Showing 33001 words to 36000 words out of 332344 words

Chapter 12 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14443

saka soyayyarki a zuciyar Omar."

Nayla tayi murmushi ta ce, "Amin Didi, Don Allah kar ki faWa masa." Didi ta ce, "ya kamata ace ya sani, ai abin arzu?i ne ai."
"A'a don Allah, na faWa miki ne ma saboda kar ki sake yi masa zancen bana so ya fahimci ma ana yi tunda ba kallon tv yake yi ba." Didi ta ce, "Shikenan Nayla bazan faWa masa ba, Allah ya biya ki ya baku zaman lafiya na har anda."
"Amin Didi. Yaushe zaki zo?."
"Ai sai cikin sallah in sha Allah."
"Ina so nazo kafin azumin nan ya fita."
"Allah ya kawo ki."

Nayla ta ce, "Amin ya rabbi." Didi ta ce, "ki fa isar da sa?ona, ki ce na ce ina godiya sosai." Tayi ?ar dariya ta ce, "a'a Didi ba da ni ba." Didi ta ce, "kina bada mata Nayla, Allah rashin sakewa nan da baya yi da laifin ki. Amma bara ayi sallah zan zo mu tattauna."

Nayla ta ce, "Didi ai marmari daga nesa ne." Suka yi dariya a tare kafin Didi ta kashe wayar Nayla ta cigaba da kallon kayan. Sai a lokacin taga kuWi a cikin kaya har dubu hamsin. Nayla ta wara ido tana irga kuWin ta ce, "Lallai su Damisa manya, an san a bada kayan sallah da kuWin Winki."

Salma ta kira a waya aka yi sa'a suna tare da Twiny hira ta bar?e a tsakaninsu tana basu labari da nishaWi su kuma suna ta tsokanarta.

Dawowarsa da taji ya saka ta kashe wayar ta tashi ta saka hijjabi ta fita da niyar yi masa godiya. A zaune ta same shi yana cin Apple da take hannunsa. Zama tayi a Wan Warare ta ce, "Na ga sa?o na gode Allah ya saka da alkhairi." Bata ji ya amsa ba daman ta san baza ta ji ba ta mi?e tsaye a lokacin Bashir ya shigo da kaya masu yawa.

Ajjiye kayan ya yi ya kalli Nayla ya ce, "Antyn mu an sha ruwa lafiya." Tayi murmushi ta ce, "Lafiya lau, ya ka ke?."
"Lafiya lau." Daga haka bata sake cewa komai ba ta wuce zuwa kitchen. Bash ya kalli Boss Win nasa sai ya ga kamar harararsa yake yi ya Wauke kai ya ce, "Tiger an kai kayan Abuja." Omar ya ce, "ya sanar da ni."

Bash ya ce, "Damisa muna ta samun alkhairi cikin kwanakin nan sosai, wani abokina ya ce ya kamata mu yiwa companyn register saboda ba a san inda zai je gaba ba." Omar ya kalle shi ya ce, "nayi wannan tunanin nima, amma ban san ya abin yake ba."
"Nima ban san a ina ake yi ba, amma in na tambaye shi zan sanar da kai, tunda har an fara karSar kaya ana sakawa a store gwara mu dinga yiwa takalman kwali da Rc number da komai."

Omar ya girgiza kai cikin gamsuwa ya ce, "in ka s??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????amu ka sanar da ni." Nayla da take tsaye ta fito daga kitchen ta ji abinda aka ce ta ?araso ta ce, "Zan iya magana?." Kallon ta ya yi kafin ya ce wani abu ta ce, "Rc number a nasan wani ma'aikatan da suke aiki a ?ar?ashin CAC inda ake yin number kenan, zan iya sakawa ayi number ba sai an nemi wani ba."

Bash ya ce, "shikenan faWuwa tazo daidai da zama Antyn mu, abu ya zo har gida." Kallon da Omar ya yi masa ne ya saka shi ya mi?e ya ce, "Damisa na koma company, sai ka shigo. Antyn mu sai da safe." Bai jira ta amsa ba ya fita saboda kallon da yake yi masa ya san ba kyau.

Bai motsa ba kamar bai ji ma abinda ta ce ba, ganin haka sai ta koma tana mamakin hali na wannan bawan Allah. Shi kuwa Omar gabaWaya haushi ta bashi, meye dalilin ta na zuwa yana tare da wani tana magana?, Ya saka ta ne ko kuma dole sai tayi magana Bashir yana wajan?. Tsaki ya yi yana nan zaune har goma na dare sannan ya mi?e ya shiga Waki. Kaya ya canja sannan ya sake fitowa ya same ta a tsaye tana Waukar ruwa a fridge har lokacin hijjabin yana jikinta.

Kamar zai yi magana sai ya fasa kawai ya fita dan ba a gidan zai kwana ba zai je ya saka su a gaba dole ayi aikin ko ba so. Har zai fita kuma sai ya da fasa ya dawo ya kalle ga ya ce, "ki rufe ?ofa." Abinda ya ce kanan ya fita. Nayla gabanta ya faWi a bayyane ta ce, "ba dai ba a nan zai kwana ba?." Sai kuma ta ce, "wata?ila zai dawo sai dare." Maimakon ta je ta rufe sai ta koma ciki ta kwanta saboda kanta na ciwo sosai.

Omar kuwa aiki ya saka ana yi sosai a company saboda sun karSi kuWi mutane kuma babu kaya sosai a ?asa ga sallah na zuwa. Ganin idanunsa dole ya saka ake yi ko ba a so, ya bada kuWi aka siyo abinci kar ma wani ya ce yunwa yake ji.

Da yake daren azumi ne kuma goman ?arshe mutane suna ta kai kawo ana tafiya masallaci baza ka ce dare ya yi ba. A lokacin Goje ya shiga shagon ya kalli Omar da yake zaune yana kaWa ?afarsa. Goje ya ce, "Damisa akwai matsala." Ya kalle shi alamun me ya faru. Ya ce, "Wannan yaron Kb wanda ka yi silar zuwan sa prison ya fito, ya kuma yi alwashi a akan ka ko matarka. Ya samu labarin auren ka yanzu haka an sanar dani sun taro mutane zasu tunkari gidan."

Omar kallon sa yake yi kawai jin abinda aka faWa masa, a hankali ya ce, "Meye sahihancin maganar?."

"Darr Damisa, bazan kawo abinda ban tabbatar ba. Na faWa ne dan mu kwashi kayan aiki mu je mu nuna musu zaren ba kalar yadin bane." Omar ya mi?e tsaye sai Tk da Bash ma suka mi?e ya Waga musu hannu yana kallon su ya ce, "a tabbatar da an gama aikin nan a daren nan, kar wanda ya biyo ni." Goje ya ce, "Amma Damisa zuwan mu yana da mahimmaci."
"Kar wanda ya biyo ni!" ya faWa yana nuna su da yatsa tare fita kai tsaye ya nufi gidan.

Nayla tana kwance a Waki ta ji wata ?ara mai ?arfi da hanzari ta mi?e zaune tana raba idanu, ta sake jin ?a?ar alamun ana ?o?arin buWe gate Win gidan da ?arfin gaske. Gabanta ya faWi ta dafe ?irji ta ce, "Lafiya ake dukan gate Win nan haka? Kai ashe na manta ban kulle ba" ta faWa tana mi?ewa da?yar saboda ciwon kai ta fito a hankali kamar munafuka.

Tana zuwa falon aka sake dukan ?ofar da ?arfin har lock Win ya cire tunda iya shi kaWai ne a jiki bata saka key ta kulle ba. Shigowar mutane take ji ana cewa, "Wallahi yau ko shi ko matarsa sai Waya ya ba?unci lahira. Ya yi silar zuwa mu prison shi ya zo yana zaune ya ma yi aure yana jin daWin rayuwa, na rantse da Allah bai isa ba yau sai ya ba?unci lahira." Nayla ta zaro ido gabanta ya faWi jikinta ya hau rawa a lokacin ta ji ana taSa ?ofar falon. Tsalle tayi ta koma da baya cikin matu?ar tsoro ta gudu ciki ta shiga Waki ta shige can ?arshe jikinta na matu?ar rawa tana hawaye.

Motsi da ta ji a Wakin ne ya saka ta Wagowa a razane ?irjinta ya buga ta sake zabura cikin tsananin tsoro kamar wacce ta zauce.
KRB3P011

Nayla a gigice take matu?a hakan ya saka suna haWa ido da Omar da ya shigo Wakin a karo na farko ta diro daga kan gadon a hanzarce, cikin sacannin da bai wuce biyu ba ta zo inda yake ta ri?e shi jikinta na rawa tana faWin,  Tsoro nake ji, tsoro nake ji ka taimaka min zasu kashe ni. Yadda jikinta yake rawa zai tabbatar da gaske a tsorace take bata cikin nutsuwarta. Ta ri?e masa riga gam hannunta sai rawa yake yi sosai.

A karo na farko da hannunta yazo jikinsa shima na sa hannun ya je jikinta, duk da shima baya cikin nutsuwa hankalinsa a tashe yake yana tunanin ko wani abun ya same ta ya dawo gidan, sai da yaji haWuwar hannunsu a waje Waya a jikinsa da zuciyarsa, duk da hannun nata rawa yake yi amma hakan bai hana shi jin ba?on yanayi a tare dashi ba.

 Babu abinda zai same ki, ki nutsu ya furta a tausashe yana kallon yadda take kuka sosai kanta ko Wankwali babu. Gashin ta yana cure a tsakiyar kanta ta Waure shi da ribbon. Kamar ma bata ji me yake faWa ba har lokacin bata cikin nutsuwarta saboda tashin hankalin da taji yana ?o?arin tunkaro ta, kasheta fa taji ana zancen za a yi, to ba dole hankalin ta ya bar jikinta na wani lokaci ba.

Nayla har lokacin hawaye ta ke yi tana ri?e dashi ta ce,  Tsoro nake ji, zasu kashe ni. Sun Salla gate sun shigo, Ka taimaka min ta sake faWa a tsorace sosai tana ri?e hannayensa duka biyun tana waige-waige. Abinda ya ji ya ratsa hannunsa mai kama da jan wuta shine ya saka shi yi mata tsawa ya ce,  ba na ce ki nutsu ba! Ki saurara da wannan shirmen! Ya faWa da ?arfi ba tare da ya sani ba saboda shock Win da ya ji ya ratsa hannayensa ya shiga har cikin jininsa ya zaga sa?on ya tafi har ?wa?walwarsa lokaci guda.

Firgigit Nayla tayi ta tsaya cak tana kallonsa har lokacin jikinta bai daina rawa ba amma ta saki hannunsa babu shiri. Kallon ta yake yi kamar yadda take kallon sa tana share hawaye ya ce,  babu abinda zai same ki, ki nutsu ki daina yi min shirme ya faWa yana fita ya bar ta a wajan jiki na karkarwa.

A gefen gadon ta zauna tana ajiyar zuciya, tsoron da take ji ya ragu ganin Omar Win yana nan amma har lokacin a tsorace take ta kasa sakewa gani take kamar zasu dawo su kashe ta Win.

Shi kuwa harabar gidan ya fita zuciyarsa na yi masa zafi akan abinda aka yi masa, yana fitowa harabar gidan ya tarar da Bash da Goje da Tk suna jiran fitowarsa. Yana ganin su ya ce,  bana ce ku zauna kar ku fito ba?. Goje ya ce,  Haba Damisa, an shigo har gonar mu kuma mu zauna muna kallo?. Tsaki ya yi ya ce,  to da ku ka zo me zaku yi?.

 Umarnin ka mu ke jira, wallahi yau baza su kwana lafiya ba. Azumin gobe sai dai su yi shi a kabari. Hayaniya yake jiyo daga waje ya ce,  su waye a waje?. Bash ya ce,  masoya ne, sun Webo kayan aiki suna jira ka ce wani abun.

Tsaki ya sake yi ya fita zuwa wajan dan ganin abinda yake faruwa, yana fitowa ya ga matasa da makamai an taru ana jira ya fito, yana fitowa suka fara hayaniya wannan yace wannan wancan ya ce wannan. GabWaya baya fahimtar abinda ake faWa hakan ya saka ciki cikin tsawa ya ce,  ya isa! Ya isa!.

Duk suka yi shiru ya kalle su ya ce,  ban ce kowa ya yi wani abun ba, ban ce kowa ya aikata wani abun ba. Kar wanda ya yi musu komai, a bari hukuma tayi aikin ta. Ina sake maimaitawa, kar wanda ya Wauki doka a hannunsa. ?aya daga cikin matasan ya ce,  Madugu har gida fa, har gida suka zo aka yi mana ba daidai ba kuma ka ce mu bari?. Kaima wasa ka ke yi baza mu ?yale su ba wallahi. Ranmu fansa ne a gare ka Damisa, zamu iya Satawa da kowa mu shirya da kai wallahi.

Omar ya ce,  ni dai na ce kar wanda ya yiwa kowa wani abun, in kuma ba haka ba duk wanda ya aikata saSanin abinda na ce zai haWu da fushina mai yawa. Kowa ya wuce ya tafi ya yi alwala ya tafi masallaci ya yi sallah. Wani zai sake magana cikin tsawa ya ce,  Na ce ku bar nan ko!. Dukkan su barin wajan suka yi ya kalli su Bash ya ce,  ban ce kowa ya aikata wani abun ba, haka zalika ban bawa kowa umarnin tura wasu su yi wani abun ba, ku ?yale ni ni nasan matakin da zan Wauka.

Tk ya ce,  Amma Damisa& .
 Shiru! Na ce a ?yale ni ya faWa a tsawace yana kallon sa dole ya yi shiru suka fita shi kuma ya koma ciki. Kamar ya shiga Wakin ya duba ta amma sai ya fasa ya yi zaman sa yana kaWa ?afa cikin Sacin rai mai yawa.

Wai shi za a zo har gida aka yiwa wannan wula?ancin, in ba dan kura tayi lafiya ba ai da gobe garin Kano an wayi gari jini ya Sata ko Ina, azumin gobe jama ar Kano da jini zasu sha ruwa. Babbar sa ar da suka yi Omar Win dah dana yanzu akwai banbanci, in ba dan haka ba da duk sai dai iyayensu su haifi wasu, koda bai Wauki mataki da kansa ba za a Waukar masa. A bayyane ya ce,  ko ya ya kayi ?o?arin zama mutumin kirki sai an yi abinda za a saka ka koma na banza.

Tsaki ya yi ya fita yana kallon gate Win ya mayar ya rufe dan ba Salla shi suka yi duka suka yi masa har lock Win ya zare. Ko key bai saka ba ya dawo ya zauna a kan kujera yana kaWa ?afa yana tunanin irin hukuncin da ya kamata ya yi musu. Yana wanna tunanin ya ga ?arfe uku na dare ta yi ko ina sallah ake yi. Kawai sai ya tashi ya yi alwala shima ya tayar da ta sa sallar.

Nayla kuwa baccin wahala ta yi alarm Win wayar ta ne ya tashi ta, ta tashi da nauyin jiki da ciwon kai daman dashi ta kwanta gashi tayi kuka kuma bata samu baccin kirki ba, alawala tayi ta tayar da sallar tahajjud.

Washe gari sai ?arfe goma na safe ya tashi, kasanacewar juma a ce manyan kaya ya saka ya fita, kai tsaye police station Win da ya saka kai yaran ya wuce. Da yake Dpo da suka saba ne suka tattauna ya ce masa za a Wauki mataki mai ?arfi, zuwa ranar monday za a tura su kotu bisa tuhumar tayar da faWa har cikin gida al?ali yanke musu hukunci.

Omar ya san za a yi hakan shiyasa bai damu ba ya wuce zuwa shago. Kowa mamakin ganin sa yake yi kuma ba a ji wani tashin hankali ya sake faruwa ba, kowa mamaki yake yi da labari bai zagaye gari ana cewa Tiger ya mayarwa da kura a niyar ta ba. Duk inda ya wuce kallon sa ake yi yana kuma sane da kallon da ake masa kawai babu wanda ya isa ya tunkare shi da maganar ne sai dai kallon kawai.

Nayla ranar bata je aiki ba ita da aiki sai ranar monday, tana zaune kiran Didi ya shigo wayar ta tana Wauka a gigice Didi ta ce,  Nayla lafiya ki ke dai ko? Na ji labarin abinda ya faru jiya. Ina fatan dai kina lafiya?. Nayla a kasalance ta ce,  Lafiya lau Didi, Amma a tsorace nake sosai.
 Ina Omar Win?.
 Ni ban sani ba ta faWa murya na rawa sosai.

 Ki nutsu Nayla, babu abinda zai same ki. Bara na kira Omar Win naji abinda yake faruwa ta faWa tana yanke wayar. Nayla tayi ajiyar zuciya har lokacin zuciyarta bugawa take yi dan bata taSa ji ana cewa za a yi kisa a zahiri ba sai dai a film.

Abu na social media nan da na labari ya zaga ko Ina da ko wanne gari. Arewa bloggers suna ta rubuta an kaiwa Omar Tiger babban Wan daba mai murabus hari har cikin gidan sa ana yi yun?urin kashe matarsa.

A can Madina a lokacin Mama tana zaune bayan sun dawo daga sallar juma a suna zaune ita da Abiy sai ga yaran nasu gabaWaya sun shigo Wakin Abiy gashe shi. Suna zaune ana hira Mama ta Wauki waya tana dubawa.

Mama ta ce,  Innalillahi wa inna ilaihir raji un! A tare duka suka kalle ta a gigice jin salatin da tayi Abiy ya ce,  lafiya?. Mama ta kalle shi ta kalli wayar ta ce,  Jiya da daddare an kaiwa babban Wan daba na jahar Kano mai suna Tiger hari har cikin gidansa, an yi yun?urin kashe matarsa Allah ya ta?aita Mama ta faWa cikin sigar karanto musu abinda yake da rubuta.

Jidda ta ce,  Innalillahi wa inna ilaihir raji un! Mama Twinny! Ta faWa a gigice tana wara idanu waje. Mama a ruWe ta ce,  ku kira mana wayar ta da hanzari don Allah. Yaya J da Yaya Ahmad da Jidda har rige-rigen kiran wayar Nayla ake yi cikin tsananin tashin hankali.

Abin haushin gabaWaya basa samunta sai kira ake yi amma bata shiga. Yaya J yayi tsaki ya ce,  Ba a samun ta a waya. Abiy ya bisu da kallo ganin duk sun ruWe su ga masu ?ar uwa, ya yi dariya ya ce,  meye duk ku ka tashi hankalin ku haka? Abinda ta aura kenan daman, kuma kun san haka zata iya faruwa ko yaushe, to meye na Waga hankali kuna salati haka?.

Yaya ya ce,  Abiy batun kisa ake yi fa, kisa fa. Abiy ya Wauke kai bai ce komai ba. A lokacin Jidda ta same ta WhatsApp call tana Wauka ta saka a speaker ta ce,  Twiny lafiya ki ke dai ko? Yanzu mu ka ga abinda ya faru jiya a social media, kina lafiya?.

Nayla a sanyaye ta ce,  Lafiya lau nake Twiny, babu abinda ya same ni.
 Kin tabbatar? Ya na ji maganar ki haka kamar kin yi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login