Showing 168001 words to 171000 words out of 332344 words

Chapter 57 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14408

masa ta ce, "enter your pin." Kallon fuskarta ya yi kafin ya Wauke kai ya faWa mata pin Win ta shigar ya buWe, wara ido ganin balance Win kuWin account Win, ta kalle shi ta sake kallon balance Win tana mamakin wai ko bata gani daidai ba ne. Bata ce komai ba ya ce, "akwai account number Win Bashir a beneficiary ki duba, ki tura masa ki miliyan Waya." Abinda ya ce kenan ta yi abinda ya ce ta sake cewa, "pin Win." Ya sake faWa ta saka ta tura kuWin ta ajjiye wayar. Mamakin kuWin da ta gani take yi, nasa ne ko kuma ba nasa bane oho.

Shi bai ma kula da abinda take yi ba, lissafin adadin kayan da aka karSa yake yi kafin ya ja tsaki kaWan ya ajjiye ya kwantar da kansa a ?irjinta ya ce, "na gaji Jidda." Nayla ta ware yatsunta ta saka a gashin kansa tana shafawa a hankali ta ce, "Allah ya cigaba da taimaka maka." Da min ya amsa, ya kulle idanunsa bai ce komai ba yana kwance a ?irjinta yana sha?ar ?hamshin turarenta da ya zauna daram a fatarta.

Wayar ce ta yi ?ara, ta duba ganin mai aikin ta ce sai ta Wauka ta ce ta koma zata kira ta sannan kashe wayar. Ya kalle ta bayan ta kashe wayar ba tare da ya mi?e zaune ba ya ce, "waye yake biyan ta kuWin aikin?." Nayla ta ce, "Bani nake biyanta ba, kawai dai tana zuwa ne, kuma an ?ara mata kuWi a gidan Hajja."
"Ya kamata a fara biyanta" ya faWa yana sake mayar da kansa ?irjinta ya ri?e ta sosai.

"Ana bata daman ai, amma a gidan Hajja."
"Za a dinga biyanta a gidan mijinki, ki tambaya nawa ne kuWin sai a dinga bata."
"Amma...." Ya katse ta ya ce, "shii! Bana son musu, ki ce to kawai." Nayla ta ce, "to." Shiru ya yi bai sake cewa komai ba sai kuma ya buWe ido ya kalle ta, ya ri?o hannunta da ta Wora a kansa yana kallon zoben da ya saka mata a jiya yadda ya yi matu?ar kyau a hannunta.

Bai ce komai ba hannunta kawai yake kallo, ta kalli idanun shi ta Wora Waya hannun a goshinsa ta ce, "Baka ce min komai akan Narma ba." Kulle ido ya yi ya buWe cike da gajiya da zancen Narmar nan da take yi masa ya ce, "Na faWa miki zaki ji haushi."
"Ina so na ji."
"Kin tabbatar?." Ta Waga kai alamun eh. Ya bita da kallo ya ce,  in na fara ba a katse ni, kin yarda?. Ta sake Waga masa kai alamun eh.

? ??Ya Wan yi shiru na wani lokaci kana ya ce, "Bayan Didi a rayuwata babu wata mace da na taSa zama ni da ita sai Narma, duk da faWa mu ke yi bana Waukar shirme, ba mu taSa shiri da ita ba sai lokacin da aka ritsa ta aka ?wace mata waya har aka ji mata ciwo. Daga ranar sai ta canja har ta zo duba Didi da bata da lafiya, zuwa duba Didi da tayi ya saka na bata girma a idona, a duniya bani da kowa Didi. Kin san halina bani da saurin sabo da mutane kuma na tsani ba?o, tana ta so mu saba abin bai yu ba. Daga ?arshe kawai na ganta a gidan mu ta zo ta ce tana sona" ya faWa yana kallon idanunta kamar yadda take kallon nasa.

Nayla ta ce, "Sai kaima ka ce kana sonta?." Ya girgiza kai ya ce, "da farko na yi tunanin tana shirya wani abun ne a kaina shiyasa ta ce haka, amma daga baya na tabbatar da gaske take sai na rasa gane abinda nake ji a raina akanta. Tausayi take bani, sonta nake yi, kusancin da ta samu dani ne ya yi tasiri oho ban sani ba. Ni bana mu amala da maza balle mata, indai ba Didi ba babu macen da magana mai tsaho ta taSa haWani da ita balle kuma wani abun. Amma Narma ce mace ta farko a duniya da ta fara......" sai ya Wago ido ya kalle ta yaga ko ?ifta idonta bata yi a kan nasa, jira take ta ji me zai ce sai kawai.? Ya yi murmushi ya ja hancin ta bai ce komai ba.

Nayla cikin ?aguwa ta ce, "ina jinka, itace ta farko da ta fara meye?." Bai ce komai ba sai kallon ta da yake yi, har lokacin yana jikinta a kwance, ya Wan mayar da lips Winsa na ?asa ya tostsa kaWan ya kalle ta ya ce, "Ita macen da ta fara hugging Wina, haka ku ke cewa da turanci ko?." Nayla bata Wauke ido daga kallonsa ba saboda wani abu da ta ji mai zafin gaske ya daki zuciyarta, ta kasa koda ?ifta ido tana kallonsa kamar yadda yake karanto kishinsa a kwance a idanunta.

"Ina jinka" ta sake faWa ko motsa idonta bata yi. Ya ce, "Ta yi hakan ina tunanin sau biyu ne ko uku dai na manta, san......" katse shi ta yi ta ce, "har sau uku tana rungume ka kuma baka dakatar da ita ba?." Ya kalle ta ya ce, "ki jira na gama baki labarin mana."
"Ni bana so" ta faWa tana ?o?arin Waga kansa daga jikinta, ya sake ri?ota ya ce, "ai baki isa ba, na faWa miki daman haushi zaki ji kika ce kina so, sai ki bari na kai ?arshe."

Nayla ta haWe rai ta ce, "ni bana so, ban san me zan ji a gaba ba." Ya yi ?ar dariya ya ce, "ai kam zaki ji" ya Wan saka yatsan da ya sosa girarsa guda Waya ya ce, "tana da wata irin dabi'a ta shigar banza Jidda, Narma haka take shigarta ko yaushe a kuma ko ina. Itace mace ta farko a duniya da na taSa tsayawa na kalli halittarta, kuma a kan Narma na fara jin ina sha'awar mace Jidda!. Amma ba wani yanayi mai girma ba fa, sai yanzu na tabbatar da abinda naji a kanta bai wuce cikin cokali ba. Wani irin dogon tsaki Nayla ta yi, ta yun?ura zata mi?e ya zaunar da ita ya mi?e zaune ya ce, "ba ki isa ba wallahi, ai tunda na fara sai na gama. Baki san ba a katse min magana ba?.

Nayla ido ya ciko da hawaye ta ce, "bana son ji, ni ka ?yale ni bana son jin labarin na ka" kawai sai ta fashe da kuka mai sauti tana rufe fuskarta da hannayenta. Omar ya yi murmushi ya ce, "tun farko na faWa miki ki ka ?i ji, dan haka sai na gama baki labari babu inda zaki je."
"Ni bana so! Bana son labarin. Ni na ce ka bani labarin ko? To yanzu bana so!" Ta faWa cikin kuka sosai.

Ri?ota jikinsa ya yi ta ?wace ta ce, "ni ka daina taSa ni." Kallon ta yake yi ganin yadda take kuka bil ha??i kamar wacce yacewa wani abun ya shiga tsakaninsa da Narma. Ya Wan taSe baki yana dariya ya ce, "Haba Ashiq, kin san bana son kukan nan ko?."? Nayla cikin kuka da shagwaSa ta ce, "to ba kai ka saka ni kukan ba? Na ce bana son labarin ka ?i ka daina. FaWa min ka ke yi fa wata ta taSa hugging Winka har sau uku, kana ce min akanta ka fara sha'awar mace, ni ka ?yale ni kawai" ta faWa tana kuka har lokacin.

Ajiyar zuciya ya yi ya ce, "Ba ?arya na yi miki ba gaskiya na faWa miki. Wannan tausayin nata da nake ji saboda son da take yi min, da wannan kusancin da muka samu, da wannan sha'awar da na faWa miki shine ya saka nake ji a raina ina sonta ne. Ban taSa ala?antuwa da mace ba sai ita, ban taSa son mace ba shiyasa nake ji a zuciyata sonta nake yi amma ba wai ina sonta Win ba ne. Kai tsaye in aka ce a wanne matsayina ajjiyeta zan ce kawai tana burge ni ne a lokacin, kuma yanayin shigarta ya saka ina jin wani abu a jikina, yana sakawa na ji nima namiji ne, kuma ina da lafiya....amma fa a dah ban da yanzu. Shiyasa na kasa gane me nake ji a kanki, indai har ita sonta nayi ke me nake miki?. Ita a gangar jikina kaWai ta taSa yin tasiri, ke kuma kin tattara komai kin shiga ciki, zuciyata, jikina, jinina, raina, da komai ina jinki a cikinsa. Shiyasa nake gab da zarewa a kan ?aunar, wallahi Jidda soyayyarki ta ?iris take jira ta haukata ni.

Kuka take yi sosai, ya matse ta a jikinsa, duk da kukan da take yi sai da ya kai ?arshen labarin hankalinsa ya kwanta, ita kuwa haushi ya cika mata zuciya, tayi dana sanin tambayarsa da ta yi.

A tausashe ya ce, "na fara sonki a lokacin da ban taSa ganin ko wacce halitta ta jikinki ba, na fara sonki a cikin hijjab da nake ganinki kullum kuma jikinki a rufe. Kishinki nake ji koda da hijjab Win ki ka fita haushi nake ji a zuciyata. Ita kuwa ban taSa jin kishinta ba, ban taSa jin ina jin haushin shigarta ba, ban taSa jin haushi in naga surar jikin ta bayyane ba, ban taSa jin haushi in ta ri?e wani namiji ko in tana magana dashi ba. Da ace naso Narma duk abinda zai faru wallahi bazan rabu da ita ba, inda ace sonta nayi a wancan lokacin duk abinda mahaifinta zai yi sai dai yayi amma bazan taSa rabuwa da ita ba. Da yake ba sonta nake ba cikin lokaci kaWan na manta da ita da rayuwarta. Jidda ke nake yiwa asalin so, inda ace kece a matsayinta abinda ya faru a gidansu ya faru a gidan ku& .hmm! Sai dai a kashe ni a yarda gawata, dan wallahil azim bazan rabu dake ba. Ki yarda dani, ban taSa son Narma ba, kuma bazan so ta ba har abada!.

Duk da ya faWi kalamansa dan ta ji daWi ne amma sai ta ji haushi ya mamaye mata zuciya. Ta Wauke kai tana harare-harare. Ya Wan murmusa kaWan ta ji ya ce, "Kin ji matsayinta a wajena wanda ya riga da ya wuce, ni ko kamanninta ma ni manta, amma itace silar canjawar Omar. Ba dan na je gidansu an faWa min maganar da aka faWa min ba da yanzu ina nan bana sana'ar komai, wata?ila da aurenki ma ba a bani shi ba. Rabona ne yazo ta silarta, kuma kin san baka tsallake ?addararka, sannan baka tsallake raboka, duk inda yake sai ya same ka koda a cikin mahaifiyarka ka ke. Wannan shine silar haWuwata da ita, Allah ya yi nufin canja min rayuwa ta silarta shiyasa hakan ya faru. Wannan shine amfaninta kawai a gare ni!."

Tana ?irjinsa tana share hawaye, kishinsa take ji a zuciyarta kamar ta kurma ihu, sai kallon ?irjin nasa take yi tana tuna yanzu Narma ta kwanta a abinda yake mallakinta, sai ta ji Sacin rai ya sake mamayeta ta kawar da idanu daga kai tana kuka.? Cikin sigar rarrashi ya ce, "to meye na kukan uhummm? Ke ki ka ce na faWa miki, dan na faWa miki ki ke jin haushi?."

"FaWa min ka ke yi tana burge ka, wata mace ce take burge ka fa, in ban yi kuka ba me zan yi?" Ta faWa murya ta a rarrabe. Shafa kanta yake yi a hankali ya ce, "ai na faWa miki a dah kenan, amma ban da yanzu."

"A da Win ai, a dah Win itace ta farko kafin ni."
"Keda na yi kishin ki shekara goma baya ta ya zata zama ta farko? Kawai rigima ki ke ji da ita. Kafin na santa ai ke na sani ko?." Ta kalli idanunsa tana turo baki gaba ta ce, "amma a kanta fara jin abinda ka faWa min kafin ni." Ya ri?e fuska ta da suka hannayensa guda biyun ya ce, "kin cika rigima kawai, amma wannan ai ya wuce bai kamata ya dame ki ba. Bana son kukan nan Jidda, bana so, ki daina."

Ta share hawayen tana kallon ?asa bata ce komai ba, ya Wan yi murmushi kaWan ya ce, "to ki yi dariya mana, duk da in kina fushi ma kyau ki ke yi, amma dariya ta fi yi miki kyau." Ta kawar da kai ba tare da ta yi dariyar ba ta ce, "ni kaya zan je na saka."

"A haka nake so yau ki zauna, bana so ki saka komai a jikinki."? Ta langwaSar da kai cikin shagwaSa ta ce, "Allah ni duk na takura."
Juya idanunsa ya yi ya ce, "Haka mijinki yake so" ya faWa yana kwantar da kansa cinyarta wacce take ta Waukar ido. Shiru tayi bata ce komai ba tana tuna surar Narma tana jin kishi kamar ana chaka mata wu?a a zuciya. Murmushi ya ke yi bai ce komai ba dan itace ta saka shi, da bata ce ba da bai bata labarin ba. Ya sake kallon ta ya Wauke kai yana taSe baki, inda ta san ?an?antar yanayin da yaji a akan Narma da bata Sata lokacinta tana kuka, sai a yanzu ya tabbatar da sha awar da yaji a kan Narman ba komai bace akan wacce yake ji akan Nayla.
KRB3P061
Nanahaleema
? ? ? ? ??
Har cikin Wakin Mama Abiy ya shiga fuskarsa a Waure sosai, ya kalle ta daga tsaye ya ce, "Me ya kai ki gidan Nayla? Ina ki ka ce min zaki je a Kano?." Mama ta kalle shi da mamaki ta ce, "dan na shiga Kano bazan je gidan ?ata ba? Akwai laifi dan na je gidan Nayla?."

Abiy ya ce, "inda ace da zuciya Waya ki ka je da bazan yi miki magana ba, amma duk abinda ki ka aikata ya dawo kunena. Meyasa ki ke son kashe auren Nayla bayan a lokacin baya ke kika bata goyan bayan aurensa?." Mama ta ce, "kamar ya ba da zuciya Waya na je ba Abiy? To da zuciya nawa na je in ba da zuciya Waya ba?."

Abiy ya ce, "duk abinda ki ka aikata a gidan ya dawo kunnena Zeenatu, kin je kin faWi magana mara daWi a gaban mijinta, kina cewa indai kina da rai sai kin raba aurensu, ba haka aka yi ba?." Mama bata musa ba ta ce, "Saboda bai dace da ita ba, ita ba kalar aurensa ba ce. Duk wani farin cikin gidan miji ita take siyawa kanta, aikin da take yi da shagonsu tana yi ne saboda taimakon kanta. Me yake dashi da zai iya ri?eta?."

Abiy ya bita da kallon mamaki ya ce, "kin san da hakan meyasa da ki ka bata goyan baya?." Mama ta kalle shi da mamakin abinda yace, ya Waga mata kai ya ce, "na san ke kika zuga Nayla, ke kika faWa mata auren ta dashi abu ne mai yuwa tunda tana so, ki ka sake Worata akan turbar zaki saka na amince ya aureta. Ki ka sakata ta amsa min tana sonsa, sannan da ki ka ga na yi fushi da amsarta sai kika saka ta tafi Kano, ni kuma ki ka ce min baki san ta tafi ba guduwa ta yi. Ki ka saka aka yi hacking WhatsApp account Winta aka turo min messages Win da take bayyana min in ban aura mata Omar ba zata shiga duniya. Ki ka dinga faWar kalaman da zasu zuga ni na sake jin bana son auren kuma na yi fushi da ita, Ba a yi haka ba Zeenatu?."

Jikin Mama ya yi sanyi matu?a, ta kalle shi zata yi magana ya katse ta ya ce, "Kin fi kowa murna a lokacin auren, Nayla tana kwance bata da lafiya amma ke murna ki ke kina siyan kayan aurenta, kece kan gaba a kaita gidanta. Baki taSa faWa min alkhairi akan auren nan ba, kullum cikin kushewa ki ke. A bayan idanuna kuma kin fi kowa son aurenta dashi. Me ya saka ki ka canja yanzu kina ganin bai dace da ita ba?." Mama ta dake kamar ba ita ba ta ce, "ni fa ban gane akan wa ka ke magana ba, ni gabaWaya ban fahimta ba."

Abiy ya yi murmushin takaici ya ce, "meyasa ki ke son Nayla ta sha wahala a gidan aurenta? Dan kin ga yanzu tana cikin farin ciki ko? Kina ganin wanda ki ka raina kika tsaya kai da fata aka yi auren ya baki mamaki shiyasa ki ke so a raba auren?. Kin ga yanzu keda da Nayla ba ku da banbanci, kina cikin farin ciki, tana cikin farin ciki, babu abinda ya gagareki, babu abinda ya gagareta, ganin hakan shine ya jawo bakya jin daWi a zuciyarki. Ba haka ki ke so ki gani ba, so ki ke Nayla ta wahala kullum ki kasnace mai taimaka mata. Haka ne ko Zeenatu?."

Mama ta kalli Abiy cikin son Soye yanayinta ta ce, "ni ka ke faWawa wannan maganar akan Nayla? Ni ce mai yiwa Nayla ba?in ciki saboda kar ta samu jin daWin gidan aure?."

"Ke Win fa Zeenatu!. Kin raini Nayla tamkar ?ar da kika haifa, kin bata tarbiyya daidai da ta Jidda, kin so ta, kin nuna mata ?auna, baki taSa barinta ta yi kukan rashin uwa ba. Amma daga ?arshe kin zobe ladanki, kin gaza ?arasa amanar da aka bar miki, kin gaza ri?e amanar marainiya da Allah ya dam?ata a hannunki, kin gaza cigaba da kula da amanar da mahaifiyarta ta bar miki. Mahaifiyarta ta amince dake ta bar miki ?arta guda Waya da ta haifa a duniya, mahaifiyar Bilkisu tana da rai a duniya har yanzu, amma ta ce ita ke take so a barwa Nayla ki raine ta saboda ta yarda dake. Tana da ?an uwa maza da mata a duniya, amma ta ce ita da Zeenatu ta amince, a hannunki take so Nayla ta tashi. Anya baki ci amanar wacce ta amince miki ba?."

Mama ta fara kukan borin kunya ta ce, "'ni ka ke faWawa bana so Nayla ta yi farin ciki? Ni na raini Nayla fa, na bata tarbiyya mai kyau, ni ka ke kallo ka ke cewa bana son ta yi farin ciki na fi so ta sha


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login