Showing 324001 words to 327000 words out of 332344 words

Chapter 109 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14417

kukan sai lokacinsa ya yi.

Ta kalli fuskarsa ta ce, "nida ko kazar amarcin nan ta hausawa baka siya min ba." Ya yi dariya sossi yana girgiza kai tare da murza goshinsa da yatsu biyu ya ce, "ni fa ban san da ita ba a lokacin, sai yanzu da nayi abokai nake ji ana faWa, amma wallahi a baya ni ban san ana siyan wata kaza ba Jidda. Na san dai ana yin sallah, wannan marigayi Malam Salahudden shine ya sanar dani shekaru baya da suka wuce. Addu ar da ake yi in an idar kuma a waya na iyata, yawan zama active da nake yi a kan network a haka naji malamai suna koyawa har na haddace. Duk da sallar ta mu a makare muka yi ta amma mun yi Win, kaza ce dai ba a siya ba& . Ya sauke numfashi ya ce,  Allah ya kai hasken rahama kabarin Didi, ta yi wahala dani a rayuwa sosai, ba dan ita ba wata?ila yanzu ko karatun sallah ban iya ba."

Nayla ta ce, "Amin ya rabbi. Kuma ban Wauke maka ba, sai ka siya min kazar ." Ya kalle ta yana murmushin gefen baki ya ce, "za a siya Jidda, wacce kike so, fried ko grill one?." Ta Wan juya idanunta kana ta ce, "grill Win dai."
"Yanzu zan samo miki tunda yau ma amarya ce ke ai, na je na dawo?" Ya faWa da sigar tambaya.

Ta sake kwanciya a jikinsa tana ri?e kafaWarsa ta ce, "Akwai sanyi kar ka fita, na yafe."
"Ni ban yafe ba, yanzu zan je na dawo, ki jira ni."
"A'a kar ka fita, Allah na yafe."
"Allah ban yafe ba, ina zuwa" ya faWa yana tashi ya Wauki jacket Win da yazo da ita ya saka, ya saka hular sanyi ya rufe kunnensa sannan ya fita. Da murmushi ta bisa, sai ta tashi ta shirya cikin shigar da zata gigita mata shi da ?hamshin da zai tashi hankalinsa.

Ba jimawa ya dawo, da yake tana zaune bai ma kula da shigarta ba ya ce, "na sha wahala kafin na samo miki, kin san da yake ban san ?asar ba. Maza zo ki ci." Ya faWa yana buWe kazar sai tiriri take yi. Bata musa ba ta tashi ta sakko kusa dashi suka ci tare suka ?oshi. Sai bayan ta gama ci ta ga yana yana kallon ta yana dariya tare girgiza kai, ta ce, "me ya baka nishaWi haka?." Ya Wan buWe idanunsa ya a ce, "An ce in aka ci kazar ai ana biya ko?."

Ta kalle sa kamar bata gane ba ta ce, "Kamar ya ana biya? Wai gobe sai na siyo na biya ka?." Ya zuba mata ido ya ce, "ke a nan zaki bi ai madam" ya faWa tana nuna mata kan gado Wakin. Ta kalli gadon ta kalle sa ta ce, "ban fa gane ba."
"zaki gane yanzu ai, mu je ki wanke hannunki." Tare suka wanke hannu da wanke baki suka dawo.

Nayla ta Wan harare sa ta ce, "Daman saboda na biya ka ka siyo min?." Ya Waga ido sama alamun tunani ya ce, "Eh kusan haka gaskiya, dan ina so na karSi bashin kazata da kyau."
"Ko babu kaza da kyau za a biya ka bashin da aka karSa a hannunka, meyasa sai da ka wahala ka fita ana sanyi? Da baka wahala ba ma zaka ga tanadin da aka yi maka.
"Ina son na cike gurbin da na bari ne a rayuwarmu Jidda.
"Babu wani gurbi da ka bari baka cike ba YaMar, komai ka cike sa. Ka sake buWe shafin sabuwar rayuwa a gare mu."

"Da gaske Jidda!?" Ya faWa a hankali yana kallon ta. Ido ta rufe tare da buWewa alamun eh ta ce, "komai da komai, da komai Rouhi."
"Zan iya ro?ar alfarma Jidda?."
"Komai ka ke so ka faWa kawai& 
"Ki zauna tare dani, ko yaushe ki kasance a tare dani, kar ki barni nayi kukan rashin ki, ki ri?e ni hannu biyu, ki mayar dani dan gatan ki."

"Ka Wauka an gama Rouhi, daman ko yaushe kai Wan gatan Nayla ne. Wannan alfarmar daman akwai ta, ka canja wata sai ayi maka. Ya zuba mata ido cikin soyayyarta da yake ji kullum kamar sabuwa na shiga zuciyarsa. Ganin ya zuba mata ido sai ta ce, "zan tabbatar maka da gatan da ka ke dashi Rouhi, zan baka abinda ka yi ha?uri rashinsa na tsahon kwanaki" ta faWa cikin salon da ya zautar da Omar aljanunsa su fara ?wan?wasa ?ofa. A nan suka shiga faranta junansu rai da nunawa juna soyayya mai tsayawa a zuciya.

_Jiya na yi kuka sosai, na gama editing ina burin yau na yi update gabaWaya na huta, ina shiga naga ya dawo farko=?-? over 10k words, haka na gama kukana editing ya dawo farko. Na so na gama uptade yau amma ba zai yu ba, sai zuwa gobe in sha Allah._

Nana Haleemad'?
P129

Nayla bata farka ba sai bayan sallar azahar, tana tashi agogon wayarta da ya juya zuwa na ?asar ta duba, da sauri ta diro daga kan gadon ta shiga banWaki da sauri ta watsa ruwa ta yi alwala ta fito ta tayar da sallah. Tana idarwa ta saka doguwar riga mai siririn hannu wacce take da zip ?arami a gaba. Yunwa take ji, hakan ya saka ta fitowa falon tana Waure gashin kanta dan bata saka hula ba.

A zaune ta ganshi ya bawa Marmerh wayarsa tana game, Musliha na gefen Marmerh tana taya ta kallo shi kuma ya saka Mufty a pusher yana Wan jijjiga pusher Win kaWan. HaWa ido suka yi da ita sai ta ce, "Har anyi sallar azahar ina bacci, baka tashe ni ba" ta faWa tana zama a kusa dashi. Ya bita da kallo ya ce, "Nasan kin gaji sosai, bacci ki ke son yi."

Ta kalli Mufty da yake cikin pusher ta ce, "ko dan shi ai sai ka tashe ni Rouhi, bashi da abinci sai a wajena."
"Da kina bacci ai na bashi ai."
"Me Win?."
"Abincin na sa mana." Ta sake kallon sa ta ce, "Wai ina bacci aka yi haka ban sani ba?." Ya Wan tae baki yana Waga gira tare da murmushi lokaci Waya.

?aukar Mufty tayi da yake kallon ta ta shafa fuskarsa tana murmushi ta ce, "Tunda Daddy ya saci abinda ba nasa ba ya baka ai shikenan" ta faWa a hankali saboda su Marmerh. Murmushi ya yi ya kwantar da kansa a ?afadarta ya ce, "Na haWa miki tea ko coffee?." Ta Wan Wago ido sama kamar mai tunani ta ce, "Uhumm coffee."
"An gama" ya faWa yana tashi ya nufi mini kitchen Win da yake Wakin, ya haWo mata coffee ya kawo mata ta karSa tare da sipping a hankali. Ta kalle shi bayan ta haWWiye ta ce, "DaWina da kai ka iya haWa coffee, ka koya da kyau."

Bai ce mata komai ba ta cigaba da shan coffee, shi kma ya buWe mata abincin da yake ajjiye ya ce, "Ga abinci nan, sai ki ci. Ta ce, "Thank you my love." Bai ce komai ba sai kallonta da yake yi cikin tsananin ?aunarta da soyayya. Yana tuna maganar Didi da take cewa sai ya so Nayla fiye da tunaninsa, a lokacin da take faWa haushi yake ji kamar ya sha?eta, amma tun tana duniya soyayyar ta bayyana wacce bai yi zato ba. Nayla gajiya tayi da kallon da yake yi mata, ta shagwaSe fuska ta ce, "Rouhi ka daina kallona."

"Musliha, Mummy ta cewa Daddy Rouhi" suka ji Marmerh ta faWa cikin hausar ta da take fita tar kamar ba yarinya ba. A tare suka yi dariya shi da ita, Nayla ta kalli Marmerh ta ga ita take kallo. Kafin ta yi magana Marmerh ta rigata ta ce, "Mummy kin yi kyau." Nayla ta yi dariya?yana jinjinga girmar surutun Marmerh ta ce, "Zo my baby." A tare suka taso suka taho a guje, ta rungumesu tare da yi musu peck a goshi suma suka yi mata ta ce, "Kun ci abinci?." A tare suka amsa ta ce, "To ku je ku cigaba da game."

"Mummy ni Mufty zan Wauka" Marmerh ta faWa tana kallon ta. Nayla ta ce, "A'a Marmerh, bacci yake ji yanzu, in anjima sai ki Wauke sa." Ta amsa da to ta koma ta zauna suka cigaba da game. Kallon ta yake yi yana murmushi mai cike da alfahari, ya kalle ta ya tuna ita matarsa ce wacce ta haifa masa yara yana ji kamar babu wanda ya kai sa farin ciki a duniya. Nayla ta sake kallon sa ganin har lokacin ita yake kallo, ta bashi light kiss a lips Winsa ta ce, "ka daina kallona."

Bai yi magana ba kuma bai daina kallonta ta ce, "yau ma ka zama kurma ne?."
"Uhum uhum! So nake ki huta dakyau." Tayi dariya ta cigaba da cin abincinta. Bata jima ba ta kammala, lokacin sallar la'asar ya yi suka sallah gabaWaya har su Marmerh.

Tana zaune tana cin burger su kuma suna cin shawarma. Omar ya dawo kusa da ita ya zauna,? ya saka hannu a aljihu ya Wauko ring cover kana ya ce, "na ga hannunki." Ba musu ta basa hannunta, ya kalli hannun ya ga zoben gold Win da ya bata yana nan a inda ya saka mata. Ya cire gold Win ya canja masa waje, ya buWe cover ya Wauko ya ciro diamond ring by Titan compony ya saka mata a yatsanta. Yadda ya yi mata kyau yana kalla, ya yi murmushi tare da yiwa hannun nata kiss ya kalli idanunta kamar yadda take kallonsa.

Nayla ta kalli zoben, ta Waga ido ta kalle sa ta ce, "Rouhii, diamond ring!." Ya rufe ido ya buWe a kan fuskarta?bai ce komai ba. Cikin wani irin yanayi na farin ciki ta ce, "Rouhi....."
"Ina ji dake Jidda, kina da mahimmaci mai girma a rayuwata, li saka wannan a zuciyarki.

Murmushi take yi tana kallon zoben, ta sake kallon sa cikin farin ciki ta ce, "Rouhi nima ina ji dakai, ina sonka Rouhi!. Diamond ring ne, Diomond ring compony Titan Rouhii. Siya min ka yi?." Ya murza zoben a hannunta a hankali tare da sake kissing hannunta kana ya ce, "ina da wacce zan siyawa ne in ba ke ba? Na ki ne Jidda."

"Oh my god! Oh my god! Rouhi zaka yi kisan kai fa, farin cikin da ka ke bani zai min yawa" ta faWa tana ?an?ame sa cikin tsananin soyayya da farin ciki. Bayanta ya shafa a hankali, ya Wagota daga jikinsa yana shafa fuskarta da yatsu biyu ya ce, "in dai farin ciki yana yin yawa ina so ya yi miki yawa Jidda, in kuma baya yawa ina so daga kan ki ya fara yin yawa. Ina son na saka ki farin cikin da baki taSa shigarsa a duniya ba."

"You won Rouhi, ka yi nasara akan wannan tuntuni. Ka bani farin cikin da ban same sa a ko ina ba sai a wajanka, ni ban san me zan ce ba Rouhi, ban sani ba. Na rasa wacce kalma zan yi amfani da ita wajan nuna maka farin cikina, na rasa me zance maka! Ta faWa a sanyaye tana kallon idanunsa da suke kashe mata jiki.

"Ba sai kin ce komai ba Jidda, zan iya sadaukar da duk abinda na mallaka dan na zauna dake kawai. In aka ce na zaSa a tsakanin ke da duk abinda na mallaka na Wauki Waya na zauna dashi a duniya....wallahi ke zan Wauka Jidda. Su in na rasa su zan iya samun wasu, ke kuwa har abada na rasa kenan sai dai madadin ki."

Ganin ta kwaSe fuska zata yi masa kuka ya ce, "kar ki yi min kuka Jidda, ki mayar da hawaye nan bana son ganin su akan kan kyakykyawar fuskar ki" ya faWa yana goge mata ido ya ce, "Meye diamond ring na Titan? A arzu?in da Alalh ya yiwa mijinki diamond ring ba komai ba ne, ke kin sani ai, tare muke yin komai dake, kin san nawa aka samu kin san nawa aka kashe, ko naira biyar ce ta shigo account Wina kin san da shigowarta. Jiddana..In ana siyan duniya zan iya siya miki kawai dan ki yi farin ciki." Sake komawa jikinsa ta kwanta tana jan numfashi, ta ri?e sa sosai tana cewa, "I love you so such, I love you forever and ever and ever. Thank you so much, thank you my world."

Gefensa?ya kalla ya ga Marmerh da Musliha suna kallon su, ya yi murmushi ya Wagota daga jikinsa ya ce, "Marmerh ku zo." Ba musu suka taho a guje, ya ri?e hannun Marmerh da Musliha yana kallon fuskarsu da take kama da ta juna ya ce, "Ku zama shaida, Daddy yana son Mummy sosai, yana matu?ar sonta, bashi da abinda yake so kamar ta. Daddy yana ji ina ma Mummy ta zama popcorn ya cinye." Marmerh sarkin wayo ta yi dariya ta ce, "Daddy dama mutum yana zama popcorn?." Ya ja kumatunta ya ce, "I wish Mummy ta zama haka, I want to be with her& . Sai ya daina kallon su ya kalli Nayla da take kallon sa ya ce,  for rest of my life.

Musliha ta ce, "Daddy, ina son Mummy." Ya bata hannu ya ce, "give me five." Suka tafa tana dariya, shima ya ce, "Daddy ma yana son Mummy." Marmerh ta ce, "Nima ina son Mummy." Suka tafa itama yana shafa kansu cikin ?aunarsu. Ya juya ya kalli Nayla da take ta murmushi tana kallon su ya ce, "Muna son Mummy, muna sonta sosai."

GabaWaya ta haWa su a jikinta har shi ta rungume tana ajiyar zuciya. A kunnenta ya ce mata, "I want to be with you, ki yi wani abun, kin ji Mummy." Kallon sa ta yi ya Waga mata yalwatacciyar girarsa sama, ta yi murmushi tana jin ?aunarsa na sake shiga zuciyarta da gangar jikinta.

Tashi ya yi ya shiga Waki bai ce komai ba, ta kalli su Marmerh da suka koma suka cigaba da game a wayarsa, sai ta kunna musu tv ta kai cartoon, suka ajjiye waya suka fara kallon tv. Nayla ta Wauki Mufty ta shiga dashi Wakin.

Ajjiye sa ta yi a kan gado, ta nufi Omar da hanzari Wafe a jikinsa. Omar ya Wagata sama yana juyawa da ita a cikin Wakin cikin tsananin soyayya. Sai da ya gaji sannan ya sauke ta, ya ri?e fuskarta tare da haWa goshinsa da tana idanunsa a rufe. Nayla ta ce, "Na gode Rouhi." Kai ya girgiza alamun baya son godiya ta sake komawa jikinsa tana ji kamar za a raba su.

Haka zaman Canada ya kasance cikin shau?i da soyayya kamar amare, sun ?ara sha?uwa da ?aunar junansu a cikin kwanakin, Nayla ta tabbatar da har yanzu babu wata a zuciyar Omar sai ita kaWai. Satin su Waya suka shiga America, daga nan suka shiga Qatar, daga nan suka shiga Egypt, daga nan suka shiga Riyadh. Satin su biyar basa ?asar sannan suka dawo Nigeria.

*Bayan wasu shekaru.......*

Nana Haleemad'?
P130

Abubuwa da dama sun faru a shekarun, ciki harda samun cigaba da Omar ya samu a fannin kasuwanci, ya shahara matu?a, har ta kai ta kawo yanzu bai cika harka da ?an Nigeria ba, da yawan abokan kasuwancinsa ?an foreign countrys ne. Kasancewar da turanci a bakinsa babu abinda yake yi masa wahala aiwatarwa. Har lokacin kuma bai yi karatu ba, duk da Nayla tayi naci akan ya shiga ko da open university ce amma ya ce shi baya da bu?atar yi. Omar ya kuma so busy, dan kusan ko yaushe ba ya ?asar, ga su Marmerh su shiga makaranta bai cika tafiya da Nayla ba sai ya zamar masa dole. Ba ma shi kaWai ba, har Bashir wani lokacin shi yake aike wata ?asar ya dawo.

Ya aurar da su Bashir duk su ukun, shine ya Wauki nauyin komai a lokacin bikin, ya basu gida da kuma mota, ya yi komai da komai na biki, hatta abincin da ?an biki zasu ci Omar ne ya yi. Nayla itace ta Wauki nauyin lefe gabaWaya tayi musu, aka yi musu bikin ?an gata babu abinda suka kashe a kuWinsu sai abinda ba a rasa ba. Bayan an kai amare aka aika musu da abinci, aka cika musu store taf da kayan abinci harda ruwa da lemo na bawa ba?i. Ai kuwa Omar ya sha albarka a bakin ko wanne dangi, addu'a aka dinga kwarara masa, ana yiwa iyaye da Didi addu'a, ana yi masa fatan gamawa da duniya lafiya.

Omar ya zama babban Alhaji,matashi mai ji da kuWi da alfarma a nigeria dama ?asashen ?etare, kai da ka gansa ka ga yadda ya sake komawa ka san kuWi sun zauna, saboda fatar jikinsa, maganarsa, jan ajinsa da komai na da ya canja. Ya sake zama mara sabo da mutane, in baka san sa ba ku ka haWu zaka iya fassara sa a mutum mai wula?anci, amma in ka san waye shi kai zaka bada labarin kirkinsa. Duk da wannan dau?a?ar da ya samu baya fashin ziyarar kabarin Didi duk ranar juma'a kamar yadda ya saba, ba shi kaWai ba, duk sati tare suke zuwa dasu Marmerh su yi mata addu'a su fito. Yawan shiga ma?abarta da yake yi ya saka yake ganin kabarirrikan da suke da bu?atar gyara, ba tare da ya san waye a kwance a jiki ba zai bada kuWi a gyara. Har ya zama ya sanar da masu gadin ma?abartar indai an samu kabarin da ake bu?atar gyara shi a sanar dashi kai tsaye. ?angaren sadaka da taimako kuwa sai abinda ya yi gaba lamarinsa. Islamiyyar da aka gina ta zama babbar islamiyya da ake ji da ita a birnin Kano, har lokacin kuma komai free ake yi, babu ko sisin kowa.

Duk abinda ya tashi a dangi Omar yana yi kuma yana zuwa, dangi kowa alfahari ake yi dashi, dan shekara bazata zago ta koma bai kai mutane umara ba. Hakan har ya zamar masa jiki, har ya riga ya sava rabon kujerar makka kamar ba kuWi yake kashewa ba. Hakan sai ya zama abin alfahari a danginsa, ko a wani wajen in ka ce kai Wan uwan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login