Showing 243001 words to 246000 words out of 332344 words

Chapter 82 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

30875

na ganka a aiport Win nan?."

A hankali ya Wago ya kalle ta sai ya kalli Sen da yake ta kallonsa shima mamaki kwance a fuskarsa. Kafin Omar ya yi magana Sen ya ce, "Nice to meet you Mr Omar. If possible i'd like to discuss something important with you." Omar ya kalle shi yana Waga gira fuskarsa a Waure, kamar zai yi magana sai ya fasa ya mayar da kai yana danna waya tare da murza hannun Nayla. Sen ya zuba masa ido yana jiran amsa amma Omar yayi biris kamar ba dashi ake magana ba. Didi ta zira hannunta bayansa ta Wan taSa shi alamun ya bada amsa ya share kamar bai ji ba.

Ran Sentor ya Saci ganin wula?ancin da Omar ya yi masa a gaban mutane. Ya Wan juya yana kallon wajan yaga ba a kallonsu amma escort Winsa suna jin abinda yake faruwa. Sen ya girgiza kai cikin ?unar rai yana ?arewa Omar kallo da ya harWe a waje Waya yana danna waya kamar ba shi ba. Sai da ya ga dama sannan ya kalli Sen ya ce, "can I know the details?." Da mamaki Sentor yake kallonsa jin ya mayar masa da amsa da turanci, sannan sai da ya gama ja masa aji sannan ya bashi amsa, amma sai ya danne mamakinsa ya ce, "If possible come and meet me at my house."

Omar ya wara idanu yana sake ?are masa kallon wula?anci da rainin hankali ya ce, "I think if you want to talk to me you're the one who should come over to my place right? So if you're ready, try to inform my PA to book an appointment.." Sen kallon Omar kawai yake yi cike da mamaki da al'ajabi jin yana yi masa magana cikin izza, ga turancin da yake yi.

?? Narma ta ri?e hannun Dad ta ce, "Dad!" Sai hawaye suka sakko mata ta koma wajan Omar ta ce, "ko a lokacin baya ka san ina sonka ko? Dad shine ya yi komai ba ni ba. Don Allah kar laifinsu Dad ya shafe ni, I'm ready to marry you wallahi. Na kasa nutsuwa, na kasa zama cikin hankalina saboda kai. Over one year kenan ina dakon soyayyarka, please Faruk ka taimake ni" ta faWa tana zubewa a wajan tana haWe hananyenta tana kuka sosai.

Mum ce ta ?araso wajan da ta ga abinda yake faruwa ta Wago Narma daga inda take ta ce, "meyasa ki ke haka ne? Meyasa ki ke embracing kanki akan soyayya ne Narma?. Oya jirginmu zai tashi, mu je ko?." Narma tace, "Mum bazan je ko ina ba, kalli Faruk Wina, look at him Mum" ta faWa tana nuna mata Omar.

Mi?ewa tsaye ya yi ya Wauki Marmerh da take jikin Nayla a zaune, ya ri?o hannun Nayla ta tashi tsaye ya kalli Didi ya ce, "Didi mu je ko?." Mum ta bi shi da kallo ta ce, "wannan ba shine mai company Exclusive footwear ba?."
"Yes Mum, and shine Faruk Wina, ki tambayi Dad shine." Omar ya kalli Didi cikin gajiya da surutansu? ya ce, "Didi mu je!" Ya faWa yana yin gaba, haka kawai ranar yaji ya tsani ganinsu gabaWaya, tausayin Narma da yaji a kwanaki yanzu gabaWaya ya gushe daga zuciyarsa.

Wuce su suka yi yana ri?e da hannun Nayla ita kuma tana tura jakarsa da tata da ta haWesu waje Waya, Didi ma na turata ta. Fuskar Nayla a cushe matu?a Didi ma ta kasa magana, bata so ta nuna ta ji tausayin Narma Nayla tayi kishi, in kuma ta ce bata ji tausayinta ba wallahi ?arya take yi. Ta kuma san halin Omar, indai ba tsananin kiran rabo ba babu dalilin da zai saka ya Waga kai ya kalli Narma, ta san in ya wuce ya wuce kenan baya komawa, shiyasa take jin tausayinta dan ta san soyayyarsa bazata yi mata amfani ba.

A first class flight suka zauna, kujerar Didi ce a jikin taga, sai ta Marmerh da take kusa da ita, sai Nayla sai kuma shi. Kallon Nayla yake yi yadda ta Waure fuska bai taSa ganin ta haka ba, duk sai ya damu saboda ya san ba ita kaWai ba ce akwai babynsa. Har jirgi ya tashi Didi bata san inda suka nufa ba, kuma babu wanda yake magana a cikinsu. Abinci aka kawo ya kalli Nayla ya ce, "baza ki ci ba?." Kai ta girgiza bata ce komai ba.

Ya kalli Didi da take mamakin cabin chew Win da ta gani larabawa, sannan abincin bai yi kama da wanda aka basu a zuwa Abuja ba. Omar ya ce, "Didi ki ce mata ta ci, bata ci komai ba fa." Didi ta kalli Nayla ta ce, "kici Nayla, duk da ma mun kusa sauka." Nayla ta ce, "bana son ci ne Didi."

Ajiyar zuciya Didi tayi bata ce komai ba, ta san kishi Nayla take yi kuma ya kamata daman ta yi. A gaban idanunka ace ana son mijinka ai sai inda ?arfinka ya ?are. Ita babban farin cikin ta da Allah bai tashi haWa Omar da Sen ba sai da rayuwarsa ta kai wannan mataki na alfahari, wannan abun ya yi mata daWi ta kuma godewa ni'imar Allah. Tana tuna lokacin da suka zo Abuja neman alfarma, ya wula?antata yana cewa gwara dabba a kanta. Amma yanzu gashi shine yake son magana da Omar shi kuma yana ja masa aji, Narman da aka wula?anta shi ta dalilinta gata nan har yanzu haukan sonsa take yi, in ba Allah ba waye zai yi wannan?.

Hannunta ya ri?e ya ce, "wai akan abinda ya faru ki ke fushi?." Ta zame hannunta daga cikin nasa ta ce, "Don Allah ka ?yale ni."
"Bazan ?yaleki ba, meye ya faru da zaki yi fushi ki ?i cin abinci huh? Kin san abinda yake cikinki yana bu?atar cin abincinki."
"Hmm, daman tunda aka samu cikin nan ai ba damuwa ka ke da ni na ci ba, ko yaushe saboda abinda yake cikina ka ke cewa ko yaushe. To bazan ci ba, ai na ga a cikina Wan yake ko? Ka ?yale ni."

Didi ya kalla ta yi masa alama da ya yi shiru, ya Wan yi tsaki kaWan yana kallon Agogo. Didi ta ce, "kai tafiyar nan tayi tsayi, har yanzu ba mu zo ba ne?." Nayla ta kalli Didi ta ce, "Lagos zamu biya." Didi tayi dariya ta ce, "ki ce kawai yawo muka taho, ko babu komai na shiga jirgi." Nayla ta Wan yi murmushi ta ri?e hannun Marmerh da take kusa da ita.

Duk yadda ya so Nayla tayi magana ta?i, ta kuma ?i kallonsa dole ya ?yaleta har tayi bacci. Didi tana kallonsa yadda yake zuba mata idanu, da yadda zai mata kiss a goshi, da yadda zai du?a yana matsa mata ?afa. Ita dai murmushi take yi kawai dan Nayla ta cancanci a yi mata haka.

Sai da jirgi ya tsaya sannan Didi ta Wan yi mi?a ta ce, "Tafiyar Lagos kusan awa takwas kamar mun bar Nigeria?." Nayla bata ce komai ba suka fito, Didi na ta kallon wajan suka Wauki jakarsu da pusher Win Marmerh. Nayla ta ware pusher ta Wora Marmerh a kai. Didi ta ce, "wai nan Lagos ne? Naga wajan da larabawa sosai."

Sign board Win da aka rubuta welcome to Madina Nayla ta nuna mata ta ce, "ba Nigeria ba ce Didi, kina ?asar saudia, a cikin garin Madina!."
KRB3P092
Nana haleema.

Didi ta kalli Nayla ta sake kallon sign board Win ta sake kallon larabawan da suke ta aikin su a wajan. Omar ta kalla ta ga yana murmushi sai ta ce,  Omar yau Nayla na zama abokiyar wasan ta. Ya yi murmushi ya ce,  Didi ba wasa ba ne, wallahi da gaske a garin Madina ki ke. Jin ya ce wallahi ya saka ta tsaya cak ta zuba masa idanu, ta san halinsa indai ya ce wallahi to wallahi Win ce baya rantsuwa akan ?arya kuma baya yi sai ta kama.

Didi ta kalli Nayla ta ce,  Wai da gaske?. Nayla ta mi?a mata passport Win hannunta ta ce,  kin gani, daga Abuja mun taso mun sauka a ina& ? Nayla ta faWa da sigar tambaya tana nuna mata. Didi ta kalli wajan ta sake kallo ta kalli Nayla ta ce,  A Madina nake da gaske?. Nayla ta ce,  Mu je mu hau mota mu je hotel, zan kai ki masallaci annabi, na tabbatar in muka je can zaki gasgata

Ita dai Didi gani take kamar wasa suke mata hakan ya saka ta cigaba da tafiya suka fito wajan airport Win da taimakon Nayla. Zuciyar Didi ta tsinke ganin larabawa a mota, garin kana gani ka san ba Nigeria ba ce ba. Omar ya ga kamar tana jiri ya ri?eta ya ce,  Ki nutsu Didi. Ta kalli Omar ta ce,  kuma son haukata ne kai da matarka, ku daina yi min wasa don Allah.

Omar bai ce komai ba Nayla kuwa har ta gama magana da driver ta faWi inda zai kai su ta kalle shi ta ce,  mu je. Baby pusher in aka naWe aka saka a bayan mota Omar ya shiga gaba Nayla ta shiga baya ita da Didi. Didi ta zama kurma sai kalle-kalle ta ke yi zuciyarta na bugawa sosai, wai itace a Madina dan kawai an raina mata hankali, madinan masallacin gidan sarkin Kano ne da zata je lokaci Waya haka?.

Tafiya suka yi mai Wan nisa kafin su tsaya, Nayla ta Wauko kuWi ta biya ta ri?e hannun Didi ta ce,  Didi zo mu je Hannunta ta ri?e suna takawa Nayla na jan jaka Waya haka Didi ma na ja Omar da Marmerh suna tafiya. Hotel suka shiga Nayla ta zaunar da Didi suka ?arasa reception ita da Omar, Nayla ta nuna musu evidence na rooms Win suka yi reserving da komai suka bata card Win Wakin.

Wajan Didi suka dawo ta kalle shi ta ce,  ka taho da kayan zamu je da Didi, floor 18 ne.
 Mu je tare dai.
 To tsaya na samu empty elevator sai mu shiga gabaWaya, ko da yake lokacin sallar asuba ya kusa da?yar a samu empty. Barin wajan ta yi ta ?arasa wajan elevators ta danna Waya aka ayi sa a aka samu, suka saka kayan ya ri?o Didi suka shiga Nayla ta danna floor 15 suka wuce.

Suka fita daga elevator Win Nayla ta ?arasa wajan Wakin ta saka card Win ya buWe suka shiga da kayan parlor, ta buWe rooms Win ta ga bedrooms biyu ne da parlor kamar yadda ta yi booking. Didi ta kalla da ta zama kurma sai kallon Wakin take yi cikin ruWewa. Nayla ta ce,  Didi mu je ki huta kin gaji. Didi ta kalle ta ta ce,  Nayla kar ku haukata ni don Allah. Kiran sallar asuba aka fara yi, sai Nayla ta ce,  ga kira nan ana yi, Rouhii zamu je sallah ko sai ta huta?. Ya girgiza kai ya ce,  A gajiya ki ke kema, ya kamata ki huta.
 Amma ina so Didi ta fita daga ruWanin nan, gwara mu je kawai. Didi taso ki yi wanka zamu je masallaci na tabbatar miki.

Didi kamar Nayla umarni take bata ta tashi suka shiga Waki Waya daga cikin Wakunan, Nayla ta buWe mata banWaki ta fito da kayanta ajjiye harda sabulun wanka ta ce,  ki yi wanka Didi. Fita tayi ta barta a Wakin, tana fitowa tayi kamar zata faWi ya ri?ota ya ce,  Yi a hankali, kin gaji ko?. Gimtse fuska tayi ta kalle shi ta ce,  ta shiga wanka, nima wanka zan yi ta faWa tana jan jakarta shiga da ita Wakin Didi, ta buWe ta Wauko hijjab da doguwar rigar da zata saka ta fito da kayan a hannunta zuwa Waya Wakin ta shiga wanka.

Tana fitowa daga wankan ta same shi a zaune a Wakin, bata kula shi ba ta saka kaya ta Wora hijjabinta kalle shi ta ce,  Mu zamu wuce. Omar ya bita da kallo ya ce,  Ashiq ba haka muka yi dake kafin zuwa nan ba, kin ce min zaki kula da kanki da lafiyarki, yanzu meye ki ke yi haka? Daga zuwa yau kin canja maganarki. Ta yi ajiyar zuciya ta ce,  Ni ban gaji ba, kuma sallar asuba kawai zamu yi zan dawo.

Zata fita daga Wakin ya ri?e hannunta ya ce,  Jidda!. Ta tsaya cak bata juyo ba ya ce,  Duk wannan abun na meye ne wai? Duk akan& . Bata bari ya ?arasa ba ta zame hannunta ta ce,  Muna jiran ka in ka shirya mu tafi gabaWaya. Fita tayi ta bar shi ta koma wajan Didi ta tarar har Marmerh ta yiwa wanka tana mamakin kayan da ta gani na Marmerh.

Nayla ce ta ta ?arasa shirya Marmerh ta ce,  Didi mu je. Tare suka fito har lokacin bai fito ba, ta nufi Wakin zata shiga Wakin ya fito ya saka doguwar riga jallabiyya mai kyau da laushi. Ta ce,  ka Wauki key Waya ko da zamu rabu.

Bai tanka mata ba suka fito tare tana ri?e da Didi, Marmerh kuma tana hannunsa suka sake shiga elevator suka sauka zuwa reception suka fita. Da yake babu nisa sosai daga hotel Winsu zuwa masallaci ba jimawa suka ?araso. Didi tunda ta hangi masallacin jikinta yake rawa dan ta tabbatar da gaske ne ba ?arya ba.

Tana saka ?afarta a harabar masallacin ta ji wata faWuwar gaba da wani ?hamshi da bata taSa ji ba, ta kalli Nayla ta ce,  Nayla mafarki nake yi ko gaske?. Nayla ta ce,  da gaske ne Didi, gaskiya ce. Didi bata sake cewa komai ba ta zube a wajan a sume.

Omar ya ?araso da sauri ya ri?e Didi yana kiranta amma Didi ta suma. Da gaggawa ?an agajin masallacin suka ?araso aka saka ta a motar da take yawo a cikin harabar masallacin aka wuce da ita zuwa asibitin da yake can ?arshe a masallaci. Duk tare suke, Nayla tana ri?e da hannunta, ana zuwa aka karSe ta aka kwantar dan taimaka mata.

Nayla ta zauna akan kujerun da aka tanada ta dafe kanta, ya zauna kusa da ita Marmerh tana jikinsa dan ta tashi daga bacci ya ce,  Ashiq don Allah ki nutsu, ki nutsu don Allah bana son wannan yanayin na ki. Kwanciya tayi a jikinsa dan ta gaji sosai kanta ya yi nauyi tana bu?atar bacci. Ri?eta ya yi ba tare da ya ce komai ba, ba su jima da zama ba aka tayar fa i?ama, tare suka fita dashi ya hau sahun maza ta hau na mata bayan ya bata Marmerh suka tayar da sallah.

Shi kansa mamaki yake yi wai yau shine ya yi sallar asuba a masallacin ma aiki, abinda bai taSa kawo shi zuciyarsa ba ko da wasa, sai gashi cikin lokaci kaWan Allah ya yi masa ni imar ziyarar masallacin annabi har ya yi sallah a cikinsa. Sai ya samu kansa da zubar da hawayen rauni da godiya ga Allah, ya goge idonsa ya kalli Nayla da take kallonsa daga can gefe, suna haWa ido ta Wauke kai ya yi murmushi yana mamakin wanann kishin na ta.

Tare suka koma aka yi musu bayanin dalilin suman nata, suka ce sun saba samun irin haka, shau?i ne da farin ciki yake saka mutane suma. Aka tabbatar musu da lafiya lau take ta kuma farfaWo. Tare suka shiga Wakin suka same ta a zaune, Nayla ta ?arasa ta zauna kusa da ita ta ce,  Didi sannu, ya ki ke ji?. Didi ta ri?e hannunta ta kalli Omar da yake tsaye ta ce,  Nayla ya aka yi haka ban sani ba? Ta faWa hawaye yana sakko mata.

Nayla ta ce,  Duk aikin ?aninki ne Didi, ya ce yana so ya baki mamaki ya kuma saka ki farin ciki shiyasa ba ya da bu?atar ki sani, shiyasa da aka faWawa Yaya AbdulHamid aka ce kar ya faWa miki. YaMar ya yi ne dan ki ji daWi ki kuma yi farin ciki, sannan ki san Allah ya azurta shi zai iya yi miki komai dan ki ji daWi.

Kuka sosai Didi take yi cikin farin ciki, ta kalle shi cikin kuka ta ce,  Omar!. Zuciyarsa sai ta karye yaji rauni ya mamaye masa zuciya, ?aunarta da tausayin wahalar da tasha dashi suka zo zuciyarsa, ya tako a hankali ya zauna kusa da ita ya ri?e hannunta guda Waya ta Wora kanta a kafaWarsa tana kuka sosai. A hankali ya ce,  Ki daina kuka Didi, kinga baki da lafiya. Bata iya magana ba ta fi mintina biyar tana kuka kafin ta koma sauke ajiyar zuciya.

Ta Wago ta kalle shi shima ita yake kallo ta ce,  Omar& ! Sai ta kasa magana ya ce,  ba sai kin ce komai ba, don Allah ko yi shiru, ki nutsu mu je ki yi sallah ki huta. Didi ta goge ido ta ce,  Omar na rasa me zan ce, na rasa me zance Omar.
 Ba sai kin ce ba Didi, kawai ki kwantar da hankalinki shine abinda nake so.

Didi ta yi ajiyar zuciya ta kalli Nayla da take kallon ta itama tana hawaye, ta sake ri?e hannunsu duka biyun ta ce,  Nayla me zan cewa Omar? Da wacce kalma zan yi magana?.
Nayla ta ce,  Didi ba sai kin ce komai ba kamar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login