Showing 192001 words to 195000 words out of 332344 words

Chapter 65 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14384

da ido alamun shagwaSa ya ce, "kina yi min kuka sai na baki mamaki yau a gidan nan, ke ce mai bakin kuka ko?" Ya faWa cikin faWa yana shiga ciki ya barta zuciyarsa cike da kewarta amma haushin ta yake ji ga haushin da Didi ta bashi.

? ? Bata sake ganinsa ba itama bata neme shi ba dan sai ta ji itama ya sake bata haushi, ya tsaya ta bashi ha?uri ya ?i sai wani kauce-kauce yake yi kamar shi aka fara yiwa laifi a duniya. Bayan sallar la'asar mai aikin ta gama gyara mata gidan ta tafi aka fara ruwa mai ?arfi, ta kalli agogo a lokacin ?arfe huWu na yamma, ta tashi ta kunna bunner ta saka turare a gidan sai gidan yayi daWi ga ruwa ga ?hamshi.

?aki ta shiga ta kwanta a kan gado tana danna waya, da ta tuna shi sai ta kawar dashi daga kanta dan son bashi ha?urin gabaWaya ya fita daga ranta. Maganar Didi ta tuna sai ta mi?e tsaye tana kallon window, murmushi ta yi ta ?arasa wajan kayanta ta canja kaya zuwa doguwar riga ?ar kanti mai laushi, yadin yana da laushi da kwantawa a jiki, sannan daga bayan rigar a tsage take har cinya, hannu Waya kuma hannun vest ne guda Waya ne mai Wan kauri kaWan. Daga gaban rigar an yi ?aton cylcle a buWe yake, daga ?asa wajan wraist Win rigar shima a buWe yake sai igiyoyin da za a Waure, sannan daga sama ana iya hango jikinta.

Daman gashi in period Win ta yana hanya tana samun fullnesses of breast, suna cika sosai su yi kyau har sai bayan ta kammala suke saki su dawo yadda suke, ta wannan hanyar kaWai tana fahimtar lokacin period Win ta ya kusa.

Turare ta shafa a jikinta ta saki gashin kanta kamar yadda ta san yana son gani, dan ko ta Waure indai yana kusa tabbas sai ya sake shi, kallon kanta take yi ita kanta ta san tayi kyau amma tana jin kunyar abinda take niyar yi. Ajiyar zuciya tayi tunawa da kalaman Didi sai ta samu ?arfin guiwa ta nufi Wakinsa.
KRB3P070
Nana haleema.


Yana zaune ko riga babu a jikinsa ya jingina da kansa da kujera yana aikin tunaninta, imagination yake yi ace gata a kusa dashi yadda garin nan ya yi daWi ga khamshin turaren da gidan yake ji wanne irin moment zasu samu? Wanne irin farin ciki da jin daWi zai samu daga gare ta a wannnan lokacin?. Wannan tunanin da yake yi sai ya fara hargitsa shi yanayinsa ya fara canjawa, amma baya so ya je gare ta sai ta gane ta yi masa laifi. Duk da gab yake da kasa jurewa, amma yana ?o?arin jurewar kafin ya gaza.

BuWe ?ofar ya ji anyi kafin ta yi magana ?hamshin turarenta ya bashi tabbacin isowarta. Ya ja numfashi ya sauke tare da runtse idanunsa, ?arar saukar ruwan sama ya cika ko ina amma shi bugun zuciyarsa kawai yake jin sauti. Ya rasa wanne irin so yake yiwa Nayla, ya rasa me yake ji a kanta, ji yake kamar kowa ya mutu a duniyar a bar su su biyu kawai, ji yake kamar su kaWai ne a duniyar babu wanda ya kai shi sa a a rayuwarsa.

Ajiyar zuciyar ya ke yi a hankali cikin jin daWin ganinta. Murya a tausahe yaji ta ce, "YaMar! Rouhi!" Ta faWa a tare cikin muryar da ta saka ?wa?walwar sata tafi hutun rabin lokaci, ya buWe ido a hankali ba tare da ya kalle ta ba.

Ta sake cewa, "YaMar don Allah ka Waure min igiyar bayana, bazan iya ba" ta faWa tana kallonsa kamar zata yi kuka. BuWe ido ya yi a hankali ya kalle ta, ya ja numfashi da?yar ganin yadda tayi mahaukacin kyau ga komai da yake bu?ata ya bayyana daidai da ra'ayinsa. Zuciyarsa daina bugawa tayi na wasu da?i?u, kafin daga ta fara bugawa da gudun har sai da ya dafe ?irjinsa jin tana neman fasa masa ?irji, wani abu na yawo a cikin jininsa yana zagawa har cikin ?wanyar kansa.

Ya ?amar da idonsa akanta ko ?iftawa baya yi, shau?inta na sake fizgarsa zuwa gare ta, ji yake kamar ta dawwama a haka yana kallon ta saboda abinda yake ji. Nayla ta kuma cewa, "YaMar don Allah!" Ta faWa tana takowa inda yake hakan ya bawa jikinta damar motsawa, ya yi saurin runtse ido yan jin yadda jijiyoyin jikinsa suke harbawa musamman jijiyar kansa kamar yana ciwon kai.

Kafin ya buWe ido ta ?araso ta juya masa baya ta sake cewa, "Please YaMar!" Ta faWa ba tare da ta kalle shi ba. Bayan na ta ya zubawa ido yana kallon kwantaccen farin gadon bayan ta da Allah ya yi mata, jikinsa ya fara rawa kamar ko yaushe, ya yi ?o?arin mi?ewa tsaye ya tsaya a bayanta yana kallon bayan ba tare da ya aikata komai ba. A hankali ya kai hannu ya ri?e igiyoyin bayan yana ?o?arin Waurewa tayi baya kamar zata faWi ya yi saurin ri?o ?ugunta jikinsu ya haWe waje Waya.

Shiru suka yi dukkansu, ya yi shiru yana sha?ar ?hamshin turarenta yanayinsa na sake canjawa jikinsa na cigaba da rawa. A hankali ta ce, "Ka Waure min Rouhii!."
Ba tare da ya sani ba ya ce, "Zaki zauta ni Ashiq!" Ya faWa idonsa a rufe. Nayla jin tarkon ta ya kama shi kamar yadda tayi niya sai ta sake motsawa a jikinsa ta ce, "Ka Waure min YaMar!." Da hanzari ya juyo ta ya bata kyakykyawar runguma yana kissing Winta jikinsa na cigaba da rawa.

Dariya Nayla tayi a zuciyarta tana, _akace baka ji YaMar, ashe taurin kan naka yana da limit, na Wauka zaka yi gardama, kai ga Damisa. Damisar gaske ma bata isa ta tsalle tarkon nan ba balle kai._ ta faWa a zuciyarta tana murmushi. Tana jin yadda ya ?an?ameta kamar zata gudu, duk da ita kanta bata cikin yanayin da zata iya guduwa ta bar shi amma tana so ta gwada ko dan abinda yace Wazu baya bu?atar komai daga gareta.

Yadda jikinsa ya saki babu ?arfi ya bata damar iya zare jikinta ta Wan matsa daga kusa dashi tana kallon fuskarsa kamar yadda yake kallon idanunta. A hankali ta ce, "tunda baza ka Waure min ba shikenan!" Ta faWa da shagwaSa tana motsa jikinta ta juya zata tafi.

Da hanzari ya ri?on hannunta murya a disashe ya ce, "ina zaki je?." Nayla ta fara kuka ta ce, "Waki." Ya jawota kusa dashi ya kasa magana sai kallon ta da yake yi. Nayla ta ce, "zan tafi."
"Ki bar ni da wa?" Ya furta can ?arshe ma?oshi, ba dan tana kusa dashi ba ma bazata ji ba. Nayla ta turo baki gaba ta ce, "Kai ka ce baka son ganina kusa da kai, kuma ka ce.....!" Bai bari ta ?arasa ba ya hanata ?arasawar, dan ji yake in ya bari ta cigaba da magana tsaf za a zare masa rai daga jikinsa.

Duk yadda Nayla ta so ga hana faruwar komai ta kasa dan ita kanta ya birkitata kamar yadda yake a birkice, daman ga maganin da Mama ta bata take ta sha kafin ta dawo daga Kaduna, ya taka rawar gani wajan saka shi ya fita daga hankalinsa. Uwa uba haWin kan da ya samu daga wajan Nayla, ?iris ya rage bai sume mata ba duk yadda take tunanin yanayin nasa ya wuce haka, ya susuce mata, aljanun da suke tashi kuwa tuni sun yi sallama.

? ? ?? Nayla kunyar duniya ta isheta, da ta rufe ido sai ta tuna da abinda ya faru da irin gudumawar da ta bayar sai tsigar jikinta tashi taji kamar ta tashi ta gudu saboda kunya. Ya matse ta ya hanata motsi a jikinsa, da ta motsa zai sake haWe ta da jikinsa idanunsa a kulle ya kasa ce mata komai. Agogo Nayla ta kalla ta ga shida da rabi yamma kuma har lokacin ruwa ake yi, da ya Wan lafa zai dawo da ?arfinsa.

"Ashiq!" Ya furta cikin wata irin murya da ta saka ta sake ri?e shi sosai dan bata so ya buWe bakinsa a yanzu kunya zai bata matu?a. Bata amsa ba ya ce, "na gode, Allah ya yi miki albarka." Murmushi ta yi bata ce komai ba ta dai amsa da amin a zuciyarta. Kiss ya yi mata a goshi ya kalle ta amma ta hana su haWa ido, da ya Wago da kanta sai ta rufe ido ta ?i bada damar da zai ga ?wayar idonta. Shi kuma so ya kalli cikin idanunta ko zai samu sau?in bugawar zuciya da kewarta da yake ji amma ta hana faruwar hakan.

"Jidda ke ce aljannata kuma duniyata!" Ya furta a hankali yana kallon fuskarta har lokacin bata buWe ido ba.

"Ina sonki, ban san adadin son da nake miki ba. Ban taSa zaton soyayyar mace zata shiga zuciyata haka kamar yadda nake sonki ba, ina ?aunarki, ina ?aunarki, zan iya rabuwa da komai indai za a bar ni da ke zan rayu cikin farin ciki. Ki kasance dani kin ji, kar ki rabu dani zan iya rasa rayuwata a kan ki!."

Murmushi ya ga ta yi amma bata buWe ido ba shi kuma idon yake so ta buWe amma ta ?i sai ma sake rufesu da take yi gam. Murmushi shima ya yi ya sake yi mata kiss a lips Winta, ya manta ma fushi yake da ita sai yanzu ya tuna hakan ya saka shi murmushi, ko giya yake sha shi ya isa ya cigaba da fushi da ita a wannan lokacin.

Dan tickling Winta ya yi sai kuwa ta yi dariya amma bata buWe ido ba ta ce, "Ka bari Rouhii bana so." Bai bari ba ya cigaba da yi mata sai da yaga tana dariya sosai sannan ya tsaya ya ce, "ki buWe min na ga idanunki Jidda!" Ya faWa yana Wago fuskarta. No?e kafaWa tayi ta koma jikinsa ta ce, "kunya nake ji."

"Ni bana so kina jin kunyata, meye abin jin kunyar? Akwai abinda ya rage a tsakanina dake ne?. Ki buWe ido na kalli idonki Jidda." Ganin bata buWe ba ya ce, "To kunyar ta meye? Dan kin farantawa mijinki shine ki ke jin kunya Ashiq? Dan kin saka aljanun dare tashi da yamma sai ki ji kunya?." Sai kuwa ya sake bata kunya sosai ta sake cusa fuskarta a ?irjinsa.

Murmushi ya yi in ya tuna yanayin da suka kasnace sai ya ji kamar ana sukarsa, duk wani farin ciki da yake so ya same shi a gare ta shiyasa gabaWaya ya ruWe mata, baya so ta bar kusa dashi gani yake da ta motsa kamar zata gudu. A hankali ya raWa mata ya ce, "ni fa na ji kin ?ara daga yadda ki ke, ko daman idan mutum ya kwana biyu bai shiga duniyarsa ba tana canjawa ta sake kyau da daWin shiga Jidda? Ki duba har kusa suma nayi, hawaye kusa kamar an kunna fanfo. Ashe da gaske akwai jin daWin da yake saka hawaye, na Wauka babu amma yanzu na tabbatar. Yau ba aljanun dare ne suka tashi ba, iskokan yamma ne" ya ?arasa faWa a kunneta yana Wan ciza fatar kunen. Nayla ta runtse ido bata ce masa komai ba.

Murmushi ya sake yi dan da gaske yake tambayarta, ya san bazata ta bashi amsa ba shiyasa ya yi murmushi. Nayla daga ?irjinsa ta ce, "ka daina fushi da ni?." Omar ya ce, "ni Win banza, ba dole na daina fushi dake ba Ashiq?. Irin wannan abin arzu?i da na samu in ban daina fushi dake ba ai sai Allah ya tambaye ni, meye ma fushi ni na manta meye?."

Dariya ta yi sosai ta rungume shi ya ri?e ta ya ce, "kar ki sake aikata hakan, duk inda ki ka je da kin shiga ki kira ki sanar dani hankalina zai fi kwanciya. Ke ce kaWai wacce nake so, ke kaWai nake ?auna, da ke na damu, In ban ji ya kika je ko ya kika dawo ba bazan iya samun nutsuwa ba." Nayla da shagwaSa ta ce, "in sha Allah bazan sake ba, kuma daman ba ina sane nayi hakan ba."

"Uhum to na ji." A hankali ta buWe ido suka haWe ido zata rufe ya ce, "kina rufewa ni da ke ne, Allah sai na yi miki abinda zaki ji kunyar da hujja."

Ta tsayar da idonta amma bata kalle shi ba ya ce, "Haka akwai ki dinga kunyar mijinki? Kunyar ta yi yawa ko yaushe kunya?. Ni fa ina so na zama Wan gatanki, ki bani kulawa kamar dai yau Win nan da kika haukata ni kika saka ni aljanun yaamma, ki ki saka na gigice miki na zubar da hawaye, ki ka saka na kusa su....!" Hana shi magana tayi ta hanyar rufe masa baki da bakinta, ya wara ido a cikin idanunta sai ta rufe tana ruf.

Kamar jira yake yi ya shiga sarrafata yadda yake so, kiran sallar magrib ya dakatar dashi ya koma gefe yana kallon ta idanunta har lokacin a rufe kafin ya tashi dan in ya cigaba da zama sallar ma za su rasa. Itama bata zauna ba fita ta shiga Waki a can ta yi sallah duk da ta san shima bazai fita ba dan ana yayyafi kaWan-kaWan.

Yunwa take ji sosai, tana idarwa kitchen ta shiga ta fara dama custard ta fara sha kafin ta dafa abinci. Kitchen Win ya shigo ya jingina da kitchen island yana kallonta cikin shau?i da soyayya. Jiyowa ta yi ta kalle shi ta Wauke kai, ya tako yazo inda take ya tsaya a bayanta yana kallon custard Win da take sha ya kalli fuskarta, gani ya yi ta sake yin haske lokaci Waya sai Waukar ido take yi. Nayla ta ce, "Yunwa nake ji shiyasa? nake shan custard kafin na dafa abinci."

"Ki shiga custard Win za a kawo abinci." Ta juyo tana kallonsa jikinta yana gugar na sa ya zuba mata ido kamar ya cinyeta ta ce, "kana sangarta ni da ?in dafa abinci yanzu." Sai da ya kai bakinsa kunnen ta sannan ya ce, "girman ki ne Ashiq!." Murmushi ta yi ta sake sunkuyar da kai, ya Wago kanta da yatsunsa yana kallon dogayen gashin idanunta da suke kwance a fuskarta.

Shi kam ya rasa wanne irin abu yake ji akan Nayla. Sonta, ?aunarta, kishita, shau?inta, sha'warta gabaWaya suke tarar masa lokaci guda shiyasa yake rikicewa in yana tare da ita, saboda abubuwa da yake ji suna ?o?arin fin ?arfin tunaninsa da hankalinsa. Sai ya ji kamar an saka igiya ana jansa da ?arfi, in yana kusa da ita baya ganin komai sai ita. Ya zuba mata ido kawai yana kallon fuskarta kafin ya ce, "Kina jin irin abinda nake ji a kan ki Jidda!?."

Ta buWe idanun ta kalle shi ya Waga yalwatacciyar girarsa sama ya ce, "Gab nake da zama zautacce akanki, kullum ?ara sonki nake yi, kishinki ?aruwa yake a raina. Kullum sha'awarki ?ara yawa take yi min, bana taSa gajiya dake, bana tunanin akwai ranar da zan gaji da kasancewa da ke" ya ?arasa maganar yana zare hular kanta gashinta ya bayyana yana shafawa a hankali.

"Kina jin abinda nake ji a kan ki? Kina kishina? Kina jin sha'awata?."

Bata bashi amsa ba dan tambayar ?arshe ta bata kunya, sai dai ta yi murmushi bata ce komai ba. Ya ce, "ki yi magana, ina so na ji kin furta wani abun Jidda!" A hankali yake magana kamar mai raWa. Nayla ta ce, "duk abinda ka ke ji a kaina ina ji a kanka Rouhii!."
"Mai ?arya?." Sai ta yi dariya jin tambayar da ya yi mata kamar wani yaro ?arami, ya shagala da kallonta tana dariya. Ya yi murmushi ya ce, "uhum bani amsa."

"Ina ji mana Rouhi!."
"To meyasa baki taSa faWa min ba? Kuma meyasa bakya nuna min?."
"Ina nuna maka mana."
"Uhum uhum ni ban taSa gani ba sai yau, yau ne na tabbatar da ni Wan gata ne a gare ki, yau na tabbatar da kema kina jin son kasancewa tare dani, dah ni kaWai nake jin shau?inki ke bakya jin nawa."

Kunya yake bawa Nayla sosai jin irin kalaman da yake faWa shiyasa ta yi shiru ta kasa bashi amsa. Ta ya zata iya bayyana masa abinda take ji a kansa? Ita kunya take ji gwara dai ta yi shiru.

Jin ta yi shiru bata ce komai ba ya ce, "kina so na tabbatar?." Ta Waga masa gira alamun eh ya ce, "ki cigaba da kasancewa kamar yau, shigarki, khamshinki, jan ajin, shagwaSar da komai da ya faru yau. In ki ka yi haka zan tabbatar da kina ji dani Jidda!." Lumshe ido tayi ta buWe a hankali, dan ta fahimci yau Win ta gama ruWa shi shiyasa yake ta zuba kamar ?a?an bishiya. Ta Wan yi murmushi kaWan ta ce, "zan kasance fiye da haka a gare ka Rouhii! Zan kasance fiye da yadda ka ke so a duk lokacin da ka ke da bu?atar hakan."

Ajiyar zuciya yayi ya ja ta jikinsa ya ce, "thank you so much Jidda! Thank you for being so sweet to me, hankalina ya gushe, tunanina ya tsaya cak ta silar farin cikin da kika bani. I love you so much, my heart beats for you alone. I can't do anything without you my heart. I feel lost without you, You're my everything, not just my love!" Ya furta a kunneta cikin salo na Waukar hankali.

Da sauri ta Wago tana kallonsa ido cikin ido sai ya Waga mata gira ya ce, "na lura yaren nasara shine yake sakawa ki kalli idona, ta dole na fara koya tunda sai na faWawa matata take iya kallon idona." Bata Wauke ido daga kansa ba ta ce, "Allah ban yarda koya ka fara ba, daman can ka iya." Shima baby face ya mayar da fuskarsa kamar yadda take yi ya ce, "Yanzu dai turancin ki ka ji ba kalaman ba?" Ya faWa yana binta da mayen kallo. Nayla ta yi dariya ta ce, "duka na ji my Love." Rungume shi ta sake yi sai kiran sallah suka ji ana yi sannan suka saki juna.

Tare suka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login