Showing 264001 words to 267000 words out of 332344 words

Chapter 89 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14372

him." Hannunsa har rawa yake ya Wauko waya ya kira Abiy, bata jima ta ringing ba Abiy ya Wauka ya ce, "Mai girma Sen Sagir." Sen ya ce, "Class captain, Kwana biyu ba a jinka."
"Ku ne dai ba a ji, harkar zaSe ta gabato."
"Bari kawai, abubuwa sun kwaSe."
"Allah ya tabbatar da alkhairi."
"Amin Captain. Kana Kaduna ne?."

Abiy ya ce, "Ina cikin Kano, jiya na shigo amma gobe zan koma in sha Allah." Dad ya ce, "Yauwa na ji daWin hakan sosai, Ina son magana da kai da gaggawa, if possible ina so na zauna da kai a yau."
"Babu damuwa ai, ina gida ko yanzu ma."
"Okay, ka tura min location Win zan zo."
"Alright, babu damuwa." Daga nan suka kashe wayar.

Ya kalli Mum ya ce, "Zan je na same shi face to face, kar ki damu na tabbatar ma zai iya yi masa magana ya amince." Mum ta goge hawaye ta ce, "Narma...."
"Ki yi ha?uri, zata samu lafiya." Dad ya rungume Mum yana bubbuga bayanta cikin rarrashi.

Sun jima a zaune har Narma ta farka suka shiga Wakin a tare, Mum ta ri?e hannayenta ta ce, "Kar ki damu Narma, zaki auri Omar kin ji?." Narma binsu take da kallo kawai kanta na yi mata mugun ciwo. Likita ne ya shigo ganin yanayin da take ciki ya sake yi mata allurar bacci su Mum suka fito. Dad yana fita kai tsaye gidan Abiy ya wuce da ya turo masa location. Yana zuwa aka buWe masa gate ya shiga dan Abiy ya sanar da mai gadin zuwansa.

Falon ya shiga da sallama, Abiy ya tare shi da fara'a suka gaisa cikin girmama juna kafin Dad ya ce, "Wajan ka nazo Captain, ina neman alfarma." Abiy ya ce, "in dai bata fi ?arfina ba Senator zan yi maka, alfamar me ka ke so?." Dad ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ka tuna wannan yaron Tiger da ka taSa karSarsa daga hannuna?"

Abiy ya girgiza kai ya ce, "Na gane shi, ba Omar ka ke nufi ba?."
"Exactly Captain."
"Wani abun ya faru ne?."
"Ka san a lokacin baya Narma tana matu?ar sonsa, ka tuna har na ce maka asiri ya yi mata?."
"Na tuna komai."

Dad ya ce, "Captain ba asiri bane, Narma ta haukace tana son yaron nan kullum cikin kuka da tashin hankali take. Yanzu maganar da nake yi maka tana asibiti a kwance, Dr ya ce ta samu high blood pressure. Kuma tun a Abuja an sanar damu zata iya samu heart attack." Abiy da damuwa ya ce, "Subahanallah! Narman?."
"Ita fa Captain."
"Amma ba ka ce min ta auri Ashraf ba?."

Dad ya ce, "Forget about him, yaron nan bashi da kirki haka ya dinga wula?anta min ita. Zancen da nake maka ya sake ta har saki uku, har aborting Babynta ya yi." Abiy ya ce, "Subahanallah! Gaskiya bai kyauta ba, abu sam bai yi daWi ba Senator. Ba mu yi tunanin haka daga wajan Ashraf ba."

Dad ya ce, "Ya bamu mamaki sosai, kuma daman Narma bata so, mun yi forcing Winta ne muna ganin in ta zauna dashi komai zai zama normal. To abin ya ?i yuwa har aka yi saki."
"Allah ya sa haka shine mafi alkhairi."
"Amin Captain. Kamar yadda na faWa maka Narma ta haukace akan yaron nan Omar, ta zama kamar mai mental illness saboda shi. Na amince da gaske take sonsa ba wasa ba, kuma yanzu a shirye nake da na aura masa ita saboda kar na rasa ta."

Abiy ya ce, "To ina jinka." Dad ya ce, "Ka ganni Wazu daga wajansa nake, har office na je na same shi akan maganar nan amma yaro nan ya kalle ni ya ce shi bazai auri Narma ba, daman ba sonta yake ba, da magana dai kala-kala marasa daWi Captain. Daman ba tarbiyyar kirki ce dashi ba, na san kuma daban bashi da kunya baya jin tsoron kowa, haka ya saka ni a gaba da kalamai na rashin kunya kala-kala. Komawa ta gida kenan ina faWawa babarta abinda yake faruwa ashe ta ji, shine ta faWa a wannan condition Win aka kaita asibiti."

"Kai amma abin bai yi daWi ba ko kaWan, lamarin ya wuce tunani tunda har ana maganar high blood pressure." Dad ya ce, "shiyasa nazo wajan ka, da nace bazan sake neman sa ba sai dai Narma ta ha?ura dashi, amma na kasa saboda halin da take ciki. Bazan iya bari ta rasa ranta akan soyayya ba, na amince zan bata aurensa indai zai amince ya aure ta. Yanzu daga asibitin sallah kawai nayi na zo gidan nan mu yi magana. Captain tunda kuna da ala?a dashi me zai hana baza ka yi convincing Winsa ya auri Narma ba?."

Abiy ya yi murmushi ya ce, "To Senator ni da ba mahaifinsa ba ta ya zan iya saka shi ya auri Narma?." Dad ya ce, "ai bazai manta da abinda ka yi masa ba shima, zai iya amincewa ya aureta ta silar kyautatawar da ka yi masa. Captain ka yi min wannna alfarmar don Allah, na rasa ya zanyi ne, Narma na gab da rasa hankalinta a kansa. In ba dan Narma da take cikin tsananin ciwo da azaba ba wallahi da hakan bai faru ba."

Abiy ya yi ajiyar zuciya yana murmushi dan ya san Sen bai san Nayla yake aure ba, ya kalli Dad ya ce, "To zan yi masa waya na kira shi, in yana da lokaci yazo mu yi magana a kai, in ya amince zan sanar da kai, in bai amince ba sai ayi ha?uri."
"Zai ma amince Captain, na gode sosai."
"Babu komai. Amma da ka hana shi aurenta har kana cewa asiri ya yi mata, amma yanzu kuma kana cewa ya aureta, meyasa da ka hana shi yanzu zaka bashi?."

"To ya zanyi Captain? Ai tana sonsa ne. Kuma rayuwarsa ta baya ai ba irin wannan ba ce, yanzu yana da babban matsayi, ya kai wani mataki da zai iya aurenta." Abiy ya yi murmushi yana jinjina ?arfin hali irin na Sen kana ya ce, "Shikenan, zan kira shi zuwa anjima in sha Allah." Dad ya godewa Abiy daga nan suka yi sallama ya tafi.

A Sangaren Omar yana zaune shida Didi Abiy ya kira Omar. Omar ya Wauki wayar yana kallon Didi ya ce, "ki yi shiru, sirikina yana waya." Didi tayi dariya shima haka sannan ya Wauka. Ba su jima suna wayar ba ya kashe ya kalli Didi ya ce, "Abiy ya ce naje yana nema, zan je na dawo." Didi tana ta dariya tana tsokanarsa ya yi dariya ya fita daga gidan.

Kamar yadda Abiy ya faWawa Omar location na gidan ya je, ya shiga har cikin gidan a lokacin an idar da sallar i'sha. A falo ya samu Abiy suka gaisa yana tambayarsa Musliha ya amsa sannan Abiy ya ce, "Omar Senator Sagir ne yazo min da wata magana, yazo Wazu ya same ni akan maganar ?arsa Narma." Omar bai ce komai ba Abiy ya ce, "Ya tabbatar min da ?arsa tana kwance a gadon asibiti saboda son da take maka."

Nan ma Omar bai tanka ba yana jiran Abiy ya gama magana sannan ya furta abinda yake bakinsa. Abiy ya ce, "Yazo yana neman alfarmata akan na ro?eka ka karSi auren Narma, saboda son da take maka tana gab da rasa lafiyarta. Shine na kira ka na ji ta bakinka, zaka iya aurenta ko dan ceto rayuwarta Omar?." Omar ya sauke numfashic a hankali ya ce, "Abiy yaje har office ya same ni Wazu, kuma na faWa masa ni bani da ra'ayi, nace masa bana so kuma bazan yi ba."

"Amma meyasa baka so Win? Naga a dai kai ma ka so ta ko? Zaka iya yin ha?uri a yanzun ma ka karSeta ko dan lafiyarta." Omar kai tsaye ya ce, "Abiy in nace ban taSa sonta ba ban yi ?arya ba wallahi, ta shigo rayuwata ne saboda naje gidansu a faWa min maganar da Senator ya faWa min ya zama silar canjawar rayuwata. Ta shigo rayuwata ne saboda ta zamar silar da zan tashi daga can na dawo nan, kuma amfaninta ya ?are a wajena da rayuwata gabaWaya."

"Haka ne Omar, daman komai yana da sila a rayuwa, ita ta kasance silar canjawar rayuwarka. Amma ko dan saboda ta silarta canji yazo a rayuwarka meyasa baza ka amince ka aureta ba? Tana tsananin sonka, yazu haka tana asibiti a kwance saboda ta ji mahifinta yana cewa ka ce baza ka aureta ba. Kuma lokacin da iyayenta suka yi maka wannan abun ita meye laifinta? Duk da haka ta cigaba da nuna maka so bata daina ba, har tayi aure ta fito baka bar zuciyarta ba, Allah kaWai ya san abinda take ji akan ka. Omar zaka iya karSar aurenta ko dan matsayin silar canjin ka da take dashi, zaka iya karSarta ko dan son da ta ke maka, koda kai baka sonta zaka iya zama da ita."
P102

Omar bai Wago ya haWa ido da Abiy ba saboda nauyinsa yake ji sosai, amma da wani ne yake masa wannan maganar ba Abiy ba da mai raba su Allah. Omar ya ce, "Abiy wallahi bani da ra'ayin ?ara aure a rayuwata gabaWaya, ko ina da ra'ayin auren nan gaba bata daga cikin matan da zan iya aura. Mahaifinta ya hanani aurenta a lokacin baya saboda ban kai matsayin ya bani aurenta ba, a yanzu kuma yana so na aure ta saboda na kai wani mataki wanda bai yi tunanin zan kai ba. Kai tsaye zance ba saboda Allah ya bani ita ba, ya bani ita ne saboda wani buri a zuciyarsa."

Abiy ya murmusa ya ce, "Haka ne Omar. Amma abinda nake so ka duba ita yarinyar bata da laifi tun asali, ko dan saboda son da take maka ya kamata ka yi wani abun. Tun farko ita bata ?ika ba, bata nuna maka ?iyayya ba, ko bayan abinda iyayenta suka yi maka bata guje ka ba, itama sai kayi mata adalci ka amince da ita. Ba mahaifinta zaka duba ba, ita zaka duba, mahaifinta shine yayi maka laifi ba itace tayi maka ba."

Omar ya sauke numfashi ya ce, "Abiy kamar yadda na faWa maka bani da ra'ayin ?ara aure a yanzu ko nan gaba a rayuwata gabaWaya. Kuma ita kawai ta zama sila ne na canjawata, har gobe ina tunawa da ita kuma ina yi mata addu'a da ta zama silar canji, dan kome na zama bazan manta da mafari ba, amma batun zan aureta ko ina sonta bai tashi ba Abiy. Shiyasa na faWawa mahaifinta gaskiya, dan ni ban iya Soye abu a raina ba."

Abiy yana sauraron yadda yake magana cikin girmamawa, ya san kuma zallar gskiyarsa yake faWa masa, yana tausar sane saboda halin da akace Narma tana ciki, shiyasa yake maimaita masa ya aure ta. Abiy ya ce, "Duk da haka ka yi tunani Omar, wata?ila zaka iya bata gurbi a rayuwarka." Omar ya yi shiru bai ce komai ba, in ba dan Abiy Win bane da ashar zai yi wallahi, baya son yana tafiya ana dawo dashi baya, ya ce baya so to a bar maganar mana lallai sai an yi masa dole.

Ajiyar zuciya ya yi ya ce, "Abiy ba musu nayi maka ba, amma bani da bu?atar tunani. Bani da bu?atar ?ara aure gabaWaya a rayuwata balle na saka ran zan aureta, In har na amince da auren ta bai kai zuciya ba, kuma na cutar da kaina na cutar da matata. Sannan mahaifinta ya samu abinda yake so, ya?i ni a lokacin da yake amfani da rayuwata, yaso ni a lokacin da rayuwata zata yi masa amfani. Abiy ba kowa ne irin ka ba a duniya, ba kowa ne zai Wauki ?arsa ya bawa mutum kamar ni ba."

Abiy ya yi murmushi ya ce, "in baka san me zai faru a rayuwar mutum ta gobe ba baka yanke masa hukunci Omar, dani da kai da kowa babu wanda ya san me zai faru gobe, ba ma gobe ba, fitar ka daga gidan nan babu wanda ya san mai zai faru sai Allah kaWai. Amma mutane sai su dinga yiwa mutum hisabi bayan basu san gaibu ba. Allah ya kyauta, yasa mu dace. Tunda baka so shikenan, zan sanar dasu in sha Allah."

"Na gode Abiy. Don Allah a sanar dashi kar su sake takura min, a ?yale ni, tunda nace
bana so a rabu dani. Su yiwa ?arsu addu'a Allah ya bata lafiya, amma batun aurena a daina kawo shi." Abiy ya ce, "To Omar zan faWa masa sa?onka in sha Allah." Omar bai jima ba suka yi sallama ya tafi yana girmama ?arfin hali irin na Sen.

Omar da ya koma bai tarar da Didi ba daman ya san ta tafi, ya shiga Waki ya yi wanka ya canja kaya ya tsaya a jikin window yana kallon layin unguwar ta su, so silent as usual. Tunani ya tafi yi, tabbas maganar Didi gaskiya ce, Nayla ta sadaukar masa da komai na rayuwarta, haka zalika Abiy ya yi matu?ar ?o?ari da ya iya bashi aurenta, duk da abin ya faru ne a cikin wani yanayi amma tabbas ya yi ?o?ari. Abinda ya faru tsakaninsa da Sanata a office yake tunawa yana mamaki, wato yanzu ne ya zama mutum yake ji zai iya bashi ?arsa tunda ya kai wani mataki a rayuwarsa, shiyasa ya manta da batun asiri ya yi mata take sonsa har yaje ya samu Abiy akan maganar. Jinjina ?arfin halin Sanata yake yi, wato ya same shi kai tsaye yace bazai yi ba shine ya zaga wajan Abiy.

BuWe ?ofar aka yi aka katse masa tunani, ya juyo ya kalli Nayla da ta shigo cikin pyjamas green riga da wando masu dogon hannu da high neck. Hannunta ri?e da Musliha ta ?araso ta ce, "Musliha ta zo ta cewa Daddy good night." Takowa ya yi a hankali yazo yana kallon fuskar Musliha da take bacci ya sumbaceta a goshi ya ce, "Ki yi bacci lafiya Yayata" ya faWa yana shafa fuskarta cikin ?auna da soyayyarta.

Nayla bata ce komai ba, ta gyara Musliha a hannunta ta juya zata fita ya ri?o hannunta ta tsaya bata juyo ba. Shiru ya yi bai ce komai ba itama bata juyo ba, ya ri?e mata hannu shi bai saki ta tafi ba kuma bai ce mata komai ba. Sai da yazo gab da ita, ya tsaya a bayanta sannan ya ce, "Babar Musliha baza ta ce min good night Win ba?."

Nayla bata juyo ba ta ce, "Fushi ake yi da ita ai, ta bada ha?uri an ?i a ha?ura shiyasa ta kama kanta." Zagayowa yayi ya karSi Musliha a hannunta ya kwantar da ita a kan gado, ya dawo kusa da ita ya Wago fuskarta yana kallon ta ya ce, "Waye zai iya fushi dake Jidda? Ni?" Ya faWa yana nuna kansa.

Nayla cikin shagwaSar da take saka shi narkewa a cikin shau?inta ta ce, "To tun yaushe nake baka ha?uri ka ?i ka ha?ura, ko magana baka yi min ba sai dai ka yiwa ?arka, in ba fushi ka ke yi ba me ka ke yi?."

"Kishi nake yi, kishinki da kishin ?ata nake yi ba fushi ba. Jidda kin san me naji kuwa? Kin san yadda ki ke da mahimamci a tare dani? Kin san adadin mutane da suka kira ni saboda sun ga hoton nan?. Zuciyata zafi ta dinga yi, ji nake yi kamar na dinga dukan kaina har sai na ji a jikina hakan ya yi min. Ina tsananin kishinki, na faWa miki a akan kishinki zan tashi nigeria gabaWaya."

Nayla ta ce, "Amma na faWa maka kuskure ne, kuma ba za a sake aikatawa ba ba sai ya wuce ba? Tunda ka san ban taSa aikatawa ba sai ka yi min uzuri ko?." Ya ri?e fuskarta da hannayensa duka biyun, ya zura hannunsa a gefen kumatunta har yana taSo kunnenta ya ce, "kin faWa, amma ko yanzu hotunan basu daina yawo a duniya ba. Ana ta yabon kyaun matata da surarta, ba mutum Waya ba, kuma ba biyu ba, to ya ki ke so nayi? Dariya ki ke so na dinga yi bayan wasu banzaye suna kallon ki suna jin daWi?."

Nayla a sanyaye ta ce, "Shiyasa na baka ha?uri ai. Duk da nima an taSa ni, ana yabon ka kaima fiye da yadda ake yabona, harda wacce ta ce sai ta nemo inda ka ke. ?an malama hide my id kuwa sun fara turawa ana cewa ana sonka tunda aka ganka. Nima ban iya bacci ba, kana fushi dani sannan ga kishinka da nake ji, ga gajiyar taron da akayi suka haWu suka haifar min da ciwon kai. Duk da kaina da yake ciwo haka na kasa runtsawa...." Ta faWa murya na rawa alamun zata fara kukan shagwaSa.

Omar ya ce, "Jidda na san zaki yi kishi amma ki ajjiye maganata a gefe, ni daman na mutane ne ai ina shiga cikin mutane ana ganina ko yaushe. Amma ke fa? Addini cewa ya yi na killace ki, ni ne kaWai halak Winki, To a kan me wasu banzaye waWanda ban sansu ba zasu yabe ki?." Ta yi shiru bata ce komai tana ?ifta idanu kamar ko yaushe.

Jin ya yi shiru bai cigaba da magana ba ta Wago ta kalle shi ta ga ita yake kallo ta ce, "Ai nace ka yi ha?uri ko?." Ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Kin ce, amma na tambayeki?." Ta Waga kai alamun eh, ta? ji ya ce, "Meyasa bana iya dogon fushi da ke? Ko ya nace zan yi fushi dake sai zuciyata ta gaza yi?. FaWa min wacce irin mallaka ki ka yiwa zuciyata ne haka Jidda? Allah ko Didi ce ta yi abinda ki ka yi sai na kwana biyu bana kulata, amma ke jikina rawa yake in na ganki, kasa sarrafa kaina nake yi a lokacin da ki ka zo kusa dani. Uhumm faWa min meyasa...? Wajan wanne malami ki ka kai sunana?."

Bata ce komai ba ta shiga jikinsa da sauri ya saka hannu ya rungume ya lumshe ido cikin tsananin kewarta da ?aunar da yake


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login