Showing 207001 words to 210000 words out of 332344 words

Chapter 70 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14820

?alau" ta ?arasa faWa cikin salon da ya saka shi lumshe ido yana buWewa akan fuskarta. Ya matso da fuskarsa kusa da ta ta ya ce, "ciwon ki fa, babu matsala?." Bata ce komai ba saboda yadda yake bin wuyanta da hancinsa yana sauke mata numfashi mai zafi hannunta yana cikin gashin kansa.

Kissing wuyanta ya yi ba tare da ya Wago ba ya ce, "Ashiq!." Nayla da?yar ta iya buWe baki ta ce, "Uhum."
"Bani da kuzari mai yawa, zaki taimaka min?." Ta buWe idanunta ya kalle ta da ido ya Waga mata gira tare da haWe bakinsa da nata cikin tsananin kewa da soyayya.
KRB3P076
Nana haleema
#Thebeginingofsuccess!

Haka suka cigaba da zama cikin soyayya da ?aunar juna, abinda ya faru ya saka Omar ya ?ara ninka kulawar da yake bata. Ko fita ya yi baya jimawa zai dawo, in kuma ya kira wayarta aka yi rashin sa a bata Wauka ba lokaci Waya sai hankalinsa ya tashi ya dawo gidan. Baya iya bari ta fita ita kaWai, duk inda zata je sai ta jira ya kaita in ba haka ba sai dai a fasa. Ya shiga damuwa akan abinda ya faru, shiyasa yake kiyaye duk wata hanya da za a sake cutar da ita. Da yake abin bai baza duniya kamar wancan lokacin ba ba kowa ne ya san ya faru ba.

Cikin ikon Allah babu abinda ya sake faruwa, tun yana jin fargaba har ya daina ya sake suka cigaba da rayuwarsu. Wannan sabuwar kulawar da yake bata sai ta sake zama ?ar gata a wajansa, kulawa yake nuna mata zalla wacce babu sirki a ciki. Ko sau Waya ka je gidan zaka tabbatar da irin ?aunar da Omar yake nunawa Nayla, baya iya Soyewa ko kaWan, ko yaushe cikin faWa mata sirrin zuciyarsa yake baya iya yin shiru.

?angaren kasuwancinsa sai dai ace alhamdulillah, kuWi ne suke shigo masa ta ko ina kuma suna fita. Harka ta buWe ta ko ina, dan zuwa lokacin ya siyi bus da machine na kai kaya, sannan yaransa uku duk ya siya musu machine na hawa.

Babu wanda yake aiki a ?ar?ashinsa baya jin daWin zama dashi, sai dai yana da faWa wanda duk yaransa sun saba da faWansa, in yana yi ma wani lokacin basu cika damuwa ba saboda sabo, amma kyautatawa kam yana yi sosai. Naira biyar in ta shiga account Winsa sai Nayla ta sani, baya iya Soye mata samunsa haka in asara aka yi itama zata sani. Duk ribar da za a samu da abinda zai siyawa Didi da Marmerh, ya canjawa Didi waya da sauran kayan amfani musamman a Sangaren sana'arta. Marmerh kuwa ko shi ya haife ta sai haka, duk abinda zai samu sai ya siyawa Marmher wani abu, kayan wasa kuwa kamar banza haka yake siya ya kai.

Nayla kuwa abin ba a cewa komai, siyayyar kayan sakawa da tarkace kayan kwaliyya haka zai kawo Nayla. Wani lokacin ya kan rasa me zai siya mata saboda sai ya ga komai tana dashi, shiyasa ya fi mayar da hankali a siya mata kayan ado tunda ya ga tana so.

Omar ya sake yin haske saboda zaman da kuWi suke a hannunsa, ya sake zama mai class na ?arshe, magana ma sai ka zama mai sa a za a yi maka. Dan yanzu harkar kasuwancin sai in ta kuWi masu yawa ne ake maganar dashi, amma komai da Bashir ake yi.

? ? ?Kamar ko yaushe yana zaune a falo tana kusa dashi yana ri?e da hannunta saboda ciwon kan da take fama dashi, yana bin tabon ciwon da aka ji mata da yatsansa a hankali ya ce, "Kin san me?." Nayla ta ce, "sai ka faWa."

"Akwai abubuwa da yawa da nake son siya, Akwai machines da kayan ado da za a dinga amfani dashi amma ance sai an je China ake samu." Nayla ta ce, "to ya za ayi yanzu kenan?."

Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ina tunanin zan je China Jidda, amma ance samun visa China yana da wahala sosai, shiyasa kaina ya kulle na rasa ya zan yi. Kuma bana so na tafi na barki, bana son yin nisa da inda ki ke kar a sake cutar min da ke.

Nayla ta Waure fuska ta ce,  ana zancen arzu?i zaka kawo wannan maganar, don Allah ka daina faWar haka komai ya wuce. Ya sauke numfashi ya ce,  to na daina, ina jin ki.

Nayla ta yi murmushin ta ce, "Indai ta visa ne baka da case, akwai wanda Abiy zai yiwa magana a cikin sati Waya za a iya buga maka visa China." Ya ce, "Da gaske?."
"Da gaske wallahi, Indai har zaka je Win kayi passport da komai,?zan yiwa Abiy magana."

Ya Wan yin murmushi ya ce, "Shikenan, Gobe zaki raka ni passport office Win sai ayi." Nayla ta rungume shi ta ce, "Allah ya kaimu Rouhii, Allah ya cigaba da saka maka albarka a duk abinda ka saka a gaba." Ya yi murmushi yana shafa fuskarta ya ce, "Amin, ki cigaba da taya ni addu'a."

"Addu'a ko yaushe cikin yi maka mu ke yi." Ya kalle ta ya ce, "Daman ke ?ar baiwa ce ai, addu'arki da wuri karSuwa." Tayi dariya kafin ta yi magana ya ce, "da gaske nake. Tun daga ranar ashirin da bakwai ga watan ramadan na tsorata da lamarinki, kina kuka kina faWawa Allah abinda yake zuciyarki, a lokacin na ji a zuciyata Allah ya sa ba ?arata ki ke kaiwa ba."

Ta kwanta a jikinsa tana dariya ta ce, "kuma na kai masa ?arar ka, a lokacin da ka ke hararata, nace Allah kana ganin bawan ka, ina jin tsoron idanunsa yana hararata. Ya yi dariya mai sauti bai ce komai ba. Nayla ta ce,  Kukana nake kai masa, kuma wallahi Allah ya bani, babu abinda na ro?o wanda Allah bai cika min shi ba a wancan lokacin."

Ya yi murmushi ya ce, "shiyasa na ce ke ?ar baiwa ce ai. Ko zaki raka ni China? Kin ga dai ban taSa zuwa ba." Nayla ta ce, "ai da yawa wanda suke fara zuwa China duk basu taSa zuwa ba, a hankali suke gogewa su dawo ?an gari. Kuma da aka kashe min kuWi a tafi dani gwara ai siyi wani abun da kuWin, kar ka manta ginin gida ake yi."

Ya taSe baki yana kallon ta ya ce, "wai ke irin mai tausayin nan ko?." Tayi dariya sosai ta ce, "eh mu je a haka." Dariyar shima ya yi ta kalle shi ta ce, "zuwa nan da yaushe ka ke saka ran tafiya?."
"In aka samu visa nan da sati biyu ma zan tafi." Nayla ta ce, "lokacin bikinsu Ya J." Ya Waga girarsa ya ce, "Uhum sai ki yi abinda ki ke so ko? Shiyasa ki ke murna." Nayla ta langwaSar da kai ta ce, "ya za a yi na yi murna bayan Rouhiina zai yi tafiya ya bar ni?."

"Hmmm kya ji da shi dai" ya faWa yana murmushi ba tare da ya kalle ta ba. Itama murmushin ta yi kafin ya sake kallon ta su haWa ido ya ce, "Ya ciwon kan na ki?."

Nayla tayi murmushi ta ce, "tunda ka zauna ka ke tambayata, na ce maka na ji sau?i." Ya Wan yi shiru yana kallon ta kafin ya ce, "?azu Didi ta ce min ina ki ke, sai na ce baki da lafiya, shine ta ce min ko ciki ne dake." Nayla ta Wauke ido daga kallonsa sai ya ja tsaki ya ce, "yanzu sai ki ce na baki kunya ko?." Nayla tayi dariya ta Wago ta ce, "ni bani da komai."

"Ya aka yi ki ka sani?."
"Ka manta ina on period ne yanzu haka? Shine ma ya saka min ciwon kan." Ya Wan yi ajiyar zuciya ya ce, "To yaushe zaki yi cikin? Da Didi ta faWa sai na ji ina so ki yi cikin, sai ta saka min sha'awar ace kina da ciki Jidda. Yaushe zaki yi?."

Ta Wan kawar da fuska bata ce komai ba, ya ce, "Allah ki ka sauke ido ?asa zamu yi faWa dake, ke komai kunya yake baki? Maganar ma kunya take baki?." Nayla ta yi dariya dan ta san yana adawa da wannan kunyar, baya sonta ko kaWan, ita kuma tana ?o?arin ta rage amma wani lokacin bata sanin ta nuna masa ta ji kunya.

Nayla ta ce, "Allah ya baka ha?uri Rouhii, ba kunya naji ba. Dariya ka bani da ka ce yaushe zan yi ciki." Ya harare ta ya ce, "ni zaki faWawa ba kunya ki ka ji ba? Wanne hali ne naki ban sani ba Jidda?." Ta sake yi murmushi ta ce, "Allah dariya ka bani."

"Dole na baki dariya ai, ni ba wasa nake ba da gaske nake yaushe zaki yi ciki?. Yaushe zaki karSi ajiyar Wana ko ?ata Jidda?. Ina so na ga kin haihu, kin ga nida Didi kawai iyayenmu suka haifa, abinda zan haifa da wanda zata haifa shine ahlin mu."

Nayla ta karyar da kai tana kallonsa ta ce, "To YaMar samun ciki ai sai lokacin da Allah ya yi." Ya girgiza kai yana kallon ta ya ce, "haka ne....amma komai da niya ko?" Ya faWa yana buWe idanunsa yana kallon cikin nata ido. Ya bata kunya sosai, amma bata so ta nuna masa sai ta daure ta ce, "To na kusa."

"Yauwa, ki da gagagwa kin ji? Yara nake so da yawa in Allah ya bani, kamar guda goma haka." Ta wara ido waje ta ce, "goma zaka haifa?."
"Zaki haifa min dai."
"Duk ni kaWai?."
"A'a ni da ke."
"Ka san wahalar haihuwa kuwa Rouhii?."
"Ke kin sani ai, tunda kin haihu Win" ya faWa yana kallon ta. Sai tayi dariya sosai shima kansa murmushi yake yi ta ce, "Goma fa da yawa, in na haihu goma ai na tashi aiki."

"Baki tashi aiki ba, ai ni kika haifarwa kuma tare da ni zamu zauna." Nayla ta girgiza kai ta ce, "To YaMar Allah ya bamu masu albarka."
"Amin Ashiq!. Zan yi ?o?arin ganin na baki ajiya? ke kuma sai ki yi gaggawar karSa, in na mi?o miki ki karSa a wannan karon kar ki ?i kin ji?."
Nayla ta ce, "Me zan karSa?."

"Cikin Mana." Ta rufe ido ta ce, "Allah ka bani kunya." Ya taSe baki ya ce, "to bani kayata." Ta buWe ido ta ce, "me?."
"Kunyar mana, kin ce na baki kunya shine na ce ki dawo min da ita."

Murmushi ta yi tana jan gashin fuskarsa a hankali ta ce, "Babu wanda zai ce kana magana haka, in aka ganka sai a Wauka baka da baki nan kuwa saura kaWan ka kai parrot. Sai an zauna da kai ake fahimtar waye kai. Duk da a zama da kai Win sai kaso a fahimta Win, in baka so ba baza a gane ba. Duk da akwai ka da faWa da zare idanu, amma ka ?aro wani class shiyasa ?an mata suke maka layi." Murmushi ya yi mai sauti ya ce, "kece ?an matan ai."

"Don Allah ba a cewa ana sonka?." Ya kalli idanunta ya hango tsantsar kishinsa a ciki sai ya ce, "kema kin san matashi kamar ni ai dole a gani a yaba" ya faWa yana juya idanu kamar mace. Sai kuwa ta Wauke fuska zata bar jikinsa ya ri?ota yana dariya ya ce, "wasa nake miki, ni bani da farin jini ai balle ace ana so."
"Kai Win? Kana kallon kan ka a madubi kuwa?." Ya kwaikwayi muryarta ya ce, "bana gani, ni ai kece madubina Jidda."

Ta kwanta a jikinsa ta ce, "ni dai kar ka dinga kula su, kuma kar ka yi min kishiya, in ka yi min kishiya Allah mutuwa zan yi." Dariya ya sake yi ya ce, "Kina cemin yara goma sun yi miki yawa ba dole na fara tunanin wata ba."

Da sauri ta kalle shi ta ce, "zan iya, ko ashirin ka ke so zan yi, amma kar ka ce zaka yi min kishiya aka ji" ta faWa zata fara kuka. Ya yi dariya ya ce, "wasa nake miki, kar ki yi min kuka, shagwaaSSiya sarkin kuka. Wasa nake yi, ki kwantar da hankalinki kin ji?." Kai ta Waga kamar mara lafiya ta lafe a jikinsa tana sauraron bugun zuciyarsa, itama ta ta tana bugawa saboda kishinsa.
KRB3P077
Nana haleema.

? ? ?A washe garin ranar kamar yadda ya ce suka ce aka yi international passport, a ranar aka yi aka basu, Nayla ta faWawa Abiy abinda ake so ya ce a tura masa visa page Win Passport Win. Kamar yadda ta faWa cikin kwanaki kaWan aka samu visa ta fito, ya siyi ticket Win ta tafiya duk da taimakon Nayla ake komai tunda itace ta saba.. Ana e gobe zai tafi da daddare ta ishe shi da rigima da shawagaSa, sai rarrashinta yake yi duk ta ruWa shi. Shi kansa sai ya ji tafiyar ta fita daga ransa, dan baya so ya yi nisa da ita kamar yadda bata so.

? ? ?? Tana jikinsa tana jan numfashi a hankali alamun ta yi kuka ta gama, cikin sigar rarrashi ya ce, "in kina kukan nan ni ya ki ke so na yi? Tafiya zan yi fa, in na tafi ina tunanin na bar ki kina kuka bazan yi abinda ya kai ni ba. Sati uku kawai zan yi, kuma kinga biki za ku yi zaki ga lokacin ya yi saurin dawowa tunda kina cikin ?an uwanki."

Nayla ta Wago ta kalle shi suka haWa ido ya yi mata kiss a goshi yana shafa fuskarta a hankali, ta Wora hannunta a fuskarsa tana shafa gashin fuskarsa ta ce, "Ni ba cikin ?an uwa nake so na zauna ba, tare da kai nake so na zauna Rouhii. Zan yi kewarka, sati uku fa da yawa, Zan yi sati uku babu kai" ta sake faWa hawaye na sakko mata. Omar cikin damuwa ya ce, "kukan ne bana son gani kin san da haka, ki kwantar da hankalinki zan dawo ai." Ganin ta?i yin shiru sai ya sakata shirun ta dole dan kukan na ta yana tayar masa da hankali sosai.

? ? ? Ta yi matu?ar ?o?arin bada gudunmawar da zata tsaya masa a rai ya dinga tunawa koda baya nan, ai kam ta yi nasara, dan ya ji yayi tafiyar ta fita daga ransa duk ya bi ya damu baya so ya tafi ya barta. Sai tattalinta yake yi, da ta motsa ya dinga tambayar me ya same ta ko me take so, a haka suka wayi gari. Da kanta ta yi breakfast duk fuskarta da damuwa, a haka suka ci tare yana sake rarrashinta amma ta kasa sakewa yadda yake so.

Bayan sun kammala cin abincin ne ya ri?e hannayenta yana kallon ta ya ce, "Ki yi ha?uri ki kwantar da hankalinki, da na tafi zaki ga lokacin dawowata ya yi." Ta Waga kai ta ce, "Allah ya kiyaye hanya."
"Amin Ashiq. Ta so mu je ki taya ni haWa kayan kin ga lokacin tafiya ya kusa." Babu yadda ta iya tare suka haWa kayan dan jirgin ?arfe biyu zai hau.

? ? ?? Karfe sha biyu na rana Didi ta zo gidan yi masa sallama, da ta shigo ya yi murmushi ya karSi Marmerh da tayi wayo sosai yana yi mata wasa tana dariya. Ya kalli Didi ya ce, "Gidanki nake niyar zuwa sai ga ki." Didi ta ce, "Dole na fito ai na yi maka sallama." Ajiyar zuciya ya yi ya kalli Nayla, ya kalli Didi ya ce, "ki rarrasheta Didi, sai kuka take yi, kukan ne ni kuma bana so wallahi." Didi tayi murmushi ta ce, "To ai dole ta yi Omar, tafiya zaka yi har na sati uku fa, ta saba da kai dole ta damu."

Ya kalli Nayla da ta sake rau-rau da ido, ya sake kallon Didi a tausashe ya ce, "Ya zaki dinga zuga ta Didi? Yanzu sai ta fara kuka." Didi ta ce, "yanzu zaka tafi?." Omar ya ce, "Sai na yi sallar azahar, zuwa ?arfe Waya in sha Allah." Didi ta kalli Nayla da take tsaye har lokacin ta kalle shi ta ce, "Allah ya nuna mana lokacin."

"Amin, Zan je wajansu Bashir na dawo." Didi ta ce, "to sai ka dawo." Ya kalli Nayla ya ce, "Don Allah ki daina Waure fuskar nan ko kyau bakya yi" ya faWa da tsokana yana kallon ta. ?an kawar da kai tayi bai ce komai ba ya fita da Marmerh a hannunsa.

Didi ta dinga rarrashin Nayla da kalamai masu daWi har ta sake suka cigaba da hirar bikin Salma da Jawad. Ba jimawa ya dawo Marmerh tayi bacci a kafaWarsa ya kwantar da ita ya shiga cikin Waki. Nayla ta tashi ta bi bayansa ta samu ya shiga wanka ta dawo wajan Didi ta zauna. Ba jimawa ta sake komawa ta tarar ya shirya cikin ?ananun kaya wanda suka yi masa matukar kyau sosai. A tsaye ta tsaya a bayansa tana kallonsa shima yana kallonta ta madubi, a sanyaye ta tako ta ?araso inda yake ta rungume shi ta baya.

Juyowa da ita ya yi ya ri?eta ta gaba ya lumshe ido yana ji kamar ya tattara ta su tafi. Sun jima a haka a tsaye kafin ya Wago fuskarta ya yi kissing lips Winta na ?an mintina kafin ya kalli idonta ya ce, "Zan yi kewarki Ashiq!." Ta kalle shi ta ce, "Nima zan yi kewarka Rouhii! Zan yi kewar ka sosai."

Cike da tsokana ya ce, "ki faWa min gaskiya ni zaki yi kewa ko aljanun dare?." Dariya ta yi ta ce, "Duka biyun." Ya Wan buWe ido ya ce, "Ki ce Jidda itama ta zama ?ar hannu, itama yanzu ta zama always available." Kwanciya ta yi a jikinsa cikin kunya, ya yi dariya ya shafa bayanta ya Wago da ita daga jikinsa yana kallon ta. Ya kalle ta ya ce,  Ban da fita ke kaWai Jidda, ban da yawo a mota ko yaushe. Duk inda zaki je ki faWa min, sannan ki saka a kai ki kar ki fita da kan ki. Ganin zata yi kuka ya ce, "Kar ki min kuka, zo mu je" ya faWa yana ri?o hannunta ita kuma ta ta jawo trolly bag


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login