Showing 189001 words to 192000 words out of 332344 words

Chapter 64 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14432

ya Wan taSa hannunta, ta Wauke da sauri tana yarfe hannu tare furta, "Washhh!." Da hanzari ya ri?e hannun yana cewa, "?onewa ki ka yi? Na gani, amma babu zafi ko?" Ya faWa a tare yana kallon ta ya manta ma fushi yake da ita.

? ? Ganin ta samu kansa sai ta fashe da kukan shagwaSa, sai lokacin ya kula ya kwafsa ya saki hannun nata ya koma ya zauna yana jinta tana kuka bai ce komai ba. Mamaki take yi ganin ya share ta kamar ba shine in tana kuka yake damuwa ba, ta sake ?ara volume Win kukan nata sai ta ga yana dube-dube a aljihunsa. Abinda ya Wauko? ya bata mamaki ta har ta buWe baki tana kallon sa, ya ma?ala AirPort a kunnensa alamun ta cigaba da kukan shi baya jin ta.

Nayla ta bishi da kallon mamaki tana kuka. Gajiya tayi da shariyar tasa ta taso ta dawo jikinsa ta zauna ta kwantar da kanta a ?irjinsa tana kuka mai sauti wanda yake ratsa kunnensa har zuciyarsa dan babu abinda yake ji. Gajiya ya yi da jin kukan nata, a hankali ya cire abinda ya saka a kunnensa ya ce, "to ya isa haka, kukan ya isa ki bari."

Numfashi take ja ta ce, "ban san me nayi maka ba ka ke fushi dani."
"Jiya da ki ka dawo kin kira gida kin ce musu kin sauka lafiya kuwa?." Nayla ta Waga kai ta ce, "tun kafin na shigo gidan nan ma na kirasu saboda kar na manta." Murmushin takaici ya yi kafin ya haWe rai matu?a cikin kaushi ya ce, "ni ne wanda ki ka raina da ki ka kasa kirana ki ce min kin sauka lafiya ko? Ni da yake na damu dake da na kira ki sai ki ka ?i Wauka, kuma baki tashi kirana ba sai dare. Ni ne wanda bashi da mahaimnaci a rayuwarki, baki damu da ki faWa min kin sauka lafiya ba, ko ya na kai ga son sanin ya kika sauka ke bai dame ki ba."

Sai a lokacin ta fahimci dalilin fushin nasa, zata yi magana ya ce, "kar ki ce min komai, tashi ki bani waje." Zata sake magana ya buWe idanu ya ce, "na ce ki tashi!." A firgice ta mi?e daga jikinsa ta ja ta tsaya ba tare da ta fita ba, dan yanzu ba ko yaushe faWansa yake bata tsoro ba, amma yanzu kam a tsorace take tana Soye tsoron ne kawai. Shi kam bai kalle ta ba ya mi?e ya shiga banWaki.
KRB3P069

Nayla jiki a sanyaye take a tsaye har ya fito tana kallonsa, tana so ta faWa masa uzurinta amma ya?i bata wannan damar. Kallonsa ta tsaya yi tana matsar ?walla, tana so tayi masa magana tana tsoron kar ya yi mata tsawar da bata so. Shi ma yana kallon ta hankalinsa yana kanta, amma baya so ya nuna mata ya yi kewarta sai ta fahimci kuskuren da yake ganin ta yi masa. Inda ya biyewa zuciyarsa da yanzu ya karSi ha?urinta saboda bugawar da zuciyarsa take yi. Allah ya Wora masa ?aunarta a lokacin da bai shirya ba, zuciyarsa bata taSa bugawa akan komai ba sai a kanta. ?iris ya rage ya kasa jurewa share ta Win da yake yi, shiyaasa ya ke so ta fita ta bashi waje amma ta ?i.

Ganin ta ?i fita ta ja ta tsaya tana masa kukan shagwaSa sai ya tashi ya Wauki wayarsa ya fita ya bar mata gidan gabaWaya ko tea Win da ta ajjiye bai sha ba.

Nayla ta bishi da kallo har ya fice tana hararar bayansa ta ce, "mutum sai masifa, ya tsaya ya ji uzurina ma bazai tsaya ba" ta faWa tana fita daga Wakin. (Lallai Nayla kin waye>?#?).

?aki ta koma ta zauna ba tare da tana yin komai ba, sai ta gaji da zaman sannan ta taso ta dawo falo duk zaman gidan ya isheta. Salma ta yiwa waya ta ce don Allah ta zo, Salma ta ce mata tana gidan Daddy bata gidan Hajja. Kamar ta kurma ihu haka take ji, tunda suka fara shiri ana soyayya bai taSa fushi da ita kamar haka ba shiyasa duk ta damu.

Kamar wasa ta ji ana buga gate Win gidan ta taso ta buWe. Ganin Didi ya saka ta faWawa jikinta kawai ta fashe da kuka. Didi ta shigo ta rufe gate Win tana cewa, "Nayla lafiya? Me ya same ki?." Nayla bata iya magana ba suka shiga ciki Didi ta zauna ta ce, "Lafiya ki ke kuka Nayla? Wani abu ya faru ne?." Nayla cikin kuka ta ce, "Didi YaMar ne." Didi ta sauke Marmerh da take bayan ta tana bacci, ta kwantar da ita a gefe ta kalli Nayla ta ce, "meya samu Omar Win?."

Nayla ta ce, "Fushi yake tayi dani" ta faWa tana sake fashewa da kuka. Didi ta saki baki tana kallon Nayla cike da mamaki da kuma takaici, sai kuma ta yi dariya tare da yin tsaki ta ce, "Fushin Omar Win ki ke yiwa kuka?."

"Didi daga Kaduna na dawo jiya amma ko kallona bai yi ba, na rasa me nayi masa tun a can Kaduna baya Waukar wayata, in na kira shi da wata number da ya ji nice zai kashe. Ashe fushi yake yi dana sauka ban kira shi na ce na sauka lafiya ba, kuma ya kira ni ban Wauka ba. Allah yana gani ban ji kiransa ba, kuma bacci na yi shiyasa ban kira shi ba."

Didi ta bita da kallon takaici ta ce, "har yanzu wai baki rage tsoron Omar a ranki ba Nayla? Mijinki ne fa, in baki sake dashi ba da wa zaki sake?. Kuma na faWa miki tsoron nan nasa da ki ke nunawa nan gaba zai cutar dake wallahi, saboda zai dinga juya ki yadda yake so saboda ya san kina tsoronsa duk abinda ya ce zaki yi. Ban ce kar ki ji tsoronsa ba, ban ce kar ki yi abinda ya ce ba, amma ki dinga ja baya, wani abun ki daina nuna kin damu ko fushinsa yana gabanki, in ba haka ba zaki yi dana sani Nayla." Nayla ta ce, "na rage tsoronsa Didi, ni kaina na san yanzu bana tsoronsa kamar dah. Kawai na damu ne da yake fushi dani shiyasa."

Didi ta ce, "ba sai ki bashi ha?uri ba?."
"Na bashi ya?i ya ha?ura, sai share ni yake yi."
"Kema sai ki share shi, tunda kin bashi ha?uri ba sai ki ?yale shi ya ?araci ba?in halinsa ba?." Nayla ta langwaSar da kai ta ce, "Didi amma ai laifina ne." Didi ta yi dariya ta dafa Nayla ta ce, "ke kika san ta yadda zaki bashi ha?uri ya ha?ura, to meye na wannan kukan don Allah?." Nayla a sanyaye ta ce, "Didi tsawa fa yake yi min, ni na manta rabon da ya daina min magana balle tsawa."

"Shiyasa na ce fushin Omar har kuka zai saka ki? Daman shi ba ka yi masa komai ba fushi yake yi balle kin yi masa. Fushinsa ya daina tayar miki da hankali daman halinsa ne. In yayi ki barshi ya ?araci ?uncinsa zai dawo kan hanya." Nayla ta goge ido ta ce, "Inaso dai ya ha?ura Didi, ki bashi ha?uri don Allah. Kuma ba sa yin aiki ranar asabar sai yamma, amma ya fita ya bar ni."

Didi ta yi dariya tana mamakin shagwaSar Nayla ta ce, "babu ruwana, bazan bashi ha?uri ba ke zaki bashi ha?uri."
"To ya ?i ya ha?ura."
"Ke kin san ta yadda zaki saka shi ya ha?ura, kin san ta hanyar da zaki bi dashi ya ha?ura ko da bai yi niya ba. Ina zafin kan da yake ji dashi? Duk ya tattara ya ajjiye saboda son da yake miki, dole wani lokacin ya motsa tunda halinsa ne, hali kuma baya canjawa. Masifa, tsawa, da faWan duk suna nan, yanzu sun je hutu ne saboda amarci, gashi tun amarcin bai yi nisa ba sun fara ?wan?wasa ?ofa. Sai kin cigaba da ha?uri kawai, sannan ki san yadda zaki saka ya sauke ko baya so."

Nayla ta yi shiru kana ta ce, "Didi wani lokacin baka gane kansa gabaWaya, yanzu zaki ganshi fari anjima ya koma ba?i." Didi ta dinga dariya ta ce, "Kar ki bani kunya mana Nayla, ai na Wauka kin gama karanta Omar kin haddace ashe har yanzu da saura. Halinsa bazai canja ba, abinda zaki yi kawai ki koya kan ki jurewa akan halin nasa shikenan an zauna lafiya."

Nayla bata ce komai ba sai ?ar dariya da ta yi, Didi ta bita da kallo tana murmushi kafin ta ce, "ke kar ki damu, ki jira ya dawo ki san duk yadda zaki yi ki bashi ha?uri ni na san zai ha?ura. Omar din har wata tsiya ce a hannunki? A waje yake Omar amma a wajanki bai wuce jaririn da zaki sarrafa shi yadda ki ke so ba. GabaWaya ya susuce a kanki, tafiyar nan da ki ka yi rasa sukuni ya yi, ya kira ni kamar zai min kuka shi wallahi gidan baya masa daWi bakya nan, na ce haka zaka yi ha?uri harta dawo. Yana yi miki wannan son ki kasa amfani dashi wajan saka shi ya daina fushi?."

Nayla ta yi shiru bata ce komai ba Didi ta ce, "ki yi amfani da hikima a matsayinki na ?a mace ki san abinda zaki yi wanda in kika yi kin san yana jin sa a zuciyarsa, da wannan abin zaki kama shi har ya ya daina fushin." Nayla ta kalli Didi bata ce komai ba, Didi ta ce, "ki gane inda nake nufi, kar na fito miki free ki ce bani da kunya, amma na san kin fahimci karatun yanzu." Nayla tayi dariya tare da rufe fuska da hannunta. Didi ta yi dariya ta ce, "kyayi dariya ai. Ki wahalar dashi, ki rama share ki Win da ya yi. Ni bana so ki dinga ?yale shi wallahi, ban ce ki raina shi ba amma in ya share ki ki share shi, da ?afarsa zai zo inda ki ke. In shi ya tashi yanka miki wula?anci bazai raga miki ba, rufe ido zai yi kamar bai san ki ba, dan haka kema kar ki raga masa."

Nayla ta sake yin dariya Didi ta ce, "kar ki ce shawarar banza nake baki, na yi shiru" ta faWa tana dariya itama Nayla dariyar take yi kafin ta ce, "to Didi, zan yi duk abinda ki ka ce." Didi ta ce, "Allah na tuba fushin Omar har wani fushi ne? To akan rashin dalili ma fushi yake yi."

Nayla ta yi murmushi ta ce, "Didi ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ban kawo miki ruwa ba" ta faWa tana tashi tsaye Didi ta ce, "Daman kina ta kuka ta ya zaki bani ruwa?." Murmushi tayi ta kawo mata ruwa ta ce, "Me zan dafa miki?." Didi ta ce, "A ?oshe nake daga gidan Hajja nake, da bazan biyo ba ma Hajja ce ta ce na biyo mu gaisa, biki zan je."

Nayla ta ce, "Bikin wa?."
"Mama Zainab ce take aurar da jikarta." Nayla ta ce, "Jika ba ma ?a ba?." Didi tayi dariya ta ce, "Lallai an gaishe ki, itace mai bin Baba Adamu fa dan kin ganta mai ?aramin jiki?." Dariya Nayla ta yi ta ce, "Gaskiya dai ma sha Allah kamar ba ita ba, amma meyasa baki faWa min ba ai da na je."

Didi ta ce, "Mijinki nake tsoro, babu lallai ya bari sai dai in bai san can za a je ba. Wallahi Nayla babu abinda nake buri da ya wuce Omar ya manta da abinda ya wuce ya fuskanci danginmu amma ya ?i."

Nayla ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Kamar yadda ki ka ce na yi masa maganar na gwada, ya Sata rai ya ce in dai ina so mu yi faWa na sake maimaita masa maganar." Didi ta girgiza kai ta ce, "Babban tashin hankalina ranar da zai san wannan gidan da yake ciki na Kawu ne. Kawu ne ya bayar kyauta ya ce a matsayinsa na uba ya mallaka masa ya zauna a ciki, saboda tijara da hargaginsa ya saka na ce masa na haya ne, yanzu ya tayar da hankalinsa sai na bashi number mai gidan nan na rasa ya zan yi masa."

Nayla ta girgiza kai ta ce, "ai kuwa kafin na tafi Kaduna ma sai da ya yi zancen." Didi ta ce, "Na rasa ya zan yi na faWa masa, in ya san a gidan Kawu yake kwana wallahi daga ranar bazai sake kwana a gidan nan ba, kuma ni da na rufe maganar ya yi ta yi min masifa kenan kamar ya zane ni." Nayla ta ce, "ba sai a yi shiru da maganar ba kawai, ki samu wani ku haWa baki dashi a matsayin gidan nan na shi ne, in ya biya kuWin sai ya dawo miki dasu, in yaso duk ranar da ya nutsu akansu sai a faWa masa, amma nima ban goyi bayan ya sani yanzu ba." Didi ta yi shiru bata ce komai ba, Nayla ta Wauki Marmerh da take bacci. Didi kawar da maganar tayi suka cigaba da hira da Nayla har aka yi sallar azahar.

Nayla da ta tuna ta taho da cincin daga Kaduna ta Waukowa Didi suna ci tare ya buWe ?ofar ya shigo da sallama. Amsawa suka yi ya kalli Didi bayan ya mayar da ?ofar ya rufe fuska a haWe ya ce, "Hajiya Didi, saukar yaushe?" Ya faWa ba yabo ba fallasa. Ta yi murmushi ta ce, "Allah ya amsa bakin ka na zama hajiyar nan Omar. Tun Wazu nazo, ya aikin?."
"Alhamdu lillah."
"Ya yi kyau, Baka faWa min Nayla ta dawo ba."

Ya kalli Nayla da take kallonsa ya Wauke kai ya kalli Didi ya ce, "Yanzu da ki ka shigo baki ganta ba kenan?." Tayi dariya ta ce, "na ganta mana, wannan haWe fuskar da ka ke yi na meye?." Bai kula ta ba ya Wauki Marmerh da take jikinta a zaune, sai a lokacin yayi murmushi bai sake cewa komai ba ya wuce Waki da Marmerh a hannunsa.

Didi ta kalli Nayla ta ce, "Ki je." Nayla ta buWe ido ta ce, "A'a Didi, ki ?yale shi kawai." Didi ta yi dariya kawai bata ce komai ba. A lokacin ya dawo ya zauna da Marmerh a hannunsa, bai kula kowa a cikin su ba Marmerh yake yiwa wasa. Didi ce suke hira da Nayla sama-sama. Sai a lokacin ya ce, "Didi na rasa me kika Wauke ni, sai raina min hankali ki ke yi akan gidan nan ko?. Na rantse da Allah na sake yi miki maganar gidan nan daga ranar na daina kwana a cikinsa."

Didi ta yi murmushi ta ce, "yi ha?uri, in sha Allah dana koma zan turo maka number." Bai ce komai ba ya Wora ?afa kan Waya kamar yadda ya saba, babu wacce ya sake kalla a cikin su balle ya yi magana. Didi dai kallonsu take yi daga shi har Nayla, kafin ta yi dariya ta mi?e tsaye ta ce, "Omar bani ita na tafi, biki zan je na jikar Mama Zainab." Sarai ya ji me ta ce bazai tanka ba ne sai da ta karSi Marmerh sannan ya ce, "hadari ne a garin nan sosai, dole ne zuwa bikin?."

Didi ta ce, "dole ne mana, jikar yayar mahaifiyarmu fa, kamar ni ace ana bikin Marmerh." Kai tsaye ya kalle ta ya ce, "Yayar mahaifiyarki dai, ki daina saka ni a ciki, mahaifiyata bata da ?an uwa."Didi ta taSe baki tana mamakin halin Omar ta ce, "?arya ka ke wallahi, ko baka so Yayar babar ka ce. Biki ne ya zama dole na je."
"Addini ne?."

"Zai shiga cikin addini Omar, tunda zumunci ne." Ya bita da harara ya ce, "Ke ki ka ga zaki iya ai" ya faWa yana Wauke kai kafin ya kalle ta ya ce, "tunda ke kika saka kan ki ke ki ka sani, amma in wani abun ya samu Marmerh wallahi ban yafe ba. Ana faWa miki gari da hadari kina sake shirin tafiya, in dan ta ke ce ki je ruwa ya zane ki waye ya damu?" Ya faWa a fusace yana harararta.

Didi tayi dariya ta ce, "kome zaka ce sai na je Omar, Da Nayla zan Wauka mu je tare."
"Ta je a matsayin ta nawa?."
"Matarka mana."
"Ashe babu inda zata je kuwa, indai kin yarda matata ce ko gaisuwar mutuwa." Didi ta ce, "Allah ya yaye maka, ya kawo maka sau?i a zuciyarka. Mutum sai ba?ar zuciya kamar ta kafurai? Ai duk inda musulmi yake da yafiya aka san shi" ta faWa tana kallonsa ta gefen ido.

"Sai ki kafurta ni ai, daga yau ki buga min stamp Win karifi."
"Ni ban ce ba."
"Kima ce mana, in ke kike karSar ibadata sai ki daina daga yau" ya faWa yana kallon ta fuskarsa a Waure. Ta yi dariya sosai tana girgiza kai, ta yi kewar wannan ba?ar maganar tasa nesa ba kusa ba. Ta ce, "Musulmi mai kallon gabas yana kai goshi ?asa da yafiya aka san shi." Bai amsa ba ya Wauke kai sai kuma ya ce, "ki jira na saka a kai ki, kin ci albarkacin Marmerh, da wallahi sai dai ki je da ?afa."

Didi ta yi dariya ta ce, "na ji, na gode." Bai ce komai ba ya fita, Didi tana ta dariya ta ce, "Allah ya shirya Omar." Nayla murmushi yake yi dan dramar su da Didi burge ta take yi sosai, ya mayar da Didi itace ?anwa shine yayanta. Ba jimawa ya dawo, Didi ta fita Nayla ta raka ta har motar ta shiga sannan suka wuce ita kuma ta dawo.

? ? Tana dawowa falon ta kalle shi, haWa ido suka yi ta murguWa baki ta Wauke kai. Dariya yake yi a zuciyarsa ganin ta haWe rai kamar ba ita ba, yana girgiza kai da mamakin lallai ta waye. Sake kallonsa ta yi ta ga ya Waure fuska fiye da Wazu, gabanta ya faWi ta ce, "Me zan dafa maka?."

Da sauri ya juyo ya kalle ta yana buWe ido cikin kaushin murya ya ce, "na ce ina da bu?atar abinci ne? Ko na ce akwai abinda nake bu?ata daga wajanki? Lallai sai kin kula ni?." Nayla ta yi rau-rau


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login