Showing 108001 words to 111000 words out of 332344 words

Chapter 37 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

30883

juyo ta kalle shi ya Waga mata kai alamun abinda ya ce kenan. Ta girgiza kai ta ce, "maganar farko da ita ake amfani, ka ce baza ka taSa sona ba har abada?." Ya sauke numfashi kaWan ya tako yazo daf da ita tana jin saukar numfashinsa, idanunsa yana kallon na ta ya ce, "Maganar farko ba gaskiya ba ce, maganar yanzu itace gaskiya. Jidda ko za a raba ni da numfashina wallahi bazan sake ki ba!." Janye ido tayi daga kallonsa, ta kawar da kai tana jan numfashi. Da sauri ta juya ta shiga gidan dan tsaf zai iya karya mata zuciya, ita kuma tayi ?udirin bazata koma ba sai dai son da take yi masa ya kasheta.

Omar sai ya ji daamuwa ta mamaye masa zuciya a karo na babu adadi. Kalamanta basu tsaya masa a rai ba kamar yadda ganin hawayenta ya tsaya masa a rai, da alama abinda ya faWa mata ya yi mata ciwo sosai a wancan lokacin.

Dafe kai ya yi a bayyane ya ce, "meyasa ka ce haka Omar?." Dan ?aramin tsaki ya yi ya sauke ajiyar zuciya ya fita harabar gidan ya tarar da Daddy yana niyar shigowa. A nan suka yi sallama da Daddy cikin girmamawa ya fita ya bar gidan.
KRB3P037
Arewabooks@nanahaleema11.

Nayla a guje ta shige falo da mutan gidan suke zaune, ta shiga Waki ta faWa kan gado tana kuka mai sauti. Kuka take yi da zuciyarta da gangar jikinta ba tare da ta san dalilin kukan ba. Jikinta har rawa yake yi saboda yadda take kuka mai matu?ar sauti kamar ranta zai fita.

Wai Omar Winta ne fa yazo yana so ta koma gidansa, shine yake cewa bazai iya sakinta ba, kenan sonta yake yi ko me?. Wannan tunanin shine yake sake karya mata zuciya take kuka kamar wacce aka yiwa mutuwa.

Daddy da ya shigo falon da suke ya ga Mama da Mummy sun mi?e tsaye suna cewa, "Me ya samu Nayla take wannan kukan?." Daddy ya kalle su ya ce, "Ku ?yaleta, Mijinta ne yazo." Mummy ta dafe ?irji ta ce, "sakin na ta Win ya yi?." Daddy ya girgiza kai ya ce, "ya ce bazai sake ta ba, babu abinda zai saka shi sakinta. Ya tabbatar mana da yana matu?ar son Nayla."

Mama Sa'adatu ta ce, "to wai me ya haWa su har ta dawo gida haka?." Daddy ya ce, "ya sanar damu komai, ya tabbatar mana zaman da suka yi na wata shida ba zama ne na mata da miji ba, ya zauna da ita ne saboda dolen da Yayarsa tayi masa ba dan yana so ba. Amma a yanzu shi ya kawo kansa yake kuma so a sake bashi Nayla a karo na biyu." Mummy ta ce, "ikon Allah, da bai san da hakan ba sai yanzu?."

Daddy ya kalle su dan ya katse musun ya ce, "kuna ji, na amince da son da yake mata sosai, na kuma amince a yanzu zai ri?eta hannu biyu matsayin matarsa. Abinda ya rage zamu zauna mu ji ta bakinta gobe in Allah ya nuna mana. Sa'adatu ki barta ta kwana a nan, gobe Ali da Khabir zasu zo dan a tabbatar da abinda yake zuciyarta, in zata koma masa shikenan, in bazata koma ba babu wanda yi mata dole."

Mama Sa'adatu ta ce, "Gobe ya yi wuri Yaya, sati biyu tayi fa bai neme ta ba, shi kuma daga zuwa yau sai a zauna da Nayla gobe kamar daman jira mu ke yi ta koma? A sake bata lokaci ta Wan samu nutsuwa don Allah."

"Amma kin san tana son mijinta ko?."
"Na fi kowa sanin hakan, wannan kukan da take yi zai tabbatar da soyyayar da take masa." Daddy ya ce, "to ni dai na riga na ce masa gobe, bazan canja daga goben ba." Mama ta ce, "ai shikenan, amma gaskiya yayi wuri kamar daman shi muke jira" ta faWa tana Sata rai.

? ? Nayla kuwa Salma ce ta shiga wajan ta ganin kukan da take yi sai ta ri?ota ta ce, "Haba Nayla, wannan kukan fa? Me ya faru ki ke wannan kukan?." Nayla ta kwanta a jikin Salma tana kukan har lokacin kafin kukan ya fara raguwa a hankali tana jan numfashi. Salma ta ce, "Haba don Allah, wannan wanne irin kuka ki ke ke yi haka? Wani abu ya faru ne?." Nayla ta kalle ta ta ce, "Ya zo Salma."

"Daman ai na faWa miki zai zo ko? Kuma na faWa miki in yazo ba sakin ki zai yi ba."
"Salma na kasa gane a wannan yanayi nake ciki, ban san me nake ji ba a zuciyata."

Salma ta ce, "farin ciki ki ke ji, na tabbatar da yanzu yana sonki bazai iya kuma rabuwa dake ba Nayla." Nayla ta ce, "bai ce min yana sona ba Salma, amma ya ce bazai iya sakina ba." Salma ta yi murmushi ta ce, "To a gidan Daddy zai za?e ya nuna miki soyayya ne Nayla? Ai soyayya da ?auna sai kin koma gidansa, na tabbatar daga ranar zaki fara jin daWin duniya. Don Allah ki bar wannan kukan, abinda mu ke so ne ya samu farin ciki ya kamata mu yi ai."

Nayla ta yi murmushin jin daWi ta ce, "Don Allah bakya jin hakan kamar a mafarki?." Salma ta ce, "ke addu'ar da muka yi akan hakan ta wasa ce? Ai na tabbatar da indai Omar alkhairi ne a gare ki zaman ku zai zama na soyayya da farin ciki kamar a ?asar larabawa. Amma fa ba daga su Daddy sun tambayarki zaki koma ba, yauwa...sai kin ja masa aji wallahi, saiya Wan jigatu kamar yadda ya wahalar mana da ke." Nayla tayi dariya ta kwanta a jikin Salma ta ce, "Salma na rasa me zan yi wanda zan nuna ina matu?ar farin ciki. Wai shine da kansa yazo, baya Soye abinda yake zuciyarsa kenan abinda ya ce min gaskiya ne?. Wallahi ban san wanne irin farin ciki nake ji ba."

Salma ta goge mata hawaye ta ce, "komai zai zama labari in sha Allah, zaki fara rayuwar jin daWi daga nan Abiy ya yafe miki ya tabbatar da yanzu Omar ki ka aura ba Tiger ba. Tiger ya jima da mutuwa yanzu Omar ne yake rayuwa." Nayla ta rungume Salma cikin farin ciki.

?? Bayan sallar magriba Mama ta shigo Wakin da Nayla take har lokacin hira suke yi da Salma ta ce, "Nayla Daddy ya ce ki zauna a nan saboda gobe suna so zasu tambayeki ra'ayinki akan komawa gidan mijinki. Amma nima goben zan dawo ai, in zaki bi ni mu je gabaWaya kawai."

Nayla ta ce, "To Mama zan bi ki Win."
"Yauwa mu je mu tattauna, dan bazan bari daga an zauna dake gobe ki koma ba, akwai abubuwa da yawa da ba mu yi a wancan lokacin ba zamu yi yanzu. Na san kina son mijinki, wannan lokacin ki ke jira kuma gashi yazo, Daddyn ki ya tabbatar min da gaske mijinki yana sonki kuma zai gyara abinda ya Sata. Baza ki koma da wuri ba sai min yi shirye-shiryen da ba mu samu mun yi wancan lokacin ba." Nayla ta yi murmushin jin daWi ta kwanta a jikin Salma tana murmushi. Sai dare suka bar gidan suka tafi gidan Mama

? ? ?? Omar kuwa tunda ya fita daga gidan yake jin zuciyarsa a matu?ar damuwa, a haka ya ajjiye motar ya shiga cikin gidan ya zauna yana furzar da iska. Bai samu zarafin tunani ba aka yi kiran sallah ya tashi ya shiga masallaci.

Bayan an idar ya dawo yana tuna yadda take hawaye sosai sai ya ji jikinsa gabaWaya ya mutu.Tsigar jikinsa har tashi take in ya tuna yadda hawaye suke mata zarya akan idanunta. ?aramin tsaki ya yi kawai ya mi?e ya Wauki key Win motar ya fita ya hau motar kai tsaye ya tafi gidan Didi.

Sai da ya je a hanya ya ga wani masallaci ana sallah ya tsaya ya yi sallah sannan ya ?arasa? ?ofar gidan ya kira wayar Didi ya ce gashi a ?ofar gida. AbdulHamid ne ya fito yana cewa, "Omar kamar ba?o, har yanzu wai in kazo sai ka yi waya, baza ka shiga kai tsaye ba? Gidan Yayarka ne fa." Omar ya bi bayansa yana cewa, "Gwara dai hakan."

A falon ya samu Didi a zaune ya bita da kallon tausayi, gabaWaya tausayi take bashi ta koma wani iri kamar ba ita ba. Ya ce, "Sannu Didi, har yanzu wai lokacin haihuwar nan bai yi ba? Duk kin canja." Didi ta ce, "da saura Omar. Zauna mana." Omar ya zauna yana kallonta ya ce, "Sannu" ya faWa cikin sanyi da nuna tsnatsar damuwarsa akan yanayinta. Gaisuwa suka yi kafin Didi ta ce, "Ya na ganka da damuwa? Ko basu amince da dawowar na ta ba?."

Omar ya yi ajiyar zuciya ya ce, "A'a Didi, sun karSe ni hannu biyu fiye da yadda nake tunani, mun yi magana dasu cikin fahimta da wasa da dariya. Amma sun ce min sai an tambayeta an ji in zata koma, kamar yadda aka bani dama a wancan lokacin itama za a bata dama." Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, "gaskiya ne ai Omar, ya kamata a bata dama itama kam gaskiya. Amma meye na ga ka damu?."

"Didi...." Sai bai ?arasa ba saboda damuwa, ya yi ajiyar zuciya ya ce, "ita da kanta ta ce min ita bazata sake zama dani ba, ita dole sai na saketa ta gaji. Didi babban abin haushin ma kuka fa take yi, ban san ana jin zafin hawayen wani a cikin rai ba sai da naga tana kuka. A duk lokacin da na ga kina kuka ina ji a zuciyata, amma ban taSa jin irin haka, na kasa mantawa da yadda take kuka Didi, na kasa mantawa" ya faWa yana Wan lumshe idanunsa.

AbdulHamid ya yi dariya amma bai ce komai ba. Omar ya kalle shi ya ce, "ka ce in ina bu?atar shawara na neme ka, me zan yi?. Ni ban san me ake yi ba, ban iya rarrashi ba, ban iya magana da mace ba, ban iya komai ba. Duk ?arfina da tunanina ya ?are akan matarka, me zan ce mata?."

AbdulHamid ya yi dariya ya ce, "To ayi ha?uri da muka ?arar maka da ?arfinka, amma yanzu ya kamata ka yi tunani, a duk lokacin ka ke tare da ita duk abinda ya zo zuciyarka shi zaka faWa mata." Ya nuna Didi ya ce, "Gurguwar shawarar da matarka ta bani kenan, ta ce na faWi duk abinda yazo raina amma da na faWa mata sai ta ke kuka. Me na ce mata da ya saka ta kuka? Didi me kika saka na faWa ne?" Ya ?arasa faWa yana kallon Didi.? Didi ta yi murmushi ta ce, "babu lallai kalamanka sune suka kasa ta kuka Omar, wata?ila akwai abinda ta tuna ne. Wata?ila yadda ka kalle ta ka ce baka sonta shine abinda yazo zuciyarta har ya sakata kuka."

"Kuma fa ko Didi...ko lokacin Sata min ran da kika yi ne ya saka na ce haka, amma ko a lokacin jin abinda nake ji a kanta sosai." Didi ta yi murmushi ta ce, "ita bata ga haka a lokacin ba, dole ta ji babu daWi."
"Duk laifin ki ne, da baki Sata min rai ba da yanzu tana gida muna zaman mu lafiya."
"?ata maka rai ya yi amfani, ba dan haka ba da har yanzu baka tabbatar da kana sonta ba, kana nan kana zuba mata wula?ancin da ka saba."

Ya kalle ta ya ce, "ni bana wula?anta ta, kuma ko baki Sata min rai ba zuwa yanzu na fahimci mahimmacin da take dashi a rayuwata." Didi ta taSe baki ta ce, "kai dai ka sani. Ita abinda ta sani ka kalli fuskarta ka ce bana sonki, bata san wannan bayanan naka ba."

"To wai ita tana sona ne? Meyasa take jin haushi dan na ce ban sonta?." Didi ta kalle shi ganin ita yake kallo ta ce, "ba lallai ai sai tana sonka ba Omar, ta karSi aurenka kuma tana kallon ka a matsayin mijinta dole ta ji babu daWi in ka furta haka akanta." Ya yi ?aramin tsaki ya ce, "ni yanzu ku bani shawara kawai, in dai kuna so na cigaba da zama cikin nustuwa ku bani shawara." Didi ta ce, "Dole ka yi ha?uri na wani lokaci, kamar yadda iyayenta suka ce zasu bata dama to ka yi ha?uri ka ji me zata ce. In ta amince da kai daman abinda mu ke so kenan, in bata amince ba sai mu ha?ura."

Omar ya yi mata banzan kallo yana harararta cike da faWuwar gaba ya ce, "a ha?ura da me?." Didi ta ce, "mu ha?ura da ita mana."
"Mtsw! wani lokacin kamar kina shaye-shaye. Yanzu kina tunanin akwai abinda zai saka na rabu da ita a kaf duniyar nan? Ko meye zan yi ya?i dashi wajan ganin na yi nasara a kansa. Ai wallahi ko iyayenta ne zasu ce na rabu da ita a yadda nake jin zuciyata bazan rabu da ita ba. In kaf duniya ne zasu taru a kaina a saka min wu?a a wuya ace na rabu da ita wallahi sai dai su kashe ni, in suka kashe ni su kawo miki gawata."

Zata yi magana ya katse ta ya ce, "Don Allah kar ki Sata min rai, ki bar ni da iya abinda yake raina ki adana kalamanki bana so, kar ki sake tarwatsa min tunani. Kar ma ki sake saka min baki, da mijinki nake magana ba ke ba." Abdulhamid shi dai dariya yake yi sosai, saboda dramar Didi da Omar abar dariya ce, umarni yake mata kamar shine yayan itace ?anwa.

AbdulHamid ya ce, "ka yi ha?uri Omar, ka bada lokacin kamar yadda akace, ni na tabbatar baza ta ?i dawowa gareka ba. Kaine fa Tiger, ga kyau, ga aji, ga nutsuwa, ga kuma soyayyar da ka ke yi mata, ta ya zata bari wannan damar ta kuSuce mata?."

Wani irin kallo Omar ya yi masa ya ce, "Matar ka bata faWa maka bana son zuga ba? Haushi take bani, na tsani a zuga ni, ka faWa min gaskiya ba abinda zan ji daWi ba." Abdulhamid ya sake yin dariya mai sauti ya ce, "ba zuga ba ce Omar, amma tunda baka so shikenan. Maganar gaskiya sai ka jira tukunna, sannan ka yi ?o?ari kana ganinta ko kana waya da ita, hakan zai sake nuna mata da gaske kana sonta."

Omar ya Wan yi shiru yana jin nauyi a zuciyarsa sannan ya ce, "Bani da number ta, kuma ni babban tashin hankalin ban san me zance mata ba, ban iya magana da ko wacce mace ba a duniya sai Didi, ban san ta ya zan faWi maganar da zata amince ba." Didi ta ce, "Da ka fara maganar zaka ji tana fitowa daga zuciyarka Omar. Wai kamar baka so Narma ba? In kana waya da ita da wanne irin kalamai ka ke amfani wajan yi mata magana?."

Ya kalle ta yana buWe idanu ya ce, "Ai na ce ki daina saka min baki ko? Kuma ita Narma ban taSa rarrashinta ba, ban taSa tsayawa na yi wani abu dan faranta mata ko dan nuna ina sonta ba, ko yaushe itace take takura min da waya, na kan manta da ita in ba kirana tayi ba. Ki daina sakata a maganata. Magana ake ta wacce nake so ba waccan sharar ba, ki daina haWata da matata kamar cin fuska ne a gareta."

Didi ta ce, "yi ha?uri, amma ya kamata ka koyi yadda ake tafiyar da soyayyar mace, musamman kai da ka faWa mata kalamai marasa daWi. Ka nemi class na koyar da tattalin mace ka shiga" ta ?arasa faWa cikin sha?iyanci tana dariya.

AbdulHamid ya ce, "Omar ita soyayya wani lokacin sai ana haWawa da ?arya tafi armashi, zaka iya faWa mata wani abun wanda kai kanka ka san ?arya ka ke yi itama tasan ?arya ne amma zata ji daWi a zuciyarta."

Omar ya hakimce yana wara idanu yana kallon Abdulhamid ya ce, "Oh to ke kin ji Didi, daman can wasu kalaman na sa ba na gaskiya bane ?arya ya dinga jera miki har ki ka aure shi." Didi tayi ?ar ?aramar dariya dan bata jin daWin jikinta dauriya kawai take yi.

Omar ya kalli AbdulHamid da yake ta dariya ya ce, "Ban tsara rayuwata akan ?arya ba, dan haka bazan tsara aurena a kan ?arya ba, duk kalaman da zan faWa zan tabbatar da na gaskiya ne zan sanar da ita. Dukkan ku taron tsintsiya ne babu shara, dana sani ma ban zo ba" ya faWa yana shafa kansa.

Didi ta ce, "Ka ga ka yi duk abinda ka ga ya kamata, amma sai ka yi ha?uri gaskiya, wannan gaggawar bazata saka ta dawo ba. Kuma ya kamata ace an haWa mata lefe, tunda yanzu kana son aurenta ya kamata ayi mata lefe kamar ko wacce mace." Ya kalli Didi ya ce, "kin san da hakan ki ka saka na kwashe kuWina na siyi waccan motar?."

"Yanzu abin ya zo raina ne Omar."
"Ana kashe nawa?."
"Iya ?arfin ka iya kuWin da zaka kashe. Ba zaka yi abinda ya fi ?arfin ka dan a burge ba, duk abinda zaka bata tafi ?arfinsa dan kawai kayan aure suna da daWi."

"To ai baki da lafiya, waye zai yi wannan aikin in ba ke ba?.." Didi ta ce, "Zamu ga ni dai, bara mu ga zuwa yaushe zata dawo." Omar ya bita da kallo sosai cikin kulawa ya ce, "kina lafiya kuwa? Ni ban yarda dake ba, kin canja gabaWaya."

Didi ta ce, "na gaji ne kawai, kwanciya zan yi."
Omar ya ce, "ki je ki kwanta, nima zan tafi yanzu." Wayar Didi ya Wauka ya Wauki number Nayla ya ce, "in wani yaji bani da number ta akwai raini a ciki, ko iya ganin number ta zai rage min kewa." Murmushi ta yi kawai suna hira da AbdulHamid kaWan-kaWan har ya raka shi ya tafi.

? ? ? ?? Kusan raba dare Omar ya yi yana kallon number Nayla, ya rasa wanne suna ya kamata ma ya saka mata. In ya saka Nayla ya goge, in ya saka Hauwa ya goge, in ya saka Jidda ya goge ya rasa wanne ya kamata ma ace ya saka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login