Showing 135001 words to 138000 words out of 332344 words

Chapter 46 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

30917

don Allah."

Ajiyar zuciya ya yi ya kalli window bai kalle ta ba ya ce, "na yi ha?uri ko Nayla? Kin san abinda nake ji da zaki ce nayi ha?uri?." Jin ya fara magana a kausashe ya saka ta sake langwaSewa ta ce, "ban sani ba, amma ka yi ha?uri wallahi ba halina ba ne, in kana ganin ?arya nake ka tura har inda nake aiki a tambaya."
"Hmmm!" Shine abinda ya furta kawai bai ce komai ba.

Barin jikin window ya yi ya ?araso ya zauna akan sofa ya harWe hannayensa waje Waya yana kallon wani wajan daban. Nayla ta ?araso inda yake tana kallonsa bata ce komai ba.

Shiru ya ratsa tsakaninsu, ya zubawa waje Waya bai ce komai ba ita kuma bata yi magana ba. Ajiyar zuciya ya yi ya kalle ta ya ce, "Tun farko na san da maganar aikinki, iyayenki sun faWa min amma a lokacin na ce ina ruwana, in ma duniya zaki bari ba aiki ba bai dame ni ba. Ashe na yi babban kuskure, ashe na yi kuskuren da ban taSa yin irinsa ba a rayuwata. Barin ki kina aiki kamar a ha?a rami ne a binne ni da raina. Amma...." Ya ja numfashi mai tasho kana ya ce,

"Bazan hana ba, bani da wannan ikon na hanaki aiki tunda na san dashi, in na hanaki ma na cutar dake. Amma akwai gabSar da za a zo zaki ajjiye aikin matu?ar kina son zama dani, bazan juri wannan abubuwan a tare da matata ba. Amma a yanzu zan yi ha?uri, na san da batun aikinki tun ba yanzu ba, ban isa na hana ba" ya faWa tana Wan lumshe idanunsa a hankali yana buWewa a hankali. Nayla ta ce, "i'm sorry." Ya kafa mata ido ?irr yana kallon fuskarta, ita kam idanunsa da suka koma ja ya saka ta sunkuyar da kai bata ce komai ba.

"Jidda kin san zan iya tashin garin Kano a kan kishinki? Zan iya fuskantar ko wanne ?alubale akan hakan. Zan iya aikata komai akan kishinki, zan iya...." maganar ma?alewa tayi yana girgiza kai kafin ya ce, "Ki kula!" Ya faWa yana girgiza kai yana cize bakinsa cikin sautin da yake nuna takaicin da zuciyarsa take ciki.

"Ka yi ha?uri!."
"Laifi ki ka yi ki ke bani hakuri!?." Yadda ya yi maganar cikin kaushi ya saka ta Wan yi baya bata ce komai ba.
KRB3P47

Omar ya ja dogon numfashi ya kulle ido ya sake jan numfashi ya Wora ?afa a kan Waya ya ce, "laifina ne, ban san abin zai zama haka ba da tun farko bazan amince da aikinki ba. Bazan amince ba!" Ya faWa yana shafa fuskarsa da duka hannayensa.

Nayla ta ri?e hannunsa kawai ta fashe da kuka ta ce, "I'm sorry YaMar bazan sake ba, kuma in kana so sai na daina zuwa aikin gabaWaya. Kuma ni bana kula kowa, bana magana da kowa sai maganar aiki kawai." Yana jinta amma bai san me zai ce mata ba, dan wallahi a yadda yake jin zuciyarsa bai san abinda zai iya aikatawa ba.

Ta jima a haka tana ri?e da hannunsa kafin ya ce, "ki je." Nayla ta Wago ta kalle shi ta ce, "ba ka ce ka ha?ura ba ai."
"Na ce ki bani waje." Nayla zata yi magana ya ce, "na ce ki bani waje!" Ya faWa yana wara idanunsa da suke matu?ar bata tsoro.

Sai kawai ta sake fashewa da kuka ta sake shiga jikinsa ta ri?e shi tana kuka sosai. Kanta yana shimfiWe a ?irjinsa a daidai saitin zuciyarsa, ta zaga da hannun ta ri?e shi sosai tana kuka.

Wani irin abu yake ji daga zuciyarsa yana sauka kamar abu yana zubewa a ?asa, ya lumshe ido yana jin sassauci akan kishin da yake addabar zuciyarsa. Sun jima a haka kuma bata daina kuka ba ya ce, "ya isa, ki bar kuka ki je ki kwanta." Ta girgiza kai ta ce, "ka yi ha?uri?." Shiru ya yi bai ce komai ba ta ce, "in baka yi ha?uri ba babu inda zan je." Lumshe ido ya yi ya sake buWewa ya raba ta da jikinsa dan hakan ba ?aramin canja masa yanayi yake yi ba ya ce, "na yi, ki je."

Nayla ta kalle shi har lokacin fuskarsa babu walwala ko kaWan ta ce, "a nan zan kwana" ta faWa tana sunkuyar da kai.
"Yau me ki ka gani a Wakin?."
"Babu komai, a nan dai zan kwanta." Kawar da kai ya yi tare da yin murmushi kaWan ya koma ya zauna bai ce komai ba.

Nayla ta wuce ta je ta zauna a gefen gadon tana goge hawaye. Ta jima a zaune shima yana zaune babu wanda yake magana a cikinsu, shi waya ma yake dannawa. Kwanciya ta yi jiki a sanyaye sai da ta jima da kwanciya sannan ya tashi ya kwanta bayan ya kashe hasken Wakin ya kwanta. Shiru bai motsa ba itama bata motsa ba, ya juya ya kalle ta bai ce komai ba dan ya san idonta biyu kafin ya ga bacci ya Wauketa.

Murmushi ya yi da ya tabbatar tayi bacci ya matso yana kallon fuskarta. Abin mamaki yake bashi, Omar ne da wata a kwance a gado Waya sunan matarsa, Omar da son wata a zuciyarsa yana jin kishin ta kamar ya Wora hannu a kai ya yi ihu saboda zafin kishin. Bai taSa kawowa hakan zai faru a rayuwarsa ba sai gashi ya faru. Fuskarta ya shafa a hankali ya ja hancinta kafin ya koma ya kwanta dan fushi yake da ita.

Tun asuba ta lura da bai bar fushi ba fuskar sa tana nan a yadda suka kwanta, ta dai gaishe shi ya amsa daga nan bai sake cewa komai ba. Da safe ta yi breakfast bai ?i ci ba ya ci amma bai ce mata komai ba daga nan ya fita. Da wannan damuwar ta yini ranar, Allah ya taimaketa Jidda ta zo, zuwan Jidda ya saka aka kira Salma suka baje suna hira. Sai yamma Jidda ta tafi bayan ta sake bata shawarar da take ganin in tayi amfani da ita zamansu zai sake wuce yadda yake. Salma ma ta wuce gidan Hajja aka bar ta ita kaWai.

Girki ta yi Wan kaWan ta ajjiye masa, bai shigo ba sai gab da magriba shima bai jima ba ya fita bai dawo ba sai bayan i'sha. Yana shigowa tana fitowa cikin fitted gown ta lace mai bala'in kyau, lace Win pink colour ne hakan ya saka ya karSe ta ya amshi fatar jikinta. ?are mata kallo yake yi cikin shau?i da tsantsar qauna da kuma zallar sha'awarta da ta fara mamaye masa zuciya da gangar jikinsa lokaci Waya.

Ita kanta ta tsargu da kallon da yake yi mata, domin ba kallo ne na ko yaushe da ya saba ba. Ta Wan sunkuyar da kai ta ce, "sannu da zuwa." Bai amsa ba kuma bai daina kallon ta ba, ta Wago kai a hankali ta kalle shi, ta Wauka da suka haWa ido zai janye idonsa amma sai ta ga bai yi ba sai ma lumshe idon da ya yi ya sake buWewa a kanta. Ta ce, "YaMar sannu da zuwa." Sai a sannan ya Waga mata kai alamun yauwa tare da yin ajiyar zuciya.

Wuce ta ya yi ba tare da ya ce komai ba, Nayla ta bishi da kallo ta ce, "Wannan bawan Allah yana da abin mamaki, yau ya koma fari, gobe ya koma ba?i." Tana so ta shiga wajansa kamar yadda Jidda ta ce amma nauyin hakan ta ke ji a zuciyarta, kawai sai ta zauna tana jiran fitowarsa.

Ya Wan jima a Wakin sannan ya fito da alama wanka ya yi ya canja saka doguwar riga, yana fitowa ya buWe ?ofa ya sake fita bai kulata ba. Bai jima ba ya dawo Nayla dai tana zaune tana kallonsa ya zauna akan kujerar yana fito da kayan da ya karSo.

Waya ya Wauka yana dannawa yana kuma kallon kayan, da alama a jikin kayan akwai abinda yake gani yake rubutawa. Nayla ta rasa abinda zata yi masa ya sakko daga dokin fushi, sai ta tashi ta Wauko abincin gabaWaya ta kawo ta ajjiye a gabansa ta ce, "YaMar!." Ido ya Wago ya kalleta ta ce, "Ina ta yi maka magana kana share ni, tun Wazu nake ta jiranka."

Ido ya lumshe a hankali ya buWe, ya Wauke kansa daga kallonta bai ce mata komai ba. Zama ta yi a gefensa ta ce, "YaMar!." Ajjiye abinda yake hannunsa ya yi ya kalle ta a Wan fusace ya ce, "bakya ganin aiki nake yi?."

Idonta ya yi ?wal-?wal zata yi kuka sai ya janye idon daga kallon ta ce, "To ka yi magana, tun Wazu nake jira ka har girki na yi maka."
"To na gode" ya faWa ba tare da ya kalle ta ba yana cigaba da abinda yake yi. Serving Win abincin ta yi ta mi?a masa ta ce, "ka ajjiye aikin ka ci abinci don Allah, ba don ni ba, don Allah."

Tsayawa ya yi da abinda yake yi ya ajjiye Win kamar yadda ta ce, ya karSi abincin ya fara ci amma bai ce mata komai ba. Murmushi ya ga ta yi sai ya ji daWi a ransa ko babu komai ya sakata murmushi. Kamar yadda ta lura da bashi da cin abinci sosai shiyasa bata zuba masa da yawa ba, hakan ya saka ya cinye ya ajjiye ya cigaba da abinda yake yi.

"Ya yi daWi, na gode." Jin maganar ta yi a sama ba tare da tayi zato ba, ta kalle shi ta ga ba ita ya ke kallo ba. Murmushi ta yi mai sauti bata ce komai ba, yana zaune kafin ya tashi ya tattara kayan ya shiga Waki. Tashi ta yi ta shiga Waki ta saka rigar bacci mai santsi da siririn hannu amma tana da kauri kuma iyakacinta guiwa. Kamar yadda ta saba haka ta shafe jikinta da sabon turarenta na wajan Jidda.

Frame Win da ta siya masa ta gani a inda ajjiye, sai ta yi murmushi ta Wauka ta buWe ta ce, "bara na je a saka." Har zata fita a haka sai ta dawo ta saka hijjab ta Wauki frame Win ta fita. Da ta shiga Wakin baya nan, hakan ya saka ta jawo stool na madubi ta taka ta cire frame Win Wakin ta ajjiye, ta Wauki wancan zata saka. Hijjabin jikinta ne yake harWeta ya hanata sakawa, ta cire shi ta cilla kan gado ta Wauki frame Win ta kafa a wajan. Murmushi ta yi tana kallon frame Win ya yi kyau sosai a wajan.

?afa ta sako da niyar sakkowa ?afarta ta juye ta yi baya zata faWo ta ji ya ri?ota ta faWo jikinsa gabaWaya. Hannunsa yana kan cinyoyinta dan ta faWo jikinsa gabaWaya ya cafeta kamar ?ar baby. Gabanta ya faWi sosai ta fara ?o?arin sauka daga jikinsa, bai hanata ba ya ajjiyeta kamar zai yi magana sai ya shareta.

Frame Win da ta saka ya Waga kai ta kalla kafin ya ?arasa ya zauna, ta kalli inda hijjab Winta yake taga ya zauna a kai. Tana tsaye cak a waje Waya bata motsa ba saboda kunyar rigar jikinta gashi ya zauna akan hijjabinta kuma babu fuskar da zata yi masa magana. Shi kam tun daga kalamin ?afarta yake kallonta har kanta da yake sanya da hula wacce ta rufe kunnenta da ita. Ganin tsayuwar tayi yawa ta Wago ta kalle shi a hankali ta ce, "Hijjab Wina" ta faWa tana nuna masa.

"Zo ki karSa" ya faWa ba tare da ya kalle ta ba, ta tako a hankali ta ?araso inda yake zaune. Tana zuwa ya jawo hannunta ta faWa jikinsa da ?arfi dan bata yi zaton hakan ba shiyasa ta tafi gabaWaya.

Lumshe ido ya yi jin ?hamshinta ya daki hancinsa ya ratsa zuciyarsa, tsigar jikinsa ta tashi zuciyarsa ta fara wani irin bugawa da sauri. A hankali ya saka hannunsa ya zagaya dashi ya ri?e ?ugunta ya sake haWata da jikinsa sosai ya saukar da hancinsa wuyanta yana jin ?hamshin da yake ruWa shi yana tashi a wajan.

Nayla ta tsorata sosai, idanunta a waje dan ko kusa bata kawo hakan zai faru ba, gashi ta kasa koda motsi balle ta ?waci kanta ta gudu. Ya dabaibayeta ya kuma ri?eta gam ta yadda bazata iya motsawa ba. Tana jin yadda yake yawo da hancinsa a wuyanta yana sha?ar khamshin da yake fita daga wajan a hankali, ?hamshin yana saka shi cikin wani irin yanayi. Lokaci Waya yanayinsa ya canja ya saka hannu ya zame hular kanta ya cire ribbon Win da ta Waure gashinta ya saka yatsunsa ya warware gashin ya sauka a jikinta gabaWaya. Zuciyarta bugawa take yi, jikinta ya fara rawa, murya a sha?e ta ce, "YaMar!."

FaWar hakan da tayi sai ta sake kashe masa jiki, yayi shiru bai ce komai ba tana dai jin sautin numfashinsa da yadda zuciyarsa take bugawa. Nayla ta tsorata matu?a da yanayinsa, hankalinta ya tashi sosai tsoro ya gama mamaye mata zuciya da gangar jikinta. Murya na rawa ta ce, "YaMar....!" Yadda ta ja sunan bai san ya Wago fuskarta ya haWe bakinsu waje Waya ba jin tana neman zare masa hankalinsa daga jikinsa.

Wara idanu Nayla tayi jin abinda bata kawo shi a zuciyarta nan kusa ba, ta fara ?o?arin zamewa amma ta kasa dan ya ri?eta sosai, bata daina ?o?arin ?wacewa ba ta cigaba da motsawa dan ta gudu amma babu dama. Motsawar da take yi sai yake ji tamkar tana taya shi ne ya sake ri?eta sosai yana kissing Win ta a hankali.

Yanayin ya zo musu a ba?on yanayi, hakan bai taSa faruwa ga ko wannen su ba sai a lokacin, dalilin da ya saka take ji zuciyarta na bugawa sosai tana ji kamar yana zu?o jinin jilinta ne saboda yadda yake kissing Winta.

Ba tare da ya daina abinda yake yi ba ta ji yana saukar da hannun rigar ta ?asa. Hankalinta ya kai ?arshe wajan tashi, jikita ya cigaba rawa sosai tana so ta ?wace amma ta kasa sai hawaye da yake zuwa daga idanunta.

Ba zato babu tsammani ta ji ta koma kan gadon ta kwanta jikinta ya cigaba da rawa ta fara kuka mai sauti ta ce, "YaMar don Allah ka yi....ha...?u....ri!." Yana jinta amma a yadda yake jin gangar jikinsa a wannan lokacin ba zai iya ?yaleta ba, jikinsa shi kansa rawa yake yi, abinda yake ji a jikinsa ba?o ne bazai iya jurewa ba, ji yake in ya jure zai iya rasa ransa. Gangar jikinsa ce take sarrafa zuciyarsa, ya ruWe ya zama kamar zararre, ya rasa inda zai saka ransa ya huta. Ya zama kurma saboda kunnensa sun daina aiki, ya zama makaho saboda idanunsa sun daina gani. Abinda ya saka a gaba kawai yake yi ba tare da tunanin komai ba.

Ganin duhu ya mamaye Wakin ya saka Nayla ?ara ?arfin kukanta, kafin ta yi yun?urin mi?ewa ta ji ya cigaba da kissing Winta, yadda jikinsa yake rawa haka nata ma yake rawa, zuciyarsu dukka bugawa take yi saboda ba?on yanayin da yake kawowa gangar jikinsu barazana.

OKAY! KRB3P048

Tun bayan shuWewar wasu Wa?i?u jikinsa yake rawa, zazzaSi ya yi masa dirar mikiya, ciwon kai da ciwon gaSoSi suka tarar masa a lokacin da bai yi tunani ba. Ko motsi ya kasa yi, yana kwance saboda ciwon da yake ji bai taSa jinsa a jikiinsa ba. Idanunsa sun yi ja fuskarsa ma haka, har ruwan wahala ne yake sakkowa daga idanunsa saboda azabar da take ratsa ilahirin jikinsa. Juyawa ya yi ya kalli Nayla da take kwance a inda ya barta, bacci take yi ko a sume take bai sani ba. Tun da yana jin maganganunta ?asa-?asa har ya ji ta ja dogon numfashi, daga nan bai sake ganin tayi ko motsin ba.

Runtse ido ya yi ya dafe kai da hannayensa a wahale ya furta, "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!." Sake ?o?arin mi?ewa ya yi a karo na babu adadi amma ya kasa, ya koma ya kwanta yana jin kansa kamar ana dukansa da guduma. Ita kawai yake kallo, so yake ya tabbatar da halin da take ciki amma ya rasa ta ina zai fara.

Ya fi awa Waya a haka ya kasa koda motsin kirki, idanunsa har yaji suke yi suna lumshewa zasu rufe. Da?yar ya tattaro ?arfin da ya rage masa ya tashi zaune yana jan numfashi da?yar cikin tsananin azabar da yake ji. Gwada mi?ewa tsaye ya yi amma sai ya kasa saboda jirin ya kwashe shi ya cilla shi kan gadon. "Hasbunallahu wani'imal wakil, Allah ka taimake ni na duba wannan baiwa ta ka" ya faWa kamar zai yi kuka.

Da?yar ya iya tashi tsaye ya dafe bango yana ji kamar zai kifa, motsa ?afarsa ya yi da niyar takawa sai ya kasa jin ta WaWWaure irin wanda ya yi aikin wahala ya gaji. A wahale ya ce, "Ya Salam!." Sai da ya huta sannan ya sake takawa, yana yi yana hutawa har ya kai kansa banWakin. Ya kwashe mintina sama da talatin a ciki sannan ya fito, yana takawa da?yar cikin dauriya yana cize baki ya ?arasa inda take ya zauna.

Kanta ya tallafo zuwa jikinsa sai ya yi saurin saki jin wani mahaukacin zafi ya ratsa tafikan hannunsa. Sake ri?e kan nata ya yi ya Wago ta ya jijjigata a hankali ya ce, "Jidda! Jidda!! Jidda!!!" Furta hakan yake yi a raunane yana jijjigata da ?arfin da ya rage masa, amma ko alamun motsi Nayla bata yi.

"Wayyo Allah, me yake faruwa haka? Jidda! Nayla! Hauwa! Ashiq ki buWe ido don Allah, ki taimake ni ki buWe idanunki!" Ya faWa kamar zai yi kuka yana jijjigata amma Nayla bata ma san yanayi ba. Ajiyar zuciya ya yi ya fitar da iska mai zafin gaske cikin rashin sanin abinda zai yi mata. Hannunsa ya kai hanci ta wai ko zai ji tana numfashi amma ji bai ji komai ba hakan ya saka shi ya tsorata sosai.

Da?yar ya lallaSa ya iya mi?ewa ya shiga banWakin ya Webo ruwan sanyi ya dawo yana shafa mata a fuska a hankali, jikinsa rawa yake yi sosai saboda zazzaSin da ya ke damunsa, amma ita yake so ya ga tayi ko da dogon numfashi ne hankalinsa zai fi kwanciya.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login