka saka yarda da ya?ini sannan zaga amfaninta, in ka yi don gwaji ba tare da amincewa ba bazata yi maka aiki ba.).

Nayla tunda hannunsa ya sauka a goshinta ta ?ame ?am saboda gudun da zuciyarta ke yi, ta tabbatar da zai kasa kunne da kyau zai ji yadda zuciyar take bugawa dan ba bugu take na wasa ba, bugu take mai ?arfin da kuma sautin da take iya jiyo shi a kunnenta. Hannun Omar masoyinta akan goshinta ai dole zuciyata buga ko bata shirya ba.

Bata san ya gama ba ta ji ya zare hannunsa a kasalance kamar baya son magana ya ce, "Ki kwanta, sannan ki daina kuka. Ban da shirme me neman maganin ciwon kai meye zai kai shi kuka" ya faWa yana tashi daga wajan.

Nayla ta ja numfashi ?hamshin turarensa ta sha?a lokacin da ya motsa, ta kwanta a hankali a lokacin duhu ya mamaye Wakin dan ya kashe hasken ya ga yana damunta. Cikin mintina da bai wuce biyar ba bacci mai daWi ya Wauke Nayla.
KRB3P021
Arewabooks@nanahaleema11.

Omar yana kallon ta har baccinta yayi nisa sosai sannan ya Wauke kai daga kallon ta ya tashi ya dawo kan gadon dan bazai yi kwanan takura irin jiya ba. Kwanciya ya yi a can ?arshe itama tana ?arshe akwai space mai yawa a tsakiyar su.

Kallon gefenta ya yi yana mamakin wai shine kwance da wata mace a kan gado Waya, Allah mai iko mai yadda ya so a lokacin da ya so, in ba dan ikon Allah ba shekaru biyar masu zuwa baya kawo aure a ransa. Juya mata baya ya yi tunani kala-kala yana zuwa ransa dan shi kam ya kasa bacci. ?hamshin turaren ta ya dame shi, ko ya ya motsa sai ya ji shi a hancinsa.

A haka shima bacci ya Wauke shi da?yar, bai farka ba sai ?arfe biyu na dare ya buWe ido. Kallon inda take ya yi yaga tana yadda take amma ta juya yanzu tana kallon bayansa saSanin lokacin da ta kwanta. Sake rufe ido shima ya yi ya cigaba da bacci bai tashi ba sai asuba. Yau ma har ya yi alwala ya saka jallabiya bata motsa ba.

Tunani yake ya tashe ta ko ya ?yaleta? Kallonta ya ke yi sai yaga ta buWe ido kai tsaye suka haWa ido da ita, ganin haka sai ya janye idonsa ya fita daga Wakin.

A inda ya same ta bayan ya dawo tana wajan kamar jiya, ya zauna akan kujera kamar jiya bai ce mata komai ba. Nayla ta ce, "Ina Kwana." Maimakon ya amsa sai ya ce, "ya ciwon kan?." Nayla ta yi murmushin jin daWi har tsakiyar ranta sannan ta ce, "ya daina ciwon gabaWaya tun a jiya." Bai ce komai ba daman bata yi tunanin zai ce ba ta ce, "na gode."

Nan ma bai ce komai ba sai ?aramin jarbinsa da ya zaro a aljihu yana ja a hankali. Nayla ta ce, "YaMar zan je asibiti anjima, sannan na wuce wajan aiki." Ya jita amma ya share bai ce komai ba, Nayla har ta fitar da ran zai amsa mata sannan taji ya ce, "Shi zuwa aikin dole ne?." Ta kalle shi jin abinda yace amma ga mamakin ta idanunsa a kulle suke kamar ba shi ne ya yi magana ba. Ta ce, "eh."

Shiru ya sake yi bai ce komai ba amma yana mamakin ita da bata da lafiya aikin me zata je kuma?. Nayla ta ce, "Ka bar ni na je?." Ya buWe yana kallon ta cike da mamaki ya ce, "kin ji na ce kar ki je?." Ta girgiza kai ta ce, "A'a."
"Da in zaki tafi tambaya ki ke yi?." Nayla ta bishi ido tana kallon sa shi kuma ba ita yake kallo ba kuWin da yake ajjiye akan table Win yake kalla.

Nayla ta ce, "kaine ka ce ba sai na tambaya ba ai, Amma ka yi ha?uri." Mamaki ta sake bashi jin harda bashi ha?uri, kamar zai yi mata magana sai ya fasa kar ta ga ya za?e da yawa a lamarinta. Tashi tsaye ya yi ya ?arasa wadrobe ya buWe ya Wauki abinda zai Wauka ya dawo inda yake zaune amma bai zauna ba, a lokacin Nayla ta mi?e tsaye ya mi?a mata kuWi ta saka hannu ta karSa ya ce, "ki siyi magani." Nayla ta kalli kuWin ta kalle shi har ya juya ya koma ya zauna. Nayla ta yi murmushi farin ciki, annushuwa tana mamaye mata dukkan ilahirin jikinta da zuciyarta, ta ce, "Na gode YaMar."

Bai motsa ba balle ya tanka, ita kuwa daWi yayi mata yawa da tana da dama da tabbas da ta taka rawa saboda farin cikin da take ji. Agogo ta kalla ta ga har shida ta yi ta ninke sallayar da tayi sallah ta ajjiye inda ta Wauka tana ta murmushi ita kaWai. ?arasawa tayi bakin gadon ta fara kokarin gyarawa dan in ta fita babu lallai ta dawo Wakin.

Bai ce mata pim ba har ta gyara gadon tsaf ta zo zata wuce shi ta ce, "Sai anjima YaMar" ta faWa tana fita daga Wakin tare da ja masa ?ofar. _Wai YaMar, inda ta iya faWar R Win ma da sau?i, amma wata kalmar take faWa daban a madadin R Win. Na rasa meyasa sunan yake min daWin ji a bakin ta._ abinda yake faWa a zuciyarsa kenan yana murmushi shi kaWai wanda bai san dalilinsa ba. Kawar da tunanin ya yi ya tashi ya kashe haske ya kwanta.

Yau ma ya jima yana bacci sai goma ya tashi, ya yi wanka ya sake gyara Wakin kamar yadda ya saba ya shirya. Yau wankan maroccon yallabiya ya yi marron kala mai shegen kyau da faWi kamar kayan sarakai haka take. Fitowa ya yi falon ya yi karo da Didi a zaune tana sha tea.

?arasowa ya yi ya zauna ya ce, "Ina kwana." Kallon sa ta yi ta ce, "ka tashi lafiya." Bai amsa ba kamar yadda ta san bazai amsa ba daman.
"Ina ta jiran ka daman, ga abinci nan ka ci."
"Bana jin yunwa." Hararasa tayi ta ce, "ka ci don Allah, ai Nayla bata nan balle ka ce baza ka ci ba."
"Daman na ce miki saboda ita ne bana ci?."
"Baka ce ba, amma zaki fi sakewa ka ci in bata nan tunda haka ka Worawa rayuwarka."

Ajiyar zuciya ya yi bai ce komai ba amma yana tunanin ko ta je asibitin, ko me aka ce yana damunta, ko ya ciwon kan nata yanzu bai sani ba. Didi ta kalle shi ganin yayi shiru kamar mai damuwa ta ce, "nima gidan zan kulle, shiyasa na ce mata ta Wauki key dan gidan Hajja zan je, bazan sake dawowa nan ba gida zamu wuce." Omar bai ce komai ba ya sake yin shiru yana sauke numfashi Didi ta zuba masa ido ta ce, "lafiya na ganka kamar mai damuwa?." Ya ce, "lafiya" ya furta kafin ya sake kallon ta ya ce, "Shi zuwa aikin nan nata wai dole ne?."

Didi ta ce, "dole ne mana, dashi ai ka aureta kuma iyayenta sun faWa maka zata cigaba da aikinta." TaSe baki ya yi bai ce komai ba, Didi ta ce, "kana da matsala da zuwa aikin na ta ne?."
"Ko Waya, na ga bata da lafiya ne kawai." Didi ta ce, "ta ce min zata biya asibiti daman yau." Shiru ya yi bai tanka ba Didi tana murmushi da mamakinsa, gabaWaya sai ta ga ya canja, tana kuma da tabbacin ko ba ya son Nayla to yana gab da faWawa, domin alamun hakan sun bayyana a tare dashi.

Maganar abinci da ta sake yi masa tana magiya ya saka shi ya sha tea kawai ya fita itama ta ce bazai dawo ya tarar da ita ba zata gudu. KuWi ya bata ya ce kuWin mota ne ta san hali babu damar ta ?i karSa ta shiga uku da masifarsa.

Nayla ma da ta tashi daga wajan aiki gidan Hajja ta wuce a can ta samu Didi, ta zauna suna ta hira har sai da Didi ta tafi sannan itama ta dawo gida. Bashir ya shigo mata da mota ya bata key Win sannan ta shiga cikin gidan.

Kamar yadda ta yi zato baya nan, ta kunna hasken falon sai ta tuna Didi ta ce ta dinga duba yanayin solar gidan hakan ya saka ta ta je inda Didi ta nuna mata dan ita ba sani tayi ba ma. Ganin da ?arfinta sosai ya saka ta komawa ciki ta yi wanka ta saka kayan bacci ta fito ta zauna a inda ta saba zama tana ta aikin dana laptop saboda aikin da aka turo mata ta gmail.

Bayan ta gama Netflix ta shiga ta fara kallo kafin ta kashe ta shiga application Win da take kallon ball ta saka tana kalla. Sai kuma ta tashi ta kunna tv falon da bata saba kunnawa ba, ta shiga tashar ball a nan ta ga dstv Win subscription ya ?are. Tsaki ta yi ta fara danna waya lokaci kaWan ta tura kuWin, ta tura musu number dstv Win nata aka sako mata kati. Kashe laptop Win ta yi ta cigaba da kallon ball din a tv, yadda ta ke kalla tana fahimtar komai zai baka tabbacin ta saba gani.

Tashi tayi ta shiga Waki ta Wauki maganinta da aka rubuta mata a asibiti ta zo ta sha ta zauna tana cigaba da kallo. GabaWaya kewar Didi ta dame ta a zuciyarta kamar sun jima a gidan haka take ji. Waya ta Wauka ta kira Didin, tana Wauka ta ce, "Wallahi Didi kamar ki dawo haka nake ji, gabaWaya gidan babu daWi." Didi tayi dariya ta ce, "ba kuma zan sake kwana a gidan ba har abada." Nayla tayi dariya ta ce, "kin je gida lafiya?."
"Lafiya lau Nayla, Ashe haka ki ka lodawa yallaSai lemo a bayan mota ban sani ba? Har da su madara."
"To Didi na san in nace zan bayar hanawa zaki yi, ni kuma sun yi min yawa kar ai ta asara. Kinga da azumi ma haka na dinga bayar da kayan saboda kar a yi asara, wa nake dashi in ba ke ba?."

Didi ta ce, "To Nayla na gode Allah ya bar zumunci, Allah ya bar ?auna tsakaninki da Damisa." Nayla tayi murmushi kawai bata amsa ba, Didi ta ce, "baki ce amin ba." Nayla ta ce, "To Amin." Didi ta yi dariya ta ce, "Ina fatan babu ciwon kan ko?."
"Babu ko kaWan, yanzu ma na sha magani."
"Haka nake so na ji, Sai ki tuna da abinda na ce miki." Nayla ta yi dariya ta ce, "Hajiya Didi kenan."
"Zaki ga Hajiya Didi." Sallama Nayla tayi mata ta kashe wayar tana murmushi.

Wai ta koma Wakin Omar da kwana, yo haka kawai ta je yana zare mata idanu? Dan ya yi mata mutunci jiya shi ai kamar wahainiya yake ko yaushe canjawa yake yi. Baza ta je ba, daman dole aka yi mata kwana biyun, yanzu tunda Didi ta tafi ya sha zaman sa.

Sallamarsa ce ta katse mata tunani kamar ko yaushe, Nayla ta amsa dan ta san babu lallai ya ?araso shiyasa bata motsa ma daga inda take ba. Sallama ta sake ji a inda take sai ta kalli inda yake ta ganshi ya shigo har inda take zaune sai ta mi?e sosai ta ce, "Sannu da zuwa." Kallon tv ya yi yana mamakinta, bai taSa ganin mace na kallon ball ba sai ita, yana yawan ganin ta tana kalla.

"Ya jiki?." Nayla ta yi murmushi ta ce, "Da sau?i."
"Me aka ce yana damunki?." Ba Nayla ba hatta shi da ya yi tambayar sai da ya ji wani iri a zuciyarsa, amma sai ya maze bai nuna ba. Nayla ta sunkuyar da kai ta ce, "na samu low blood pressure ne, sai malaria amma babu yawa, amma sun bani magani." Girgiza kai ya yi ya ce, "Okay, Allah ya ?ara lafiya." Nayla ta yi murmushi ta ce, "Amin, na gode."

Juyawa ya yi zai bar wajan sai ya dakata bai juyo ba ya ce, "in akwai wani abun zaki iya sanar da ni" yana faWa ya wuce ta bishi da kallo.

Baya ta yi ta kwanta a kan kujera tana jin farin ciki na zaga ko Ina na zuciyarta, wai Omar shine yake tambyar lafiyar ta cike da kulawa haka. Gaskiya yanayin ya yi mata daWi bata san lokacin da ta fara hawayen farin ciki ba, tabbas ta yarda da addu'a, ita kanta ta san addu'ar da tayi a watan ramadan a jikinta take jin Allah ya amsa, gashi kuwa tana ta ganin canji tun ba a yi nisa ba, ko a yanayin yadda take gaisawa da Abiy ta san Allah ya amsa mata addu'arta. Da wannan farin cikin Nayla ta yi bacci mai daWi.

(?an uwa mu yarda da addu'a, kar ka sare da faWawa Allah bu?atarka, duk daren daWewa Allah zai amsa maka. A hankali ake ganin canji, a hankali komai zai gushe ya zama labari. Allah ya amsa mana bu?atun mu baki Waya).

Omar shi kansa mamakin kansa ya dinga yi, wai shine ya damu da rashin lafiyar wata mace har yake tambayarta ya jikinta. Tunda ta tafi ya kasa sukuni yana so ya ji ya jikinta, rasa sukuni yake? yi a duk lokacin da ya tuna yadda jijiyoyin kanta suke harbawa a daren jiya.

Juyawa ya yi ya kalli inda ta kwanta jiya ya saka hannu ya jawo filon da ta kwanta yaji gabaWaya ?hamshinta yake yi. Cillar dashi gefe ya yi tare da yin ajiyar zuciya ya rufe ido ya buWe ya ce, "Me nake ji haka wai? Me yake damuna ne? Mtsw" Ya furta yana kwanciya yana jin wani iri a zuciyarsa.

? ? ? ? ?? Bayan Kwana biyu.

Tun daga wannan ranar suka cigaba da rayuwa kamar da, bata ganinsa sai dare amma in ta gaishe shi yana amsawa daga nan babu wata magana. Tunda ya hana ta fita bata fita, daman ba wajan zuwa ne da ita ba sai dai ta biya in ta dawo daga aiki, wajan zuwa baya wuce wajan Salma ko gidan Jidda.

Tafiya ta Wan yi nisa kaWan, har an shiga watan babbar sallah, kamar yadda ta saba indai bata je aikin hajji ba duk shekara azumin nan guda goma cif sai tayi sai dai nigeria.

Ranar lahadi ya kama saura kwana uku sallah ya shigo da yamma ya same ta a zaune tana karatun alqur'ani, ganin ya shigo sai ta rufe ya zauna yana kallonta. Tana burge shi sosai a fannin addini da karatun alkur'ani sosai, in ya ganta tana sallah musamman da daddare sai yaji ta burge shi sosai. Nayla ta ce "Sannu da zuwa." Kai ya Waga kafin ya kalle ta ya ce, "zaki iya aikin sallah?."

Nayla cikin shagwaSa ta ce, "A'a gaskiya, ban taSa yi ba." Ta ?asan ido ya kalle ta ganin yadda take magana kamar wata ?ar baby, ya Wauke kai daga kallonta yana tunnain daman Didi ce ta ce ya tambaya, amma shima ya san ba iyawa zata yi ba, Didi ce ta takura masa ya tambaye ta don Allah.

Ya ce, "baki so?."
"ba wai bana so ba, ni ban iya aikin ba gaskiya, kuma....kawai a bayar sadaka duka" ta faWa tana wasa da hannunta. Daman abinda ya ce kenan Didi ta nace sai an tambayeta gashi itama ta faWi abinda ya faWa. Bai sake cewa komai ba ya tashi ya bar wajan Nayla ta bi shi da kallo ta ce, "wai ni ma na zama matar gida har tambayata ake yi aikin naman sallah, Ina zan iya wannan wahalar? A rabar kawai daman bai dame ni ba."

Ranar arfa babu aiki kuma ta san Hajja na haWa shan ruwa a gidanta idan bata je aikin hajj, hakan ya saka ta zumuWin zuwa gidan Hajja dan gabaWaya ake haWuwa a sha ruwa sai dai in wani ya je saudia ne baya nan. Tun safe itama take aiki tana son yin sadaka.

Da azahar ta ji motsinsa ya shigo ta mi?e da sauri ta fito falon tana jiran fitowarsa daga Waki, bata jima a tsaye ba sai kuwa gashi ya fito ya Wauko wani abu da alama shi ya manta ya dawo Wauka. Kallonsa ta yi ta ce, "Yaya Mar."


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login