Showing 288001 words to 291000 words out of 332344 words

Chapter 97 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14374

zaSa ya yiwa baiwa irina, kamata ya yi ki yi sujjada ki godewa Allah Jidda."

Kallon idonsa ta yi ya Waga gira ya ce, "ko ba haka bane? Jarumi ne ko akasin haka?." Shiru tayi bata amsa ba kuma bata yi dariya ba, ya ce, "ki amsa min mana, jarumi ne ko rago?." ?an murmushi ta yi amma bata ce komai ba ya ce, "kin gani ba, murmushi ki ke yi alamun jarumtar kenan, inda akasin haka ne fuskarki zata canja zuwa akasin murmushi. Kina alfahari da jarumtar mijinki har a zuciyarki, mijinki baya taSa baki kunya a kan gadonsa, yana nuna miki jarumtar da take saka ki gigicewa har ta tayar miki da aljanu, sannan ta saka ki maga...." Dariyar da ta yi tana rufe fuska ya saka shi yin murmushi yana kallonta. Daman so yake tayi dariyar kuma ta yi.

BuWe fuska ta yi ya ?ifta idanunsa ya ce, "Ko ba haka bane?." Bata amsa ba ya ce, "to dan ance miji irin wannan ya sake yiwa matarsa ciki a cikin wata bakwai ai ba abin damuwa bane." Ya sake ri?o hannunta cikin sigar rarrashi ya ce, "ki kwantar da hankalinki, zan taya ki rainon cikin, zan kuma taya ki rainon Musliha in sha Allah, in kuma kina da ra'ayi zaki iya Wauko mai kula da ita, zan iya biyanta ko nawa ne in sha Allah. Ni dai burina cikin nan ya rayu cikin aminci" ya faWa yana Wora hannunsa akan cikinta.

Ajiyar zuciya tayi ta ce, "Haihuwa fa da wahala Rouhii."
"Allah yana tare da ke, zan ta yi miki addu'a har Allah ya sauke ki lafiya."
"To Allah ya sa" ta faWa a sanyaye.

"Ko kefa, amma kina son cikin ko?."
"Ina so mana, abu a jikina ka tambaye ina sonsa? Tunda wanda nake so ne ya samar dashi ai dole na so." Yayi murmushi tare da jan kumatunta ya ce, "Na gode Habibty. Ki yi ha?uri da faWan da nayi miki, kin san bana jure Sacin rai." Ta kalle shi a sanyaye ta ce, "to ya zanyi maka? Na ha?ura."
Ya Wan buWe ido ya ce, "Babu dole, in baki ha?ura ba sai ki rama, ki ta yi min faWa har sai kin gaji, in ma dukana zaki yi ki dake ni."

Nayla ta ce, "Kaine dai ?iris ya rage ka zane ni." Ya buWe ido alamun razani ya ce, "ni Omar na daki matata? Har abada in sha Allah."
"Amma ai ka Wora min wu?a a wuyana a gidan Didi." Murmushi ya yi mai sauti yana shafa wuyan nata ya ce, "itama wannan ta qaunarki ce Jidda." Ta Wan taSe baki kamar yadda yake yi ta ce, "Ya batun shari'ar da ka ce zaka yi da Didi? Wajan wanne alqali zaka je?."

Kiss ya yi mata a lips Winta ya ce, "Kotu zanje na cewa alqali matata da Yayata sun haWa kai sun zubar min da ciki, ya yanke mu ku hukunci kuma ku biya ni cikina." Ta yi da???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?riya tana kallon sa ta ce, "ta ya zamu biya ka?."

Ya kalle ta ganin tana murmushi sai ya Waga gira sama tare da rage girman idanunsa ya ce,? "Ta hanyar bani ke na saka ki a Waki baza ki fito ba har sai kin yi cikin mana...." Bata ce komai ba sai murmushi da take yi, ya zuba mata ido ya ce, "Ke Win ce ai dole ma ki yi ciki da wuri, kullum canjawa ki ke yi daga zuma zuwa zam zam, ance babu abinda ya kai zam zam daWi da magani ba? To shi ki ke komawa Hauwa!."

Ta yi dariya ta ce, "DaWin baki."
"Da gaske nake, kin san bana yi miki daWin baki ai."
"Da gaske nake, da anyi magana abinda ka ke furtawa kenan, wannan kalma ta zauna a wannan Wan ?aramin bakin nan naka" ta faWa tana nuna bakinsa tana murmushi.

"Yanzu me ki ke so ki ci?."
"Tsiren kan titi nake so, sai gurasa ta masu tsiren mai yaji." Omar ya girgiza kai ya ce, "An gama ranki ya daWe, yanzu za a kawo miki, In kin ci sai me?." Ta lumshe ido ta buWe ta ce, "Sai nayi bacci a jikin my hero." Ya Waga kai ya ce, "duk kin samu, bani mintina kaWan zan kawo miki" ya faWa yana tashi ya fita ta bishi da kallo tana mamakin wayonsa, duk yadda take jin haushinsa da haushin cikin ya kau daga zuciyarta.

Duk yadda Omar zai yi ya Wauke hankalin Nayla daga kan samun cikin nan ya yi, tarewa ya yi a gida ko yaushe suna tare sai dole ce take firar dashi. Zamansu tare yana rage mata damuwa, amma duk da haka akwai zazzaaSi da ciwon kai da take fama dashi. In ya gaji da zaman gidan ya Wauke ta su fita su ta yawo sannan su dawo duk dan ta samu nutsuwa a zuciyarta. Cikin kwana biyun Didi na ta fama da ciwon ciki suna yawon zuwa dubata gida har ta samu lafiya.

Cikin Nayla yana da wata biyu yayin da Musliha take da wata tara da ?an kwanaki a duniya. Laulayin da take yi ya Wan ragu sai zazzaSi, amma yawan yin amai ta daina. Tana son zuwa Kaduna amma bata so ta je Mama ta gane tana da ciki, dan babu wanda ta faWawa, kunya take ji a ganta da wani cikin dole ta ha?ura da zuwan.

Suna zaune ita dashi suna hira akan abinda ya shafi kasuwnacinsa da irin cigaba da ake samu Didi ta zo gidan. Nayla ta mi?e tana yi mata oyoyo harda hugging Winta, Didi ta ce, "ya ?arfin jikin?." Nayla ta ce, "ke za a yiwa ya ?arfin jiki ai Didi." Didi ta ce, "kedai Nayla, ni kam ai na warware."

Omar ta kalla da Marmerh ta tafi da gudu ta haye jikinsa yana bata hannu suna tafawa. Didi ta yi murmushi ta mi?a masa hannu ta ce, "Omar mu gaisa." Yatsine fuska ya yi ya ce, "in na ?i fa?" ya faWa yana mi?a mata hannu suka gaisa ta ce, "so nake na ji Wumin ?anina."

Murmushi ya yi ta zauna a gefe ya kalle ta ya ce, "Amma kin warware ko?."
"Alhamdu lillah, na ji sau?i sosai."
"Allah ya ?ara miki lafiya Didi." Ta amsa da amin suka cigaba da hira har da ita, kafin ta kalle shi ta ce, "Omar bikin ?annenka za a yi na gidan Baba Adamu, mata zai aurar guda biyu da jika guda Waya, takanas na zo na kawo maka iv."

Kallon iv da take mi?o masa ya yi ya karSa ya a watsar a gefe ba tare da ya buWe ba ya ce, "Allah ya bani ikon zuwa."
"Amin, amma ka saka niya." TaSe baki yayi ya ce, "zan duba na gani. Tsabar neman wajan zama da shishshigi irin naki wai ?annena, mtsww!."

Tayi dariya ta ce, "Allah ya kawo ranar da komai zai wuce a zuciyarka, Allah ya nuna min ranar da zan ga zuciyarka da fuskarka sun yi rauni, wannan wacce irin zuciya ce haka? Abu kusan shekara sha kaza amma ka kasa mantawa." Bai ce komai ba, ya dai yi murmushi kawai yana cigaba da biyewa Marmerh da take ta yi masa surutu.

Didi ta ce, "to ni zan wuce, abinda na zo na kawo maka kenan." Ya Wago ya kalle ta ya ce, "Sau Waya ki ka taSa kwana a gidan nan, har na gaji da yi miki magana." Da mamaki ta ce, "ikon Allah! Omar da aurena zan zo gidan ka na tare?."
"Amma saboda ke aka yi wajan, ba sai ku zo da mijin naki ko sati Waya ku yi ba?." Ta yi murmushi tana girgiza kai ta ce, "Wata ran zamu zo Omar."

"Haka ki ke cewa kullum ai." Bata amsa ba suna magana da Nayla. Omar ya taso ya zo kusa da ita ya ce, "wai me yake damunki? Naga kin canja gabaWaya." Ta kalle shi tana murmushi ta ce, "ka san ai bani da lafiya ko?."
"Amma yanayin naki ba na ciwo bane, akwai abinda ki ke so ne?."
"Me zan so a duniyar nan Omar? Na je Saudia har sau huWu, a shekara Waya na ziyarci madina sau huWu. Sannan ka kaini dubai, ka kaini England, ka kaini China, ka siya min mota, ka kuma canja min mota, ka bani wannan, ka bani wancan, me zan nema kuma Omar?."

"?an adam ai ba a rasa shi da buri Didi, wata?ila akwai abinda yake zuciyarki wanda ki ke so ni ban san shi ba. Ki faWa min ko meye don Allah, ko meye shi a shirye nake nayi miki Didi." Didi ta yi murmushi tana kallonsa ta ce, "Babu komai Omar, bani da wani buri na irin waWannan abubuwan a yanzu. Burina kawai ka shirya da danginmu, shine abinda zaka yi min ya saka ni farin ciki mai tarin yawa. Bayan wannan bana bu?atar komai, domin duk wani abu na duniya na jin daWi wallahi ka gama samar min dashi, babu abinda nake so." Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "ina ji a raina kamar akwai wani gurbi da ban cike miki ba, meye Didi?."

Ta sake yin murmushi ta ce, "Omar babu komai, ka amince dani kawai. In ba akwai gurbin bai wuce maganar danginmu ba Yaya Omar." Ya sauke numfashi yana murmushi jin sunan da ta faWa masa, ya ri?w kafaWarta ya ce, "in dai akwai wani abun waya Waya ta biya miki bu?ata."
"An gama Babban Yaya." Suka yi dariya ita da Nayla, tare suka raka Didi har mota sannan ta tafi.

Bata jima da fita ba suka fita shi da Nayla. A hanyarsu ta dawowa gida ne AbdulHamid ya kira yake shaida masa Didi na asibiti, kai tsaye asibitin suka wuce suka samu AbdulHamid a tsaye Omar ya ce, "Lafiya? Me ya same ta?." AbdulHamid ya ce, "ciwon cikin nan ne dai, ta ce na sanar da kai shiyasa ma na kira ka."

"Tana ina?."
"Tana Waki ana dubata, bara su fito sai mu shiga." Zama Nayla ta yi shi Omar kam ya kasa zama har sai da likitoci suka fito suka shiga Wakin. A kwance suka samu Didi tana kallon masu shigowa, tana ganin Omar ta yi murmushi yana ri?e da hannun Marmerh ya ?araso ya ce, "Didi sannu, Meyasa Wazu baki ce min baki da lafiya ba?."

Didi ta yi murmushi Omar ya zauna akan kujerar da take gabanta har lokacin Marmerh na kusa dashi ta ce, "Bayan na koma gida ciwon ya samu Omar." Ya ri?e hannunta ya ce, "Amma da sau?i ko?." Ta Waga masa kai tana kallonsa da murmushi.

Didi ta kalli Nayla ta ce, "Nayla sannu."
"Didi ya jiki?."
"Da sau?i Nayla." Omar ya ri?e hannunta ya ce, "Babu abinda ki ke ji?" Sai ya kalli AbudlHamid ya ce, "ko dai zamu kai ta wata ?asar a duba wannan ciwon cikin nata? Yana damuna wallahi." AbdulHamid ya ce, "kuma lafiya lau ta koma gida daga gidan ku, tana sallar magriba sai ta ce cikinta na ciwo shiyasa muka taho."

Ya sake kallon Didi ya ce, "Sannu Didi, ya kamata a san abinda za a yi akan ciwon nan naki, zan je na samu likita mu yi magana." Didi ta yi murmushi ta ce, "Kar ka damu Omar, zan samu lafiya." Nayla ya kalla da take gefe ya ce, "Zo ki zauna da ita mu je mu dawo." Nayla ta dawo inda Omar ya tashi ta zauna.

Omar ya kalli hannunnsa ganin Didin bata sake shi ba, ya kalli fuskarta ya ce, "Didi." Murmushi ta sake yi shima ya yi murmushi ya Wora hannunsa Waya akan hannunta ya ce, "yanzu zan dawo." A hankali ya zame hannunsa ya bar kusa da ita.Marmerh ta saka kuka tana kiran Daddy ya Wauke ta suka fita tare shida AbdulHamid.

Nayla ta ri?e hannun Didi kamar yadda ya yi ta ce, "Sannu Didi." Didi ta yi murmushi ta ce, "Marmerh tana ?aunar Omar, yadda take ma?ale masa in ta ganshi ko babanta bata yiwa haka."Nayla ta yi murmushi ta ce, "Shima yana sonta ai." Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Nayla cikin wata nawa?." Nayla ta yi murmushi ta ce, "Wata biyu ne kacal."
"Kai! Ashe akwai sauran tafiya."
"Sosai ma Didi."
"Allah ya raba lafiya, ya baki ikon iya kula dasu."
"Amin Didi."

Didi ta ri?e hannun Nayla ta ce, "in ki ka haifi namiji ki saka sunan Abiy, shine ya zama silar aurenku, In mace ki saka sunan Hajja." Nayla tayi dariya ta ce, "in ?an biyu ne duka mata fa?." Didi ma tayi ?ar dariya ta ce, "Sai ki saka sunan Hajja da sunanki, in duka maza ne ki saka sunan Abiy da sunan Omar shikenan an raba." Nayla ta yi murmushi ta ce, "Allah ya kaimu."

"Amin Nayla. Zafi nake ji, bakya ji?." Nayla ta kalli Wakin ta ga ac aiki take yi, ta kalli Didi ta ce, "Ai kam babu zafi, bara na ?ara miki gudun ac."
"Bar shi kawai Nayla, Bacci nake ji." Nayla ta ce, "to ki kwanta mana Didi, ki yi bacci zaki fi jin daWi."

"Amma bani ruwa na sha Nayla." Nayla ta mi?e ta kawo mata ruwa ta bata ta sha, Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Kamar ban sha komai ba Nayla, sake bani na sha." Nayla ta sake bata, Didi ta shanye roba Waya na ruwa Nayla ta ajjiye robar. Didi ta ce, "ikon Allah, kamar ban sha komai ba, Amma bar shi kar ya ?ulle min ciki."

Nayla ta koma ta zauna ta kuma ri?e hannun Didi tana kallon ta kamar yadda take kallon ta. Didi ta ce, "Uwar gidan Omar, Allah ya bar ?auna har aljanna. Omar yana sonki kina sonsa, ban taSa ganin halittar da Omar yake so kamar ki ba Nayla, yana sonki kamar ya haWWiyeki."

Nayla ta yi murmushi ta ce, "Didi ai nima dai ina son shi, kar ayi min gori. Tun yana Wora min wu?a a wuyana nake son shi." Didi tayi murmushi ta ce, "Ni na isa na yi miki gori Nayla? Ina faWa miki ne dan ki sake ri?e min shi hannu biyu. Ki cigaba da ha?uri dashi, halin Omar sai fa ha?uri, ki cigaba da rarrashinsa akan danginmu Nayla"

Nayla ta ce, "ki yi baccin ki Didi, in kin tashi ma cigaba da maganar." Didi ta yi murmushi ta rufe ido sai kuma ta ja numfashi ta ce, "Hasbunallahu wani'imal wakil, Astagafirullah, allamuhmma salli ala Muhammad wasalmin" ta faWa a tare tana goge gumin goshinta ta mayar da ido ta rufe.

Nayla ta ce, "Sannu Didi." Ta buWe ido ta kalle ta ta yi murmushi ta ce, "nima fa ina son Omar, ba ke kaWai ki ke sonsa ba." Nayla tayi dariya bata yi magana ba, Didi ta kuma yin murmushi ta sake maimaita salatin da ta yi ta rufe ido tana sauke numfashi a hankali. Nayla na rike da hannunta kusan mintina ashirin sai ga Omar da AbdulHamid da likita? sun shigo.

Likita ya ?araso wajan Didi ya kalli Nayla ya ce, "ta yi bacci ne?." Nayla ta ce, "ta ce min bacci take ji." Likita ya kalli ruwan da yake shiga jikinta ya kalli hannun Didi, sannan ya juyo ga kallonsa kan fuskarta da idonta yake a rufe. Hannunta ya ri?e na wani lokaci sannan ya ajjiye hannun, ya Wora stethoscope a ?irjin Didi, ya kalli computer da take daidaita numfashi ya yi ajiyar zuciya.

Likita ya kalli AbdulHamid da yake kallonsa, ya kalli Omar da yake Sarewa Marmerh chocolate, ya kalli Nayla da take danna waya har lokacin hannun Didi na cikin nata, sai Musliha da take jikin Nayla tana bacci. Likita ya sauke numfashi ya ce, "Allah ya yi mata cikawa, ta rasu!." ?irjin mutane uku suka buga a lokaci guda Waya, AbdulHamid ya zaro ido waje cikin tsananin tashin hankali da ruWani ya ce, "Wai wacece ta rasu?."

Likita ya ce, "Gata a kwance."
"Haba likita, dubata da kyau mana, mintina ashirin da fitar mu tana kwance tana magana yanzu ka ce ta rasu? Ko dai bacci ta yi?."

Likita ya tako ya dafa AbdulHamid ya ce, "ka yi ha?uri abokina, Allah ya yi mata cikawa, ta amsa kiran mahaliccinta, ta mutu ta bar duniya." AbdulHamid ya tako da hanzari zuwa wajan Didi yana kallon ta, ya kalli likutan ya ce, "Da gaske ka ke? Ko dai ka kira wani likitan ya sake bincikawa? Ta ya za a ce ta mutu bayan yanzu muka fita muka barta tana magana?."

"Ba a wasa da mutuwa, bazan faWi abinda ban tabbatar ba abokina, Allah ya yi mata cikawa sai dai ku yi ha?uri."

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!! Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!!!. Likita yanzu fa...." Sai ya kasa faWa saboda rauni da karyewar zuciya ya mamaye masa jikinsa.
P113

Omar kam yana tsaye ?yam yana jin me suke cewa amma ya kasa fassara kalamansu, mutuwa ya ji suna cewa wai ta rasu, to wacece ta rasu Win? Meyasa AbdulHamid yake salati haka? Meye ma mutuwar, ya ake yin ta ya kasa tunawa. Likitan ne ya zo zai gifta ta gaba Omar ya ri?o shi ya ce, "Ni ban gane ba, wacece ta rasu Win?." Likita ya kalli Didi ya kalle shi ya ce, "Gata nan a kwance, gawarta ku ke tare da ita amma babu ranta" ya faWa a tausashe yana kallon Omar.

Omar ya kalli Didi ya sake kallon likitan ya yi masa kallon baka da hankali baka san aikinka ba, ya ja tsaki ya ce, "Amma dai baka da hankali ko?." Likita ya yi murmushi kawai bai tanka ba.

Nayla da take jin kalaman da ake yi duk da faWuwar gaban da take ji haka ta daure ta ce, "Likita me ka ke cewa ne? Kalli hannunta fa har yanzu yana ri?ewa da nawa, bacci fa kawai ta ce min zata yi shine zaka ce ta mutu?. Gaskiya baka san aikinka ba."

Omar ya yi tsaki ya taka zuwa inda Didi take kwance yana kallon fuskarta, gabansa ya yanke ya faWi ba tare da ya san dalili ba, rauni ya fara mamaye masa zuciya ya sauke Marmerh da take kafaWarsa ya ri?e hannun


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login