Showing 99001 words to 102000 words out of 332344 words

Chapter 34 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

30882

gidan a kuma Wakin Nayla, sannan ko yaushe cikin jin muryarta yake tana kiran sunansa. Ya shiga damuwa sosai wacce ta haifar masa da kasala da kuma zazzaSi mai shegen zafi. Kansa ya yi masa nauyi saboda ciwo, ya rame lokaci Waya sai haske da ya sake yi, dan shi daman zama waje Waya yana saka shi haske.

Bashir ya kira a waya yana zaune a falon ya aike shi siyo magani saboda yadda yake jin zazzaSin na ratsa ?asusuwan jikinsa. Bayan ya kawo masa ya sha, Bashir ya tsaya yana ta yi masa sannu bai taSa ganin Ogan na sa a wannan yanayi ba.

Bashir shi ya sanar da Didi Omar ba shi da lafiya, da daddare mijinta ya kawo ta dan ta duba shi. Da ta shiga falon a zaune ta tarar dashi idanunsa a rufe, ta kalle shi da kulawa ta ce, "Sannu Omar, ashe baka da lafiya ban sani ba."

Tashi zaune ya yi sosai suka gaisa da mijinta kana ya kalle ta ya ce, "ZazzaSi ne kawai." Didi ta ce, "Wannan ya wuce kawai, kalli yadda ka koma fa, ka je asibiti?." Kai ya girgiza alamun a'a ta ce, "Zama ai ba naka bane, asibiti ya kamata ace ka je. Ka rame, fuskarka ta bayyana rashin lafiyarka a fili."

Juyawa ta ga ya yi yana kallon falon kafin ya kalle ta ya ce, "Wai baku ji ana kiran sunana ba?." Didi ta kalli AbdulHamid kafin ta kalle shi ta ce, "ni ban ji komai ba."
"To meyasa ni nake jin muryarta tana kiran sunana? Ko dai aljana ce daman?." Didi ta ?yalk?yale da dariya ta ce, "Ko kuma aljanun ne suka ji sunan yayi musu daWi suke kiranka ba." Share maganar ya yi bai ce komai ba ta ce, "Omar kwanaki na ta tafiya har ta kwashe kwana takwas a gida, yaushe zaka je ka kai mata takardar ne?."

A fusace ya ce, "ni ban san meyasa ki ka damu haka ba, ki ?yale ni mana duk lokacin da na ga dama zan yi ai na faWa miki. Meyasa ki ke min naci a kaine? Na tsani wannan kalmar nan da ki ke faWa, bana jin daWinta meyasa baza ki gane ba!?." Didi ta ce, "masifaffe, Allah ya baka ha?uri, tuna maka nayi dan ka sauke abinda yake wuyanka."

?aramin tsaki ya yi ya kalli AbdulHamid ya ce, "Ka yiwa matarka magana ta daina bana so, ta ?yale ni in nayi ra'ayi zan yi ai."

Abdulhamid ya ce, "To Omar." Kallon gefensa yake yi bayan ya dafe goshinsa, zuciyarsa kamar ana gasata a tukuba haka yake ji. AbdulHamid ya kalli Didi ya yi murmushi itama murmushin ta yi sannan ta ce, "Omar me ka ke ji a zuciyarta ka? Anya baza ka je asibiti ba?." Kamar jira ya ke tayi magana sai ya Wago ya ce, "Nima tunanin da nake yi kenan, ya kamata naje na ga likita wannan yanayin bana lafiya bane, wata?ila na kamu da ciwon zuciya."

"To kai meye a zuciyar taka da zai saka maka ciwo Omar?"AbdulHamid ya faWa yana kallonsa. Omar ya kalle shi ya ce, "Komai ma akwai."

Abdulhamid ya ce, "Ba sai ka je wani asibiti ba, zama ya kamata ka yi ka tuna daga yaushe ka fara jin haka, in ka tuna rana da lokacin sai ka tuna me ka rasa a lokacin wanda kafin ka fara jin wannan yanayin yana tare da kai, bayan ka rasa shi ka fara jin abinda ka ke ji. Ko da ace wayarka ce ka tuna ita ka rasa daga lokacin da ka fara jin hakan da zarar ka sake mallakar wayar zaka daina jin abinda ka ke ji, duk abinda ka binciko ka ga shine silar shigarka wannan yanayi to tabbas kana matu?ar ?aunarsa Omar!, kana yi masa soyayya ba ta wasa ba, soyayya ka ke yi masa wacce baza ka iya ha?uri da rashinsa ba."

Omar ya zuba amsa ido yana kallonsa ko ?ifta ido baya yi. AbdulHamid ya ce, "in mun tafi ka zauna kayi tunanin, duk abinda ka rasa a lokacin zaka fahimci maganata gaskiya ce."

Omar ya yi ajiyar zuciya ya kalli Didi da take kallonsa ta ce, "abinda ya kamata ka yi kenan, ta haka ne kaWai zaka samo maganin damuwarka." Omar a raunane ya ce, "to zan yi. Amma ina neman alfarmarki don Allah kar ki sake yi min maganar yaushe zan kai takardar saki, ki ?yale ni na gama da abinda yake gabana kafin komai ya biyo baya. Ta lafiyata nake yi, wannan yanayin ya canja ni gabaWaya ko aiki bana iya yi. An buWe shaguna har guda huWu amma babu wanda na iya zuwa na gani saboda wannan abinda yake damuna. Rauni ba bai yi daidai da zubina ba, ni ba mutum mai rauni bane wallahi, ki bari na samo abinda ya saka zuciyata rauni in ya so sai mu yi magana. Ni nace bana son aurenta kuma ni zan raba shi."

Didi ta ce, "To Omar na daina." Kai ya girgiza bai ce komai ba Didi ta ce, "ga abinci nan na kawo maka in ka ci sai ka sake shan magani, Allah ya kawo mafita??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????." Bai amsa ba AbdulHamid ne ya amsa da amin suka tashi suka tafi dan su bar shi yayi tunani.
KRB3P033
Arewabooks@nanahaleema11.

A mota AbdulHamid ya kalli Didi ya ce, "Omar bazai iya sakin yarinyar nan ba, yana matu?ar ?aunarta wallahi, yana yi mata soyayyar da bai san yana yi mata ba."

Didi ta ce, "na so na fahimci hakan, amma kuma in na tuna waye shi sai naga anya zai yu kuwa?. Ka duba har yanzu shi baya kawo ta cikin damuwarsa, tunda gashi ka ji ya ce shine yace baya so kuma shi zai raba. Ni ban Wauka yana da hankalin da ya san ko nida kai ya furtawa ya saketa ta sa ku ba, ya ?i furta kalmar koda wasa."

AbdulHamid ya yi dariya ya ce, "yana da hankali da ilimi fa, ta ya zai aikata hakan? Saki ko baka je makaranta ba indai kana social media yadda malamai suke wayar da kai a kansa ai zaka sani. Balle ga makarantar da ki ka ce yana attending online, ko ya manta wani abun zai tuna indai yana bibiyar karatun. Ki zuba ruwa a ?asa ki sha, Omar yana sonta wallahi, baza ki bini bashin rantsuwa ba, Omar bazai iya sakin yarinyar nan ba."

Didi ta yi murmushin jin daWi ta ce, "in hakan ya kasance zan fi kowa murna da farin ciki. Amma anya Omar zai je gidansu Nayla kuwa? Har yanzu bai amince da soyayya ba fa."

"Ai daman a yanzu bazai amince ba, sai ya sake ji a jikinsa sannan zai damu. Ke wacce damuwa ki ka taSa ganin ta saka shi rauni haka har da zazzaSi?." Didi ta ce, "Wallahi babu, ko lokacin yarinyar nan Narma bai koma haka ba, ya cigaba da rayuwarsa normal kamar komai bai faru ba, amma ita kaga harda ciwo. Shine nake tunanin a tsakanin Narma Da Nayla Win wa yake so?."


"Wacce tunaninki ya baki."
"To abun ne da Waure kai, na farko ka ga Narma itace wacce ya furta min yana sonta, amma ko kusa bai shiga irin wannan damuwar ba. Ita kuma Nayla itace ya ce baya so amma ya shiga damuwa mai tarin yawa har ta haifar masa da rauni da ciwo. Kamata ya yi ace akan Narma ya shiga damuwa tunda ita yake so ba wai Nayla ba."

Didi ta yi shiru ta sake cewa, "Kenan dai Nayla yake so da gaske ba Narma ba, amma meyasa a baya ya ce yana son Narma?." Ya ce, "Wata?ila wani abun ne daban ba soyayya ba."

Didi ta ce, "Bayan ni a duniya Narma itace mace ta farko da Omar ya samu kusanci da ita, magana da ita a waya da komai ma a duniya. Amma meyasa ko lokacin da ya ce yana sonta ko waya tayi masa sai ya ga dama yake Wauka? ko da suka rabu ban ga alamun ya damu ba, sai ma mayar da hankalinsa da ya yi akan sana'arsa. Amma ita kuma Nayla...." Sai kuma tayi shiru bata ?arasa ba.

AbdulHamid ya ce, "ki bar wannan lissafin, Omar yana sonta kawai ki yarda, ita waccan labarinta ya wuce ta shigo rayuwarsa ne dan ta zama silar canja shi, amma asalin wacce yake ?auna wannan ce. Labarin zuciya ai a tambayi fuska, kina kallonsa kin san tsananin kewarta da son da yake mata ne ya mayar dashi haka, har rama yayi ga ciwo da yake fama dashi. ina shiga falon muna haWa ido dashi na san Omar ya faWi a ?asa warwar wallahi" ya faWa yana murmushi.

Didi ta yi murmushin farin ciki ta ce, "Naji daWin wannan abun abun wallahi, Omar na son Nayla. Na rasa inda zan saka kaina saboda farin ciki." Abdulhamid ya yi murmushi yace, "ke dai kawai ki tabbatar da ya je gidan su."
"0n sha Allah" ta faWa cikin zumuWi tana murmushi.

" " " " " " " "

? ?? Yadda ya ke zaune zai tabbatar maka da ransa a matu?ar Sace yake, ya zubawa waje Waya ido yana kallo kafin ya daki table Win gabansa ya ce, "Wallahi sai Narma ta dawo wajena, babu wanda ya isa ya saka na sake ta wallahi." Abokinsa da yake gefensa ya ce, "calm down maza, haba wannan ba ajinka ba ne."

A fusace Ashraf ya ce, "har ni Dad Winta yake cewa wai in ban sake ta ba zasu kai ni court, ka ji rainin hankali. Ai zama da Narma yanzu na fara shi wallahi, ban gaji da zama da ita ba, a bari duk lokacin da na gaji da morarta sai na saketa. Amma yanzu ban kammala ba tukunna." Dariya sosai abokin nasa ya yi ya ce, "To wai kai ka san baka son Narma meye na damuwa kuma haka?."

"Saboda ban gama abinda na aure ta dan shi ba. Yarinyar nan ta wahalar dani, babu ta hanyar da ban biyo mata ta amince dani ba ta ?i. Ban taSa jin sonta a zuciyata ba, haka ban tana jin ina qaunarta ba. Da fari dai na Wauka soyayya ce, amma daga baya na tabbatar da sha'awarta kawai nake yi. Har gobe ina da bu?atarta wallahi, sai yanzu ma tabbatar da Ikky itace wacce nake so ba Narma ba."

Sharif ya murmusa ya ce, "To na ga ai ka samu abinda ka ke so har na watanni da yawa, har yanzu baka kashe ?ishin da kake ji a kanta ba?."
"Sharif na kashe, sam bata wani burge ni sai in amfanin ta ya tashi, amma ni kaWai a san abinda yake jikinta. Ni ne mutum na farko da tayi tarayya dashi, ina da tabbacin har gobe babu wani ni sai ni Win kawai. Ban gama da ita ba har yanzu, ban gama da mallakarta ba har yanzu, babu wanda ya isa ya aureta sai na gama abinda nake so."

Sharif ya ce, "to ai matarka ce har yanzu." Ashraf ya ce, "iyayenta sune suke so su raba mu kuma wallahi ba su isa ba." Sharif ya ce, "Mtsw! Ni fa tun daga kan ka da Narma shikenan mata masu shiga half niked Win nan basa burge ni, da zarar na ji sun burge ni zan saka a raina ba soyayya bace jikinsu ne kawai ya burge ni. Ka duba Ikky da ka ke magana yanzu, yarinya mai hankali ko yaushe cikin shiga mai mutunci da rufe jikinta take, amma ka rufe ido ka ce kai sai Narma saboda surarta da ka ke gani a bayyane. Yanzu gashi ka tabbatar itace wacce ka ke so, Narma kuma jikinta kawai ka ke so kuma ka samu."

Ashraf ya ce, "Kai ka san sau nawa Narma ta karya min alwala? Ka san sau nawa Narma ta saka ni wanka ban shirya ba?. Haka zata saka kaya jiki a bayyane ta zo tayi hugging Wina, don Allah wanne yanayi ka ke tunanin zan shiga?" Ya ?arasa faWa yana dariya.

Sharif ya yi dariya sosai ya ce, "i'm sorry, she's your wife dole zaka ji kishi, but yarinyar nan she's too sexy." Ashraf ya ce, " Sorry for what? Do you think i have been jealous of what you've said about her? Mtsw shirme. Wallahi sam bana kishin Narma, ban jin wani abu a zuciyata a kanta in dai ba sha'awa ba. Yadda ka yi maganar Ikky yanzu na fi jin haushi a kanta."

"Ita Ikky kana sonta ne ba surarta ka ke so ba, ita kuma Narma ba ita kake so ba jikinta ka ke so. Na tabbatar iri ka ma su son jikin Narma suna nan da matu?ar yawa saboda Narma she's too hot. Wacce ka ke so ita zaka yi kishi ba wacce ka ke sha'awa ba daman ai" Sharif ya faWa yana kallon sa.

Ashraf ya ce, "ni yanzu zan sake komawa Abuja, dole a dawo min da matata, in na ?ara ko da wata biyu ne tare da ita sai mu rabu na dawo wajan Ikram Wina."

"Ka san Sen bazai baka wanna damar ba."
"Nima kuma bazan sake ta ba wallahi, sai dai ayi bala'i da masifa."
"Kar ka yi haka Ashraf, da mahaifinka da mahaifinta abokai ne matu?a. Kuma mahaifinka gov ne, kar ka yi wani abun da zaka Sata masa harkokinsa. Ko yanzu ka rabu da Narma ai ka ci riba." Ashraf ya ce, "Yadda take ta?ama da bata sona so nake na nuna mata ikona a kanta, wallahi so nake sai tayi shekara biyu sannan na saketa."

Ya yi dariya ya ce, "Wannan ai mugunta ce, tunda ka samu abinda ka ke so ba sai ka share ba kawai." Ajiyar zuciya ya yi ya ce, "za dai mu ga abinda ya kamata ayi" ya faWa yana Waukar wayarsa ya cigaba da dannawa.

" " " " " " "

Kamar yadda AbdulHamid ya bawa Omar shawara ya yi nazari ya tabbatar da Nayla ce abinda ya rasa a lokacin da ya fara jin wannan yanayi, kenan dai ita yake so meye?. Shi dai ya san ba haka ake jin so ba tunda ya taSa son Narma a baya, amma ba haka ya ji a kanta ba gabaWaya yanayin bai kai haka ba.

To in har abinda ya ji akan Narma shine so meyasa bai shiga yanayin da ya shiga a yanzu ba? Sannan ita Nayla me yake mata kenan? ?inta yake yi ko kuma wani abun ne daban?. Babu mai bashi amsa sai kawai ya share maganar ya danne zuciyarsa yana ?o?arin cigaba da harkokinsa amma ya gaza hakan.

Bayan kwana biyu da zuwan Didi da daddare suka sake zuwa, yana gidan shi kaWai a zaune amma yanzu aikin yanka fatar takalmi yake yi. Tunda suka gaisa da su Didi yana yanka takalmin sai ya ma rasa ta yadda zai yi kawai ya ajjiye.

AbdulHamid ya ce, "Ya jikin?." Omar ya ce, "na samu sau?i." AbdulHamid ya ce, "Ka samo abinda ka rasa Win kuwa?." Omar ya sauke numfashi ya ce, "Ni babu abinda na rasa balle na ce shi nake so, kawai ina jin mutuwa zan yi shiyasa nake jin wannan yanayin. An ce daman in zaka mutu kana ji a jikinka, wata?ila ita Win nake ji" ya faWa cikin gaskiyarsa.

AbdulHamid ya ce, "A'a Omaar, ka dai sake tunani, akwai wani abun bayan wannan." Omar ya ce, "to meye? Na rasa gane me nake ji Win." Didi ta kalle shi a nutse ta ce, "Meyasa ka ke zaune a gidan nan? Na Wauka kana gidanmu ne ai." Omar ya ce, "kawai ina so na zauna a nan ne."
"Kana kewar matar gidan kenan?." Kallonta yake yi ko kiftawa baya yi kafin ya janye ido ya ce, "amma meyasa ki ka ce haka?."

Didi ta ce, "Wanda ake kewa shi ake zama a inda yake saboda a dinga tunawa ana ganin kamar yana tare da kai. In kana kewar mutum kana kallon hotosa in baka dashi har inda yake zama kana gani, kana zuwa ka zauna inda mutum yake zama dan ya rage maka abinda ka ke ji a zuciyarka. Shiyasa nake tunanin ko kewarta ka ke yi."

Omar ya Waga kai sama ya sauke, ya kalle ta sai ya sauke kai ?asa ya furzar da iska ya ce, "indai har haka ake jin kewar wani tabbas ina kewarta, in ba a Wakin da take kwana na kwanta ba bana jin daWi ko kaWan. Ina kewarta Didi, ina kewarta sosai!" Ya faWa yana girgiza kai alamun tabbatarwa. Didi ta yi murmushi mai nuni da zallan farin cikin da ya mamaye mata zuciya, ta kalli mijinta shima ita yake kallo.

Ta sake kallon ta ce, "in dai har kana kewarta
kenan kana sonta?." Kallon Didi ya sake ya yi yana juya ?wayar idanunsa akan fuskarta kamar mai neman wani abun a kan fuskar tata. Ganin ya zuba mata yana ?are mata kallo sai Didi ta ce, "Eh Omar, sai kana son mutum ka ke jin kewarsa irin wannan."

?an ?aramin tsaki yayi ya ce, "ni kewarta na ce ina yi ba so ba, bana sonta kamar yadda na faWa miki a baya. Na yarda ina kewarta kamar yadda ki ka ce, amma ba wai so ba." Didi ta sake yin murmushi mai sauti ta ce, "Omar kana sonta, so ba Wan kaWan ba, soyayya mai yawa ka ke yi mata."

Sai ta fusata shi ya mi?e a firgice ya ce, "na ce miki bana sonta, bana son aurenta dole ki ka yi min na karSa! Meyasa ki ke maimaita ina sonta bayan ni ba haka nake ji zuciyata ba?."

AbdulHamid ganin yadda Omar Win ya birkice sai ya ?arasa kusa dashi ya dafa kafaWarsa ya ce, "Kwantar da hankalinka, koma ka zauna." Omar ya zauna yana cewa, "matarka ce take son tarwatsa min ?wa?walwa, na ce mata ba sonta nake yi ba dole sai ta ce ina sonta ne?" Ya ?arasa faWa a sanyaye yana kallonsa.
KRB3P034
Arewabooks@nanahaleema11.

Didi ta bishi da kallo sannan ta yi dariya tana Soye farin cikin ta ta ce, "to meye na fusatar dan na ce kana sonta?." Dafe kai ya yi da hannunsa yana sauke ajiyar zuciya a hankali. Didi ta tausasa murya ta ce, "Na san ka so Narma a baya ko? Sannan....." katse ta ya yi? ya ce,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login