Showing 30001 words to 33000 words out of 332344 words

Chapter 11 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14424

na farko da zamu fara siyar dashi a store Win mu. Ka bani lokaci da dama ina so na zo mu tattauna."
"Zaka iya zuwa ko wanne lokaci daga yanzu."
"Shikenan, zuwa anjima zan zo in na shigo Kano zan kira ka." Omar ya amsa sannan suka yi sallama ya kashe wayar.

Wayar yake Wan bubbugawa da hannu Waya yana girgiza kai cike da mamaki, cikin kwanakin nan yana ta samu kira daga inda bai yi tunanin zai samu ba, ya rasa ta ya akayi product Win nasu yake trending yana shiga inda bai yi tunani ba. A bayyane ya ce, "ya akayi takalmani nan ya zaga ko Ina haka?." Bai tsawaita tunanin ba ya fita daga gidan.

Da yamma ya yiwa Didi waya ya ce ta bashi address Win gidan ta zai je. Abin ya bata mamaki dan bai taSa zuwa ba hakan ya yi mata daWi sosai. Ko da ya je ?ofar gidan ya sauka daga machine Win Bashir, ya kalli unguwar yana mamakin rashin mutanenta. Didi ta buWe gate Win ta ce, "Omar sannu da zuwa." Murmushi ya yi ya ce, "Haka unguwar ta ke shiru babu jama'a?."

Didi ta ce, "Shigo ciki sai mu yi magana. Bashir ka shigo kaima." Bashir ya ce, "A'a babbar Yaya, barni a nan akwai gidan ?anwata a nan da zan biya. Tiger in ka fito." Kai ya Waga masa shi kuma ya bi bayan Didi.

Gidan Didin ya burge shi ya yi kyau sosai ya zauna yana kallon falon ya ce, "Gidan ki ya yi kyau sosai, kin zama ?ar gayu." Ta zauna ta ce, "abin makamki yau sai gaka kwatsam." Ya yi murmushi kaWan ya ce, "mijin na ki baya nan?."
"Yana nan, yanzu zai fito." Tana magana sai kuwa gashi ya fito yana cewa, "Alhaji Omar, yau kai ne a gidan nan?."

Didi ta ce, "nima haka na ce, yau sai gashi kwatsam bayan dogon lokacin da ya Wauka bai zo ba." Gaisuwa suka yi da Abdulhamid, Omar ya ce, "Daman unguwar da ka kawo min Yayata kenan? Wannan unguwa babu jama'a." Murmushi ya yi ya ce, "gashi muna zaune lafiya kuma ba." Kai ya girgiza bai ce komai ba Didi ta ce, "Ya Nayla? Tana Lafiya?."
"Wace haka?" Ya faWa yana kallon ta.

Harararsa tayi sai ya yi murmushi itama ta yi ta ce, "kayi murmushi mana. Allah in ina ce maka ya Nayla kana cemin wace haka za mu yi faWa da kai." Omar ya ce, "Daman ai faWa mu ke yi da ke tunda ta shigo rayuwata, akanta har korata ki ka yi daga falo, ki ka ce min ina shirme kuma bana aiki da hankali."

Didi ta ce, "Na shiga uku ni Aisha, wai baka manta ba?." Ya kalle ta ya ce, "taS" ya furta a ta?aice yana Wan murmushi. Didi tayi dariya ta ce, "ashe-ashe itace matar ta ka. Narma ta shigo rayuwarka ne saboda ta canja ka, ita kuma ta shigo saboda ta zauna da kai."
"Hmmm" kawai ya ce ba tare da ya yi magana ba.

AbdulHamid ne ya tashi ya fita hakan ya saka Omar ya mi?a mata ledar da ya zo da ita ta karSa ta buWe. Laces ne guda uku masu shegen kyau, sai atampa guda biyu, sai mayafi guda biyu da takalmi irin wanda suke yi guda biyu, sai na AbdulHamid shima ?afa biyu. KuWi ya ajjiye mata ta a gefenta tasan na Winki yake nufi kamar yadda ya saba duk shekara.

Didi da farin ciki ta ce, "Omar wannan duk ni kaWai? Wannan kaya masu kyau da tsada Alhaji Omaar?. Kai amma na ji daWi wallahi, Allah ya ?ara buWi ya Waukaka rayuwarka." Omar ya ce, "amin." Didi ta ce, "Na gode sosai Omar, Allah ya bar zumunci ya ji?an iyayen mu."
"Amin" ya amsa a ta?aice bai sake cewa komai ba. Didi ta irga kuWin ta ce, "Omar har dubu
hamsin na Winki? Bayan wannan kaya da na san ka kashe fin dubu Wari?."

"To Didi in ban kashe miki abinda nake samu ba wa zan kashewa?." Didi ta yi murmushi tana kallonsa ta ce, "Haka ne Omar, wannan shekara tazo mana da alkhairi. Allah ya cigaba da ri?o da hannun ka a duk abinda ka saka a gaba. Lokacin da baka da sana'ar kirki ma ka ke yi min balle yanzu? Na gode Omar." A zuciya ya amsa da amin, Didi ta fuskance shi a nutse ta ce, "Amma ka siyawa matarka ko?."

Ajiyar zuciya ya yi bai ce komai alamun bai yi ba kenan, Didi ta ce, "Kar ka ce min baza ka yi ba, ha??in yi mata a kanka yake Omar. Ni yanzu ha??in yi min Winki ba a kan ka yake ba, ha??in yi min yana kan mijina, kyautatawa ce kawai ka yi min matsayina na ?ar uwarka. Wacce ya zama dole a kayi mata matarka ce Omar, kar ka yi la'akari da komai ka yi mata domin sauke nauyin da Allah ya Wora maka wuyan ka." Ajiyar zuciya ya yi ba tare da gardama ba ya ce, "To Didi" ya faWa yana shafa kwantaccen gashin da yake kansa. Jin ya amsa kai tsaye sai tayi murmushi ta ce, "Yauwa ko kai fa. Allah ya sake buWa maka, ya sa ka fi haka a rayuwarka."

"Amin Didi." Didi ta yi murmushi tana sake duba kayan ta ce, "Harda su Yallabai kenan? Godiya mu ke mai company Exclusive footwear." Bai ce komai ba ta sake cewa, "kai naga kun bawa Arewa24 advert ko? Ana samun mutane amma ji?."

Ya kalle ta ya ce, "su waye haka?."
"Kai fa ka cika rainin hankali, tashar arewa Win ne baka sani ba?."
"Na sani mana, na ji kin ce talla ne ai."
"Inyee ashe ka san meye advert Win" ta faWa cike da tsokana tana dariya. Tsaki ya yi ya kawar da kai ta sake yin dariyar nishaWi da farin cikin ganinsa a gidanta ta ce, "Allah da gaske nake, talla ake yi kullum ma sai anyi musamman da daddare. Tun shekaran jiya nake so na yi maka magana sai na manta."

"Tallah kuma a gidan tv!?" Ya maimaita yana kallonta. Didi ta harare shi ta ce, "ban sani ba." Ya kalle ta ya ce, "gaskiya baki gani daidai ba." Jin ya raina mata hankali sai ta share shi ta ce, "amma ana samun mutane yanzu sosai ko?."
"Sosai ma, yau ma wani yazo daga Abuja sun siya da yawa zasu saka a store, kuma sun biy? gabaWaya. Ni na yi tunanin ma sai an siyar zasu biya ni."
"Ma sha Allah, Allah ya saka taimaka maka Omar."
"Amin."
"Nima ai ana siya a wajena sosai fa Omar, musamman yanzu da sallah ta zo."
"Bash ya faWa min yana kawo miki."

Zata yi magana AbdulHamid ya shigo ta kalle shi tana cewa, "Kayan sallah Omar ya kawo min har g1da." Da murmushi ya zauna yana taya ta godiya shima aka bashi nasa ya ce, "Har da mu kenan? Na gode sosai Allah ya ?ara arzu?i." Ya amsa da amin yana kallon Agogo. Tashi tsaye ya yi ya ce, "Didi zamu wuce." Ya faWa yana kiran wayar Bash sai ya katse bayan ya Wauka.

AbdlHamid ya ce, "na Wauka yau a nan zaka sha ruwa?." Didi ta yi dariya cikin tsokana ta ce, "Ina magidanci Ina shan ruwa a wani waje?." Abdulhamid ya yi dariya ya ce, "gaskiya dai, kar amarya ta saka mu a ba?in littafi mun ri?e mata Ango." Shi dai bai ce komai ba ko murmushi baya yi.

Didi ta ce, "tsaya na baka sa?o ka kaiwa Nayla." Kafin ya tanka ta shige ciki ya fita shida mijinta yana kallon unguwar ya ce, "Gaskiya da na san haka unguwar nan take Yayata baza ta zauna ba. Ka dai dinga kular min da ita bana so komai ya same ta."

AbdulHamid ya ce, "An gama Tiger." Murmushi ya yi mai sauti jin sunan da ya kira shi dashi shima Abdulhamid Win haka. Didi ce ta fito ta bashi abu a leda ta ce, "ka kaiwa Nayla don Allah." Kallon ledar ya yi ya kalle ta ya ce, "kin san ba a bani sa?o ko?."
"Don Allah na ce ai." Bashi da zaSin da ya wuce ya karSa ya bawa Bashir da yake kan machine dan ya ri?e masa, sannan ya hau suka tafi Didi ta bishi da kallo tana murmushi.

Suna zuwa ?ofar gidan na sa ya tarar Nayla ta sauka daga motar wani, ga ta ta motar a baya wani namiji ya ajjiye ya bata key Win ita kuma tana magana da wanda ya kawo ta Win tana murmushi. Wani abu yaji yana mamaye masa zuciyarsa ba tare da ya sani ba, nan da nan ya sake tamke fuska har suka ?araso gate Win gidan inda suke tsaye.
KRB3P010

Nayla tana juyowa suka haWa ido dashi yana tsaye yana aiko mata da kallon tsakiyar ido, haka kawai sai gaban ta ya faWi, tayi saurin kawar da kai daga kallon sa a lokacin wanda ya sauke ta ya tafi. Tk da yake ?ofar gidan ya ?araso ya ce, "Antyn mu kawo na shigar miki da ita." Ba musu ta bashi key Win ta ce, "na gode sosai Tk." Gidan ta shiga ta zauna akan kujera zazzaSi gabaWaya ya mamaye mata fatar jikinta.

Da?yar ta iya samu tayi wanka ta canja kaya zuwa doguwar riga ta shan iska wacce take a tattare da roba a ?irji, ta saka hula ta kwanta akan kujera tana mayar da numfashi saboda zazzaSi ne a jikinta sosai. Bata tunanin zata iya koda dafa tea saboda yadda take bata jin daWi ko kaWan.

Sallamarsa ta ji kamar ko yaushe a ciki bata fito sosai ba, ta Wago ta amsa ya ?araso har inda take ya ajjiye key Win motarta da tk ya bashi akan table Win da yake kusa da ita. HaWa ido suka yi ta Wauke kai ya tsaya kafin yana kallon ta ya ce, "shi wannan Win waye?."

Babu zato babu tsammani taji maganarsa, hakan ya saka ta Wago ta kalle shi ba tare da tayi tunanin ita yake kallo ba. Janye idonta tayi ta mi?e zaune gabanta yana faWuwa matu?a ta ce, "Colleague Wina ne." Kamar bai ji me ta ce ba, yayi shiru yana zagawa da idanunsa ko ina na jikinta. Nayla ta diririrce ganin kallon da yake yi mata, murya na rawa ta ce, "Abokin aikina ne, bani da lafiya bazan iya driving ba shine ya kawo ni sai cleaner ya dawo da motar."

"Shi cleaner Win bazai kawo ki ba sai abokin aikin ki?." Da sauri ta sake kallon sa jin abinda ya sake faWa, fuskar nan ta sa tana Waure matu?a sannan babu a alamun wasa a tare dashi. Nayla gabanta faWuwa yake yi dan bai taSa tsayawa sun yi doguwar magana shida ita haka ba, ta sunkuyar da kai ta ce, "da a can zan bar motar sai daga baya aka yi tunanin cleaner ya kawo." Shiru ya yi yana kallonta ko motsin kirki baya yi, ya kafa mata ido kawai yana kallo ba tare da ya san asalin abinda yake nu?ur?usar zuciyarsa ba. Wanda ya ajjiyeta a motar kawai yake gani a idonsa, bazai ce ga abinda yake ji ba amma ya san zuciyarsa tayi nauyi sosai.

Nayla da taji shiru ta Wauka ya fita, hakan ya saka ta kalli inda yake suka sake haWa ido tayi saurin Wauke kai jikinta har tawa yake yi.

Sa?on Didi ya ajjiye mata ya ce, "Kar na kuma ganin hakan!" Ya faWa cikin kakkausar murya. Nayla saboda tsoro bai barta ta iya bashi amsa ba hakan ya saka shi ya ce, "sa?on Didi" abinda ya ce kenan ya bar wajan.

Nayla ta yi sauke ajiyar zuciya mai tsaho ta ce, "na kuSuta!. Iko Allah to shi wannan mutum me ya ke nufi ne? Kishi yake yi ko me oho?." BuWe abinda ya ajjiye mata take yi tana cewa, "nima ba a son raina hakan ya faru ba ai, babu yadda zan yi ne matan office Win duk sun tafi saboda matan aure ne ana sauri aje ayi girki."

"Wow!" Ta furta ganin pack mai kyau ta sako mata awara manya-manya wacce taji sauce har da mayonnise da aka zuba mata. Nayla tayi murmushi ta ce, "Wayyo Allah! na huta cin komai in an sha ruwa." Sai kuma tayi murmushi ta ajjiye pack Win ta ri?e haSa ta ce, "wai yanzu kenan kishina yake yi?..." sai ta girgiza kai ta ce, "A'a dai Nayla, ta ya zai yi kishin ki bayan ba sonki yake yi ba?. To amma meyasa ya nuna ya ji haushi har ya ce kar ya sake gani?." Sai ta sake yin ?aramar dariya ta ce, "Dole Twinny ta ji labari, addu'ar da suke yi min Allah yana karSa."

Tana zaune tana wannan tunanin aka yi kira ko addu'ar kusa da shan ruwa bata samu ba. Ruwa ta Wauko ta sha ta Wauki awarar guda Waya ta ci tana lumshe ido saboda tayi mata daWi. Sallah ta tayar bayan ta idar ta shiga kitchen ta haWa tea ta dawo tana sha tanacin awarar da tayi mata masifar daWi. Tana gamawa ta sha paracetamol ta zauna tana hutawa. GabaWaya abinda ya faru ya ?i fita daga kanta, ta lura kwana biyu yana iya yi mata magana ko dan ya saba da ganin ta ne dai oho.

Aiki take so tayi ta turawa ogan su amma baza ta iya ba saboda ciwon kai, tana nan zaune a wajan har aka yi i'sha ta tashi tayi sallah aka tayar da sallar tarawee. Bayan an idar da hijjabin jikinta ta fito babban falon dan ta Wauki alkur'anin ta da ta bari a kan table. Shigowarsa ta gani ta amsa sallamar da yake yi kamar baya so, wucewa take niyar yi ya ce, "tsaya."

Babu musu ta tsaya bata juyo ba kuma bata dawo baya ba. "A kausashe ta ji ya ce, "Ni zan zo na same ki kenan?." Jin abinda ya ce sai ta dawo da baya dan daman gudun kar ta yi laifi ya saka bata dawo ba. Leda ya ajjiye mata babba mai girma sosai ya nuna ledar da hannunsa ya ce, "ki Wauka" abinda ya ce kenan ya wuce Waki ya barta a wajan. Nayla ta Wauki ledar ta shiga zuwa ?aramin falon da ta saba zama dan ta fi sakewa a can.

BuWe ledar ta yi ta fito da laces masu shegen kyau guda uku, sai atampa guda uku, sai veils masu shegen kyau da tsada gida uku, ba?i da milk da blue kalar lace guda Waya, sai kuma takalma ?afa uku. Nayla kallon kayan take yi kawai tana murmushi a zuciyarta na jin wani farin ciki na mamaye ko Ina. Farin ciki ya gama mamaye zuciyarta, ji take yana zaga jininta yana shiga ko wanne lungu da sa?o sa jikinta.

A bayyane ta ce, "shine ya siya min kayan sallah? Kenan ya karSe ni matsayin matarsa? Allah na gode maka, Allah na gode maka da ka ke karSar addu'ata." Ita kaWai take surutai tana fito da kayan daga cikin ledar. Hannu na rawa ta shiga WhatsApp zata kira Salma voice call ta bata labari sai kuma ta dakata saboda kiran Didi da ya shigo.

Da murmushi ta Wauka suka gaisa Nayla ta ce, "Didi an kawo min awara mai daWin gaske, gaskiya na gode sosai ita kawai na ci. Daman yau na dawo da zazzaSi daga wajan aiki."
"Amma dai kin samu lafiya ko?."
"Eh ya sauka, daman gajiya ce."
"Allah ya ?ara lafiya."
"Amin Didi. Na gode sosai."

Didi ta ce, "kar ki damu Nayla. Yau ya kawo min ziyara ya kuma kawo min kayan sallah, ki ta ya ni yi masa godiya Allah ya ?ara arzu?i." Nayla ta yi murmushin jin daWi da annushuwar da take jin zuciyarta ta ce, "Amin Didi. Nima yanzu aka ajjiye min nawa, kaya masu kyau Didi naji daWi sosai." Diid ta ce, "To ya yi min ma balle ke matarsa? Allah ya cigaba da daidaita ku kawai, amma na faWa miki daman tun a baya da zarar kun saba shikenan komai ya ?are. Yana da matu?ar wahalar sabo ne kawai, amma da an saba wallahi sai kin yi mamakinsa, dan gani zaki yi kamar an canja shi gabaWaya."

Nayla ta yi murmushi cikin gamsuwa da abinda Didi tace dan itama ta fahimci haka. Didi ta ce, "A taya ni godiya." Nayla tayi murmushi Didin ma haka kafin ta ce, "Amma zaki samu Winki dai ko?."

"Didi bani da tailor a nan Kano ai, da dai akwai wanda zai kai min Kaduna ne tailor na ko ana e gobe sallah zai Winka min. To nan ban san kowa ba." Didi ta ce, "Ko Salma ki tambaya ta haWa ki da nata, ni na san nawa Winkinsa bazai miki ba, kin saba da na ku na manya." Nayla tayi dariya ta ce, "Haba dai Didi, in dai ya iya Winki ai shikenan."
"Ki tambayi Salma in zai miki sai ki bashi, in bazai miki ba sai na tambayar miki nawan in za a samu."

Nayla ta ce, "in sha Allah." Didi ta ce, "kinga tallan companyn na ku ake yi a arewa, Wazu nake yi masa maganar yake raina min hankali. Wai wanne talla? Na ce ban sani ba." Nayla tayi dariya mai sauti ta ce, "bai sani Win ba ai Didi. Tsakani da Allah ni da Bashir muka tsara komai na je tashar muka yi komai ba tare da ya sani ba. Kuma da yake ba kallon tv yake yi ba shiyasa bai san ma ana talla ba." Didi taji wani daWi ya mamaye mata zuciyarta, kana jin maganarta ka san taji daWin maganar Nayla ta ce, "Yanzu Nayla da kan ki ki saka aka yi tallan nan kuma ke kika Soye masa?."

Nayla ta ce, "Don Allah kar ki faWa masa, kin san halinsa ya ce na daina shiga harkarsa, in ya san ni na bada advert Win bazai ji daWi ba ?arshe ma ya ce a daina haskawa. Ni kuma nayi tsakani da Allah saboda kayan nasa suna da kyau sosai, advert shine zai saka su zaga ko ina a san da company."

"Amma kuWin da kika kashe da yawa, kwanaki naji ana zancen tallah nan ana kashe kuWi sosai."
"Babu komai Didi, duk cikin cigaban mu ne ai."
"Allah Sarki! Allah ya saka miki da alkhairi, Allah ya biya ki ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login