Showing 102001 words to 105000 words out of 332344 words

Chapter 35 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

30853

"Shiyasa na ce miki ba sonta nake yi ba, saboda abinda na ji akan ?ar Senator daban itama na ta daban. Kuma ke kika tabbatar min da ina son Narma, kinga kenan ita wannan ba sonta nake yi ba."

Didi ta ce, "Ka nutsu ka bani amsar tambayar da zan yi maka don Allah."

"kar ki tambayi abinda zai Sata min rai."
"To YaMar" ta faWa tana kallonsa dan ta ga reaction Winsa. Ai kuwa da sauri ya kalle ta ya ce, "Maimaita abinda ki ka ce." Didi ta ce, "cewa na yi YaMar." Lumshe ido ya yi ya buWe yana kallon wani wajan daban ya ce, "meyasa ke ban ji komai a raina ba da kika faWi wannan sunan nan? Ita kuma duk sanda zata faWa sai gabana ya faWi" ya juyo ya zubawa Didi ido tare da zaro su waje ya ce, "Na shiga uku! Anya Didi ba da aljanna kika haWa ni zama ba?."

AbdulHamid da yake kallon dramar Omar ya yi dariya Didi ma murmushi ta yi ta ce, "ta ya gabanka zai faWi dan na faWi sunan da matarka take kiran ka dashi? ni fa jininka ka ce ba mata ba, taya zaka ji irin abinda ka ke ji a lokacin da matarka ta faWa?."

Shiru ya yi yana sauke numfashi a hankali, a tausashe? Didi ta ce, "Omar na san ka so Narma a baya, abinda nake so na tambayeka shine; lokacin da ka ke tsakiyar sonta ka ji irin abinda ka ke ji a yanzu a kan Narma?." Kai ya girgiza alamun a'a yana kallonta, ta ce, "lokacin da ku ka rabu ka ji irin wannan yanayin a zuciyarka?." Nan ma ya girgiza mata kai alamun a'a.

"Ka yi kewarta kamar yaddaka yi kewar Nayla?, zuciyarka ta buga a lokacin kamar yadda yanzu take bugawa? Ka ji rauni a lokacin kamar yadda ka ke ji yanzu? Ka yi zazzaSi kamar yadda ka yi yanzu?. Ka jure zama da Narma kamar yadda ka jure zama da Nayla? Ka ji zafi a zuciyarka in wani ya yabi wani abu na Narma kamar yadda ka ji zafi a lokacin da aka yabi ?afar Nayla?." Omar ya yi tsitt yana sauraren Didi yana kuma kallon ta. Ajiyar zuciya Omar ya yi ya girgiza kai ya ce, "A'a duk ban ji ba."

"Amma ka ji kishi da wani ya biyo Nayla ya ce yana sonta, ka ji zafi da ka ga ?afarta na zaga social media ana yabonta, ka ji babu daWi a lokacin da nake hirar samarinta. Ka damu da rashin lafiyarta har jikinka ya yi sanyi kana so kaji ya take, ka jure zama da ita sama da ko wacce mace a duniya, zuciyarka ta karye akan rashinta har ka ke jin kanka kamar kwalin da babu komai. Haka ne ko Omar?." Omar ya yi ?aramin tsaki cikin gajiya ya ce, "Haka ne Didi, ki kai ?arshen maganarki na gaji da wannan tambayiyon."

Didi ta ce, "Omar ba son Narma ka yi ba." Ya Wago ya sake kallonta kafin ya musa ta ce, "Ta ya zaka WanWana karayar zuciya bayan Narma itace take sonka ba kaine ka ke son ta ba? Itace mace ta farko da ka samu kusnaci da ita shiyasa a lokacin ka Wauka sonta ka ke yi amma ba so bane. Zaka WanWana karayar zuciya da rauni ne in ka rasa wacce ka ke so Omar!" Ta faWa tana kallonsa kamar yadda yake kallonta.

Abdulhamid ya ce, "hakan yana nufin kana son matarka so mai yawa Omar, duk abinda ka ke ji a yanzu shi ake kira da tsananin so. Baza ka taSa dawowa daidai ba in dai baka je ka dawo da ita ba."

Omar ya yi shiru yana sauraren su, jin maganarsu yake yi kamar film ko kuma tatsuniya. Ta ya zasu ce masa wai Nayla yake so ba Narma ba? Bayan ya san Narma ita ce akace ya so ta? Shi abinda yake ji akan ta daban, abinda ya ji akan Nayla daban. Ta ya zai banbance soyayya da kuma abinda Didi take faWa? Shi gabaWaya sun saka shi a tsaka mai wuya.

Omar ya kalli Didi ya ce, "Didi ba sonta nake yi ba, na yarda dai ina kewarta kamar yadda ki ka ce, ina kewarta sosai na yarda da wannan amma ba wai ina sonta ba, ki bar zancen nan don Allah." Didi ta ce, "shikenan na bari Omar, ka yi tunanin maganar da na faWa maka, in ka tabbatar ba haka bane tana gidan ?anwar mahaifiyarta ka je ka sallame ta."

Ya lumshe idanu ya ce, "Na faWa miki ki daina yimin zancen nan amma kin ?i ji." Didi ta ce, "kai da ka ce baka sonta meye na damuwa dan ina znacen zaka sake ta? Kaga....." jajayen idanunsa ya zuba mata hakan ya saka ta yi murmushi kawai bata ?arasa ba.

AbdulHamid ya ce, "Ka yi tunani Omar, in kana bu?atar shawara ?ofa a buWe take zaka iya kirana. Wata shawarar namiji yana da bu?atar tattaunawa da Wan uwansa namiji, na san baka da aboki shiyasa nake so na zamar maka aboki Omar."

Omar ya yi ajiyar zuciya ya ce, "to" ya kalli Didi ya ce, "na gode, ku je g1da kawai" ya faWa yana jingina da kujera yana tunani. Didi bata sake cewa komai ba dan ta riga ta gama dashi gabaWaya. Ta san ko ya zai motsa sai ya tuna da kalamanta, a cikin kalamanta kuma dole ya samo gaskiya.

Omar kansa ya kulle ya kasa tunanin hakan ya saka ya tashi shima ya fita daga gidan saboda in ya zauna tunani zai saka kansa ya yi bindiga.

Nayla ta kwashe sati biyu cif a gida, duk kauce-kaucen Omar ya tabbatar da maganar Didi gaskiya ce. Abin ya wuce gizo da take yi masa mafarkinta kawai yake yi, indai zai kwanta ya tashi sai ya yi mafarkinta. Zuciyarsa na bugawa a kanta ya kan rasa inda zai saka kansa, sai ya ruWe ya rasa inda zai je ya samu sassauci. GabaWaya ya susuce yana gab da zama zararre akan Nayla. Ya yarda da Nayla yake so ba Narma, sai yanzu ya tabbatar da inda ace abinda yake akan Nayla shi yaji a lokacin Narma da babu halittar da ta isa ta raba shi da ita, kamar yadda ta nemi ya gudu da ita tabbas zai iya aikata hakan. Sai dai kash! Ba akanta yake jin wannan yanayi ba, akan Nayla yake jinsa!.

Babban abinda yake Waure masa kai shine in dai son Nayla yake yi ita Narma me ya yi mata a baya? Sonta ya yi ko tausayinta yaji ko kuma meye bai sani ba.

Hankalinsa ya gama kaiwa ?arshe wajan tashi, ya tsayar da tunaninsa waje Waya ya kuma yarda da gaske dai Nayla yake so ba wai da wasa ba. Abin ka ga soyayyar farko, in yana tunaninta jikinsa har karkarwa yake yi saboda azabar da zuciyarsa take yi masa, fatar jikinsa har Waukar zafi take yi saboda yanayin da zuciyarsa take ciki. Nauyi ?irjinsa yake yi masa sosai, har ya kai ya kawo in ya motsa yana jin zafi a ?asan zuciyarsa. In ya yi tari sai ya ji numfashinsa yana neman tsayawa cak, sai ya ja numfashi da ?arfi sannan yake samun sassaucin nauyin da yake yi.

Ranar asabar bayan sallar azhar ya kasa jurewa, ya rasa ya zai yi ya kasa cin abinci tun safe. Ya haWa tea amma ya kasa sha ruwa kawai yake zubawa cikinsa. Ya kasa cin komai, baya sha'awar cin komai balle ya nema ya zuba a cikinsa, duniyar yake ji ta yi masa zafi tana juya masa. Nayla kaWai yake so ya gani, itace abincin da idanunsa da zuciyarsa take marari, muryarta yake so ya ji ta furta sunan da ta saba faWa masa. Ya tabbatar da ya ji wannan suna daga bakinta duk abinda yake ji a zuciyarsa zai daina ji. Ganin yana neman kashe kansa da tunani sai ya kira Didi a waya dan tunda tazo basu sake magana ba, tana Wauka kafin su gaisa ya ce, "Didi meye abu na gaba?."

Didi ta ce, "Ya naji magnarka haka, Omar ko ka je asibiti a duba ka?."
"Didi gab nake da zaucewa wallahi, tafasa jinina ake yi kullum" ya faWa a sanyaye." Didi ta ce, "Allah ya kawo mafita Omar."
"Ina tambayarki, meye abu na gaba?."
"kamar me kenan?."
"A ina zan sameta?."
"Ita wa kenan?."
"matata!" Ya faWa kansa tsaye ba tare da wani tunani ba.

Didi ta yi dariya mai sauti ta ce, "ban gane abu na gaba ba." Ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Me aka ce zan yi?." Didi ta ce, "akan dawowarta?."
"Uhum."
"Gidan iyayenta zaka je."
"Ina ne gidan? Ki tura min address Win gidan zan je."

Didi ta ce, "Da gaske ka ke?." Omar ya ce, "kin san ba wasa nake yi ba ai, zan je ina bu?atarta tare dani. Na yarda da duk abinda ki ka faWa, da gaske ina matu?ar sonta Didi, Ina yi mata son da bana yiwa kaina. Didi ko abinci na kasa ci, kamar ana gasa zuciyata haka nake ji. Kullum da zazzaSi nake kwana, damuwa ta yi min yawa, zuciyata ta kasa jure wannan yanayin. In na sake na kai gobe ban ganta ba wallahi zaki iya zuwa ki Wauki gawata, ni kaWai na san yanayin da nake ciki Didi, na kasa jurewa!" Ya faWa a hankali kamar zai yi kuka.

Didi ta yi ajiyar zuciya cikin farin ciki tace, "Alhamdu lillah! Allah na gode maka da ka nuna min wannan rana, ko yau Allah ya Wauki raina ya cika min burina. Omar yana son Nayla, Allah na gode maka." Shiru ya yi bai ce komai ba Didi ta ce, "Yaushe hakan ya faru? Yaushe ka fara jinta a zuciyarka?."

Omar ya yi ajiyar zuciya shima ya ce, "Ban sani ba Didi, ni kaina bazan ce ba. Abinda na sani kawai soyayyarta ba yanzu bace, Didi ta jima a raina, ban fahimta bane sai yanzu. Wallahi Didi ina sonta, ina ?aunarta sosai." Didi cikin zumuWi ta ce, "To yanzu yaushe zaka je?."
"In anjima, amma ina so mu je tare dake, Ina jin nauyin mutanen nan sosai, ban taSa jin nauyin mutum kamar yadda nake jin nauyinsu suda mahaifinta ba, lokacin da mu ka je Kaduna kasa magana nayi saboda girmansa da naji a idona da zuciyata."

Didi ta ce, "bazan je ba, kai kaWai zaka yi faWan ka, in har da gaske kana sonta kai kaWai zaka je ka dawo da ita. Amma ka kwana da sanin babu lallai ta dawo a zuwan farko."

Omar ya Wan murmusa ya ce, "Hmmm Didi kenan. A yadda nake ji a zuciyata ko da za a shekara bata dawo ba indai zata dawo zan iya jira." Didi ta yi murmushi ta ce, "Gaskiya ne Omar, Allah ya tabbatar da alkhairi ya daidaita ku."
"Amin Didi. Ki tura min address Win."
"An gama angon Nayla." Murmushinsa ta ji mai matu?ar sauti kafin ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Kin san an kawo min motar da na siya? Kwanan ta huWu kenan, da yake bana cikin nutsuwa ban ma ganta ba sai jiya da daddare."

Didi ta ce, "ma sha Allah Omar! Allah ya sanya alkhairi. Wallahi shigowar Nayla rayuwarka alkhairi ne, daga lokacin da ta je Saudia na ce ta yi maka addu'a daga lokacin Narma ta shigo rayuwarka. Shigowar Narma rayuwarka kamar farkar da kai daga dogon baccin da ka ke yi ne."

Murmushi ya sake yi ya ce, "Didi!."
"Na'am angon Nayla." Murmushi ya sake yi wanda ya nuna mata ya ji daWin sunan har cikin zuciyarsa ya ce, "ina jin daWi in kika faWi sunan nan, amma yanzu dai ki faWa min inda zan je kin san bana son Sata lokaci."

Didi ta yi dariya ta ce, "To yanzu kuwa."
"Basai na siyi komai ba?."
"Zaka iya siya mana, koda kayan marmari ne zaka iya siya ka kai musu duk girmamawa ce."
"To" ya amsa a ta?aice. Kwatancen gidan Daddy tayi masa ya yanke wayar da niyar in an idar da sallar la'asar zai je ya samu Daddy dan ya dawo da matarsa.


Omar zai je bikon Nayla=؃??p?>?#?
KRB3P035
Arewabooks@nanahaleema11.? ?

Omar cikin ?arfin guiwa da karsashi ya shirya cikin manyan kaya, ya saka shadda kalar golden mai kyau sai Waukar ido take yi, sabuwa ce dal bai taSa sakata ba, tana cikin wanda ya Winka gab da Nayla zata tafi dan shi mutum ne mai son Winka suttura. Bayan ya kammala shiryawa ya saka hula ya tsaya yana kallon kansa.

Samun kansa ya yi da murmushi cikin mamaki wai shine yake wannan zumuWi akan wata mace, tabbas ya amince da maganar Didi ba son Narma ya yi ba, dan a cikin kashi goma na abinda yake ji yanzu ko kashi Waya bai ji ba a lokaci Narma. Wayarsa ce tayi ?ara ya san bazai wuce Didi ba yana dubawa yaga itace ya Wauka ya saka a kunne.

Da to kawai ya amsa sai ya kashe sai ga video call Win Didi ya shigo. ?auka yayi daga can Sangaren Didi ta ce, "kai ma sha Allah angon Nayla, gaskiya ka yi kyau sosai, daman Ina ta fargabar kar ka ce zaka je da ?ananun kaya shiyasa na kira ka."

Murmushi ya yi mai sauti ya ce, "Haba Didi! ya za a yi na saka ?ananun kaya?."
"Ai na san hali ne."
"Lokacin da bana so kenan, yanzu kuwa ai ina so." Didi tayi dariya ta ce, "Gaskiya ne Omar. Ka yi kyau wallahi, Allah ya dawo da kai Lafiya.
Duk abinda ya faru ina jiran labari, Kuma don Allah kar ka je ka ce zaka zauna akan kujera ka yi Warea-Ware, gidan sirikan ka ne dai."

Fuska a sake ya ce, "To Didi. Baki zo kin ga motar ba." Didi ta ce, "kai zaka kawo min ai, kai kuma yanzu hankalin ka baya jikinka, ka gama da dawo mana da Nayla in ya so komai ya biyo baya." Murmushi ya sake yi ya ce, "yaushe zaki haihu ne?." Didi ta ce, "na kusa, ka cigaba da yi min addu'a Allah ya sauke ni Wafiya."
"In sha Allah." Didi ta ce, "ka je ka dawo." Yanke wayar ya yi ya fito daga Wakin yana kallon falon.

Zuciyarsa ya ji tana bugawa sosai ya dafe saitin zuciyarsa yana jan numfashi, bai san me zai tarar ba in yaje shiyasa yake fargaba. A bayyane ya ce, "Allah ka bani ikon iya sarrafa kaina koda wani abun zai Sata min rai." Ya furzar da iska ya fito yana kallon sabuwar motarsa da take ajjiye. Motar mai kyau ce Sa?a wuluk zubin matasa ?an kwalliya kamarsa sai Waukar ido take yi.

Tunani yake ya je a motar ko kuma ya kira Bashir ya kai shi a machine?. Katse tunanin ya yi ya kira Tk ya ce yazo gate Win gidan. Ba jimawa yazo yana ganin Boss Win na su sai ya yi murmushi ya ce, "Allah ya biya Damisa, irin wannan kyau haka, gaskiya ka yi kyau sosai."

Murmushi yaga ya yi amma bai ce masa komai ba. Tk ya yi mamaki sosai dan kwana biyu ko fuska baya saki balle murmushi, lallai yana cikin tsananin farin ciki sosai. Motar ya buWe ya kalli Tk ya ce, "BuWe min gate Win." Tk ya buWe gate shi kuma ya fita da motar bayan ya bawa Tk key Win gidan dan ya kulle, Tk bayan ya kulle ya dawo masa dashi sannan ya ja motar da bismillah ya bar unguwar.

Kasancewar ranar babu aiki Nayla suna gidan Daddy ita da Salma da Ummimi. Ta ware sosai tana harkokinta duk da akwai abinda yake damunta daga zuciya amma bata bari ya yi tasiri, musamman da aka Wauki wannan lokacin Omar bai zo ba sai ta sake ?o?arin kawar da tunaninsa dan ta san bazai zo ba. Daman ta san ko number ta bashi da ita balle ta yi tunanin in bai zo ba zai yi mata waya, wannan ya saka ta daure ta danne zuciyarta ta cigaba da addu'a tana shiga cikin ?an uwa ana hira da ita.

Suna zaune a falon Daddy har da Daddyn kasancewar ranar asabar ce yana gida. Hira kawai suke yi tana cikin su tana dariya, Mummyn su Salma tana basu labarin ?uruciyar baban yayan su Salma wanda ya kasance mai tsare gida baya son raini.

Abba ne ya yi sallama ya shigo falon yana cewa, "Nayla tun daga bakin ?ofa nake jin muryarki." Dariya tayi a tare suka ce, "Abba sannu da zuwa." Ya amsa suka gaisa gabaWaya.

Abba ya kalli Daddy ya ce, "na je gidan Hajja sai take shaida min kwana biyu baka da lafiya, shine na shigo mu gaisa." Daddy ya ce, "Hajiya Hajja kenan, mura ce fa kawai take damuna, amma kowa sai da tace masa bani da lafiya.Yanzu Sa'adatu ma ta shiga ciki." Abba ya ce, "Ai mura ciwo ce babba Yaya." Ya kalli Nayla da take yiwa Salma raWa a kunne ya ce, "Nayla kina da aure fa, meyasa ki ke yawo ne haka? Jiya ma na ga motarki a kan titin maiguuri road, ki daina yawo ba tare da izinin mijinki ba, har yanzu da aure a kanki."

Nayla ta tsayar da dariyar da take yi ta sunkuyar da kai ta ce, "Abba gidan Twiny na je jiya." Abba ya ce, "amma a satin nan kin je gidana ai, sannan ga aiki da kike fita kullum, yau kuma ga ki a gidan nan, gobe kuma ki ce kin tafi gidan Khabir. Matar aure ce ke ki daina biyewa su Salma." Nayla ta ce, "To Abba."

Daddy ya kalli Salma ya ce, "ke wai Salma me yake fito dake kina barin Hajja ita kaWai ne?." Salma ta ce, "Daddy duba ka nazo yi fa."
"To ki yi gaggawa ki gama ki koma gida." Abba ya ce, "Ku shiga ciki Salma." Duk gabaWaya suka tashi daga main falo suka shiga ciki gidan.

Bayan fitar su Abba ya kalli Daddy ya ce, "har yanzu mijin Hauwa bai yi magana ba? Ni fa na gaji da jira wallahi, kawai a raba auren nan kowa ya huta." Daddy ya ce, "Bai zo ba Ali, abinda yasa bana so ayi gaggawa saboda Nayla tana son mijinta har yanzu, babarta Sa'adatu ta ce tana son mijinta wani dalili ne ya saka take cewa a raba auren." Abba ya ce, "Zancen


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login