Showing 72001 words to 75000 words out of 332344 words

Chapter 25 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14414

?an rufe ido ya yi ya buWe, kashe masa jiki take yi in ta faWi sunan bai san meyasa ba.

Bata jira ya amsa ba ta ce, "Zan je gidan Hajja." ?an kallon ta ya yi yaga ba shi take kallo ba ya ce, "kina faWa min ne daman in zaki fita?." Nayla ta Wago kai suka haWa ido, tayi rau-rau da ido kamar zata yi kuka ta ce, "ai bana zuwa ko ina, aiki fa kawai nake zuwa."

Muryarsa a can ?asa babu alamun tsawa ya ce, "Shi aikin ba wani waje bane ba kenan?." Nayla ta bishi da kallon mamaki jin abinda ya faWa, kuma shi fuskarsa ba a sake take ba balle ta Wauka ko wasa ya ke yi mata. Shiru tayi bata tanka ba, to me zata ce masa kuma? Shi fa ya ce ba sai ta tambaya ba amma yanzu kuma shine yake cewa aikin ma bata tambayarsa take zuwa. Bai sake yi mata magana ba ya wuce ya fita Nayla kawai sai fara hawaye, yanzu me yake nufi kenan? Ta je ko kar ta je ita bata gane masa ba.

Nayla haka ta ci kukan ta godewa Allah, tana ganin kiran Salma ta?i Wauka saboda kar ma ta Wauka ta ji hayaniyar ?an uwa ranta ya sake Saci. Kitchen ta shiga ta cigaba da haWa abincin sadaka da tayi niya. Kiran Karima mai aikinta tayi tazo tana taya ta aikin dan su yi sauri.

A lokacin ta gama dafa fried Chinese rice da kaza, ita da mai aikin ta suka zuba a packs guda hamsin, sannan aka Wora ruwa da lemo da kuma naira dubu Waya. Mai aikin ce ta Wauka ta fita dashi tana rabawa bayan ta gama ta dawo ta gyara mata kitchen Win ta wanke kayan sannan ta koma gidan Hajja dan can ma aiki ake yi sosai.

Nayla Bashir ta kira a waya ta ce yazo ya karSar musu sa?o. Kamar da ?aramar sallah tare suka shigo da Omar tana jin muryar Bashir ta san tare suka shigo dan da zata ji yana buga gate, da hijjab a jikinta fito falon, yana ganinta ya ce, "Antyn mu barka da yamma." Ta yi murmushi ta ce, "Barka dai Bashir, ga abincin iftar"ta faWa tana bashi manyan packs masu girma guda uku. KarSa ya yi ya ce, "godiya mu ke Antyn mu, Allah ya saka da alkhairi."
"Amin ya rabbi" ta faWa tana juyawa ta koma shi kuma Bashir ya fita.

Omar dai bai ce komai ba ta sake dawowa a sanyaye kanta na ?asa, ta so ta daure amma Allah ya sa tana son zuwa gidan Hajja shiyasa zata sake yi masa maganar. Nayla ta kalle shi ta ce, "YayaMar." BuWe ido ya yi ya kalle ta tare da mi?ewa tsaye. Azumin ne yake Wan bashi wahala kasancewar ana rana sosai, duk da yamma tayi amma har lokacin da zafin rana. Ta ce, "Don Allah Ina so na je gidan Hajja."

Kallon ta ya yi dan shi ba dan ya ganta ba ya Wauka ta tafi, ganin yadda take hawaye sai abin ya bashi mamaki ya ce, "zan hana ki ne?." Nayla hawaye ya sake sakko mata ta ce, "baka ce na je ba." Yadda take ?ifta idanu ne ya Wauki hankalinsa, duk da kuka take yi amma hakan ya burge shi sosai. Zuba mata ido yayi yana kallon yadda take motsa bakinta gashin idanunta yana sama da ?asa, ido ya lumshe ya buWe ido tare da yin ajiyar zuciya ya ce, "ki je, daman ai bakya tambayata ko?."


Nayla murya na rawa ta ce, "Ka yi ha?uri." Ya Wan taSe baki ya ce, "Laifi ki ka yi?." Nayla ta Wan Wago ta kalle shi ta ce, "Ka ce ina fita bana faWa maka."

Bai bata amsa ba kiran waya yashigo wayarsa, bai Wauka ba ya datse kiran bai ce mata komai ba. Nayla ta ce, "in baka ce naje ba yau babu inda zan je." Yadda ta yi maganar a raunane ya saka shi ya sake kallon ta, sai ya yi murmushi wanda bai san dalili ba. Ita kuwa jin shiru bai yi magana ba kuma bata ji motsin wucewarsa ba sai ta Wago kai suka haWa ido, janye idanunsa yayi ya ce, "daman in zaki je ai bakya jira na ce." Nayla ta sake raunana murya da shagwaSa ta ce, "Yau zan jira" ta faWa tana sunkuyar da kai dan ta san baya jure doguwar magana, ta Wauka zuwa yanzu zai mata tsawa ne.

Shi kam ya ?i katse maganar ne saboda yadda take maganar da shagwaSa ba karamin burge shi hakan yake yi ba, shiyasa yake yin maganar da dole sai ta bashi amsa. ?an kawar da kai ya yi yana murmushi kafin ya juyo ya mayar da fuskarsa yadda ta ke ya ce, "ki je." Murmushin da ta saki mai sauti tare da yin ?aramin tsalle cikin farin ciki. Ba ?aramin tafiya da imaninsa hakan ya yi ba, ya zuba mata ido zuciyarsa na bugawa kafin ya Wauke kai ya juya zai fita.

"YaMar!" Ta sake faWa cikin sanyin murya da dauriya kar ya yi mata masifa. Cak ya tsaya bai juyo ba ta ce, "Na bar abincin iftar, don Allah ka ci." Juyowa ya yi ya kalle ta suka haWa ido ta janye idanunta dan gaban ta faWuwa yake yi in tana kallonsa ta ce, "Don Allah." Bai tanka ba ya fita.

Murmushi ta yi ta ce, "YaMar Ina sonka sosai, Allah ya saka maka sona a zuciyarka" ta faWa tana juyawa da sauri ta Wauki hijjab da abinda zata kaiwa Hajja ta fita a guje sai gidan Hajja cike da zumuWi.
KRB3P022
ArewaBooks@nanahaleema.

Nayla a gidan Hajja ta sake tana ta harkokinta, kana kallon ta zaka ce bata da wata damuwa saboda ta shiga cikin ?an uwa ana ta hira ana dariya. Kaf Win su ?a?a da jikoki suna tare da Hajja, mahaifiyarta ce? kawai babu amma ita ta maye gurbinta. Haka aka sha ruwa cikin wasa da dariya an saka Hajja a tsakiya wanna ya ce wannan yace.

Bayan an gama shan ruwa ne Nayla ta koma gefe Hajja ta kalleta ta ce, "Hauwa ya aikin sallah? Zaki iya kuwa?." Nayla ta kalli Hajja a shagwaSe ta ce, "ni bazan iya ba, da yayi min maganar ma na ce a bayar sadaka kawai ni bazan iya aiki ba. Ban ma taSa yi ba fa Hajja." Hajja tayi murmushi ta kalli iyayenta maza da suma suka yi murmushin, ko ba ta faWa ba sun tabbatar da ana samun canji sosai a zaman ta da Omar.

Hajja ta ce, "Ashe ma ya tambayeki, ni na Wauka kawai sai dai ki ga an kawo namn sallah." Nayla tayi ?ar dariya, bata fahimci bugun cikinta Hajja take yi ba ta ce, "A'a ya tambaya zan iya nace a'a kawai in an yanka a rabar, in ina son ci zan turo nan." Hajja ta yi murmushi ta ce, "To ai shikenan, Allah ya taimaka." Aka amsa da amin kafin Nayla ta mi?e tana amsa waya ta bar wajan.

Mama Sa'adatu ta kalli Hajja ta ce, "Yanayin Nayla bai yi kama da wacce take cikin damuwa sosai ba, duk da har yanzu bata mayar da jikinta na baya ba amma walwalarta ya nuna bata tare da Sacin rai." Hajja ta ce, "Na faWa mu ku ni a jikina nake jin auren nan nata babu abinda zai raba shi sai mutuwa."

Daddy ya ce, "Ni ta yadda hankalina ya kwanta da auren yadda gabaWaya aka daina tashin hankali da mijin na ta, sannan sana'ar da yake yi Allah ya saka mata albarka lokaci kaWan." Abba ya ce, "wannan shine kawai abin farin cikin, ni kaina in na tuna a yanzu ya dogara da kansa Ina jin daWi. Amma ina ganin har yanzu zaman su bai wani daidaita yadda ake so ba."

Baba ya ce, "In sha Allah komai zai wuce ya zama labari." Aka amsa da in sha Allah suka cigaba da hira har Nayla ta dawo ta zauna suka koma gefe ita da Salma suna hira.

Sai kusan tara na dare sannan suka taho ita da Salma a ?asa suna hira. Nayla ta ce, "Salma kin san meye?."
"Sai kin faWa."
"A farkon auren mu YaMar ya ce in zan fita ba sai na faWa masa ba, babu ruwan shi da inda zan je, amma yanzu in na fita ban faWa ba sai naga kamar yana jin haushin hakan, ya ki ke gani, na dinga tambayarsa ko na share tunda ai shi ya faWa tun farko?."

Salma ta ce, "canjin zaman naku da aka samu shiyasa yake jin haushi, ni fa wallahi gani nake kamar yanzu shima yana sonki Nayla, kawai shegen banzan halinsa ne ya hana shi ya bayyana. Ki yi ha?uri kar ki ce na zagar miki miji, amma akwai abinda yake ji a zuciyarsa game da ke. Tunda ki ka bani labarin yadda ya dinga faWa akan ?afarki ake advert da ita na saka question mark akansa."
"Kema wai tunanin ki kishina ya ke yi?."
"To meye in ba kishi ba?."
"Kawai ya tsane ni mana, baya so na shiga cikin abinda ya shafe shi."

Salma tayi murmushi ta ce, "Nayla kenan, kin riga da kin saka hakan a ranki ne shiyasa. Amma ni yanzu gani nake yi yana jin wani abun a kan ki sosai." Nayla ta yi ajiyar zuciya ta ce, "ban saka a zuciyata ba Salma, kar ma na saka yazo ya dame ni gwara na tsaya a inda ya ajjiye ni. Ina sonsa har gobe, babu abinda ya ragu daga son da nake masa. Ban saka a raina yana sona ko yana kishina ba, amma ya canja sosai daga zaman mu na farko zuwa yanzu. Kuma maganar Didi ce ta tabbata da ta ce bashi da saurin sabo ne, da zarar mu saba wani abun zai canja kuma gashi."

Salma ta ce, "to da hakan, amma wannan ya wuce saurin sabo Nayla, kawai mu cigaba da addu'a, Allah ya kawo silar daidaitawar ku. Allah yasa ya so ki fiye da yadda ki ke sonsa." Nayla ta yi mumurshi ta ce, "Amin Sis."
"Ki cigaba da tambayarsa duk inda zaki je Win, daman ai mijinki ne."

"Wani lokacin tambayar ce sai a hankali, Kamar wahainiya yake canjawa yake a ko yaushe. Yanzu zai yi kirki anjima ya birkice ya hauni da masifa." Salma ta yi dariya ta ce, "zai yi ya gama, akwai lokacin mu da zai zo mu wahalar da Wan banza." Dariya itama tayi har suka zo bakin gate Win Salma ta koma ita kuma ta shiga ciki.

Daman ta san baza ta same shi ba, amma babban abinda ya bata mamaki yau kam ya ci abinda ta ajjiye Win duk da sai ka kula zaka fahimta bai ci da yawa ba amma ita da ta ajjiye ta san an taSa. Sosai ta ji daWin hakan a zuciyarta ta kuma amince da yanzu Omar Win ya canja sosai.

Washe gari sallah ba su haWu da safe ba saboda baccin da tayi sai tara ta farka, ta ji haushi sosai dan ta so ta sake zuwa sallah amma Allah bai yi ba. Wanka tayi ta ci kwalliya cikin atampa Winkin fitted gown. GabaWaya atamfar ta dame ta, saboda ita bata saba saka kaya fitted ba ta fi gane wanda zata sake sosai. Tana Waura daknwali tana mita, Salma ce ta saka tailor Win gabaWaya ya yi mata wannan Winki, daga fitted gown, sai straight, sai kuma riga da siket masu ?aramar riga.

Bayan ta gama Waura Wankwalin ta kalli kanta a madubi, ita kanta ta san tayi kyau rigar ta fitar da ko wanne lungu na shape Win da Allah ya yi mata. Tabbas ta yi kyau matu?ar kyau, Wankwalin da komai ya zauna daram.

Waya ta Wauka ta kira Abiy dan tayi masa barka da sallah amma bai Wauka ba, ta kira Mama ma bata da??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????uka ba sai ta kira Yaya. Shi ta same shi suna ta hira har ya haWa ta da matarsa da ?arsa suna ta hira sosai kafin ta kashe ta kira Yaya J.

Shima ya Wauka, sai ta fita ta shiga kitchen ta saka wayar a speaker tana aiki suna hira da Jawad. Sun jima suna hira dan har ta yi making sandwish da milkshake suna waya. Da ta kashe ta kira Jalila, duk da ta san suna tare da su Mama a saudia itama bata Wauka ba.

Falon ta fito tana kallon falon a bayyane ta ce, "Yau na san Karima baza ta samu damar zuwa ba suna aikin sallah a gidan Hajja, kuma falon nan ya Wan yi ?ura kaWan" ta faWa tana shafa tv stand Win da ya WN yi ?ura. Ajiyar zuciya ta yi, gabaWaya bata son yin aiki a ranar Allah ya sani, Wan tsaki ta yi kaWan ta motsa da niyar barin wajan aka turo ?ofar falon aka shigo.

Juyowa ta yi ta kalle shi yana sanye da yadi blueblack mai ?ananun zane, hatta hular kansa blue ce, kayan sun karSe shi sosai dan ya yi kyau matu?a. HaWa idanu suka yi shi da ita, a cikin second biyar ya ?are mata kallo tun daga sama har ?asa sai ya Wauke kai kamar bai ga komai ba.

Nayla ta ce, "Ina kwana." Sake kallon ta ya yi kafin ya ce, "lafiya."
"An yi sallah lafiya?."
"Lafiya."
"Allah ya maimaita mana." A hankali ya furta amin. Murmushi tayi dan wallahi ya yi mata kyau sosai, ji take kamar ta je ta tsaya tayi musu selfie dan billahillazi ya tafi da imaninta.

Shi Win ma ba ?aramin kyau ta yi masa a ido ba, rigar tayi mata kyau ta zauna daram a jikinta kamar a jikinta aka Winka. Shape Win ya fita sosai ta fitar da figure 8 a jikinta. Ga wuyan rigar daga sama a Wan buWe yake dan wuyanta a waje yake duk da ba a hango ?irjinta sosai amma wuyanta a bayyane yake gabaWaya. ?an motsawar da tayi ne ya saka ya kai idanunsa wuyan nata a nan yayi farin gani domin kuwa ana iya hango saman ?irjinta daga inda take tsaye. Ajiyar zuciya ya yi zuciyarsa na harbawa da sauri, jikinsa ya yi sanyi sosai yanayin da bai taSa jin irinsa ba yana mamaye jikinsa, a haka ya taka zai shiga ciki ta ce, "YaMar har an yi yankan?."

Kai ya Waga mata kawai bai ce komai ba dan in ya yi magana zata iya fahimtar canji a muryarsa. Nayla ta ce, "Allah ya bayar da lada." Bata ji ba amma ta san ya ce amin.

"Ga breakfast." Juyowa ya yi ya kalle ta ya ga ita ba shi take kallo ba waya ma ta ke dubawa da tayi ?ara a lokacin. Bai tanka ba ya wuce ya shiga ciki cikin sabon yanayin da yake mamaye zuciyarsa da ganganar jikinsa.

Rana ta farko da ya ganta cikin shigar da ta bayyanar da surarta, rana ta farko da ya tsaya ya ?are mata kallo har ya ga tsadaddiyar surar da Allah ya halitta a jikinta. Surarta ta firgita shi sosai, kwaliyyar tai mata kyau kamar kar ya daina kallonta haka yake ji a zuciyarsa. Sai gilma masa take a yi a ido, ya rasa dalilin da ya saka ya ga kayan sun yi mata kyau sosai, a ?asan ransa kuma haushi yake ji in ya tuna wata?ila ma namiji ne ya yi mata Winkin ba tare da ya san dalilin jin haushin ba.

Narma ce ta zo idanunsa kawai sai ya lumshe ido ya buWe, ya kasa banbance me yake ji akan Nayla dan ba irinsa ya ji akan Narma ba, abinda yake ji akan Narma daban da abinda yake ji akan Nayla. Nayla zuciyarsa bugawa take yi koda haWa ido suka yi, Narma kuma daga ranar da furta tana sonsa bai sake jin irin wannan bugawar zuciyar ba. Iya ranar kawai ya ji faWuwar gaba, ranar da ta ce tana sonsa. Hana rantsuwa ya ji faWuwar gaba a ranar da ta kira shi da Faruk, bayan nan bai sake ji ba. Shi kaWai ya san abinda ya ji a zuciyarsa a lokacin baya har ya furta yana son Narma, to ita kuma Nayla sam ba haka yake jin abinda yake ji a kanta ba, shiyasa bai taSa kawowa a ransa yana sonta bane tunda a ganinsa ya san so tunda ya so Narma.? (kai dai ka sani malam Omar>?(?).

Haka aka cigaba da hidimar sallah banda gidan Nayla, ko kasko nata Wora ba kullum tana zaune tana aikin danan waya sai dai a aiko mata daga gidan Hajja da zafinsa ta saka masa yaji tana ji. Har Didi sai da ta kawo musu nama mai yawa, ita kuma a lokacin ya fita daga ranta shi kuma ba ci yake yi sosai ba. Dambun nama Mama Sa'adatu ta aiko mata dashi da yawa kamar bata so, ya yiwa Nayla daWi kuwa domin ta fi jin daWinsa akan naman.

Sallah ta wuce kowa ya cigaba da harkokinsa Nayla ma ta koma bakin aikinta. Ranar juma'a da daddare tana zaune kamar ko yaushe ta yi wanka ta saka kayan bacci aka kira wayarta. Ganin kiran mijin Jidda sai abin ya bata mamaki, ta Wauka ta saka a kunne. Abinda ya mata ya saka ta yin ihu ta buga tsalle tana murna tana cewa, "To gani nan zuwa yanzu" ta faWa tana mi?ewa da gudu ta shiga Waki ta saka abaya akan kayan baccin ta yafa mayafi ta zari key ta fito falon.

Cak ta tsaya tunawa da sai fa ta tambaye shi gashi bata sani ba yana nan ko baya nan ma oho. Hankalinta gabaWaya baya jikinta, zumuWin haihuwar da Twiny ta yi ya saka ta ?aguwa har ta ?arasa bakin ?ofar tana son ta ji yana ciki ko baya nan. Ta kasa kunne ko zata ji motsi amma shiru, ba tare da ta lura ba ya buWe ?ofar ta gaba kamar zata kifa ta faWa jikinsa.
KRB3P023
Gabanta ya faWi jin ba?on yanayi da ya kawo mata ziyara lokaci Waya, da hanzari ta bar jikinsa ta sunkuyar da kai ?asa ?irjinta yana sama da ?asa. Shi kansa abinda ya ji kenan a jikinsa, lokaci Waya yaji abu ya gauraye masa jininsa ba tare da ya sani ba. Bai nuna mata hakan ba ya bita da kallo ganin ta da shirin fita sai abin ya bashi mamaki yana


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login