Showing 156001 words to 159000 words out of 332344 words

Chapter 53 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

30863

da babu abinda na sani, bana tunanin zan iya koda karatun sallah. To Didi hana ni sakewa ta yi, gashi bana iya yi mata musu, shima kuma marigayin bana iya ja da magarsa, na jima ina karatu a wajansa har na sauka nayi, daga baya ne na gudu."

Nayla ta sake yin dariya sosai? ta ce, "ba sai ka koma ba." Ya Wora yatsunsa biyu na farko a goshinsa ya Wan sosa da guda Waya, ya kalle ta ya ce, "Ina attending online a yanzu haka. Ni ai babu mai iya zama dani ido da ido har ya koyar dani, sai dai ke Win, in baza ki tuna min ba shikenan kin huta. Kuma fa iyawa ne ban yi ba, na iya fiye da ke, wahalar karantawa wani wajan yake yi min."

Nayla ta sake yin dariya ta ce, "ni na isa? Ka yi ha?uri zan tuna maka. Daman alkur'ani haka yake, in ka barshi da kwana Waya zai barka da sati, in ka barshi da sati zai barka da wata, in ka barshi da wata zai barka da shekara, in ka bar shi da shekara zai barka har abada."

Kai ya girgiza ya ce, "balle ni bai bar ni har abada ba kuma bai bar ni da shekara ba, da ne bana karantawa saboda Wabi'ar da na saka a gaba, shiyasa haddar da na fara duk ta zube, amma daga baya an godewa Allah. Tunda har nayi register da kuWina na shiga ajin ai na san abubuwa sun canja" ya faWa yana Wan murmushi. Nayla ta wara ido ta ce, "daman ka fara haddar alku'arni?." Harararta ya yi ya ce, "ban sani ba."

Dariya tayi sosai ta kwanta a jikinsa ta ce, "sorry my love." Ya yi murmushi ya ce, "A'a,YaMar." Ta yi murmushi ta ce, "Sorry YaMar." Kissing Win lips Winta ya yi bai ce komai ba. Waya aka yiwa masa ya Wauko yana kallon wayar ya dafe kai ya ce, "tun Wazu ake kirana da wannan number, in na Wauka bana gane yaren da ake yi." ?auka ya sake yi ya saka a speaker, ana fara magana zai kashe Nayla ta karSa suka fara magana da matar.

Bayan sun kammala ta kalle shi ta ce, "Shugabar wani babban store ce daga garin Abetuka, tana so ka bata dama tana so ku haWu zata fara karSar kayanku tana kaiwa garinsu. Pidgin English take yi shiyasa baka ji, nima dan na zauna da su a school ya saka na Wan iya kaWan." Ya taSe baki ya ce, "to ni English Win ma na iya ne balle wani pidgin? Yanzu yaushe zata zo?."
"Kai zaka bata time."
"Zan gani" ya faWa tana cigaba da danna wayarsa ko a jikinsa.

Nayla ta ce, "Amma YaMar ya kamata ace ka faWaWa english Winka, ba a san inda wannan aiki zai kai ka ba. Zaka iya haWuwa da turawan da suke son kayan nan, kuma ka ga dole sai da english za a yi magana dasu." Ya kalle ta ya ce, "ke ba kin iya ba?." Nayla ta ce, "na iya."
"To kin iya mana, bani da ra'ayi kuma bazan yi ba." Nayla ta yi shiru dan ta san bazai yi Win ba ta koma jikinsa ta kwanta ya ce, "Tashi mu je gidan Didi." Ta amsa da to ta tashi hijjabi kawai ta saka suka tafi.

Yana ajjiye motar AbdulHamid yana fitowa daga gidan zai tafi masallaci. A nan suka gaisa shida Omar suka wuce masallaci ita kuma ta shiga gidan. Tana zaune suna hira da Didi duk da kunyarta take ji, amma sai ta ga Didi bata tambaye ta komai ba sai itama ta basar suka cigaba da hira. Suna cikin hirar suka dawo da sallama, suna shigowa Umma ta tashi ta shiga Waki su kuma suka zauna.

Didi ta kalle shi kafin ta yi magana ya ce, "Didi ina yini." Ta yi murmushi ta ce, "lafiya lau Omar, ya ka ke?."
"Lafiya. Ina Marmerh?." Didi ta ce, "gata a hannun Nayla, zaka iya Waukar ta Win ne?."
"Tsoron Waukarta nake ji Didi."

Ta yi dariya kaWan bata ce komai ba, Omar ya kalli AbdulHamid ya ce, "ni daman wajanka na zo." AbdulHamid da murmushi ya ce, "to Allah ya sa lafiya."

"Godiya zan yi maka akan abubuwan da suke ta faruwa, na gode."
"Me ya faru?."
"Komai ma" ya faWa ba tare da ya kalle shi ba. AbdulHamid ya yi murmushi ya ce, "to ni dai ban san me ya faru ba Omar, nima kuma na gode da ka bani auren Yayarka." Kallon ?asan ido ya yi masa kamar zai yi magana sai kuma ya share bai ce komai ba yana taSe baki.

Omar ya kalli Nayla da take ta wasa da Marmerh ya ce, "Sai na ce ki bani Marmerh sannan zaki bani?." Nayla ta kalle shi da mamaki ta ce, "in na kawo ta baka ce ba cewa zaka yi ai baka ce ba shiyasa." Harararta ya yi, ta girgiza kai ta mi?e ta mi?a masa ita, ya zaunar da ita a kusa dashi bai ce komai ba.

? ?? Ita kuma wallahi kunyar Didi take ji ga mijinta a zaune shi kuma ko a jikinsa. Didi ta yi dariya tana kallonsu ta ce, "YallaSai mu yi masa gori don Allah, mu tuna masa abinda ya wuce. Na ga alama kansa yana rawa, ya manta mun san dawar garin, ba dan mu ba da yanzu bai yi rawar kan nan ba." AbdulHamid ya yi dariya ya ce, "A'a babu ruwana."

Shi ma Omar Win murmushi ya yi dan ya san dashi take, tana magana akan aurensa da Nayla da yadda ya dinga tijara a kai. Ya ce, "Yauwa, ya batun gidan hayar nan da muke ciki ne? Yaushe kuWinsa zai ?are?." Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Ai da yake na faWa maka gidan abokin YallaSai ne, da ya ji Wan uwana ne a gidan sai ya ce kawai ya bar gidan har sai nan shekara biyu sai a sake biyan kuWin. Dan haka yanzu sai wata shekarar in Allah ya nuna mana."

Harararta yake yi cikin kallon kin raina min hankali, ya haWe fuska kamar ba shine yake murmushi ba ya ce, "kin san ban yarda da wannan karatun na ki ba ko? Kamar ya an barshi har shekara biyu a naira dubu Wari biyar? Wannan gidan ne za a bayar a haka?. Didi wai mai ?aramar ?wa?wala ki ka mayar da ni ne?." Didi ganin zai fara halin nasa sai ta ce, "kwantar da hankalinka ai ba ?arya nake yi ba, ga yallaSai ka tambaye shi ka ji. Ba haka aka yi ba?" Ta faWa tana kallon AbdulHamid tana yi masa alama da ya amsa.

AbdulHamid babu yadda zai yi dole ya yi ?arya ya ce, "Haka ne Omar, muna mutunci dashi sosai shiyasa ya yi haka."
"To ban nema ba, bana so ko kaWan, ni na tsani ace za a yi min alfamar a rayuwata. Nan gaba tsaf za a yi min gori, gwara maganin kada ayi kada a fara. Bani number shi" ya faWa yana Wauko waya a aljihunsa har lokacin Marmerh tana hannunsa.

AbdulHamid ya kalli Didi alamun kin ga maganin masu ?arya ko kafin ya ce, "Da yake ba ya ?asar, amma zan turo maka number da yake amfani da ita ta whatsApp." Kallon su yake yi duka su biyun bai ce komai ba. Didi da ta san kallon na meye sai ta ce, "ka daina zuba min wannan idanunun naka don Allah, baka yarda ba ne?." Kai tsaye ya ce, "Wallahi ban yarda ba kin ji na ce wallahi, akwai abinda ku ka ?ulla keda mijinki akan gidan nan."

Didi ta ce, "me zamu ?ulla baka sani ba? Kai a ?ulla abu ma baka sani ba ai babbar masifa ce. Babu abinda mu ka ?ulla, gaskiyar kenan." Omar ya ce, "to haWa ni da mai g1dan."
"Baka ji me ya ce maka ba ne ba? Ba ya Nigeria."
"Ko?" Ya tambaya yana kallonta. Gaban Didi ya faWi dan bata son ya gano da wuri ta ce, "eh mana."

Yatsunsa ya Wora akan goshinsa yana Wan motsa su a hankali kafin ya kalle ta ya ce, "kin san me? Ni na fara tantama akan gidan gaskiya." Didi ta ce, "ka cika rigima wallahi, to me ka ke tunani bayan wannan? Ka san dai bazan cutar da kai ba" sai ta katse maganar ta ce, "Kai ni na ga kun sake buWe shago, da na gani na ce shine Omar ko labari" ta faWa tana kawar da waccan maganar. Hakan da ta yi ya saka masa zargi a zuciyarsa, ya kafa mata ido yana nazari ita kuma ta?i kallonsa.

Ganin ya yi shiru bai ce komai ba sai Didi ta ce, "Marmerh ce ma bata Wan jin daWi, gobe zan kai ta asibiti." Sai kuwa ya kalle ta ya ce, "me ya same ta?." Didi ta ce, "mura take yi, kuma Wan yawon da muka yi ne kwana biyu." Ya dafa goshin Marmerh da take hannunsa ya ce, "kuma shine baki kai ta asibitin ba har sai gobe dan mugunta?." Didi ta ce, "Babban asibiti nake son zuwa, kuma ka ga gobe Monday."
"Baki da damuwa ne in wani abu ya same ta" ya faWa kai tsaye kamar shine mahaifin yarinyar.

Didi ta yi dariya ta kalli Nayla da ta daina magana ta ce, "Nayla kin koma shiru kamar ba ke ba." Murmushi ta yi kawai bata ce komai ba. Omar ya kalli Nayla ya kalli Didi sai ya ce, "Zamu tafi gida." Nayla ta karSi Marmerh a hannunsa suka fita shida AbdulHamid.

? ? Didi ta ri?o hannun Nayla bayan sun fita ta ce, "Nayla ba ki ga tunda Omar ya shigo Umma ta koma Waki ba?."
"Na gani Didi."
"Duk da daman in yallaSai yana nan ta fi zaman Waki, amma yanzu saboda Omar ta koma. Tana tsoron Omar ya yi disgracing Winta a gaban sirikinta shiyasa ta koma, wallahi dan ta yiwa Omar magana ya yi mata banza ko ya harareta kaWan ne daga cikin halinsa. Nayla zan Wora miki wani nauyi, a yanzu Omar bashi da wacce ta fiki, sannan ba shi da wacce yake so kamar ki, bashi da wacce yake ji a zuciyarsa kamar ki. Don Allah ki dinga convincing Omar akan dangin iyayenmu, ki dinga nusar dashi wannan banzar zuciyar da fushin da yake yi dasu babu inda zai kai shi sai dana sani. Yanzu Nayla a duniya muna da wanda suka fi su ne?."

Nayla ta girgiza kai alamun a'a ta ce, "Fuskar Umma Saroot kika kalla zaki tabbatar ita jinin mu ce, amma baya ?aunarsu gabaWaya. Hana rantsuwa ya yi mata godiya ranar da ba ku da lafiya shima kuma ni na ce, amma duk da haka saboda ke ya yi mata godiyar. Na san ta dalilinki zai iya canjawa tunda yana sonki, don Allah ki taimaka min Nayla, wannan ne kawai burina da rage min a duniya a yanzu. Daman burikan nawa bai wuce Omar ya shiryu, ya yi aure, ya zauna dake lafiya ba. Duk Allah ya cika min waWannan, wannan burin kawai ya rage min Nayla." Nayla ta ce, "Didi anya zan iya? Kin san halinsa sarai, nima ba ?yale ni zai yi ba."

"Ke fa mace ce, kin san ta yadda zaki je masa da maganar, kin kuma san a daidai lokacin da zaki yi masa maganar. Koda ya yi fushin dake akan maganar zai sakko saboda tasirinki a gare shi. In kina yi masa maganar yana yin fushi wata rana zai daina. in ya yi faWan yau, ya yi gobe, jibi bazai yi ba. Ina jin tsoron na bar duniya ba tare da Omar ya gyara zumuncin dake tsakaninsa da iyayensa ba, shine kawai burina a yanzu, ki taimaka ki cika min shi Nayla. Yana sonki, zai ji maganar ki sama da maganar kowa a duniya. Ba iyaye ne dashi ba balle a ce zai ji maganarsu a sama da ta ki, tunda babu su ke ce a kan gaba Nayla." Nayla tayi ajiyar zuciya ta ce, "in sha Allah zan gwada Didi, Allah ya bani iko."
"Amin Nayla, mu je na raka ki." Tare suka fito har ?ofar gidan, ta karSi Marmerh ita kuma ta shiga mota suka tafi.
KRB3P056

Tunda suka tafi bai ce komai ba, ta lura maganar Didi akan gidan nan ta Wan taSa ransa kuma bai yarda da abinda ta ce Win ba. Tsaki ya yi kaWan ya ce, "Didi tana raina min hankali." Daga nan bai sake cewa komai ba har suka je gida suka tarar da masu gadin gidan suna nan. To masu gadi mana, kullum suna nan sai dai in bai fita da mota ba. Suka buWe gate Win ya shiga da motar ta fita ta shiga cikin gidan.

Ba????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? i shigo ba sai da ya siyo mata kayan ciye-ciye dan ba su ci abinci ba. Ta ci kaWan dan bata son cin abinci da daddare, jikinta na da saurin karSar kiSa amma bashi da saurin karSar rama. Sai da ta gama ta tashi ta shiga Waki ta yi wanka ta saka Pyjamas kamar yadda ta saba kullum, ta zauna a kan gadon tana danna wayarta.

Kiransa ne ya shigo wayarta,ta Wauka kafin ta yi magana ya ce, "zo." Abinda ya furta kenan ya kashe wayar ta tashi ta nufi Wakin. Tana buWewa gabanta ya faWi, dan tun ranar da abin nan ya faru bata sake shiga Wakinsa ba dan tsoron ma Wakin take ji. Frame Win da ta ajjiye yana inda ta bar shi har yanzu, ta kalli wanda ta saka ta ga yadda ya yi kyau a Wakin sannan ta kalle shi.

"?araso mana" ya furta ba tare da ya kalle ta ba. Yana lura da ita, ya san a tsorace dashi shiyasa take baya baya. Ta ta ?araso Wakin bayan ta kulle ?ofar. A Warare ta zauna ta ce, "gani."
"Ai na ganki" ya faWa yana cigaba da lissafin da yake yi. Kamar bazai magana ba sai kuma ya ce, "me ya canja ki yau?." Ta kalle shi ta ce, "me ka gani?."
"Yau babu taya ni hira kin yi tafiyarki." Nayla ta ce, "na ga kamar ranka a Sace yake ne shiyasa."

"Ni haka na ce miki? Haka na ke Sacin rai cikin sau?i daman?" Ya faWa yana shan ruwan da yake gefensa ba tare da ya kalle ta. Kafin ta yi magana ya ce, "kawai akwai abinda yake zuciyarki, zo ki faWa min" ya faWa yana ajjiye wayar hannunsa yana mi?o mata hannu. Gabanta ya faWi sosai ta runtse ido ta buWe, ta mi?a nata hannun a hankali ya ri?eta ya ?araso da ita inda yake ya zaunar da ita a jikinsa ya ce, "faWa min, me ya canja ki yau?."

Nayla ta sunkuyar da kai ta ce, "babu komai."
"Ni fa bana son ?arya Jidda, ki faWa min abinda yake zuciyarki mana" ya faWa yana cire hular kanta ya zame ribbon Win kanta gashin ya sauka a fuskarsa ya lumshe ido yana sha?ar ?hamshin gashi. Nayla ta yi shiru bata ce komai ba dan tsoronsa take ji shiyasa ta kasa sakewa.

?? Hannunsa ta kalla ta ga inda ya Wan ?one da ruwan zafin har wajen ya yi ba?i, ta Wan shafa wajan sai ya buWe ido ya kalle ta kamar zai magana sai ya share ta dan so yake ya ji ta yi magana. A ?irjinsa ta kwanta tana sauraron abinda ta fi ?auna wato bugun zuciyarsa, ta kulle ido dan itama ta ta zuciyar bugawa take yi kamar zata fashe saboda tsoro.

Shirun ta ji ya yi yawa bai ce komai ba, shi kuma daga kwance gashinta da ya yi bai sake yi mata komai ba yana dai ri?e da ita idanunsa suna kulle. Jin shiru bai sake yi mata wani abu ba sai ta saki jikinta, ta saka a ranta babu abinda zai faru ta ce, "a ina ka samu wannan ciwon? Na san dai babu shi a hannunka."

Ba tare da ya buWe ido ba ya ce, "Ranar mu ta farko, daren mu na farko, lokacin mu na farko. A lokacin da nake ?o?arin na taimaka miki ruwan zafi ya taSa ni. Na manta akwai water heater a banWakin, hankalina ya gushe burina kawai ki dawo daidai. Na ji daWi da na samu tabo, kin ga in dai zan kalle shi zan tuna da wannan dare mai cike da nishaWi da ruWani."

Nayla bata ce komai ba ta yi shiru dan bata da amsar da zata bashi, lallai kuwa daren ruWani, daren da ta Wauka a kabari zata wayi gari, bata Wauka zata cigaba da rayuwa kamar kowa ba. FaWin irin wahalar da ta sha a hannunsa Sata baki ne, ita kaWai ta san abinda ta ji shiyasa take matu?ar tsoron ranar da za a sake maimaitawa.

"YaMar bacci zan yi" ta faWa a rarrabe tana kallonsa. Ya buWe ido ya kalle ta ya ce, "meye yake baki tsoro ne haka? Muryarki ta yi kama da ta wacce take cikin tsoro, faWa min meye?." Ta girgiza kai ta ce, "babu komai, bacci kawai zan je na yi."
"A ina?."
"?akina."
"A'a, a nan zamu kwana yau." Ta kalle shi suka haWa ido ya Waga mata gira ya mayar da idonsa ya kulle. Duk da tana cikin tsoro amma girarsa tana burge ta matu?a, gata a cike ma sha Allah kuma gata ba?a sosai.

BuWe ido Waya ya yi ya kalle ta suka haWa ya ce, "ki cigaba da kallona ma." Sai ya bata kunya, ta sunkuyar da kai tana murmushi ya mayar da ido ya rufe ya hanata tashi kuma shi bai motsa ba. A hankali ta ce, "to zan kwanta a kan gadon." Sakinta ya yi ta mi?e har da kashe hasken Wakin sannnan ta kwanta a takure saboda tsoro.

Shi kuwa yana yadda ta bar shi bai motsa ba, baya so ya je inda take ki kaWan, dan in ya je a yanzu tabbas za a samu matsala babba, shiyasa ya zauna har lokacin bai motsa ba kuma bai buWe ido ba. Sai da ya gaji da zaman ya tashi ya je ya kwanta ba tare da ya kai hannunsa inda take ba, dan gaskiya in hakan ya faru akwai matsala, shi kuma baya so ya sake yin abinda zai cutar da ita.

? ? Ba zato babu tsammani ya ji ta dawo jikinsa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login