Showing 174001 words to 177000 words out of 332344 words

Chapter 59 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14391

yana da hira sosai, in yana hira sai kin kalle shi kin ce daman wai yana magana." Salma ta buWe ido tana ri?e baki tana dariya ta ce, "inyee ka ga masu miji."

Nayla ta yi murmushi Salma ta ce, "na ji daWin ganin ki a cikin farin ciki Nayla, ko baki faWa ba ana kallon ki a san kina jin daWin zaman gidan nan. Ashe Omar a ?addarar ki yake shiyasa Allah ya Wora miki ?aunarsa."

Nayla ta ce, "Hmmm bari kawai, in baka yarda da ikon Allah ba ka shiga uku. Salma duk yadda zan faWa miki yadda yake ?aunata baza ki gane ba, duk yadda zan sanar dake yadda yake nuna min wallahi baza ki fahimta ba. Abu Waya na san na yarda dashi, addu'ar da nake kwana ina yi bata faWa a ?asa ba, Allah ya amsa ya kuma share min hawaye, ya tabbatar min da Omar Win ne alkhairi a gare ni." Salma ta ce, "Gaskiya ne, Allah ya tabbatar da zaman lafiya a rayuwar ku."
"Amin sis" ta faWa tana nuna mata zoben hannunta.

Salma ta kalli zoben ta ce, "siya ki ka yi?."
"Ya siya min dai."
Da mamaki Salma ta ce,"Don girman Allah? Ke wai daman shima duk ya iya irin wannan abubuwan ko ke ki ke koya masa?."
"Ban sani ba" Nayla ta faWa tana harararta. Dariya Salma tayi sosai ta ce, "dallah can, daga tambaya sai ba?ar magana? Abin ne da Waure kai wallahi, a haka simi simi dashi, yana zarewa mutane ido yana harara da tsaki, kullum fuska a Waure kamar mai fuskar shanu, ashe shima Wan air ne. To shi wannan zoben kyautar first night Win ce?" Ta faWa tana Waga mata gira.

Nayla ta yi dariya ta ce, "ina ruwanki?."
"Babu ruwana, tunda mun gama taya ki kuka ai amfanin mu ya ?are." Dariya suka yi a tare suka cigaba da hira. Bata jima sosai ba ta tafi ta bar Nayla a zaune a falo tana jiran shigowarsa.

Sai yamma sosai ya shigo da sallama a ciki, ta amsa tana fitowa babban falon waya a ma?ale a kunnenta tana magana. Cak ya tsaya yana kallon ta tun daga sama har ?asa yake ?are mata kallo, numfashinsa ya kusa barin gangar jikinsa, da?yar ya yi ta maza ya kamo numfashin ya tsaya a ?irjinsa yana sauka zuwa ciki a hankali. Ya tafi da idanunsa kamar zai rufe sai ya buWe su a kanta yana cigaba da ?are mata kallo, musamman shape Win rigar yadda ya fita komai ya bayyana ?arara. Wani irin kyau ya ga ta yi masa, kyaun ya wuce tunaninsa ya kuma zarce nazarin ?wa?walwarsa, hakan ya saka kyaun ya gigita shi har tunaninsa ya je hutun rabin lokacin kafin ya dawo daidai.

Murmushin da ta yi masa ya sake kashe masa jiki, bai san ya ri?o hannunta ba yana cigaba da kallon fuskarta ita kuma ta Wauke ido daga kansa. Hannunta ya ri?e sosai ya jawo ta kusa dashi ya rungumeta a hankali.

Shiru ne ya biyo baya tana kwance a jikinsa idanunta a lumshe ta ji ya ce, "kina so ki zauta ni ko?." Bata ce komai ba tana jikinsa a kwance, ya Wagota a hankali ya kalli fuskar ta musamman lips Winta da ya sha jan janbaki, kasa jurewa ya yi ya kai bakinsa a hankali ya shanye janbakin tass kafin ya Wagota ya haWe goshin su waje Waya idonsa rufe.

"Kin yi kyau, kin yi kyau. Kin fi kyau yin kyau!" Ya furta a hankali ba tare da ya raba fuskarsu ba kuma bai buWe idanunsa ba. Murmushi ta yi murya can ?asa ta ce, "na gode." Yadda ta yi magana ya saka shi sake mayar da ita jikinsa ya lumshe ido yana motsata a jikinsa a hankali.

Sun jima a haka kafin ya raba jikinsa da nata, ya kalli fuskar ta ya saka yatsu biyu ya Wago da fuskarta, ta kalle shi sai ta sauke ?wayar idonta ?asa. Murmushi ya yi mai sauti ya yiwa idanun nata kiss ya sake yi mata a kumatun ta ya ri?e fuskarta kawai yana kallo. Nayla cikin shagwaSar da take sake narkar dashi da kashe masa jiki ta ce, "ina ka je? Ina ta jiran ka tun Wazu har yamma ta yi."

Lumshe ido ya yi ya buWe a hankali ya ce, "an kusa sallar magrib fa, don Allah ki bari nayi sallah cikin nutsuwa, kina so na zauce ne?." Nayla ta fara bubbuga ?afa kamar yarinya ?arama ta ce, "Allah ni ka faWa min inda ka je, tun bayan sallar azhar ka fita baka dawo ba sai yanzu. Kuma ko waya baka yi min ba, ina zaune ni kaWai. Gaskiya ka faWa min inda kaje" ta faWa cikin sabon salo tana kallonsa.

"Y salam! Ya salam!!" Ya furta a hankali jin tsayuwar na neman gagararsa, salon nata yana neman haukata shi lokaci Waya. Bai san ya jawo ta da ?arfi ya shiga kissing dinta romantically ba. Tsayuwar gagararsa tayi, ya zame ta a hankali ya zauna a kan kujera ya dafe kai da hannayensa jin ana kiran sallar magrib.

Ajiyar zuciya yake yi a hankali idanunsa a rufe, ?o?arin dawowa nutsuwarsa yake yi amma nutsuwar tana neman gagararsa. Da?yar ya samu ya kamo ta duk da tana kubcewa ya sauke ajiyar zuciya mai nauyin gaske ya buWe idanunsa da suka fara canja launi.

Nayla na zaune a gefensa kamar munafuka ta wani nutsu kanta yana ?asa kamar ba ita ba. Hannunta ya ri?e a hankali ya furta, "Kin ga ana kiran sallah, na faWa miki ki bar ni nayi sallah a nutse amma ki ka ?i ko?." Nayla ta kalle shi ta ce, "ni babu ruwana" ta faWa tana kifta idanu. Hakan da tayi ya saka shi sake jin sabon abu ya soke shi a zuciyarsa, sai ya mi?e da sauri ya bar wajan dan in ya cigaba da zama tabbas akwai matsala.
KRB3P63.
Nanahaleema.

Tunda ya fita sallar magrib bai dawo ba sai bayan i'sha, dan baya so ya dawo ta sake tayar masa da hankali gwara in ya shiga ya shiga kenan. Kamar yadda ya sangartata da siyan abinci da takeaway ya shiga gidan, ya same ta a zaune a falo amma ta canja shiga zuwa riga da wando na Pakistan ta saki gashinta ta saka ?aramin Wankwali ta zagaye goshin ta dashi.

Bai kalle ta ba ya ajjiye abincin ya ce, "ki zo ki ci abinci." Da to ta amsa ta tashi ta kawo plate ta ajiiye ta koma ta kawo ruwa duk yana kallon ta amma baya so su haWa ido dan zata iya haukata shi. Haka ta zuba abincin a plate Waya kamar yadda ya saba mata da ci shida ita a waje Waya, ya Webo yana bata tana ci amma ya?i bari ya kalli idonta. Bata ci da yawa ba ta ce ya ishe ta, bai ce ta bashi ba ya ci da kansa, bayan ya gama ya tashi ya zubar da disposable packs Win ita kuma ta Wauki plate Win ta shiga ciki.

Bata dawo falon ba Waki ta wuce, ta yi brush ta canja kaya zuwa riga da wando na bacci. Wandon iyakacinsa guiwa, rigar kuma bata da tsaho
mai siririn hannu, sannan bayan rigar gabaWaya a buWe ya ke, sai wata rigar ta sama mai maWauri a gaba. Ta saka hula ta fito falon dan tana son sanar dashi gobe zata fita& &

Bata same shi a falo ba kai tsaye Wakin ta shiga da sallama, ta same shi a tsaye babu riga a jikinsa yana tsaye a gaban kayansa yana duba riga. Ita kam burge ta yake yi, kamar ba namiji ba hatta kayansa a shirye suke babu cakuWewa yadda maza suka saba. Babu rataye-ratayen kaya a ko ina a Waki, komai neat kamar mace mai tsafta dan yafi mata da yawa tsafta. Amsa sallamar ya yi ya juyo yana kallonta ta yi saurin Wauke kai, har yanzu bata saba da ganinsa babu ko da riga ba, nauyin hakan take ji kuma kwarjini yake yi mata sosai.

Ganin ta tsaya bata ?araso ba sai ya kalle ta ta shigo ciki a hankali ta tura ?ofar ta rufe amma ta kasa magana. Bai saka rigar ba ya rufe ?ofar wardrobe Win yana kallon ta. Jingina ya yi yi da wardrobe Win ya harWe hannu a ?irji yana kallon ta. Nayla jin shiru bai yi magana ba kuma bata ji motsinsa ba sai ta Wago ta kalli inda yake, suna haWa ido ya Waga mata gira yana Wan murmushi tare da taSe baki a lokaci guda. ?auke kai ta yi daga kallon sa tana murmushi kaWan. A hankali ya tako inda take, babu zato ta ji ya ja igiyar gaban rigar ta warware ya saSule ta faWi a ?asa. Kunya ta lulluSeta, ta rasa ya zata yi saboda kunya, ga hasken Wakin a kunne ga jikinta da yake waje yake musamman daga samanta.

Kallon ta yake yi amma bai ce komai ba ya dai zuba mata ido yana yawo dashi duk inda yake so a jikinta. Yadda labulen Wakin yake Wagawa ya saka shi ta kalli wajan ya ga hadari ne ya haWo sosai garin ya yi duhu alamun ana gab da yin ruwa.

?auke kai ya yi daga kallon wajan ya dawo da kallonsa gare ta, a hankali ta kalle shi suka haWa ido ta sake saurin Wauke kai ta motsa kaWan hakan ya bawa jikinta daman motsawa ta ce, "YaMar....!" Ai kamar jira yake ta buWe bakin ta ya tako inda da hanzari ya ja hannunta zuwa jikinsa ya ?an?ame ta yana yawo da hannunsa a bayan ta cikin salo na soyayyar da yake ciki.

Nayla gabanta faWuwa yake yi dan har yanzu ta kasa sabawa dashi, har gobe wahala yake bata, a gajiye take kasancewa a yayin da komai ya faru, ta kasa sakin jiki tana daurewa ne kawai saboda shi. Jin yana ?o?arin zare mata rigar ya sa ta mi?a hannu da sauri ta kashe hasken Wakin, dan ita kunya take ji, gwara dai babu hasken bata ganinsa sosai shima baya ganin ta akan ace da haske.

Iska mai sanyi ce take shigowa ta window Wakin a lokacin aka fara ruwa mai ?arfin gaske. Sauka yake yi da ?arfi har feshinsa yana shigowa Wakin saboda yadda ya taho gabaWaya. Wannan ruwa da wannan iska ta sake jefa Omar a sabon shau?i, ya shiga yiwa Nayla filla-filla yana ba je mata ?aunar da bai taSa nuna mata irin ta ba. Nayla tayi abinda bata taSa yi ba a lokacin, ta saki jikinta sosai, yanayin da suke ciki yana sake tsuma ta, zuciyarta na sake shiga kogon soyayyar masoyinta.

? ? ? ?? Tabbas sun raya wanann dare cikin ?auna da nuna tsantsar soyayyar da suke yiwa junansu, kowa ya saka Wan uwansa farin ciki tare da jefa su a duniyar ?aunar junansu. Haka suka kwana cikin farin ciki suka tashi dashi. Nayla ta kasa haWa ido dashi sai sunkuyar da kai take yi, ya kula ya kuma san abinda take jin kunyar amma bai nuna mata ya fahimta ba, rarrashi da soyayya kawai yake nuna mata ita sake narkewa a jikinsa.

Da safe kamar kullum shine ya haWa mata breakfast, ya shiga Wakin ya same ta a tsaye ta gama shiryawa kamar yadda ta saba yin kwalliyar a ko wacce safiya. "Ina kwana Ashiq!" Ya faWa yana matsowa inda take yana kallon ta ta cikin madubin Wakin. Kanta ta sunkuyar ta rufe idonta da hannunta ta ce, "Ina kwana YaMar." Murmushi ya yi mai sauti ya zagaya da hannunsa ya ri?e ?ugunta yana shafa cikin ta a hankali yana bin wuyan ta da soft kisses bai ce komai ba.

Nayla bata buWe ido ba tana jin abinda yake mata, jin yana ?o?arin kashe mata jiki sai ta Wan motsa kaWan wai ko zai bari amma bai bari ba. Rigar jikinta ya Waga ya sanya hannu a fatar cikin ta yana cigaba da shafawa a hankali har lokacin bai ce mata komai ba kuma bai daina ba. Nayla ta yi ?aramar ajiyar zuciya ta ce, "YaMar...!" Sai kuma ta yi shiru bata ce komai ba.

Ta mirror ya kalle ta ya ga ta sauke hannun daga fuskarta sai idonta da yake a lumshe. Ya kai bakinsa daidai kunnenta ya ce, "Uhum Jidda! Ya aka yi?." Bai bar shafa cikin ta sai ma matsawa da hannunsa da yake yi zuwa sama. Ta yi saurin ri?e hannunsa ya?tsaya amma bai cire hannun ba. Nayla ta ce, "YaMar ka bari." Ya kwantar da kansa a kafaWarta ya ce, "me zan bari?."
"Abinda ka ka yi."
"Bashi da suna...?" Ya faWa a kunnenta hakan ya saka ta sake rufe ido ta buWe a hankali.

Nayla bata iya bashi amsa ba ta yi shiru tana ri?e da hannunsa dan har lokacin bai cire ba. A hankali ya zare hannunsa ya ce, "Kin tashi lafiya Ashiq?." Dariya tayi jin sai yanzu zai tambaya ta ce, "lafiya lau" ta faWa a hankali tana kallon ?asa. Kunnenta ya yiwa kiss a a nutse ya raWa mata, "Kina jin yunwa?." Nayla ta shagwaSe fuska ta ce, "YaMar ni ka bari bana so." Kallon ta yake yi ganin yadda ta mayar da fuskar ta kamar ta yara ya ce, "'me zan bari? Tambayarki kawai na yi kina jin yunwa?"

Zare jikinta tayi daga nasa ta ce, "Zan ci abincin." Murmushi ya yi ya mi?a mata hannu ta saka hannun nata a cikin nasa suka fito falon. Shi da kansa ya bata tana ci yana binta da kallo duk sai ta kasa sakewa tana ganin kamar abinda ya faru jiya yake tunawa ita kuma bata so. Bayan sun gama ci ta ce, "YaMar kana sangarta ni fa, rabon da nayi girki har na manta."

"girmanki ne" ya furta yana sakkowa ?asa kusa da ?afarta. Siririn anklet ya Wauko a aljihunsa ya ri?e ?afarta ta dama ya Waura mata shi a ?afa ya tsaya yana kallon ?afar. Kiss ya yiwa ?afar ganin yadda abin ya yi mata kyau kamar daman dan shi aka yi wajan. Kallon ta ya yi ya ga itama ?afar take kallo da murmushi ta ce, "Rouhii amma ya yi min kyau sosai." Bai dawo kan kujera ba, yana ri?e da ?afarta yana wasa da yatsun ?afar tare shafa tafin ?afarta da yake da laushi sosai ya ce,

"Na ganshi a wani shago ne na siyo miki, tun daren jiya naso na baki sai kika gigita ni. Allah ya sa ya yi miki kyau.
"Yayi sosai ma, ya yi kyau sosai Rouhii, na gode." Murmushi ya yi ya sake yiwa ?afarta kiss ya kalle ta ya ce, "na hana ki cewa kin gode Win nan bakya ji." Murmushi ta yi ta ce, "dole na ce na gode ai."

Murmushi ya yi yana cigaba da wasa da ?afarta bai ce komai ba sai daga baya ya ce, "Jiya na je duba jikin Marmerh, Didi ta ce na gaishe ki."
"Amma shine ba mu je tare ba?."
"Na damu da ita ne, ina so na san ko ta warke daga mura shine kawai na je."
"Ta ji sau?i?."
"Uhum" ya furta a hankali ba tare da ya yi magana ba.

Nayla ta bishi da kalli tana kallon eyelashes Winsa da suke a kwance a kan fuskarsa. Mamaki yake bata ko yaushe canja mata yake yi, yi mata abubuwan da bata yi tunanin zai yi ba yake yi a ko yaushe, ?auna da soyayyar da bata taSa zaton zata samu daga gare shi ba yana nuna mata a ko wanne Wa?i?a. Ko yaushe cikin godewa Allah take, ya kaita matakin da bata yi tunanin zuwa ba, ya kawo mata canji fiye da wanda ta nema.

Ta Wora hannunta a gashin kansa ta ce, "YaMar gobe ina so zan je wajan aiki, da yau zan je to ka ga yau ta wuce." Ya Wago ya kalle ta ya ce, "Har monday Win ta yi kenan?." Nayla ta ce, "A'a, akwai abinda zan kai." Ya Wan yi shiru baice komai ba kafin yayi ajiyar zuciya ya kalle ta ya ce, "Don Allah ki saka wannan abin da yake rufe fuskar mata, wani ba?i dai ban san sunan shi ba. Kuma ki saka hijjab har ?asa, ban amince ki yiwa kowa magana ba. In dama ko idanunki kar wani ya gani, in zai yu a ware miki wajan aikin naki ke kaWai."

Nayla jin ya ruWe?yana ta magana cikin kishi sai ta katse shi ta ce, "Resignation Letter zan kai Rouhi, zan ajjiye aikin ne ma!." Da sauri ya kalle ta ido cikin ido ya ce, "Zaki ajjiye aiki kuma? Akan me?." Nayla ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Ina so na samu lokacin kula da mijina, in fita tun seven bazan dawo ba sai five, kuma na dawo a gajiye, da na huta burina na yi bacci da wuri saboda na tashi da wuri. Bani da enough time Win da zan kula da kai Rouhi, shiyasa zan ajjiye, daman kuma baka so."

Ya tashi tsaye ya dawo kusa da ita ya zauna ya ce, "kin ji na ce miki ki ajjiye aikinki ne? Dan kawai bana so sai ki ajjiye? Kar mu yi haka dake, ni ban ce ki ajjiye aiki ba kar ki saka a fara zargin ni na hana ki." Nayla ta ce, "Babu wanda zai yi zargi, har Abiy na faWawa na ajjiye aikin ya kuma bani support akan hakan. Daman fa ni ce mai ra'ayin aikin shiyasa Abiy ya bar ni, amma Twiny bata yi saboda bata da ra'ayi."

Ya bita da kallo ya ce, "Saboda nace bana so kuma sai ki canja ra'ayinki Jidda?."
"Eh mana. Kuma nima na gaji da zuwa aikin wallahi, gwara na ajjiye kawai zan fi samun nutsuwa na baka kulawa wacce na tanadar maka. Burina ne na yi aiki kuma na yi, ka ga ai shikenan ko?."

Ido ya zuba mata yana kallon ta cikin tunani, tabbas zai fi kowa farin ciki in ta ajjiye aikin nan dan baya ?aunarsa ko kaWan, babban tashin hankalinsa ranar da zata ce masa zata tafi aiki, gani yake in ta tafi bazai iya samun nutsuwa ba saboda kishi. Amma in ya bari ta ajjiye danginta zasu zarge shi, zasu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login