Showing 123001 words to 126000 words out of 332344 words

Chapter 42 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14396

Jawad wajan Omar ya koma suka gaisa da fara'a kamar sun saba da juna sannan ya yi masa iso zuwa ciki, ya kalli Nayla ya ce, "in kin ga dama ki ta zama." A hankali ta biyo bayansu kamar ba?uwa a gidan. Gidan yana nan yadda yake sai dai a sake yi masa fenti ya sake fitowa kamar sabo.

Apartment Win Jawad ta ga ya buWe sun shiga da Omar, ta bi bayan su a hankali ta shiga itama. Sanyin ac ya ratsa ta an gyara shi sai ?hamshi yake yi, sannan ga abinci a tray babba an ajjiye da alama dai an shiryawa zuwan na su.

Jawad ya kalli Omar ya ce, "Ku huta a nan, in ka huta sai mu je wajan Abiy Win." Omar ya ce, "da dai mun fara zuwa wajan shi."
"Shi ya ce sai ka huta, na tabbatar ka huta ka kuma ci abinci saboda gajiyar hanya." ?an murmushi Omar ya yi kawai Jawad ya kalli Nayla ya harare ta ya ce, "Sai ki yi ai" ya faWa yana fita ya bar su a falon.

Zama Nayla ta yi tana kallonsa tana mamakin ya aka yi Abiy ya san da zuwan su? Sannan ya aka yi suka saba haka da Ya J har yake masa murmushi?. Ganin kallon da take masa sai ya Waure fuska ya toshe duk wata gaSar da zata tambaye shi wani abu. Ai kuwa sai ya yi mata kwarjini, ta kasa tambayarsa amma jikinta ya gama yin sanyi sosai, bata san wacce irin tarba zata samu daga wajan Abi ba.

Fitsari take ji sosai, amma bata son tashi shi kuma bai motsa ba ya dai Wauki ruwa ya sha daga nan bai sake taSa komai ba. Nayla jin fitsarin zai hanata sukuni sai ta mi?e ta nufi ?ofar da take falon ta buWe, daman ta san empty room ne wanda ake cewa zai zama na Jalal, ta shiga tare da kullo ?ofar. Sai a sannan ya kalli inda ta shiga ya Wan murmusa kaWan bai ce komai ba.

Ba jimawa ta dawo ta zauna ta ce, "YaMar ka ci abincin, ka ga baka ci sosai ba a gida." ?ago idanunsa ya yi masu saukar mata da kasala ya Wora a kan nata idanun. Sauke idanunta ?asa ya ji tana cewa, "in na kalli idonsa wani iri nake ji, amma baya ganewa ya yi ta kallon idona" ta faWa a hankali ba tare da ta yi tunanin ya ji ba. Bai nuna mata ya ji Win ba ta ce, "ka ci abincin."

Bai ce komai ba ya dai sauke ajiyar zuciya amma bai yi magana ba sai kallonta da yake yi. Nayla ta turo baki kanta yana ?asa amma bata yi magana ba. Yana lura da duk motsinta magana ce kawai bazai yi mata ba, bai shirya maganar ba ne sai sun je wajan mahaifinta sun dawo, daga lokacin duk ma abinda take so ya ce zai ce mata, amma yanzu bazai ce ba.

Yadda ya yi shiru haka ta yi shiru itama tana kallon falon sai kuma ta Wan zame ta kwanta dan ta gaji sosai. Jawad ne ya shigo da sallama ya ce, "Omar zamu je masallaci?" Ya faWa da sigar tambaya. Omar ya mi?e tsaye ya ce, "na ji ana kiran sallah." Jawad ya kalli Nayla ya ce, "Ke wai baza ki shiga cikin gidan ba? Jalila da Jalal suna nan, Mama ce bata nan." Nayla bata ce komai ba Jawad ya yi tsaki suka fita da Omar Win.

Tana nan zaune Jawad ya dawo shi kaWai ya ri?o hannunta ya ce, "Sai wani War War ki ke yi kamar ba?uwa, Omar Win ma ya fi ki sakewa, meye haka ne wai?." Nayla ta ce, "Yaya J ni ban san nan zamu zo ba, Ina tsoron haWuwa da Abiy." Jawad ya mi?ar da ita tsaye ya ce, "Wuce mu je, shi suna tare da Abiyn ma."
"Da gaske ka ke?."
"Mu je ki ga zahiri." Tare suka fito zuwa babban falon Abiy kanta yana ?asa.

Abiy yana zaune akan kujera Omar yana zaune a kan carpet suka shigo, a hankali take takowa tana shigowa falon cikin sanyin jiki da faWuwar gaba. Abiy yana kallo ta yana murmushi ganin kanta yana ?asa kuma kuka take yi ya ce, "Mamana ke dai kin cika yawan kuka, ko gidan nan ne bakya son zuwa?." Nayla jin muryar Abiynta cikin salo na wasa ta Wago da sauri ta kalle shi ta ga yana murmushi yana kallonta.

Murya na rawa ta ce, "Abiy." Abiy ya ce, "Na'am Mamana." Da sauri ta ?arasa kusa da shi ta zube a gabansa ta Wora kanta a akan ?afarsa tana kuka sosai. Abiy ya Wora hannunsa akanta ya ce, "Haba Mamana to meye na kukan kuma? Tashi ki goge hawayenki bana son kuka kin sani." Kai ta girgiza ta ce, "Abiy fushi ka ke yi dani, Abiy na daWe ban ganka ba."
"Ni bana fusui da ke Mamana, kuma ba ga shi yanzu kin ganni ba? Ki bar kuka ki tashi mu gaisa ko?."

Nayla ta Wago kai tana kuka Abiy ya ri?e hannunta ya ce, "goge hawayenki ki zauna sosai, kar kan ki ya yi ciwo kin ga kun yi tafiya mai nisa." Zama tayi amma bata saki hannunsa ba, Abiy ya yi murmushi ya ce, "to sakar min hannun mana Nayla." No?e kafaWa ta yi tana kifta idanu kamar yadda ta saba gashin idanunta da ya jike da hawaye.

Kallon Omar Abiy ya yi ya ce, "Kana fama da Mamana da wannan shagwaSar ta ta." Murmushi ya yi kawai dan shi a duniya babu wanda ya ke jin nauyinsa da girmansa kamar Abiy, baya shi sai su Daddy. Abiy ya ce, "Ina fatan komai lafiya?." Omar ya ce, "Lafiya lau."
"Haka ake so, Allah ya taimaka ya bada nasara."
"Amin ya rabbi."

Omar ya daure ya ce, "Abubuwa da yawa sun faru a baya, da yadda aka yi auren nan da yadda komai ya faru kusan duk bai yi daWi ba. Alhaji na san kana fushi da ita, ka aura mata ni ne ba dan kana so ba sai dan dalilin da ni da ita bamu sani ba, Gata na dawo da ita Alhaji, koma meye ya faru ina ro?on alfarma a yafe mata."

Abiy ya yi murmushin jin daWin kalaman Omar ya ce, "Omar kar ka sake kirana da Alhaji, ka ce min Abiy kamar yadda take faWa ita da ?an uwanta. Ko babu Nayla ni kamar uba nake a wajanka." Omar ya yi murmushi amma bai ce komai ba.

Abiy ya ce, "Tabbas da farko na Waura auren ku da Nayla a cikin wani yanayi na zafin zuciya, Nayla ta san halina in raina ya Saci na kan aikata abinda ma ban san na yi ba. Amma daga baya na amince da auren ku da ita Wari bisa Wari, domin kuwa duk motsin ka kai da Nayla na sani, ko fita Nayla ta yi ta je gidan Hajja zan sani. Yadda ka ke bata tsaro da kulawa ya sa naji hankalina ya kwanta da zaka ri?e Nayla hannu biyu, duk da baka sonta, kuma baka son aurenta."

Omar ba tare da nauyin komai ba ya ce, "Abiy wannan duk labarin baya ne, tabbas a baya ban karSi aurenta da son raina ba sai dan an yi min dole. Amma a yanzu ko da ace babu aure a tsakanina da ita zan iya zuwa ko ina dan neman aurenta. Zan Sata adadin lokacin da ya rage min a duniya wajan rayuwa da ita."

Abiy ya yi murmushi cikin jin daWi, daman Daddy ya bashi labarin duk abinda ya faru kuma ga zahiri shima ya gani. Abiy ya ce, "ma sha Allah, haka na ke fata kuma haka nake so na ji Omar. Alllah ya sanyawa auren ku albarka, Allah ya ba ku zaman lafiya mai Worewa."

Abiy ya kalli Nayla da take kusa dashi har lokacin ya ce, "Mamana." Nayla cikin shagwaSa ta ce, "Abiy ka daina fushi da ni?."

"Ni ba fushi nake yi dake ba Nayla, da farko na Wan yi fushin amma daga baya na fahimci komai da yadda komai ya faru. Sai na barki ki mallaki abinda zuciyarki take so, na tabbatar aurenki dashi shine zai baki farin ciki tunda har ki ka iya furta min kina qaunarsa. Abinda ya saka na ji na sare a game da lamarin auren lokacin da na tabbatar bai karSi aure ki ba, ko yaushe tunani nake yi a wanne hali ki ke. Amma daga lokacin da yake baki tsoro da ?arfinsa da zuciyarsa na san baza barki ki zubar da hawaye a gidansa."

Nayla ta ce, "Amma Abiy meyasa lokacin ka yanke hukunci bayan na ce na fasa?." Abiy ya yi murmushi ya ce, "Lokacin da ki ka bar falon nan a ranar kika tafi Kano ba kin ce Maman ki ce ta ce ki je ba?." Nayla ta Waga kai ta ce, "Mama ce, itace tace na je zan fi samun nutsuwa kafin na dawo, sannan zata saka ka amince da abinda na ce."

Abiy ya ce, "Kuma ita ta ce ki yi min text."
"Eh Abiy, amma da na je sai na tarar an yi hacking WhatsApp account Win dan cewa tayi nayi maka ta whatsapp, sai da muka dawo dashi ni da Salma. Ban kai ga yin message Win ba na ajjiye wayar da na duba naga an sake yin hacking Winsa, sai da na dawo dashi sai na yi maka message Win."

Abiy ya shafa kanta yana murmushi ya ce, "Yanzu kina farin ciki da auren ko bakya yi?." Nayla ta yi murmushi ta kalli Omar da yake kallonta amma ta ?asa idanu sai ta sunkuyar da kai.

Abiy ya yi murmushi ya ce, "komai ya wuce ki Wauka daman haka ?addarar aureki take, Allah ya rubuta a lokacin sai kin zama matar Omar shiyasa komai ya zama a haka. Inda mutuwa ce haka zaki ji ana faWa Nayla ta mutu ba shiri, to haka aure ma indai rabon auren yayi kira ka amsa zance ya ?are. Ina matu?ar alfahari da auren nan na ku, Ina kuma fatan ya Wore daga nan har aljanna."

Nayla ta sunkuyar da kai tana murmushi cikin jin daWi da farin ciki. Ta kalli Abiy da shagwaSa ta ce, "Yanzu zan iya zuwa gidan nan ko yaushe?" Kafin ya bata amsa ta cigaba, "Abiy ka ce kar nazo maka gida sai ka neme ni, na daWe ban ganka ba" ta faWa cikin rauni. Murmushi yake yana kallon ta, kafin ya girgiza kai ya ce, "Nayla na ce komai ya wuce, ki Wauka komai bai faru ba, kuma ba gashi yanzu kin ganni ba?." Ta Waga kai ya yi dariya ya kalli Omar ya ce, "Omar ya kasuwancin na ka?." Omar ya ce, "Alhamdu lillah Abiy."
"Haka ake so." Nayla ta kalli takalmin ?afar Abiy ta ce, "Abiy takalmin ?afarka ma product Win mu ne." Abiy ya kalli ?afarsa ya kalle ta da mamaki ya ce, "Da gaske?." Nayla ta ce, "Allah da gaske."
"Shagon ku na je wancan satin sai na ganshi ya burge ni sai na ce a bani, ai ban san na ku bane."
"Eh Abiy, ina bayar ana kawowa, ana siyansa sosai a nan Kaduna."

Abiy ya ce, "Ma sha Allah. Omar Ashe haka takalman na ku suke da kyau?." Omar ya yi murmushi bai ce komai ba. Abiy ya ce, "Abinda zai faru mu ma a fara kawowa storea Win mu, na tabbatar za a siya sosai. Zan yi waya da wanda zai zo ya karSa, za a raba states Win da shopping complex Win suke. Amma muna son pieces da yawa gaskiya, dan wannan takalman da wuri za a neme su a rasa." Omar ya yi murmushi ya ce, "i sha Allah."
Abiy ya ce, "gaskiya takalman suna da kyau, babu wanda zai ce na gida ne kuma hannu ne yake yi. Allah ya ?arawa nema albarka."

Omar ya ce, "Amin ya rabbi, An gode Abiy." Jawad ne ya shigo Abiy yake yi masa maganar takalmin har yake nuna masa. Jawad ya ce, "Nima da na Wauka sai da abokai na da yawa suka siya, gaskiya yana da kyau sosai. Omar Allah ya ?aro kasuwa." Ya amsa da amin amma baya ?ara ko wacce magana daga amin Win nan.

Omar ya kalli Abiy da girmamawa ya ce, "Abiy zamu koma Kano." Abiy ya ce, "da wuri haka? Na Wauka sai gobe."
"Ba mu taho da shirin kwana ba, daman mun zo ne dan ka saka mana albarka kuma mun samu, na kawo ta dan mu tabbatar da ka daina fushi da ita da auren gabaWaya." Abiy yayi murmushin jin daWin kalaman Omar, hakan da ya yi ya ?ara masa girma a idanun abiy sosai. Abiy ya ce, "Ai kam gwara ku tafi, ban cika son tafiya in dare ya yi a hanya ba." Nayla ta ce, "Abiy Ina Mama?."
"Bata nan ta fita, gashi har zaki koma baku haWu ba. Amma na san zaku dawo ai." Nayla ta ce, "na so na ganta."

Nayla ta mi?e ya shiga ciki dan ta yi missing Wakinta. Sama ta hau ta shiga Wakin ta komai yana nan yadda yake har kayan ta akwai ragowa a cikin wardrobe. Jalila ta shigo suka rungume juna suna ta murna, Nayla ta ce ta bata pad ta Wauko mata ta canja, duk abinda take so sai da ta Wauka sannan ta sakko. A tsaye ta same shi shida Jawad suna hira kamar sun san juna, ta ga dai ledodin company su Omar a hannun Jawad amma bata san meye ba, sannan ga apples da manyan watermelons a ajjiye, Nayla bata ka kawo a ranta Omar ne ya kawo ba ta ?araso wajan.

Abiy ta gani ya fito da kansa dan yi musu rakiya; Nayla ta rungume shi ya dafa kanta ya ce, "Allah ya kiyaye hanya, in na shigo Kano zan zo har gidan na ku in sha Allah." Nayla ta ce, "Abiy ka gaishe da Mama don Allah, ina ta kiranta bata Wauka."

"In sha Allah zan faWa mata." Abiy ya kalli Omar ya ce, "Omar Allah ya kiyaye hanya." Omar ya Wurkusa har ?asa a karo na farko a rayuwarsa yana yiwa Abiy sallama amma Abiy ya mi?a masa hannu dole suka gaisa.

Jawad ya ce, "Abiy ga sa?o Omar ya bayar na ka da Mama harda ni ma." Abiy ya yi murmushi cikin farin cikin da ya mamaye masa zuciya ya ce, "Omar harda hidima kamar ba?o?."
"Babu yawa Abiy, a saka mana albarka."
"Mai yawan kenan, an gode sosai, Allah ya ?arawa nema albarka."
"Amin Abiy, Mu ne da godiya, mun gode Allah ya saka da alkhairi ya ?ara girma."
"Amin ya rabbi, Allah ya kiyaye hanya."
"Amin ya rabbi."

Nayla tana jikin Abiy har lokacin ya ce, "To Nayla, a gaishe da Hajja." Nayla ta ce, "Zata ji Abiy."

Ma'aikatan gidan ne suka zo wajan ganin Abiy yana tsaye, ya kalle su ya ce, "Ga mijin Nayla fa, na san ba ku san shi ba." Nan da nan aka fara gaisawa da Omar yana amsawa. Kusan ma'aikatan gidan kaf sai da suka zo suka gaisa kafin su tafi. Mota ta shiga daman shi ya jima a ciki aka buWe musu gate suka fita daga gidan.

Abiy ya kalli Jawad da yake ta murmushi ya ce, "Hundred percent na amince da auren Nayla da Omar, ?addararta alkhairi ta zaSa mata." Jawad ya ce, "Daman ni Abiy tun farko na amince dashi sosai, na tabbatar da baza ta yi kuka a aurensa ba. Allah ya basu zaman lafiya." Suka amsa da amin Abiy ya koma ciki.
KRB3P042

Tafiya suke yi Nayla na murmushi, ko babu komai ta san yanzu mahaifinta baya fushi da ita kuma ya sakawa aurenta albarka. Farin ciki take ji sosai yana ratsa sassan jikinta ta kasa Soye farin cikin ta. Shi dai yana kallon ta dan shi kansa yana jin farin ciki, ko babu komai ya sauke wani nauyi da ya ke a kansa, ya kuma tabbatar da mahaifinta yana goyan bayan aurensa da ita.

Bata yi magana ba shima kuma bai yi ba, haka suka tafiya motar shiru ko radio babu balle ta Wauke musu kewa. Kowa bugun zuciyarsa yake ji a kunne sa bayan wannan dukkan su sun kasa furta komai.

Sai yamma sosai suka shiga Kano, a ?ofar gate yayi parking ta Wauki jakarta shiga cikin gidan. ?aki ta wuce kai tsaye tayi wanka ta canja kaya ta zauna da niyar ta huta bacci ya Wauketa. Sai bayan magriba ta farka ta tashi tana yamutsa fuska ta kalli agogo, ganin lokaci ya tafi sosai ya saka ta mi?e ta koma Waki ta sake yin sabon wanka ta shafe jikinta da turare ta saka kaya marasa nauyi ta fito falo.

Tana fitowa yana shigowa suka haWa ido, sai ta yi murmushi ta ce, "Sannu da zuwa." Murmushin shima ya yi mata amma ya Wauke kai daga kallonta ya ce, "Yauwa, k????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
in sha bacci." Nayla ta yi murmushi ta ce, "ban san ma nayi baccin ba, me zan dafa maka?." Kai ya girgiza mata ya ce, "ki bar shi." Nayla ta kwaSe fuska cikin shagwaSa ta ce, "Haba YaMar, wai ban iya girki ba ne ya saka baka son cim abincina ko kuma laifi nayi maka? Ko yaushe na ce ga abinci sai ka ce baka ci."

Yadda take maganar da muryar da take amfani da ita kamar zata yi kuka ya saka ya kalle ta ya Wauke kai bai ce komai ba. Ta matso kusa dashi ta ce, "ka faWa min abinda zan dafa maka." Ya lura da farin cikin Wazu yana nan a kan fuskarta, ya ce, "kin gaji, ba sai kin yi girki ba."

"Ai na huta tunda na yi bacci, ka faWa min abinda zan girka maka." Shiru ya yi dan bai san me zai ce ba, shi baya jin yunwa amma in ya faWa ya san baza ta amince ba. ?hamshin turarenta gabaWaya ya gama kashe masa jikinsa, ya kulle ido ya buWe, kafin ya yi magana ta ce, "Ka faWa min."

Ajiyar zuciya ya yi ya kalle ta ya ce, "ki dafa duk abinda ya yi miki." Murmushi ta yi ta ce, "To" ta faWa tana juyawa ta shiga kitchen ya bita da kallo yana kulle idanunsa. Waya aka yi masa ya Wauka ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login