Showing 138001 words to 141000 words out of 332344 words

Chapter 47 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

30869

Ya kuma shafa mata ruwan amma har lokacin bata motsa ba tana hannunsa kamar matacciya. Sai da ya shafa mata ruwa sau biyar a fuska yana jijjigata sannan ya ji ta saki numfashi a hankali ta tafi luuuu ta kifa a ?irjinsa.

"Alhamdu lillah!" Ya furta a bayyane ya ajjiye abin ruwan ya ri?e kanta ya sake jijjigata ya ce, "Ki buWe ido, ki tashi don Allah, ki ta shi kin ji....?." Nayla har lokacin bata dawo duniyar ba tana duniyar suma. A bayyane ya ce, "Wayyo Allah na, me na aikata ne haka? Yanzu me zan yi? Ban san me zan mata ba, ban sani ba" ya faWa a raunane yana shafa fuskarta kamar ya zubar da hawaye haka yake ji. Bai san abinda zai yiwa Nayla ta dawo daidai ba, bashi da ilimi a wannan Sangare, ba?o ne shi kuma sabon shiga, ba?on ma wanda bashi da ilimi kwata-kwata a kai, bai taSa sanin wani abu da ya shafi yanayin da yake ciki a yanzu ba, bai san ya zai mata ba.

Tashi ya yi da?yar bayan ya kwantar da ita ya ?arasa ya kunna hasken Wakin, da sauri ya kashe yana wara idanu waje ganin abinda bai yi tunanin gani. Gabansa faWauwa ya ke yi, cikin faWuwar gaba yana tambayar kansa to wannan jinin kuma daga ina ya zo? Ba dai daga jikin Nayla ya ke ba?. Da sauri ya sake kunnawa yana kallon wajan cikin tsoro da firgici, jikinsa karkarwa yake yi saboda tashin hankali da sanyin da yake ratsa shi, ya Wauki remote Win fankar ya kashe, ya taka ya koma inda take ya sake Wauko ta gabaWaya ya dawo da ita jikinsa.

Zafin jikinta ya haWu da zafin jikinsa, sai ya sake zama wani special zafi mai huci, kallonta yake yi bai san abinda zai mai yi mata ba, bai san abinda zai yi mata ta dawowa daidai ba.

Ji yake kamar ya fashe da kuka saboda takaici, bai taSa jin haushin rashin abokai da bashi dashi ba sai yanzu, tabbas da yana da abokai da babu ta yadda za a yi bai yi ilimi a wannan Sangare ba. Cikin hirar samari ko masu aure bazai rasa sanin abinda zai yi mata a yanzu ba, ko bai sani ba zai iya kiransu a waya ya tambaya amma yanzu bashi da kowa. TaSa screen Win wayarsa ya yi ya ga har lokacin asuba ya kusa, ya runtse ido ya yi ajiyar zuciya yana sake jijjiga Nayla amma har lokacin bata numfashi. "ya zanyi!? Ya zanyi ni Omar? me zan yi mata!?" Ya faWa ?arfi cikin yanayi na rauni da ya bayyana a tare dashi. Ruwan da ya ajjiye ya Wauka ya cigaba da shafa mata a fuska yana kiran sunanta a hankali, dauriya kawai yake yi amma shima bashi da lafiya sosai.

A hankali yaji ta sake yin numfashi tana fitar dashi mai zafin gaske a ?irjinsa, ya ciagaba da shafa ruwan a fuskarta cikin salon tausayasawa da sanyin jiki matu?a. A raunane ya ce, "Kin tashi? Kina jina? Ki yi magana ina so na fahimta in kin tashi, kina jina?" Abinda yake faWa kenan yana sake jijjigata.

Nayla har lokacin bata hankalinta, tana jinsa sama-sama amma baza ta ce ga abinda yake cewa ba, tana cikin duniyar azaba da ciwon jiki ga zazzaSi mai shegen zafi. Kanta kuwa ciwo yake yi kamar zai fashe, ko ido baza ta iya buWewa ba saboda ciwon da take yi a kanta ya yi yawa. "Jidda ki buWe ido kin ji, ban san me zan yi miki ba, Ki ta shi don Allah." Bata iya motsawa ba har lokacin, ba jinsa take yi sosai ba abinda ta sani kawai tana cikin tsananin ciwo wanda bata taSa tsintar kanta a cikinsa ba.

Omar ya ce, "Wayyo Allah! Ya Allah!! ?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 Ya Allah!!!. Me zan yi ne?" Ya faWa cike da damuwa yana sake kallon ta a jikinsa idanun a rufe, fuskarta kumbura sosai idanunta sun tasa alamun kuka sosai.

_Wanka zata yi ko abinci zan bata? Me zan yi mata ne?._ abinda ya tambaya kenan a zuciyarsa yana kallonta cikin so da ?auna da kuma tsantsar tausayi. Idanunsa lumshewa suke yi saboda jirin da yake Waukarsa, amma ya ?i rufe idon saboda Nayla, ya tabbatar indai ya rufe idonsa to bai san lokacin da zai buWe ba, in ya rufe ido ita kuma ya kenan?.

Kallon ta ya tsaya yana yi tana sauke numfashi a hankali ga hawayen da suke sakkowa daga gefen idanunta, bakinta ya mutu murus ta kasa koda buWe bakin balle ta yi magana, 0danunta kuwa a kulle su ke, ko motsa idanun bata son yi balle ta buWw su.

Kiran sallar asuba na farko aka fara yi a masallaci, ya runtse ido ya kwantar da ita ya mi?e yana tunanin abinda zai yi mata. BanWaki ya shiga ya fito ba tare da ya yi komai ba, jiri ne ya kwashe shi, ya tafi zai faWi ya yi sauri ri?e bango da?yar yana jan numfashi a wahalce amma ita yake kallo. Yadda yake jin sanyi ya san itama haka, ya Wauka zai samu sau?i da ya zubawa kansa ruwa sanyi amma sai ya ji azaba ya ?arasawa kansa, shiyasa yake tunanin Waukarta ya zuba mata ruwan sanyin.

Fita yake so ya yi yaje kitchen ko zai iya dafa mata ruwan zafi amma bazai iya ba. Shi sam ya manta da akwai water heater a banWakinsa, shi daman bai damu da ruwan zafi ba, ko a gidansu haka yake yi bai cika amfani dashi ba, tun Didi tana magana har ta daina, ta kan ce an ce mai wanka da ruwan sanyi zai ji sanyin ?ashi, shi kuma ya bata amsa da ya yi sanyin nama ba ?ashi ba. Takaici yake ji a zuciyarsa, yana ji yana gani ya kasa taimakawa matarsa wacce yake matu?ar ?auna, inda ace yana da dama kuka zai yi amma kukan ma ya ?i zuwa cikin idanunsa.

Da?yar ya iya fita zuwa kitchen, biyu-biyu yake gani amma a haka ya Wauki kettle ya zuba ruwa ya kunna ya zauna a kitchen Win akan tiles yana jira ya yi. Da?yar ya iya mi?ewa tsaye ya Wauki kettle Win ya fita yana tangaWi kamar Wan maye, ruwan zafin ya Wan zuba a hannunsa ya yarfe hannu cikin azabar da ta ratsa shi, amma bai sakata ba ya shiga ciki ya juye ya kunna ruwan sanyi bai jima yana zuba ba ya kashe ya fito.

Kallon ta yake yi yana tunanin ta yadda zai iya Waukarta ya kai ta banWakin, a hankali ya ?araso yana numfashi sama-sama ya gwada Waukarta amma ya kasa ya mayar da ita ya ajjiye. Ya sake gwadawa ya sake kasawa ya sake kwantar da ita, cize bakinsa yake yi ya dafe bango yana ri?e jijiyoyin kansa da suke harbawa kamar zasu tsinke. A karo na uku ya gwada ya Wauketa amma shi da ita suka yi baya suka koma kan gadon suka zube. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Abinda yake maimaitawa kenan, ko a mafarki bai Wauka wannan yanayin zai riske shi ba, amma sai gashi ya riske shi a lokacin da bai shiryawa hakan ba.

Da?yar ya iya mi?ewa ya sake Waukarta ya taka da?yar, ya kuma takawa sai ya tsaya cak yana sauke numfashi yana jin jiri na Waukarsa. A haka aka ?arasa bandakin tana jikinsa kamar mara rai, du?awa ya yi ya zube a ?asan tiles Win banWakin, tana jikinsa har lokacin ya Wauki ruwan yana zuba mata tun daga kanta har ?afafunta a tunaninsa hakan ne zai saka ta dawo daidai.

Dogon numfashi Nayla ta ja, ganin haka ya saka shi ya cigaba da zuba mata ruwan tun daga gashin kanta har farcen ?afarta yake ji?awa da ruwa yana bubbuga fuskarta. Numfashinta sama-sama yake fita, tana jin zubar ruwan a jikintq ta kuma dawo hayyacinta kawai bazata iya magana bane, ita kaWai ta san halin da take ciki. Sai da ruwan nan ya ?are tass yana kwara mata sannan ya kalle ta ya ga har lokacin dai Nayla bata dawo daidai ba.

Ganin ta yi dogon numfashi har yana jin fitar nunfashinta sai ya ji daWi a ransa, ya sake Wau?ota a karo na biyu suka fito ya ajjiye akan sofa, kan gadon ya ?arasa ya janye bedsheet Win da ya la'ance ya Wauki duvet ya jefa a kai ya Wan ware inda zata iya kwanciya ya sake dawo da ita kan gadon. Rigar baccinta ta jiya ya mayar mata ya koma ya zube akan kujera yana juya kai saboda ciwo. Shi a tunaninsa iya abinda zai yi mata kenan, ya kuma gama yi mata shiyasa yake hutawa.

Nayla kuwa zafin ciwon kai da zazzaSi ya saka numfashinta yake sama da ?asa ta kasa fahimtar a wacce duniya ta ke. Rawar sanyi take yi sosai alamun zazaaSi, ya kalle ta sai ya mike da?yar ya fita ya shiga Wakinta ya Wauko blanket ya dawo ya rufa mata ya zauna a gefenta ya ri?e hannunta yana murzawa a hankali.

Zafin jikinta ya dame shi sosai, duk da shima haka nasa jikin yake amma ta ita yake yi ba ta kansa ba. Yana cize baki ya mi?e tsaye ya duba maganin da ya taSa siya na zazzaSi ya Wauko, fita ya yi ya Wauko ruwa ya dawo inda take ya tallafo kanta ya saka mata maganin a baki ya kafa mata robar ruwan amma sai yaga ruwan yana dawowa kamar yana bawa gawa ruwa.

Hankalin Omar ya tashi fiye da Wazu, a firgice yake cewa, "Jidda! Jidda!! Ki yi magana in kina jina, kina jina....? don Allah ki ce wani abu. Kar ki saka zuciyata ta buga mana, ki yi magana, ki yi magana naji don Allah, ki ce wani abu ko zan ji daWi!" Abinda yake faWa kenan cikin fitar hayyaci. Kiran sallar asuba da ya ji ya saka shi tsayawa cak yana mamakin gudun lokacin, inda yana da ?arfi da lafiya asibiti zai kai Nayla amma bazai iya ba, bazai iya fita a wannan hali ba. tsaf sai su yi hatsari.

Wayarsa ya jawo ya shiga number Didi yana kallo amma ya kasa kira, ajiyar zuciya ya yi, bashi da wata in ba Didin ba dole ita zai kira ta zo ta taimaka masa kar Nayla ta mutu ya shiga uku. Danna kiran ya yi ta gama ringing amma Didi bata Wauka ba, ya sake kira a karo na biyu nan ma bata Wauka ba, ya ajjiye wayar yana ji kamar ya yi ta dukan kansa saboda takaici da ba?in ciki.

In ya bar Nayja a haka ta mutu ya zai yi? Wanne hali zai shiga?. Ya juya ya kuma kallonta ya sauke ajiyar zuciya ya dafe kan da yake barazanar tarwatsewa. Yana ji aka tayar da sallar asuba amma bazai iya motsi ba, yana zaune har aka idar da sallar ya kasa motsawa daga wajan.

Ana idar da sallah kiran Didi ya shigo wayarsa, da hanzari ya Wauka ya ji muryarta a firgice tana cewa, "Omar lafiya? Me ya faru?." Bai ma ji me take cewa ba ya ce, "Didi ki zo, na rasa me zan yi, ki zo ki taimaka min. Jidda zata mutu, ki zo!" Abinda yake iya faWa kenan yana lumshe idanunsa.

Wayar faWuwa tayi a hannunsa ya sunkuyar da kai ya rasa abinda zai yi. Kallon Nayla ya yi da take yadda ya barta numfashin ma baya fita, ruwan da ya taru a idanunsa suka fara sauka tamkar hawaye, hawaye yake yi na ba?in ciki da takaicin kasa taimakonta da ya yi. Yana kallon ta a kwance, ita ba sumammiya ba ita ba wacce take hayyacinta ba, ya kasa yi mata abinda zata ji daWi zazaSin jikinta ya rabu da ita, ya kasa yi mata komai. Ya kasa sakawa ta dawo daidai, ya rasa abinda zai yi mata wanda zai sakata dawowa hankalinta.

Tunda yake a duniya bai taSa zubar da hawaye akan komai ba sai a yau, ya kasa ri?e hawayensa sai da suka sauka dan yana ganin komai laifinsa ne, shine yayi gaggawa ya kai kansa inda bai taSa zuwa ba, shine ya kai su inda basu taSa zuwa ba ba tare da yana da ilimi a kai abun ba, gashi gaggawa ta kai shi ga zubar da hawaye, ya kasa yi mata abinda zata iya ko da magana ne balle kuma ta iya tashi. Ya manta ma zai yi sallah, sai daga baya ya mi?e da?yar ya yi alwala ya dawo ya yi sallar a zaune dan bazai iya sallah a tsaye ba saboda jiri, yana idarwa ya koma inda take kwance, har lokacin numfashi ta yana sauka amma a hankali.

Kiran wayarsa ya ji ana yi bai iya Wauka ba har ta katse, aka sake kira bai Wauka ba, sai aka kira sau biyar sannan ya iya jan wayar da take kife a ?asa ya Wauka. A rikice Didi ta ce, "Omar gani a ?ofar gidan, ka zo ka buWe min." Runtse ido ya yi yana tunanin ta ya zai iya fita ya buWe gate? Ciwon da yake ji tunda yake a duniya bai taSa jin irinsa ba, ji yake kamar iska tana Waukarsa tana hujijjiga shi a sama in ya tashi tsaye, amma dole zai daure ko dan saboda ita.

Yana haWa hanya ya fita, yana fita compound Win gidan ya ji sanyi na ratsa ko ina na jikinsa, ya buWe gate Win Didi ta shigo a firgice mijinta yana jikin motarsa a tsaye shima hankalinsa a tashe. Didi ta ce, "Omar lafiya ka ke? Omar!" Ta faWa da ?arfi ganin yana ?o?arin zubewa a wajan. Da sauri AbdulHamid ya shigo ya ri?e shi yana cewa, "Subahanallah! Omar Bba ka da lafiya haka?."

Didi ya kalla da idanunsa da suka koma jajaye ya ce, "Didi, Jidda!." Da hanzari ta shiga ciki shi kuma AbdulHamid ya ri?o shi suka dawo falo ya zaunar da shi yana jera masa sannu. Didi Wakin Nayla ta shiga amma bata ganta ba, ta fito ta ce, "tana ina?." Da hannu ya nuna mata Wakinsa ta buWee ta shiga. Da sauri ta ?arasa inda Nayla take tana kiran sunanta amma ta ga kamar Nayla bata numfashi. Didi ta ce, "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Me yake damunsu haka? Nayla! Nayla!" Ta faWa tana jijjigata amma ita Nayla bata san tana yi ba.

A guje Didi ta fito ta ce, "YallaSai asibiti zamu je, dukkan su basu da lafiya." AbdulHamid ya ce, "To bara mu je mota dashi, ku fito tare da ita" ya faWa tana kallon Omar ya ce, "Omar daure ka tashi mu je asibiti, daure ka mi?e." Omar ya?i tashi saboda ya san dai Didi bazata iya fitowa da Nayla daga Waki ba, to ta ya za a tafi asibiti kenan?.

Didi kuwa da sauri ta dawo Wakin Nayla ta samu doguwar riga mai Wan kauri a kayanta, ta koma Wakin ta Wora mata a kan rigar jikinta ba tare da ta cire ba. Ta fito ta kalli mijinta ta ce, "kamar a sume fa Nayla ta ke, ta ya zamu fito da ita?." Omar yayi caraf ya ce, "zan iya."

AbdulHamid ya ce, "baza ka iya ba Omar, baka da lafiya kaima, ta ya zaka iya Wauko ta?." Omar yana jinsa amma baya tunani zai iya bari shi ya Wauketa, dan in dai ba shi Win ne ya Wauke ta ba to tabbas shi ne zai maye gurbinsa, saboda ya san aikin ya fi ?arfin Didi. Shi kuwa da hakan ta faru gwara ya Waukota koda suna tafiya suna kifawa ne ya amince da hakan.

Omar ya ce, "zan iya" ya faWa yana wuce shi ya shiga Wakin ya Wauko ta kamar yarinya, da?yar da siWin goshi ya iya fitowa falon, AbdulHamid ya ri?e shi, shi kuma yana ri?e da ita a haka aka fita yana tangaWi har motar mijin Didi.

Didi ta kalle shi ta ce, "Ina key Win gidan?." Cikin gidan kawai ya nuna mata ta shiga tana ta dube-dube amma bata gani ba, key Win motar Nayla ta gani kawai ta Wauko ta fito da sauri ta kulle gidan ta shiga gaban motar suka tafi asibiti a guje. Basu tsaya bi ta kan asibitin gwamnati ba, kai tsaye ?aramin private suka wuce dan abin na gaggawa ne ana kuma bu?atar hanzari da aikin gaggawa saboda a taimaka su dawo hankalinsu.
KRB3P049

Duk su biyun kwantar da su aka yi, ko wanne an saka masa ruwa yana shiga jikinsa saboda yadda jikin na su ya yi laushi dole sai sun sha ruwa. Bayan an gama daidaita komai dukkan su sun samu bacci hankali Didi ya kwanta, ta kalli nurse Win ta fito daga Wakin ta ce, "Don Allah me ya same su haka?." Nurse Win ta ce, "Ni gaskiya ban je kanta ba, shi dai jikinsa ne ya yi weak sosai, sai zazzaSi mai zafi da ciwon kai, amma yanzu ya samu bacci."

Wata Likita ce ta le?o daga Wakin ta kalli Didi ta ce, "Sister ji mana." Didi ta ?arasa kusa da ita ta kalli Didi ta ce, "mata da miji ne?." Didi ta ce, "eh."
"Ya ku ke dasu?."
"?anina ne uwa Waya uba Waya." Ta girgiza kai ta ce, "Sabon aure ne?." Didi ta ce, "eh to, sabon aure ne."

Dr ta ce, "Akwai abinda nake expecting ne shiyasa nake tambayarki, lokacin barina aiki ya yi amma saboda su na tsaya. Ko dai they had their first night ne? Ina nufin ko dai sun kusanci juna a karo na farko ne?." Didi ta kalli Dr gabanta yana faWuwa ta ce, "it might be." Dr ta ce, "let me check" ta faWa tana komawa ta bar Didi da tunani.

Kenan in hakan ne dalilin da ya saka Nayla suma kenan? Suma fa, har ya sumar da ita saboda wannan kawai?. Tausayin Nayla ya mamaye mata zuciya, ta koma inda take zaune ta zauna ta yi shiru ta rasa abinda zata ce.

Dr da tayi mata magana ta ga ta fito daga Wakin ta kira wata sun shiga tare basu ce mata komai ba. Sun jima kafin su fito ta kalli Didi da take zaune kusa da mijinta ta ce, "Sis zo ki ji." Ba musu Didi ta mi?e ta ?arasa inda take ta kalli Didi ta ce, "abinda na yi hasashe haka ne ya faru. Amma wannan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login