Showing 270001 words to 273000 words out of 332344 words

Chapter 91 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14370

mutanen Chad.

Didi ta katse shirun ta ce, "Omar zamu je Chad, akwai rasuwar da aka yi a can ya kamata a ce mun je mu ma." BuWe ido ya yi ya kalle ta ya ce, "Ina ne kuma Chad?."
"?asar Chad mana, asalin ?asarsu Maman mu." Omar ya taSe baki ya ce, "A matsayinki na wa zaki je? Wa ki ka sani, waye ya sanki?. Didi kin cika shishshigi wallahi, ina guje miki shan duka wata ran" ya faWa murya a ?asa saboda kansa da ya yi nauyi.

Didi ta ce, "ai har da kai zamu je ba ni kaWai ba. Kakanin mu duk a can suke, kafin Kakarmu ta bar duniya na taSa ganinta sau biyu da ta zo nigeria, amma kai baka taSa ganinta ba. Akwai danginta a can sosai, ana son a sake ?arfafa zumunci ne, zamu je a madadin maahifiyarmu." Ya zuba mata ido har ta gama bayanin sannan ya taSe baki ya ce, "Sai kin dawo, amma babu inda Marmerh zata je. Danginki ne ai ba danginta ba."

Didi ta ce, "Sai mun dawo dai, ka daina batun Marmerh; har kai da Nayla da Musliha." Kallon baki da hankali ya yi mata, ko damar magana ma bata samu daga gare shi ba balle ya tanka mata, dan a ganinsa maganar bata da amfani. Didi a sanyaye ta ce, "Omar meyasa baza ka bari ya wuce bane? Ina guje maka ganin illar ri?o wallahi. Me za a yi maka da zuciyarka zata yi sanyi? Me za a yi maka da zai saka ka manta baya ka fuskanci gaba?." Omar da mamaki ya ce, "ikon Allah, ya ki ke so nayi musu? Goya su zan yi ko me zan yi?. Kin ce bana magana dasu yanzu ina yi, to me zan yi?."

"Ka saki jikinka dasu kamar kana tare da Mama, ka saki jikinka dasu Kawu kamar kana tare da Baba. Har Gombe mun je ziyara amma ka ?i zuwa. Don Allah ka yayyafawa zuciyarka ruwan ?an?ara ka ri?e danginka, wallahi baka da kamarsu a duniya."

Sake taSe baki ya yi, sai kuma ya haWe rai ya ce, "Har yanzu ina kallo wu?alancin da suka yi miki a lokacin da muka je gidansu, mu mun je da ?arfin guiwa muna ji a ranmu mun je dangin mahaifiyarmu, ashe dukkansu taron tsinstiya ne babu shara...."ya sake cewa, "Su kuma tsofaffin munafukan har yanzu akwai shatin dukan da suka yi min a jikina, yadda wannan tabon bai Sace daga fatata ba haka na zuciyata ma bazai Sace ba. Dan ma sun raina min hankali, a rasa yarinyar da za ace ina nema sai wannan koWaWWiyar, na tsani ganin fuskarta wallahi, Tsaf zan talitseta da mota wata ran. Ki basu shawara, duk inda suka san zamu haWu su daina bi wallahi, kamminta suna nan tsaf a idona, in muka gauraya za a yi Satacciya."

Didi ta yi masa banza bata tanka ba, tana ro?on Allah ya kawo ranar da zuciyar Omar zata yi sanyi, tana faWawa Allah ya kawo silar da Omar zai sauka daga wannan dokin zuciyar. Zata so taga ranar da zai yi sanyi ya karSi danginsu. Nayla kam bata ce tak ba kuma tana jinsu.

BuWe ?ofar falon aka yi aka shigo da sallama, tunda aka yi haihuwa ba a saka lock Win ?ofar saboda masu zuwa barka, kuma gate Win gidan ba a hana shiga sosai. A tare suka kalli wanda suka shigo gabaWayansu, gaban Nayla ya yanke ya faWi ta zubawa Narma ido tana kallon ta da tsananin mamaki.
P104

? ?? Didi mamakin ganin ta take yi, shi kam Wauke kai ya yi ya mayar da ido ya rufe yana ji kamar ya tashi ya zaneta, sun takura masa ya rasa ya zai yi da su. Narma ganin Didi a zaune sai ta samu ?arfin guiwa ta ?araso kusa da Didi ta tsuguna ta Wora kanta a cinyar Didi ta fashe da kuka. Dukkansu sun yi shiru babu wanda yake magana, sai kukan da take yi a hankali amma kana jin sautinsa.

Omar gajiya ya yi da jin kukan, a fusace ya ce, "Ke!." Ba ita kaWai ba hatta Nayla da Didi sai da suka firgita, Musliha da Marmerh da suke bacci suka buWe ido a firgice. Cak Narma ta tsaya da kukan ta kalle shi ta ga ita yake kallo da alama ita yake yiwa tsawar, ya ce, "Meye na kukan!?." Shiru ta yi ta kalli Didi murya na rawa ta ce, "Didi ki taimaka min, ki taimaka min zan iya rasa hankalina."

? ? Didi ta kalli Nayla da take kallonsu ta kalli Omar da ya mayar da ido ya rufe ta sake kallon Narma ta ce, "Narma me ki ke so nayi miki?." Narma tace, "Didi Faruk!." Didi ta kalli Omar ta sake kallon Narma ta ce, "Narma ya kamata ki manta dashi, rayuwar da aka yi a baya baza a yi ta yanzu ba."

"Amma Didi kin san ba laifina bane ba ko? Kin san bani da laifi akan abinda ya faru."
"Na sani, na san da gaske ki ke sonsa, amma ina so ki san wani abun in ya wuce ya riga da ya wuce kenan har abada. Wata damar tana zuwa sau Waya tak a rayuwa, da zarar ta wuce shikenan bazata dawo ba."

Safna da take tsaye a sanyaye ta ce, "Didi ki taimakawa ?awata ki saka baki Omar ya amince da ita, wallahi har a asibiti ta kwanta saboda soyayyarsa. Yau ne kawai ta samu lafiya ta zo inda yake." Didi ta kalli Safna ta ce, "wanne irin taimako zan yi mata? Ga Omar a zaune ai, ni babu ruwana a cikin wannan maganar."? Safna cikin dauriya ta kalli Omar ta ce, "Don Allah Omar ka amince da ita, wallahi tana tsananin sonka, ban taSa ganin Narma cikin rauni ba sai bayan ta fara sonka. Wallahi in ta rasa ka zata iya shiga wani hali, dan zuciyarta tayi rauni akan soyayyarka."

Safna ta kalli Nayla da take kallonsu ta ce, "Ki yi ha?uri Madam, mun rasa mafita ne, shiyasa mu ka zo gidanki ba tare da izini ba." Nayla bata ce komai ba Narma kawai take kallo, tabbas Narma ta canja itama ta gani, duk ta yi wani iri kamar ba ita ba, gayun nan da take ji dashi yanzu duk babu. Didi ta ce, "Omar ka yi magana." Bai buWe ido ba ya ce, "Me zan ce? Mahaifinta ya same ni na faWa masa bana ra'ayi, duk da haka bai ha?ura ba ya sanar da Abiy, shima ya kira ni na ce bana ra'ayi" ya buWe idanunsa ya kalli Didi ya ce, "yanzu kuma an kawo maganar wajanki, to me ake so nayi?."

Narma cikin rauni da sanyi ta ce, "Ina so na ji daga bakinka ne, dan na san baza ka guje ni ba." Ya tashi zaune sosai ya gyara Marmerh da take jikinsa, ya kalli Nayla ya ga ta zuba masa ido tana kallo, ya Wauke kai ya kalli Narma ya ce, "Gaskiya ki ke so na faWa miki?."

Ta Waga kai alamun eh, ya Wan cize baki kana ya ce, "Ni Omar bani da ra'ayin ?ara aure a rayuwata, in ma ina da ra'ayi bakya cikin matan da zan iya aura. Ban so ki ba kuma bana sonki, kin shiga rayuwata ne saboda haka Allah ya ?ulla, tunda ki ka fita kuma komai ya ?are...." Ya nuna ta da yatsa ya ce, "Yadda nake rayuwata kema ki je ki yi taki, ki daina bibiyata, ki daina zuwa inda nake!" Ya faWa yana kallon ta.

? ?? Didi ta kalle shi jin kalaman sun yiwa Narma tsauri, a cikin wannan yanayi da take ciki da rarrashi ya kamata ayi mata magana ba da yadda Omar ya yi ba. Narma ta tsayar da kuka cak ta zuba masa idanu zuciyarta na bugawa a guje, cikin tsananin rauni da sanyi ta ce, "Da gaske baka soni ba? Da gaske baka sona?."

"To wacece ke da zan miki ?arya har ki ke so ki tabbatar? Amsa min wacece?." Narma ta sauke numfashi ta sunkuyar da kai, ta Wago a hankali taga ita dai yake kallo alamun ta bashi amsa sai ta ce, "matsayin wacce ka fara so a rayuwarka."

Dogon tsaki ya ja ya kawar da kai yana girgizawa, haushi yake ji wata banzar bazawara tana cewa wai ita ya fara so, ya sake juyowa ya ce, "Ni Omar bana sonki, ban so ki ba, kuma bazan so ki ba. Kin shiga rayuwata kuma kin fita, shigarki rayuwata ya jawo canji a cikin ta ina gode miki a kan hakan. Wata?ila da ban san mahaifinki ba da haka bai faru ba, wata?ila da baki zo Kano an haWa ni dake ba da haka bai faru ba, wata?ila da baki ce kina sona ba da hakan bai faru ba, wata?ila da ban amince har na je gidanku ba da hakan bai faru ba. Ke! Kina jina...?" Ya faWa yana Wora ?afa kan Waya ya ce, "A katse wannan maganar a wajan nan, bani da ra'ayin aurenki kawai ki ha?ura ki ?yale ni, bana son yawan maimaita magana guda Waya, tun muna shaida juna a ha?ura kafin a tunzurani." Narma hawaye ya sakko mata, cikin rauni da sanyin murya ta ce, "Ni na kasa tabbatarwa, da gaske baka sona?."

Wani irin kallo ya yi mata alamun ta ishe shi ya zuba mata ido kawai yana kallo. Didi ta fahimci wannan kallon, yanzu zai birkice ya fara masifa ya firgita kowa. Didi zata yi magana ya ce, "Ke! ni zan zauna ina yi miki ?arya? Wacece ke da zan miki ?arya?. Ina faWa miki magana kina sake dawo dani baya, dan ma kin samu lokacina da maganar!?" Ya faWa cikin faWa sosai yana kallon ta.

Didi ta ce, "Don Allah ka yi mata a hankali......."
"Bazan yi a hankalin ba, yarinya ce ita da za a tsaya ana yi mata dabara ko magana cikin magana?. Sak nake magana ke kin sani, bazan aureta ba, ta kuma daina takura min, ta je tayi rayuwata ta nayi tawa. Kar ta sake zuwa inda nake!. In na sake ganin fuskarta a kusa dani ban san abinda zan aikata mata ba" Ya faWa yana zaro idanu waje yana kallon Didi, sai kuma ya yi tsaki ya mi?e ya bar falon

? ?? Didi ta kalli Narma da take jikinta ta ri?e hannunta cikin rarrashi ta ce, "Narma ba komai ka ke so ka ke samu ba a rayuwarka ba, wani abun zaka so shi matu?ar so amma in ba rabon ka bane dole ka yi ha?uri dashi. Wani abun zaka ?i shi matu?ar ?i amma kuma sai ka mallake shi ba tare da ka yi tunani ba. Shiyasa Allah ya ce abinda ka ke tsananin so wani lokacin ba shine alkhairi a gareka ba, abinda ka ke tsananin ?i kuma shine alkhairi a rayuwarka. Allah shine ya san abinda ba mu sani ba Narma. To ki Wauka Omar ba alkhairi bane a cikin rayuwarki shiyasa baki mallake shi tun farko ba, kuma tun farko da Omar mijinki ne da sai kin aure shi, amma ba mijinki bane shiyasa baki aure shi ba har ki ka auri wani ki ka fito daga gidansa. Baza ki taSa mallakar abinda ba na ki ba, baza ki auri mijin da ba naki ba. Abinda ya kamata ki yi addu'a, ki tsaya akan addu'a ki manta da komai sai komai ya wuce."

"Kamar yadda ya faWa miki kin shiga rayuwarsa dan ki jasa zuwa gidanku ya zama silar canjawarsa haka ne, amfaninki a rayuwarsa kenan, haka Allah ya tsara babu wanda ya isa ya canja. Baki kasance matarsa a cikin ?addarar ku ba, shiyasa Allah bai yi ma kin aure shi ba. Tunda har Omar ya ce baya so wallahi baya so Win ne, Omar baya magana biyu, haka zakila baya faWar ?arya ya Soye gaskiya dan wani ya ji daWi. Shiyasa kalamansa suka yi miki zafi dan shi bai iya Soye-Soye ba. A lokacin da yake tunanin yana sonki ba so bane, ya samu kusanci dake ne a karo na farko a rayuwarsa. Bayan ni babu macen da wani abu ya taSa haWa su sai ke, wannan abinda yake ji a ransa shine ya Wauka soyayya ce. Amma yanzu da ya mallaki wacce yake tsananin so ya banbance tsakanin so da kusancin. Ki kwantar da hankalinki, ki yi ha?uri, ki fuskanci rayuwarki Narma."

Narma kuka take a jikin Didi a hankali. Didi ta ce, "ina faWa miki gaskiya ne a matsayina na yayarki, gwara ki san abinda zaki yi ki daina Sata lokacinki, sannan kuma daina tunanin Omar. In ki ka kuma zuwa inda yake gamuwar ku baza tayi kyau ba Narma. Zai yi miki abinda zaki ji ina ma baki san fuskarsa ba, duk yadda ki ke tunaninsa wallahi ya wuce wajan, gwara ki kama kanki ki cigaba da addu'a."

Narma ta yi ajiyar zuciya tana sauke numfashi. Didi ta ce, "Sannan Narma ki yi hankali ki daina shigar da take nuna jikinki. Shigar banza ba wayewa ba ce a ganina jahilce ne, nuna surar da Allah ya yi miki ba komai bane face tsantsar rashin sanin ciwon kai. Duk yadda zaki kasance wajan fidda saraici ai baki kai tunkiya ba, ita tunkiya yadda aka haife ta haka take yawo, kin ga kenan duk abinda zaka yi akwai wanda ya fi ka, kafin ka yi Waya an yi dubu. In kina nuna tsaraicinki baza ki samu wanda zai so ki tsakani da Allah ba, zasu so ki ne saboda abinda yake gani a zahiri a tare dake, da zarar ya aureki ya mallaka shikenan sai komai ya fita daga ransa, daman ba sonki yake yi ba sha'awa ce, ita kuma sha'awa tana gushewa ne da zarar gangar jiki ta samu abinda take maradi. Ba wai sai an neme ki a waje ne yake nuna illar shigar banza ba, ba sai anyi yun?urin yi miki fyaWe ko abinda ya yi kama da haka shine yake nuna illar fidda tsaraici ba, wani lokacin sai kin yi aure zaki fahimci illarta, domin auren sha'awa maza suke yi da masu irin wannan Wabi'ar ba na soyayya ba."

"Shiyasa nake baki shawara akan ki daina, tun kafin na san ki ni masoyiyarki ce, ina bibiyarki sosai saboda kina burge ni. Amma a ko yaushe ina cewa da Narma ta san illar nuna surarta a duniya da bata yi ba, a lokacin bani da matsayin da zan faWa miki gaskiya dan baki sanni ba, amma a yanzu na faWa miki na sauke nauyin da ya kamata ace na sauke. Surar da Allah ya yi miki ya yi miki ita ne dan ki yiwa mijinki kwalliya ba ki bayyanata ga duniya, in mijinki ya kalle ki ya yi farin ciki lada za a rubuta miki, wanda zaki je har ?abarinki ki tarar dashi. In akasin mijinki ya kalli surarki ya yi farin ciki zunubi za a rubuta miki, wanda zaki je ?abarinki ki tarar dashi."

Didi ta kuma cewa, "sannan ki daina wula?anta mutane shima ba abu ne mai kyau ba, Bazan ce kin yiwa Omar ba, amma wanda ya yiwa Omar saboda yana ganin rayuwarsa ta baya a yanzu ya ga yadda Allah ya mayar dashi, baka sanin abinda zai faru a rayuwar wani tunda ba kai ka tsara masa ba."

Didi ta yi ajiyar zuciya ganin Narma ta nutsu tana saurarenta, jikinta yayi sanyi alamun maganarta tana ratsa zuciyarta. Didi ta ce, "Ki je gida Narma, ki zauna ki tsara rayuwarki yadda ya kamata, amma ki manta da Omar. Ki dage da addu'a, na tabbatar da ace kina addu'a abin bazai yi muni haka ba. Ina baki shawarar yin addu'a Narma."

Narma ta kalli Didi ta girgiza kai tana goge idanunta ta ce, "Tabbas ina sakaci da addu'a Didi, ban taSa ro?on Allah akan ya kawo min sau?i a soyayyar Faruk ba."

"Ashsha! Kin ji matsalar, ta inda aka samu kuskure kenan Narma. Tun farko da kin mi?awa Allah kukan ki da yanzu kin manta da Omar, da yanzu kin cigaba da rayuwarki cikin farin ciki da annushuwa, da yanzu rayuwarki tayi gaba fiye sa tunanin ki. Indai kana ro?on Allah kana faWa masa abinda ya fika sani a kai zai shiga lamarin ya kuma sassauta maka. Shiyasa hausawa suka ce in so cuta ne ha?uri magani ne. Ki ri?e addu'a, a akan Omar kaWai ba, akan komai na rayuwa ki dinga addu'a a kai."

Narma ta girgiza kai ta ce, "Na gode Didi. Amma na tabbatar babu lallai na rayu a duniyar nan in babu shi."

"Kul, kar ki sake faWar haka. Babu wata halitta da in babu shi baza ka rayu ba, in har zaka rayu babu iyayenka a duniya babu wanda zaka ce dan babu shi baza ka yi rayuwa ba. Zaki manta da Omar in kin so hakan. Ki ri?e addu'a kiga in komai bai canja ba, ina nan zaki zo ki bani labari."

? ? ? Narma tayi murmushin takaici, dan ji take abinda Didi take faWa ba yuwa zai yi ba. Ta mi?e sai ta tafi zata faWi Safna tayi sauri ta tarota ta ce, "Yi a hankali." Narma ta kalli Nayla da bata ce komai ba amma kallonsu take yi, ta yi murmushi ta ce, "Ki yi ha?uri Nayla, Allah ya raya Musliha, na gode." Daga haka Safna ta ri?e ta suka fita daga falon.

Didi ta kalli Nayla da fuskar take a Waure matu?a ta ce, "Ki yi ha?uri Nayla, na san dole ki yi kishi, amma ki Wauka komai ya wuce." Nayla ta yi ajiyar zuciya ta kalli Didi ta ce, "Babu komai Didi. Umma Saroot ta aiko min da kaya sosai."

"Eh ta faWa min, ta ce min ita zata gyara mai jego." Nayla ta Wan yi murmushi ta ce, "Turaren wutar mai daWi sosai, haka humra ma." Didi ta ce, "Sosai ma kuwa, ga ri?e Waki da ri?e jiki. Ni naga? kamar kina sallah, har kin samu tsarki kenan?."

? ?? Da sauri Nayla ta waiga baya ta ga Omar baya nan ta kalli Didi ta ce, "Eh Didi, bayan yin suna babu jimawa ya Wauke." Didi ta fahimci bata so Omar ya sani sai ta ce, "Ma sha Allah, Allah ya ?ara lafiya." Ta amsa da amin kafin Didi ta ce,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login