Showing 126001 words to 129000 words out of 332344 words

Chapter 43 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14442

magana akan aikin kasuwancin su da abubwan da ya shafi haka. Ya jima yana wayar har ta gama dafa jollof na superghetti ta kawo masa a lokacin ya kashe wayar. Ya kalle ta ya ce, "Abiy yana gaisheki, ya kira ki kina bacci."

Nayla ta Wauki wayarta da take gefe ta duba ta ce, "Ai kam ga kiran shi, harda Ya J." Ta faWa tana kiran Abiy, yana jinta suna waya tana shagwaSa shi dai ya Wauki abincin yana ci. Ya yi masa daWi sosai, amma cikinsa gabaWaya babu space kawai yana ci ne dan saboda kar ta ce bai ci ba.

Tana gama wayar ya kalle ta kamar zai yi magana sai ya share bai ce komai ba. ta ce, "Abiy ya ce a gaishe ka."
"Ina amsawa." Ta ?asan ido ya kalle ta ganin ita bata cin abincin ya ce, "Ina na ki abincin?." Nayla ta rausayar da kai ta ce, "kai kaWai na dafawa ai, ni bana cin abinci da daddare."

"Yau zaki fara, zo ki ci" ya faWa yana nuna mata wanda yake ci. Nayla ta girgiza kai ta ce, "Allah bana ci...." Kallon da ya yi mata yana tafiya da idanunsa kamar zai kulle sai ya buWe akan fuskarta ya hanata ?arasawa. Matsowa tayi kusa dashi a hankali ya ce, "Wauki ki cinye." Nayla da shagwaSa ta ce, "ya yi min yawa."
"Ko dai bakya cin wanda na rage?." Ai da sauri ta Wauka ta fara ci yayi murmushi mai sauti yana kallonta.

Daman bata da yawa ta cinye ta sha ruwa yana kallon ta amma bai ce komai ba. Tashi tayi ta kai bowl Win kitchen a ta dawo bata same shi ba ya tashi.

Ta kama ?ugu tana kallon Wakinsa ta ce, "Shi wai wannan haka ne soyayyar ko ne? Sai dai ya kafe ka da ido kamar zai cinyeka?." Wayarta da aka kira ya hanata cigaba da mitar da take yi a zuciyarta. Ganin Yaya Ahmad ya saka ta Wauka suka gaisa yana tambayarta tana bashi amsa cikin nishaWi. Ya Ahmad ya ce, "Ina mijin na ki? In yana nan bashi mu gaisa." Nayla ta ce, "to bara na kai masa." Katse kiran ta yi ta nufi Wakinsa.

Knocking ?ofar Wakin ta yi bata ji ya yi magana ba, sai ta buWe ta same shi a tsaye yana kallonta. Nayla ta ce, "Ya Ahmad ne ya ce na kawo maka waya za ku gaisa, Baban yayana." Baice komai ba yana daga tsaye ta kira Ahmad ta bashi suka gaisa, duk tana jin abinda yake cewa kafin ya kashe wayar ya mi?a mata. KarSa ta yi ta kalle shi ta ce, "YaMar na gode."
Ya Wage gira guda Waya yana Wan murmushi kaWan ya ce, "Da aka yi me?."
"Da ka kaini wajan Abiyna."

"Nauyi ne a kaina na yi hakan, Hankalina zai fi kwanciya in na san mahaifinki ya saka mana albarka a auren mu." Nayla ta yi murmushin jin daWi ta ce, "Na ji daWi Abiy sosai, ya daina fushi da ni." Murmushi ya yi kawai bai ce komai ba bai kuma motsa daga inda yake ba.

Nayla ta ce, "Amma ya akayi Abiy ya san zamu je? Kuma ya aka yi ka gane gidan mu?" Ta ?are maganar tana kallonsa. ?are mata kallo yake yi tun daga sama har ?asa, inda bai taSa kai idanunsa a jikinta ba a lokacin ya kai, kallon ?urilla yake binta dashi wanda bai taSa yi mata irin sa ba. Ganin kallon da yake yi mata ya saka gabanta ya yanke ya faWi, ta sunkuyar da kai tana jin yadda idanunsa suke shiga cikin jikinta. Nayla kallon ya takura ta, ta kasa sakewa dan kallon ya girmi tunaninta, ta motsa zata bar da?in ta ji ya ri?o hannunta ya ce, "Ina zaki je? Ban baki amsa ba ai ko?."

Gabanta ya faWi matu?a, ta sake yin ?asa da kai kuma bai saki hannunta ba har lokacin. Ya ce, "Muna gaisawa da Abiy sosai, kuma ni na ce masa zamu zo yau. Yayanki Jawad ma muna gaisawa dashi, baban yayanki ne ban shi ba."

Nayla ta girgiza kai bata ce komai ba, dan kallon da yake mata kashe mata baki da jikinta yake yi. Ya kamo hannunta duka biyun ya ri?e a cikin nasa ya ce, "ha??i ne a kaina na tabbatar da kowa na danginki baya fushi dake ta dalilin aurena, kamar yadda Abiy ya ce ?addarar auren mu ce a haka shiyasa hakan ya faru...."

Ya girgiza kai yana kallon hannunta, yana murza hannunta da yatsansa a hankali ya sake kallon fuskarta ya ce, "An yi nasara Jidda...! Anyi nasara a kaina a karo na farko a rayuwata. Na fara ?aunarki a lokacin da ban sani ba, na fara sonki a lokacin da ban shirya ba, na fara sonko ba tare da na farga ba, na fara sonki a lokacin da ban san yaushe na fara ba. Yaushe na fara sonki, tun wanne lokaci nake jinki a raina ban sani ba, abinda na sani ina yi miki son da bana yiwa kaina, ina ?aunarki fiye da komai a rayuwata......" ya dakatar da maganar ganin ta Wago tana kallonsa, ya Wan taSe baki ya ce, "Ke dai ban san meye a ranki ba."

Nayla ta rufe ido tana jin wani abu na tsirga mata har cikin ?wa?walwarta, ta rasa gane kan wannan bawan Allah, yanzu sai ya yi maganar da zata tsuma mata zuciya in anjima kuma ya kama bakinsa ya yi shiru.

Bata kalle shi ba sai murmushi da take yi ya ce, "FaWa min Jidda, meye a ranki? Meye ra'ayinki a kaina?." Nayla hawaye ya sakko daga idanunta, ta kalli gefensa ta ce, "Ni bana so." Murmushi ta ji ya yi hakan ya saka ta kalle shi ya ce, "ni kuma ina so, da gaske nake ina sonki Jidda, in ki ka nutsu wata?ila zaki nemo Omar a ranki, haka ne?." Murmushi ya ga tayi bata ce komai ba ya ce, "kin gani ba, murmushi ki ke yi, hakan yana nufin maganata gaskiya ce."

Nayla murmushi take yi har lokacin hawaye bai daina sauka daga idanunta ba. Shima murmushin ya ke yi ya ce, "in aka ce min zan so wata mace kamar yadda nake sonki a duniya zan ce ?arya ne Jidda, amma sai gashi ya faru. Ina sonki Jidda, ina sonki, ina yi miki so mai matu?ar yawa, in aka ce min na faWi adadin son da nake miki ban sani ba Jidda. Koda za a saka min bindiga a kaina ace na faWi adadin son da nake miki bazan iya faWa ba Jidda, sai a kashe ni. Kamar yadda babu wanda ya san adadin taurarin da suke sama, wannan wanda ya san adadin ?asar da mu ke takawa, babu wanda ya san adadin ruwan sama, haka nima ban san adadin son sa nake miki ba!."

A hankali yake maganar cikin salon da zai cusa mata ?aunarsa koda bata yi, hakan da yake yi ya gama kashe Nayla, ya gama tafiya da imaninta. Zuciyarta bugawa take yi, hawayenta sun sake yin yawa, kuka mai ?arfi yana ?o?arin ?wace mata. Shi kam Omar azalzalarsa kalaman suke yi a zuciyarsa, fitowa suke yi ba tare da ya shirya ba, shi kansa fitarsu yake ji ba tare da ya suna fitowa ba. Hakan ya saka kalaman suke fita daki-daki cikin salo na soyayya da ?auna mai tarin yawa.

Fuskarta ya Wago da hannunsa ya kalli idanunta a hankali ya ce, "Ban san daidai lokacin da ma fara sonki ba, ?ila cikin rayuwar da mu ka yi dake a gidan nan, hankalinki da nutuswarki, da murmushin ki da kuma yadda hankalina yake kwanciya in kina lafiya na tsinci kaina ina sonki. Ba shigar gaggawa ya yi min ba Jidda, sannu sannu ya ratsa zuciyata Jidda!.. Ibadarki, maganganunki, dariyarki, duk da ba shiri mu ke yi dake ba, amma suna matu?ar Waukar hankalina zuwa gare ki. Wata?ila da haka na tabbatar da ina sonki. A hankali, kuma sannu sannu, ki ka shiga cikin raina, tare da tabbacin zamanki a ciki har abada. Hmmm! Kamar yadda na faWa miki, zan iya cewa ban san lokacin da na fara sonki ba Jidda, nidai na san yanzu ina sonki, kuma bazan daina sonki ba, har abada!."

Kallon idanunsa ta ke yi cikin mutuwar jiki, hawaye yana gangarowa daga cikin idanunta. Ya saka hannunsa ya goge mata hawaye ya ce, "To meye na kukan Jidda...? Ba dai gashi Omar ya zama naki ba? Kukan na meye?." Dariya tayi mai sauti tana hawaye, ya jawo hannunta slowly ya sanya ta jikinsa ya rufe ta da dogayen hannunsa da suka zaga ko ina a bayanta.

?if ta yi, numfashinta ya je hutun rabin lokaci, ta lumshe ido jinta a kwance a ?irjin mijinta Omar, sai da numfashinta ya Wauke na wucin gadi sannan ya dawo jikinta, ta ja numfashi da ?arfi ta sauke tana jinta kamar a sabuwar duniya. Duk yadda take hasashen yadda zata ji in ta kwanta a ?irjinsa abin ya wuce tunaninta, jininta take ji kamar ana tafasa shi da soyayyar Omar. Sai ta tuna ranar da ta fara ganinsa ?aramar riga, a lokacin ta ji ina ma ya rungume ta ta ji wanne irin yanayi zata kasance, gashi hakan ya faru cikin soyayya.

Shi kansa a yanayin da yake ciki kenan, duk yadda yake ?iyasta yanayin da zai shiga in ya ji Nayla a jikinsa abin ya wuce haka, yanayin yana nema ya fi ?arfin tunaninsa da hankalinsa, ya birkice yana neman ya rasa nutsuwarsa lokaci Waya. Jinsa yake kamar a sama ana zagawa dashi sai yanayinsa ya zama kamar na mai jiri saboda yanayin ya wuce inda yake tunani. Wannan dalili ya saka ya ri?e ta gam a jikinsa, idanunsa a lumshe yana jin sabon yanayi da ?auna na ratsa ko ina na jikinsa. Soyayyarta na sake shiga jikinsa tana ratsawa ta shiga jininsa tana zaga ko ina.

Sun Wauki mintina biyar a haka, ta kasa raba jikinta da nasa, shima kuma ya kasa raba jikinsa da nata. Idanunsu duka suna rufe, babu abinda Nayla take ji sai sautin bugawar zuciyarsa a kunnenta, hakan ya yi mata matu?ar daWi dan sai ta ji babu abu mai daWin saurare kamar bugun zuciyarsa.

?arar da wayarsa ta yi ya saka shi ya Wan firgita kaWan, da hanzari Nayla ta raba jikinta da nasa shi kuma ya juya yana kallon wayar. ?aramin tsaki ya yi ba tare da ya Wauka ba, ko da ya juyo tuni Nayla ta fice babu ita babu alamunta.

Murmushi ya yi ya shafa kansa, ya zauna akan kujera ya Waga kai sama yana sake tuno yanayin da ya tsinci kansa a ciki. Numfashi ya fesar mai zafi yana ji kamar har yanzu Nayla na jikinsa, ya shafa ?irjinsa yana murmushi cikin yanayi mai daWi
KRB3P044

Nayla kamar munafuka haka ta koma, ta dinga murmushi ita kaWai kamar zararriya. A bayyane ta ce, "Ya Salam! Ni Nayla a jikin YaMar, YaMar fa mai tsadar nan, wanda ko kallo ma baka ishe shi ba, yau shine ya rungume ni da kansa. Wayyo Allah, ina zan saka kaina na ji daWi." Surutai take ta yi ita kaWai cikin tsananin farin ciki. Zama tayi akan gado sai ta mi?e tsaye tana ji kamar ta koma Wakinsa amma kunya take ji baza ta iya ba. Juyawar da zata yi idanunta ya faWa kan kyankyaso da ya shigo ta window. Nayla ta wara idanu ta daka tsalle ta fito falon tana waige.

Le?a Wakin ta yi ta ga bata ganta ba ta ce, "shikenan na shiga uku, ta shiga wani wajan." Baya ta dawo dan yanzu ko za a yankata bazata iya shiga Wakin ba indai ba kashe ta aka yi ba.

A kan kujera ta zauna ta kalli agogo a bayyane ta ce, "Bacci nake ji." Tashi ta yi ta nufi Wakinsa ta yi knocking bai amsa mata ba kamar Wazu, sai ta buWe kofar ta shiga da sallama.

Da sauri ta ja ta tsaya ganinsa a tsaye daga shi sai boxers iya cinya ko riga babu a jikinsa, rigar tana dai hannunsa zai saka. Da sauri ta rufe ido dan ?irarsa ta sa ta saka gabanta ya faWi sosai, bata taSa ganinsa a hakan ba sai yanzu. Biceps muscle Winsa a bayyane, ga six pack Winsa ya fito sosai, gashi ya lulluSe ?irjinsa. Juyawa tayi zata koma ya ce, "Ina zaki je? Sannan gargaWi na ?arshe, kar ki sake zuwa zaki shigo Wakin nan ki ?wan?wasa min ?ofa."

Nayla ta yi shiru bata ce komai ba ya ce, "juyo." Nayla murya na rawa ta ce, "to ka saka kaya." Murmushi ya yi ya lumshe ido yana jin nishaWi a zuciyarsa, yana tunanin tunda ya mallaki hankalinsa ko Didi bata taSa ganinsa a hakan ba, amma yau ga wata yarinya wacce ya raina ta ganshi a hakan kuma bai damu ba, har yana tunanin nan gaba ma ganin da zata yi masa zai zarce hakan.

"Ki juyo." A hankali ta juyo ta ce, "kyankyaso na gani a Wakina, kuma na neme shi na rasa...." Ta langwaSar da kai ta ce, "in ba a kashe shi ba bazan iya bacci ba." Shiru ya yi ta Wago ta ga ita yake kallo yana ?are mata kallo, ta sunkuyar da kai da sauri .

Sai a sannan ya ce, "mu je na gani." Gaba ta yi yana binta a baya, har suka je ?ofar Wakin. Nayla ta a ja ta tsaya ya shiga yana kalle-kalle, kafin ta ga ya ?arasa ya kulle window ya ja net Win ya rufe ya ce, "ni ban ga komai ba, ki daina barin window a buWe."

Nayla ta ce, "wallahi yana cikin Wakin nan ni na ganshi."
"Ni ban ganshi ba."
"Na shiga uku, wallahi bazan iya bacci a ciki ba." Fitowa ya yi daga Wakin ya ri?e hannunta har Wakinsa ya mayar da ?ofar ya rufe ya ce, "zaki iya bacci a nan?." Kallonsa ta yi suka haWa ido ya ce, "in baza ki iya ba...." Ya faWa yana nuna mata ?ofa.

Nayla bata da yadda zata yi dole ta samu waje ta zauna gashi ko hijjab bata Wauko ba, kuma rigar jikinta bata sauka ?asa ba kuma ?aramin hannun ne da ita. Shima yana zaune amma shi aiki yake yi ba kallon ta yake yi ba, Nayla kallonsa take yi ta ga ya jawo littafin da take yawan ganinsa a hannunsa yana rubutu alamun ba bacci ma zai yi ba. Tashi tayi a hankali ta je ta kwanta a inda ta kwanta wancan lokacin, kafin ta ce wani abun ta ga ya kashe hasken Wakin sannan ya koma ya zauna yana danan wayarsa.

Ba jimawa ta ga ya ajjiye wayar ya fita daga Wakin, jim kaWan ya dawo kai tsaye kan gadon ya nufa. Sai da ya zauna ya kalle ta ya yi murmushi yana jin nishaWi a zuciyarsa sosai. Kwanciya ya yi kamar yadda take a kwance ita dai tana jinsa amma ta kasa motsawa. Yana kallon ta ya san bata yi bacci ba bai ce mata komai ba ta ji saukar hannunsa a kafaWunta.

Idanu ta wara zata yi magana ya jawo ta gabaWaya ta dawo jikinsa ya ce, "shiiii sai da safe." Nayla zuciyarta bugawa take yi, ita tunda ta ganshi babu riga ta ga yadda Allah ya ?era shi ta tsorata da shi, ta ruWe da yanayinsa sosai ?irjinta sai bugawa yake yi. Abinda ya bata mamaki sai ta ga shi ya sake da ita kamar ba shi ba, dan in ba dan ya sake da ita Win ba da bazai jawota jikinsa haka ba.

Bugun zuciyarsa take ji a kunnenta kamar Wazu, ta lumshe ido a hankali bacci ya Wauketa. Shi kam sake zagawa da hannunsa ya yi ya ri?e ta sosai yana jin sabon farin ciki da nishaWi a haka ya yi bacci shima.

Ko da ya farka ya kalle ta ta baje gabaWaya a jikinsa tana bacci, hular kanta ya zame gashinta ya baje a ?irjinsa. Rigar jiki ta daga sama ta zame ana ganin saman ?irjin ta da yake cikin half vest. Duk da Wakin da duhu yana iya ganin komai, tsigar jikinsa ta tashi a kawo na farko da ya ga wannan halittta a bayyane a idanunsa.

A hankali ya janyeta ya tashi ya shiga banWaki ya yi alwala ya fito. Ya lura bata sallah, a iya zaman da yayi da ita ya san tana da matu?ar ibada, rashin ganin bata yi sallah a Kaduna ba da kuma da suka dawo ya tabbatar da bata yi. Bai tashe ta ba ya fita har ya je ya dawo Nayla bacci take yi.

Kusa da ita ya koma ya kwanta ya sake Wago kanta a hankali ya Wora a kan ?irjinsa yana lumshe idanu. Shafa kanta yake yi a hankali a haka bacci ya Wauke shi.

?arfe bakwai na safe fitsari ya tashe ta, ta buWe ido ta kalli a inda take kwance ta ganta a kwance Ware-Ware a ?irjin Omar da idanunsa suke a kulle. Kallon fuskarsa take yi tana murmushi, ta kai hannu a hankali ta shafa gashin fuskarsa har zuwa gashin da ya zagaye bakinsa. ?an jan gashin tayi kaWan a bayyane ta ce, "Damisa tana bacci kenan, in ta farka ba ka san me zata tashi ba, a haka dai kamar ba shi ba."

Hannunta ta janye ta mike zaune ta taSa wayarta da take gefe ta ce, "kai lokaci ya tafi" Ta faWa tana tashi da sauri ta shiga banWaki ba jimawa ta fito, ta tsaya a tsakiyar Wakin ta ce, "kenan wai ya san bana sallah kenan? To in ba dan ya sani ba ya akayi bai tashe ni ba?." Ta faWa tana kallonsa idanunsa a kulle su ke alamun bacci yake yi. Komawa ta yi ta kwanta a hankali dan kar motsinta ya tashe shi, ta zubawa fuskarsa ido tana kallonsa.

Omar yana da kyau sosai, kallo Waya zaka yi masa ka hango tsantsar kyakykyawar halittar da Allah ya yi masa, babu abinda yake burgeta a fuskarsa kamar bakinsa da idanunsa, yana da manyan ido masu ban tsoro, idanunsa zagayayyu ne wanda suka fito waje sosai. Yana da ?aramin baki mai kyaun kallo ban sha'awa. Hannu ta sake kaiwa kan fuskarsa tana murmushi kawai ta ga ya buWe ido.

Da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login