Showing 117001 words to 120000 words out of 332344 words

Chapter 40 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14383

wanda zan yiwa ?arya ne dan na burge shi... sam babu." Didi ta yi murmushi ta ce, "ni sai ka kira ni kai ta masifa kuma ba ni nayi maka laifin nan ba, Nayla ce ba ni ba."

"Didi!." Jin yadda ya furta a sanyaye sai ta ce, "Na'am." Omar ya ce, "ya zan yi ta amince da gaske ina sonta? Me zan yi da zai tabbatar mata da ina son rayuwata da ita kuma bazan iya rabuwa da ita ba? Me zan yi?."
Didi ta ce, "na ce maka duk kalaman da ya zo zuciyarka shi zaka faWa."
"Ki daina Wora ni a keken Sera, haka ki ka faWa min kwanaki, da na je gidansu na faWa mata abinda yazo daga zuciyata ?arshe kuka ta dinga yi, Bana so na ga tana kuka ko kusa."

Didi ta ce, "Alhaji Omar Wan uwan Aisha, mijin Nayla baban Marmerh. Yanzu me ka ke so nayi maka?." Murmushi ta ji ya yi mai sauti amma bai ce komai ba. Didi ta ce, "Wan soyayya, Ina jinka kayi magana mana."

"Kin raina ni ko? Dan kin ga yanzu na zama wani iri ko? To Tiger har yanzu sunana ne wallahi, kawai wannan matar tawa ce ta Wora min pressure, ko ya akayi ma na faWa da yawa haka oho. Ni fa soyayya bata yi daidai da zubina ba, ban san ya aka yi na bari na yi zurfi haka ba. Allah in aka auna jinina ya hau."

Dariya Nayla tayi dan wallahi dariya ya bata sai kuwa ta ji ya ce, "Waye yake dariya?."
"Ba?uwa na yi tana yiwa Marmerh wasa."
"Amma kamar na san wannan muryar."
"Gaskiya baka santa ba."
"Ya yi. Ba fa ko wanne banza zaki dinga bawa yarinyar nan ba, wasu suna zuwa Waukar yara ne dan su cutar dashi." Didi ta yi murmushi ta ce, "to Omar, ka samu ka yi magana da Nayla Win ko zaka ji daWi."

"Ni bazan kira ta ba Didi, ki barta tayi tunani kamar yadda ta ce min. In bata da ra'ayi shikenan."
"Sai ka rabu da ita Win?."
"Hmm! Inda za a yi tashin hankali dani kenan, Allah sai na tashi garin Kano harda Kaduna garinsu. Na kira ki ne ji lafiyar ki da ta Marmerh kuma na ji, Sai anjima" ya faWa yana yake wayar ta bi wayar da kallo tana murmushi.

Salma ta ce, "Omar kenan, wato shi soyayyar ta sa ma ta musamman ce. Ita da yi masa laifi ke da shan faWa." Didi ta yi murmushi ta ce, "Ranar da ya je gidan Mama yana dawowa ya kira ni, yadda ya dinga yi min masifa sai ki Wauka wani laifin na yi masa. Ya ce na shaida bazai sake yi min maganar Nayla ba, Amma gashi ba a je ko ina ba ya kasa" ta faWa tana kallon Nayla da take murmushi.

Didi ta ce, "Nayla na faWa miki gaskiya? Wallahil azim Omar yana sonki, ban taSa ganin rauni a tare dashi ba sai a kan soyayyarki, Omar in ya ce ya bar abu ya bari amma gashi ya kasa sai da ya yi min zancen ki. Ban taSa ganin halittar da Omar ya bawa ha?uri ba sai ke, babu halittar da Omar ya yi kewa sai ke. Kamar yadda ya ce haka ne, shi ba mai yawan rashin lafiya ba ne, amma a kan ki sai da ya sha fama da zazzaSi da ciwon kai. Kar ki yi tunanin ina faWa miki haka ko dan ki koma masa ko kuma dan Omar Wan uwana ne, kin san ni mai faWa miki gaskiya ce a kansa. Bazai miki ?arya dan ya burge ba kamar yadda ya ce, duk abinda ya faWa miki wallahi ba ?arya yake yi ba Nayla, da gaske ke yana sonki da zuciya Waya da gangar jikinsa. Mace ta farko a duniya da ya so kuma yake so kece, Omar baya Soye min komai nasa, hatta yadda zuciyarsa ke bugawa a kan ki ya faWa min Nayla."

Nayla dai murmushi take yi cike da farin ciki amma sai ta kalli Didi ta ce, "Narma fa?." Didi tayi dariya ta ce, "bazan baki amsar Narma ba, amma daga ranar da zaman ku ya koma na farin ciki ki tambaye shi da kan ki, ki ce masa a wanne matasayi ya ajjiye Narma a kwanakin baya, na tabbatar zai faWa miki."

Nayla ta yi murmushi Jidda ta ce, "samun soyayyar irin su Omar abu ne mai wahala Nayla, komai yana faWa daga zuciyarsa babu ?arya balle ya faWa dan ya burge ki. Nayla ki bar hutun nan haka ki koma, kina sonsa yana sonki me za a jira kuma?."

Salma ta ce, "aji take so ta ja masa, da alama shi kuma tsinka ajin zai yi." Didi tayi dariya ta ce, "ban ga laifin ki ba Nayla, ki tsaya ki yi tunani zama da Omar wallahi sai ka shirya. Halinsa yana na babu inda yaje, sai kun zauna zaki fahimci abinda baki ma san dashi ba. Dan haka ki nutsu, in zaki iya da zafin ransa bismillah, in baza ki iya ba ki kama kan ki ki ja gefe. Abu Waya na sani kawai, Omar yana sonki."

Salma ta ce, "Didi ya ki ke zugata ne?."
"Ba zuga ba ce ba Salma, gaskiya ce. Omar ya wuce duk tunanin ku zama dashi sai da ha?uri." Nayla tayi murmushi ita dai bata ce komai ba amma hirarsa da ake yi ma daWi take ji. Sai magriba sannan suka wuce gidan Mama. Suna shiga falon suka tarar da Mama a zaune da alama su take jira.

Suna shiga ta ce, "Jidda kina da yarinya ?arama ki ta biye musu kuna yawo ko?." Jidda ta ce, "yanzu zan wuce Mama, motata zan Wauka." Mama ta ce, "Daga bara mu je saloon mu dawo sai yanzu magriba ko?." Salma ta ce, "mun Wan shiga siyayya ne daga nan sai muka shiga gidan Didi."

"Ai ya yi kyau. To Abba ya gan ku, ya kira ni yana ta faWa, yana cewa Nayla na da aure ina bari tana yawo. Dan haka umarni ne ba shawara ba, gobe ta shirya ta koma gidan mijinta in ba haka ba da ni da ku duk ran mu sai ya Saci."

Salma ta ce, "gobe kuma Mama?." Mama ta ce, "ni na aike ku tafiya yawon? Zan kira wacce zata yi mata ?unshi gobe da safe, sannan zan aika aje a gyara gidan da daddare sai ta koma" ta faWa tana bar musu wajan. Jidda ta ce, "gashi gobe bana nan zamu fita da Baby." Salma ta ce, "Tunda Abba ne ya ce kuwa sai ta koma goben, dama dai Daddy ne zai iya sakkowa, amma Abba babu wasa. Ki je zamu yi waya" Suka shiga ciki ita da Nayla ita kuma Jiddq ta fita.

Kamar yadda Abba ya ce hakan ce ta da faru, washe gari mai lalle ta zo da safe aka yiwa Nayla ?afa da hannu amma na saman fata, bata cika son wanda ake yi a tafin ?afa da hannu ba ta fi son ba?i ko ja amma na kan fata. Da wuri aka gama yi mata, daga gidan Hajja aka aika aka je gyara gidan.

Da yake da Salma duk wani abu da suka siyo Salma ta saka, daman frames ne da babu a gidan suka siya suka kafa, sai wanda ta ajjiye mata a Waki dan bata san inda zata saka mata ba. Sai kayan banWaki da ta sake siya, towels da sababbin bathrobes, sai kayan ado na falo da kitchen. Aka gyara gidan har aka gama gyaran Omar baya nan suka yi turaren wuta suka koma gida.

Bayan sallar i'sha Mama ta tarar da Nayla ta shirya cikin abaya ba?a mai kyau da tsantsi, tayi mata kyau dan gyaran jikin da aka yi mata ya karSeta. Mama ta kalle ta ta ce, "To driver zai mayar dake, Abba ya ce kar wanda ya yi miki rakiya daman ai ke kaWai kika zo. Nasiha an yi miki tun ba yanzu ba na san duk kin ri?e, abinda ana ce miki kawai ki bar komai ya wuce kamar baki dawo gida kin zauna ba, ki ajjiye komai ki yi facing zaman aurenki. Sai kin yi ha?uri, duk soyayyar film ko ta littafi da ki ke tunani ba ita zaki gani ba, za ki ga daidai misali wacce ta isheki ki faWawa duniya mijinki yana sonki. Sannan kin zauna dashi kin san halinsa, sai ki yi ha?uri akan wasu abubuwan dan aure Wan ha?uri ne Nayla. Allah ya baku zaman lafiya ya Worar da zaman ku har mutuwa, Allah ya sa ki gaji iyayen ki." Nayla ta amsa da amin. Ummimi da Mama suka rakata har mota, a lokacin Abbas yake ajjiye motarsa a wajan.

Mama ta ce, "Abbas ?anwarka zata koma gidan mijinta, ayi mata nasiha." Ya yi murmushi ya ce, "ban da rashin ji." Dariya suka yi gabaWaya ya shiga ciki ita kuma ta shiga motar suka tafi.

A ?ofar gidan aka ajjiye motar ta fita ta bashi kuWin napep sannan ta ce ya kai motar gidan Hajja ya ajjiye. Ya amsa mata da to ita kuma ta buWe gate Win gidan ta shiga.

Sabuwar motarsa tana ajjiye a wajan, Nayla ta kalla ta yi murmushi tana mamakin motar dan ita dai ta san tana da tsada sosai, ta girgiza kai sannan ta wuce zuwa cikin falon. ?hamshi falon yake yi sosai, ta yi murmushi ta wuce ciki ta ajjiye jakarta da laptop Win da take hannunta.

?akin ta kalla komai yana nan sai dai an canja komai hatta bedsheet Salma ta canja mata. Ajiyar zuciya tayi ta kalli agogo ta ga tara na dare ta kusa sai ta rasa abinda zata yi. Frame Win da Salma ta ajiiye mata ta gani ta buWe, hoton Tiger ne babba mai shegen kyau, ta buWe baki ha?oranta sun fito waje. Ajjiyewa tayi domin a Wakinsa take son kafawa. Zama tayi ta kira Didi a waya tana bata labarin ta dawo, Didi ta dinga murna da addu'a Nayla na ta murmushi.

Kitchen ta shiga tana sake kallonsa kamar wacce ta shekara bata nan, yana nan yadda yake dan daman ta san babu abinda zai taSa a gidan. Tunani take yi ta yi girki ko kuma ta ?yale girkin dare ya yi?.

Noodles ta Waukota ta kalli bayanta taga kayan miya, irish potatoes da plantain a ajjiye, ta san dai aikin Salma ne ita bata bar komai ba, koda ta bari ai ya ci ace ya lalace. Nan da nan ta dafata ta sai ?hamshi take yi ta samu flaks mai kyau ta zuba yadda baza ta huce da wuri ba.

Tana gamawa ta wanke hannu kenan ta ji motsin shigowa, ta fito ta tsaya cak tana kallonsa yana shigowa yana amsa waya. Yadda yake maganar ta gane da Didi yake waya kafin ta ga ya kashe wayar.

Kallon falon ya yi ya ce, "waye ya shigo gidan nan?." Murmushi tayi da alama Didi bata faWa masa ba kenan. Fitowa tayi daga inda take ta tako ta ce, "Sannu da zuwa." Cak ya tsaya ya Wago idanunsa ya kalle ta suka haWa ido tayi murmushi ta saukar da kai ?asa.

Zuba mata ido ya yi na wani lokaci kafin ya janye idanunsa dan shi a tunaninsa gizo take yi masa. Nayla jin shiru sai ta kalle shi ta ce, "YaMar!." Lumshe ido ta ga ya yi ya buWe, ya kalli inda take ya tsayar da idonsa ?yam akanta yana so ya tabbatar itace ko kuwa gizo take yi masa. Nayla ganin kallon da yake mata ya yi yawa ta sauke ido ?asa tana kifta idanu da turo baki gaba.

Ajiyar zuciya ta ji ya yi amma bai ce komai ba. Waya ta ga ya saka a kunne yana cewa, "na faWa miki gidan nan akwai aljanu, yanzu ba muryarta kaWai nake ji ba" ya jiyo yana kallon Nayla ya ce, "ita nake gani a gabana a tsaye, kuma dan rashin kunya irin na aljani ko tsorona ma bai ji ba kallona ma take yi."

Nayla ta ?yal?yale da dariya ganin da gaske bai Wauka ita Win bace ya Wauka aljana, ganin yadda take dariya ya saka bai ji ma abinda Didi ta ce ba. Sai da ta kira sunansa da ?arfi sannan ya ce, "ina jinki."

Shiru ta ga ya yi sannan ya ce, "wai da gaske ki ke?." Kashe wayar ta ga ya yi ya sake zuba mata ido kamar mai son tantance wani abun. Nayla da ta gama dariya cikin sanyin murya ta ce, "in baka banbance ni Win ba ce ka Wauka kawai aljanar ce" ta faWa tana murmushi murya a sanyaye.
KRB3P040

Wani irin nishaWi da daWi Omar ya ji yana mamaye masa zuciyarsa, nan da nan farin ciki ya bayyana har a kan fuskarsa, ya bita da kallo yana ji kamar ya rungume ta amma baya so ta ga ya za?e da yawa ko ta yi masa kalla Wan iska. Murmushi ya yi mai bayyana farin cikin da yake ciki, ya Wan shafa kansa kaWan yana girgiza kai ya ce, "amma an shammace ni." Nayla ta yi murmushi itama amma bata ce komai ba.

Omar ya kalle ta kamar zai yi magana sai ya fasa yana murmushi, ya sake kallonta cikin sanyin murya ya ce, "Yaushe haka?." Nayla taji farin ciki na mamaye mata zuciya, muryar da ya yi amfani da ita wajan yi mata magana bai taSa yi mata magana da ita ba. Ta Wan kawar da kai ta ce, "Wazu na dawo. Har dinner na shirya maka."

Omar ya kalle ta kamar zai yi magana sai ya fasa bai ce komai ba, yana sosa goshinsa kamar yadda ya saba. Nayla a sanyaye ta ke saboda sanin halinsa, amma tana so ta zama wayayyiyar amarya shiyasa take dakewa tunda ba ba?onta bane. Ta koma inda abincin yake ta zuba noodle Win a bowl ta kalle shi ta ce, "ka zauna." Ya kasa tantance adadin farin cikin da yake ji a zuciyarsa hakan ya saka shi ya zauna Win kamar yadda????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? ta ce.

A hankali ta tako ta zauna ta mi?a masa ta ce, "bismillah." Bai karSa ba sai kallon abinda ta mi?o masa Win ya yi, ya kalli hannunta da ya sha jan henna akan fatar hannun. Nayla bata yi magana ba shi kuma bai karSa ba sai kallon hannunta da yake yi.

A kusa dashi ta ajjiye bata ce komai ba, ta zauna kawai tana kallon wani wajan daban tana jin kanta kamar an Waure ta da igiya. Dauriya take yi kawai, amma nauyi da kunyarsa take ji sosai, tana so ta bar komai ya wuce kamar yadda Mama ta ce. Omar ikon Allah yake kallo, gata dai a kusa dashi, amma kewarta yake ji tana shiga cikin zuciyarsa, ya rasa abinda zai yi da zai ji ya gamsu da ita Win ce a kusa dashi.

Hannunsa ta ji akan hannunta, tayi saurin juyowa saboda abinda ta ji ya soki zuciyarta har fatar hannunta da ya Wora tasa sai da ta ji. Shima kansa ya ji wannan yanayi, amma yana so ya tabbatar da ita Win ce ko dai ba ita bace.

"da gaske ke ce?" Ya faWa a hankali yana binta da kallon tsakiyar ido cikin wani irin yanayi. Nayla ta yi murmushi, duk da abinda take ji a jikinta saboda haWuwar hannunsu waje Waya a karo na farko ta daure ta ce, "Ni ce." Sai ya janye hannunsa ya zuba mata ido ya sake yin shiru bai ce komai ba.

Ita kuma kallon ne yake takura ta, sai ta kasa sakewa gabaWaya ta sunkuyar da kai. Omar ya kasa Wauke ido daga kallonta, yana kallon ta girmama girman ikon Allah da hukuncinsa akan bawa a duk lokacin da ya so. Wai shi ne yake ji kamar ya haWWiye Nayla saboda son da yake mata, shine yake jin kewar Nayla kamar ya haWa jikinsa da nata haka yake ji. Ya kasa magana kuma bai daina kallonta ba, sai da ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce "Komai ya wuce ko bai wuce ba?."

Nayla sai ta yi nufin tsokanarsa da jan aji ta ce, "bai wuce ba, na zo ne kawai na karSi takardata." Murmushi ta ga ya yi bai ce komai ba bai kuma Wauki abincin ba, sai kuma ta ga ya tashi ya shiga Waki. Nayla ta bishi da kallo ta ce, "Allah ya ?ara min, gashi nan ai zan jawowa kaina." Kallon indomie Win ta yi ta Wauke ta ajjiye akan table ta tashi ta shiga Waki.

Zuciyarta duk babu daWi ta canja kaya zuwa doguwar riga ta bacci ta dawo ?aramin falon kenan ya shigo. Mi?a mata takardar ya yi ya ce, "gashi." Gaban Nayla ya yanke ya faWi, ta yi saurin kallonsa ta ga babu alamun walwala ko wasa a tare dashi. Murmushin da ta gani Wazu ya gushe gabaWaya ya dawo asalin Omar Win da ta sani a baya. Idanunta a waje take kallonsa saboda tsoro ta kasa daina kallon idanunsa.

Murya na rawa ta ce, "meye wannan Win?." Omar ya dake cikin muryarsa ta ko yaushe a kausashe ya ce, "abinda ki ka nema, na faWa miki daman bazan miki dole ba, in na tabbatar baki son zama dani zan iya abinda ki ke so, ?arSi." Nayla ta kasa karSar takardar da yake mi?o mata, hannunta sai rawa yake yi ta ?i ta motsa balle ta mi?a hannu ta karSa. Hannunta ya ri?o guda Waya ya saka mata takardar ya ce, "ki buWe domin ki tabbatar."

Yadda hannunta yake rawa zai baka tabbacin zuciyarta bugawa take yi fiye da ?a'ida,ta kasa ri?e takardar ma balle ta buWe. Cikin muryarsa mai saka yara su shiga hankalin su ya ce, "ki buWe na ce" ya faWa yana buWe mata idanunsa.

Kai ta girgiza tana hawaye, ya kulle ido ya buWe akan fuskarta ganin sai kuka take yi ta kasa buWewa. "Ki buWe!." Da hanzari ta fara buWe takardar tana sakin kuka mai matu?ar sauti. Ta buWw amma ta?i kallon abinda aka rubuta, sai kuka take yi sosai ta koma kan kujera ta zauna idanunta a kulle.

Hawaye sai sauka suke yi akan takardar da take hannunta ta kuma ?i buWe idon balle ta gani. Yana tsaye yana kallonta cikin tsananin ?auna da soyayya kafin ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login