Showing 78001 words to 81000 words out of 332344 words

Chapter 27 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14405

magriba sannan suka dawo tare da Salma gabaWaya jikin Naylan a sanyaye. Yanayin da take ciki ne ya saka Salma ta bita ciki tana ta rarrashin dan kuka take yi sosai. Ta ce, "Haba Nayla meye na kukan don Allah?." Zata yi magana Didi ta kira Nayla a waya ta Wauka ta ce, "Didi barka da dare."
"Barka dai Nayla, an samu ?aruwa."
"Eh Didi."
"Allah ya raya mana ita."
"Amin Didi."

Didi ta ce, "tana gida ai ko?." Nayla ta ce, "eh tana gida, amma gobe da zasu wuce Kaduna."
"Kaduna! Na Wauka a nan zata zauna ai."
"Ai kowa na dangin mijin yana can itama kuma kinga haka, aiki ne kawai ya kawo shi nan shiyasa zasu koma." Didi ta ce, "kai amma ban ji daWi ba, bara yallaSai ya zo ya mi?a ni na yi mata barka bazan jira har sai ta dawo daga Kaduna ba."

A sanyaye Nayla ta ce, "To Didi." Yadda Didi ta ji maganar ta san tana cike da damuwa kuma ta san damuwar bai wuce tuna gida ba, in ba dan auren Omar ba da yanzu da ita za ayi shagalin haihuwar nan amma yanzu babu ita. Sallama suka yi Didi bata tambayeta abinda ya faru ba dan ta san amsar, kuma a ganinta abinda ya faru family issue ne bai shafe ta ba.

Salma ta kalle ta bayan ta kashe wayar ta ce, "meyasa ki ke kuka don Allah? Ki yi ha?uri mana dole ne zuwa Kaduna?." Ta kalli Salma cikin kuka ta ce, "Salma Twiny fa, komai tare mu ke yi, tare muka tashi muka yi komai. Sunan ?arta ta fari ace babu ni za a yi ai dole na yi kuka."
"To ya zaki yi? Ko zaki je ne?."
"A gaban ku dai Abiy ya ce kar na sake zuwar masa gida sai ya neme ni, ta ya zan je masa gida yanzu bai neme ni ba?."

"To ki yi ha?uri, ni kukan ne bana so naga kina yi." Nayla tayi murmushi kawai ta ce, "Salma ni kaWai na san abinda nake ji a zuciyata. Mahaifina ya ce kar nazo masa gida sai ya neme ni, akwai abinda ya kai wannan taSa zuciya da sanya zubar hawaye? Tunda na zo gidan nan ko video call ban yi dashi ba, ke kin san yadda nake da Abiy dole na shiga damuwa."
"Na sani, amma ki yi ha?uri."
"Na yi Salma." Ta faWa a sanyaye ta jingina da kujera. Da?yar Salma ta rarrasheta sannan ta tafi saboda dare ya yi har an yi i'sha.

Omar duk ya ji abinda aka tattauna, yana mamakin wai meye dalilin mahaifinta na aura masa ita? Me tayi masa har ya ce kar ta zo masa gida?. Yana zaune a Waki yana tunani babu mai bashi amsa haka ya kawar da tunanin daga zuciyar sa.

" " " " " " "

Narma ta ware sosai ta samu sau?i sai dai ta zama shiru-shiru babu magana sai ta zama dole, ko yaushe tana Waki, ko aiki ta daina zuwa, bata hira da kowa sai ta ga dama. Mum ta yi mata faWan har ta gaji ta share ta itama, kuma har lokacin laifin Omar take gani shine ya saka ?arta a wannan yanayi.

Da daddare suna zaune a dining tana juya spoon Win hannunta plate Win gabanta tana yiwa abincin cin yanga. Dad ne ya kalle ta ya ce, "Daughter me yasa ki ke haka?." Ta ajjiye spoon Win ta ce, "Dad me na yi?." Dad ya ce, "kin koma wani iri ko magana bakya yi, hakan daidai ne a rayuwarki?." Kawar da kai ta yi ta ce, "Dad kawai bana son hayaniya ne."

Dad ya kalli Mum da take kallosa suka yi mata shiru bata ce komai ba. BuWe ?ofar falon aka yi aka shigo duk suka kalli wanda ya shigo suna mamakin ganinsa. Dad ya mi?e tsaye ya ce, "Ashraf! me ka zo yi gidan nan?." Ashraf ya ce, "Dad I just come here because of my wife, I need to take her out." Mum ya mi?e tsaye ta ce, "You're not serious Ashraf. Let me tell you something, Narma ta gama auren ka wallahi. Divorce paper zaka bata ko kana so baka so."

Ashraf ya ce, "Mum bazan sake ta ba, Ina son zama da matata." Dad ya kalle shi cikin fusata ya ce, "Ashraf ka fita ka bani waje, zan yi magana da babanka baza ka kuma zaman aure da Narma ba har abada." Ashraf ya kalli Narma ta da take zaune tana kallon sa ya kalli Dad ya ce, "Dad gaskiya bazan sake ta ba, Ina son matata, babu wanda zai saka na sake ta."
"Dole ka sake ni Ashraf ko baka so!" Narma ta faWa tana tasowa daga inda take tana kallon sa.

?are mata kallo yake yi, sabuwar sha'awarta na sake kunnuwa a zuciyarsa. Tana sanye da shigarta ta ko yaushe, ya ce, "Bazan sake ki ba Narma, ko me zai faru wallahi ina tare dake matsayin miji." Narma ta ce, "Wallahi sai ka sake ni, ai ko kana so ko baka so zama da ni ya ?are a rayuwarka."

"Haka ki ke tunani kawai, amma har yanzu lokaci sakin ki bai yi ba dan ban ga wanda ya isa ya saka na sake ki ba Narma. Wato na sakeki ki komawa wancan Wan shaye-shayen Wan daba ko? To baki isa ba wallahi.

"?an daba ya fi min kai sau dubu, Ina sonsa son da bana yi maka shi, kuma bazan yi maka shi ba har abada."
"Wannan ke ta dama kuma Narma, abinda na sani you're my wife, dole kuma ki yi abinda nake so" ya faWa yana ?are mata kallo.

Mum ce ta katse shi ta ce, "Ashraf fita ka bar gidan nan, ka cire komawar Narma gidan ka domin baza ta taSa komawa ba har abada." Ya kalli Mum ya ce, "Mum ko court bazata raba aurena da ita ba wallahi, Ina son zama da ita." Dad ya ce, "ka san kana sonta ka dinga wahalar da ita?." Narma ta ce, "Dad ba ya sona, ya faWa min ba sau Waya ba baya ?aunata."

A fusace ya juya ya kalle ta ya ce, "eh bana son ki, bana ?aunar ki kuma bazan sake ki ba!." Dad ya kalle shi cikin tsananin fusata ya ce, "you know what? It's my fault, laifina ne da na dau?i aure na baka ba tare da na yi bincike mai kyau a kan ka ba. Laifina ne da na duba relationship Wina da mahaifinka na dau?i my own daughter na baka ba tare da ka bayar da ko sisi ba. Amma yanzu dole sai ka sake ta ko kana so ko baka so Ashraf, zaman ta da kai ya kare."

Mum ta ce, "Ko kunya baya ji, in front of our eyes yake faWar baya son Narma, kuma kana expecting zamu sake baka ita ne ta zauna da kai? Ka goge wannan tunanin daga ranka Narma baza ta sake zaman auren da kai ba."
"I'm sorry Mum and Dad, bazan iya sakin ta ba kome za a yi sai dai ayi. Kuma zan Wauki matata a duk lokacin da naga dama" ya faWa yana fita daga falon.

Narma ta kalli Dad cikin kuka ta ce, "Dad kalli abinda ka jawo mana, lokacin da na ce bana sonsa baku saurare ni ba ku ka yi forcing Wina akan aurensa. Na ce ban so amma babu wanda ya saurare ni balle a fahimci bana so Win. Dad duk abinda ya same ni ku ne silar komai, duk halin da na shiga ku ne ku ka jawo, inaa da wanda nake so, na kawo shi gidan nan ku ka wula?anta shi saboda ra'ayinku, na Wauka duk abinda nake so zaku yi min amma kun kasa. It's over!" ta faWa tana hawa sama a guje tana kuka sosai.

Mum ta kalli Dad a fusace ta ce, "Duk abinda ya faru da ?ata bazan ?yale Ashraf ba wallahi, babu ruwan da abinda yake tsakanin ka da mahaifinsa, zan yi masa hukunci daidai da abinda ya aikata" ta faWa tana barin dining Win itama. Dad ya yi shiru ya bisu da kallo a lokacin Najwa ma ta tashi ta hau sama, ya yi ajiyar zuciya yana ji a zuciyarsa duk abinda ya faru da Narma kamar shine sila.
KRB3P025
Arewabooks@nanahaleema11.

An yi shagalin sunan a Kaduna, yarinya ta ci sunan mahaifiyar mijin suna yi mata la?aSi da Mihada. Nayla a waya take ganin komai gabaWaya ta damu da rashin zuwanta, sai da Yaya J ya kira ta ya dinga rarrashi sannan ta sake ta cigaba da harkokinta

Zaman su da Omar yana nan yadda yake babu abinda ya canja, tana fita aikin ta dawo wani lokacin ta wuce gidan Hajja ko gidan iyayenta da suke garin sai dare ta dawo gida.

Kamar ko yaushe ranar Alhamis Nayla ta dawo daga wajan aiki tana zaune tana kallo a tv, Didi tayi mata waya take sanar da ita an yi rasuwa a gidan Kawunsu inda suka taSa zuwa. Nayla ta ce, "To na taho yanzu ne Didi?." Didi ta ce, "sai gobe za a yi jana'iza, ki bari sai goben, sai dai kuma zaki je aiki."
"Babu komai zan samu na zo, ai Friday ce. Allah ya ji?an rai." Ta amsa da amin ta kashe wayar.

Washe gari kuwa da wuri ta shirya kamar zata tafi aiki ta wuce gidan rasuwar dan ta gane gidan. Tun daga bakin layin zaka san anyi rasuwa, dan manyan motoci ne sosai na mutane da suka zo jana'iza. Ta ajjiye motarta shiga gidan ta kira Didi ta sanar da ita inda take aka rakata suka zauna tare.

?arfe tara aka yi jana'iza, Didi ta ri?e hannun Nayla tana kai ta wajan wanda mutuwarta shafa tana yi musu ta'aziya. Har su Kawu sai da ta yiwa, lokacin goma na safe ta yi sannan suka yi sallama da Didi ta wuce wajan aiki a lokacin.

Bata jima sosai ba ta koma gida ta sanar da su Hajja rasuwar dan su yiwa Didi gaisuwa. Tana zaune da yamma sai ga Didi ta shigo, kana ganin yadda ta shigo ka san ranta a Sace yake sosai, ga cikinta ya girma sosai duk ta saka babban hijjabi amma ana gani, fuskarta duk ta canja tayi ja sosai. Didi ta kalli Nayla da take yi mata sannu da zuwa ta ce, "Nayla Ina Omar?."

A lokacin ya shigo falon ya kalle ta ya ce, "gani." Didi ta juya ta kalle shi ta ce, "Meyasa kai wani lokacin baka aiki da tunani ne Omar? Mutuwa fa aka ce, matar Kawu babba ce ta rasu amma ka kasa zuwa ka yi musu gaisuwa. Tun Daren jiya na faWa maka, maimakon ka je ko ladan jana'iza ka samu sai baka je ba saboda wani banzan tunanin ka. Ai mutuwa ta fi gaban wasa, tunda aka ce ta mutu ko meye a zuciyarka sai ka kawar dashi ka yi mata addu'a haka musulmi na gari yake. Kai kaWai aka yiwa laifi a duniya ne ko kai kaWai ne me zuciya!?."

Kallon ta yake yi jin yadda take yi masa faWa shiyasa ya shareta, in ya tanka ?ofar da yake tsaye a jiki ma ta tanka. Didi ta ce, "Yanzu ka wuce mu je ka yi musu gaisuwa, in har na isa da kai ka wuce mu je yanzu ba anjima ba."

TaSe baki ya yi ya ce, "bazan je ba, da nawa mahaifin ya bar duniya itace ta fara kallona ta ce an rage iri a duniya, dan yanzu ta mutu kuma sai ace na je gaisuwar mutuwarta? Kema kin san wasa ki ke yi."
"Ta riga ta mutu, ko me tayi maka ya kamata ace ka manta dashi ka yafe mata. Kuma ba dan ita zaka je gaisuwar ba, saboda Kawu zaka je da kuma ?a?anta."

Omar ya ce, "Didi babu inda zan je gwara ma ki daina wahala da bakin ki." Didi ta fusata sosai ta ce, "Sai ka je Omar, in dai na isa na faWa maka sai ka je!."
"Bazan je ba, akansu ki ke Waga min murya haka? Su Win su waye a rayuwata?."
"Iyayenka, iyayenka ne ko kana so ko baka so, danginka ne wanda baka da kamar su."

"Iyayen wasu dai amma ban da ni, ba iyayena ba ne kar ma ki sake danganta ni da su!" Ya faWa cikin muryarsa mai amo wacce ta sa Nayla ta toshe kunnenta.

Didi ta ce, "ko kana so ko baka so iyayenka ne, gwara ma ka hutar da kanka ka so. Wannan banzar zuciyar babu inda zata kai sai dana sani." Bai tanka mata ba ya kawar da kai ta ce, "Ko baka so dole ka je ka yi musu gaisuwa, in dai na isa da kai." Ya girgiza kai ya ce, "kin gama yi min dole Didi, kin ga ina yin abinda ki ka ce shiyasa ki ke yin abinda ki ga dama. To ta ?are!" ya faWa a kausashe yana kawar da kai gefe.

Didi ta matso kusa dashi ta ce, "wai wacce irin zuciya ce da kai?."
"Wacce Allah ya yi min."
"?arya ka ke, kai ka sakawa kan ka wannan ba?in hali ba Allah ba. Kuma zan gani in ina da darajar da zance ka yi abu ka yi, in kuma bani dashi zan gai." Omar a fusace ya ce, "Kina dashi, amma a wannan lokacin bazan yi ba!."

"Iyayenka ne dai ko ka ?i ko ka so, sune danginka, komai na rayuwarka sai ka neme su, su ne suka karSar maka aure!. Ko gobe zaka sake yin wani abun wajen su dai zaka je, baka da inda ya fi su, kaga kenan dole ka ce da mijin iya baba."

Nayla bata taSa ganin wannan faWan na su ba, ta saba ta ga suna hira da nishaWi da ?aunar juna, ganin su a haka gabaWaya sai ta damu saboda yanayin da Didin take ciki. A sanyaye ta ce, "Didi don Allah....."
"Ke!!" Ya faWa cikin tsananin tsawa yana kallon ta da idanunsa da suke waje suka kuma koma jajaye. Baya Nayla tayi a firgice, iya tsawar da ya yi mata ma abin tsoro ne balle kuma idanunsa da suke a waje.

Ya nuna ta da yatsa ya ce, "kar ki sake cewa komai a wajen nan, duk ba ke kika jawo ba? Ba ke kika jawo min ake yi min gorin su ne suka karSi aurena ba!?" Ya faWa yana kallon ta kamar ya tsinka mata mari. Didi ta kalle shi ganin ya koma kan Nayla ta ce, "Dani zaka yi ai ba ita ba, ni ce nayi maka laifin ba itace tayi maka ba Omar!."

"Auren da ki ke batun su suka karSar min ni nace Ina so? Ko na ce ina son auren ne? Ba haWa baki ki ka yi dasu aka munafurce ni aka yi min aure ba tare da na sani ba!?."

Didi ta ce, "ko a nan ya kamata ka fahimci matsayin da suke dashi a rayuwarka, tunda gashi kana zaune da auren da su ne suka karSe shi, hatta sadakin auren ba kai ne ka biya ba su ne suka bayar saboda su ne iyayenk???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a!" Ta faWa ido a waje itama tana kallon sa.

"Saboda ke, saboda kin yi min dole ya saka nake zaune da auren nan kema kin sani, ban ce ina so ba kuma bazan taSa so ba. Har abada bazan taSa son abinda ya zo daga gare su ba cikin harda auren nan!. Ke ka yi min dole na karSa, ke kika yi min dole nake zaune a gidan nan, ke kika yi min dole nake rayuwa a cikin gidan, ke kin san ba dan ke ba babu wanda ya isa ya saka na kalli maganar auren nan ma balle na kawo shi cikin rayuwata. Ki goge tunanin sun zama iyayena dan kawai sun karSin auren da ban ce ina so ba, kuma har yanzu ban so!" Ya faWa cikin fusata yana kallon ta.

Didi bata san ta tsinke shi da mari ba sai da ta ga yadda ya sake buWe ido yana kallonta idanunsa sun zama jajaye sosai. Irin fusata da fushin da yake kan fuskarsa ba dan Didi bace zai iya sha?e ko waye a kusa dashi. ?acin rai ne yake tasowa daga ?asan zuciyarsa yana mamaye ilahirin jikinsa, fusata yake ji tana shiga jininsa tana zaga ko wanne lungu da sa?o na jikinsa. Hannunsa rawa yake yi, hannunsa ?ai?ayi yake yi, ba dan Didi ba ce da yanzu ba wannan zancen ake yi ba.

Didi itama fushin ne akan fuskarta wanda bata taSa yi ba a rayuwarta, ta nuna shi da yatsa cikin rashin sanin abinda zata ce sai ta ce, "Kana bani mamaki."

Shi kam ya kasa magana kallon ta kawai yake yi, wai Didi ce ta mare shi, mari akan waWanda baya so da kuma auren da aka yi masa ba tare da yana so ba. Yadda yake huci ya kasa magana kana kallonsa ka san ya gama zuwa ?arshen Sacin rai, ji yake kamar ya zaro zuciyarsa ya cillar saboda Sacin ran da yake ji. Idanunsa har ruwan Sacin rai suka tara, ya kalle ta yana nuna kansa da yatsa ya ce. "Ni ki ka mara?." Didi tayi masa banza bata kula shi ba, ya girgiza kai sai kuma ya shafa fuskarsa, ya cize baki ya naushi hannunsa guda Waya. Jikinsa har rawa yake yi, cikin tsananin Sacin rai ya ce, "yau na tabbatar da kin fifita su a kaina! Su ki ke kallo a matsayin ?an uwanki bani ba!."


Didi cikin wani irin yanayi ta ce, "Ban fifita su akan ka ba, abinda ka ke yi ne bana so, kuma ina so ka sani, su ne iyayenka ne ko baka so!."

"Saboda auren da aka yi min ne ya saka ki ke cewa iyayena ne? Kema kin san in da ace da sani na babu wanda ya isa ya aikata hakan ko!?" Yadda muryarsa take fita ya saka ta kulle ido dan ta san ransa ya gama Saci, ta san zai iya furta ko wacce kalma akan auren, ta san zata iya ji ya furta kalmar saki akan Nayla ita kuma ba haka take so ba.

Baya tayi kamar zata faWi, Nayla da ta gama suman tsaye a wajan ta farfaWo ta ri?e Didi ta ce, "Ki zauna Didi." Kamar ta farkar dashi daga mafarki ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login