Showing 63001 words to 66000 words out of 332344 words

Chapter 22 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14431

ta ce,  Hajiya Nayla amaryar Omar. Murmushi tayi bata ce komai ba ta cigaba da abinda take yi. Didi ta lura so take ta tashi ta saka kaya amma nauyinta take ji hakan ya saka ta ce,  Bara na watsa ruwa na kwanta.
 To na dafa miki ruwan zafi?.
 A a garin da zafi ai, haka zan yi ta faWa tana shiga banWaki.

Ganin shigar ta ya saka Nayla ta tashi ta Wauko kayan bacci riga da wando masu kyau da tsantsi ta saka, ta fitowa da Didi doguwar riga ta ajjiye mata sai ta fita dan in ta fito ta shirya. Didi da ta fito ta ga kayan tayi murmushi ta shirya amma ba rigar ta saka ba ta saka wacce tazo da itaa.

A lokacin Nayla ta dawo Didi ta bita da kallo kayan sun yi masifar yi mata kyau, kasancewar kayan jajaye sun haska fatarta sosai, ga gashinta a kwance ya sauka har kafaWarta sai ta yi irin kamar wacce ta shirya zata je turakar mijinta.

Didi kallon ta take tana tunanin da me Narma ta fita ne har ya furta yana sonta bai ce yana son Nayla ba? In surar jikin Narma ce ta ruWe shi tabbas Nayla ta fita ?ira mai kyau da Waukar hankali, kawai ita a Soye surar take baka gani sai ka zauna da ita, saSanin Narma da take a bayyane ga kowa da kowa.

Didi ta ce,  Nayla kin yi kyau sosai, amma ki tattare gashin nan ki rufe kan ki dare ya yi. Nayla ta ce,  To Didi, amma baki saka kayan da na ajjiye miki ba.
 Ai na taho da nawa shiyasa.
 Amma da kin sani kin saka, zan ji daWi in kika saka ta faWa tana Waure kanta ta saka hular kayan ta Wauki turare ta mi?awa Didi.

KarSar turaren tayi ta ce,  Amma yana daWi sosai Nayla. Murmushi ta yi bata ce komai ba ta zauna tare da Waukar laptop Winta ta Wora laptop Win akan table Win da yake Wakin ta zauna akan cushion tana dammawa. Didi dai kallon ta take yi tana fatan Allah ya mallaka mata Omar kamar yadda take ?aunarsa, Allah ya saka zaman su ya Wore har aljanna.

Shiru suka yi baka jin sautin komai sai na keyboard Win laptop da take dannawa, cike da ?warewa dan da sauri take dannawa. Ajiyar zuciya tayi ta Wan ture laptop Win ta ce,  na gama, wani aikin Ogan mu ya bani sai da na gama hankalina ya kwanta, yanzu bacci zanyi ta faWa tana kallon agogo a lokacin ?arfe goma na dare. Didi ta ce,  da wuri haka? Na san bakya baccin wuri.
 Yanzu yi nake yi Didi saboda aiki, har na saba ma da yi Win.
 Gaskiya dai, dole ki saba.

Didi ta ce,  To ni kam zan kwanta. Nayla ta mi?e tsaye ta ce,  nima na gaji, kwanciyar zan yi. Didi ta ce,  in zaki fita ki kashe min hasken, sai da safe. Nayla da mamaki ta ce,  Ina zan je?.
 ?akin mijinki mana. Nayla ta Wan tafi tunani waye ma mijinta dan maganar Didi ta ruWata. Didi ganin ta yi shiru sai ta ce,  ?akin Omar zaki tafi.

Nayla ta wara idanu tare da dafe ?irji ta ce,  Innalillahi wa inna ilahir raji un! Didi har kin saka gabana ya faWi wallahi. Didi ta ce,  Meye na faWuwar gaban?. Nayla ta ce,  ?akinsa fa ki ka ce?.

 Eh nan na ce, kuma can Win zaki je ba. Nayla ta girgiza kai ta ce,  in kin ganni a lahira ai kaini aka yi Didi, iya faWar da ki ka yi ma gabana faWuwa yake yi balle na aikata ta ?arasa faWa tana dariya.

Didi ta lura ta Wauka wasa take yi hakan ya saka ta ce,  Ba fa wasa nake miki ba Nayla, Yau a Wakin mijinki Omar zaki kwana. Nayla ta kalli Didi a firgice ta ce,  Wai Didi da gaske ki ke?.
 Da gaske nake mana, ki wuce ki tafi. Da kina wanka ya dawo na tabbatar ya kwanta shima.

Nayla ta zubawa Didi idanu a tsorace ta ce,  Didi zan iya kwana a falo in bakya so na kwana tare dake, amma zuwa Wakinsa kamar barazana ne ga numfashina. Didi a tausashe ta ce,  Haba Nayla! Me zai hana ni kwana tare da ke? Kawai baza ki kwanta nan Win bane saboda mijinki yana nan, kuma Wakinsa akwai space ya ishe ku ku kwanta.

Nayla ta sauke ajiyar zuciya ta ce,  Didi don Allah ki bar faWa, bazan iya ba.
 Zaki iya Nayla, kuma zaki yi yanzu.
 Bazan iya ba Didi.
 Daman kin yi masa laifi ai, sai ki je ki bashi ha?uri daga nan sai ki kwanta.
 Gobe da safe zan bashi ha?uri amma ban da yanzu Didi, don Allah ta faWa a raunane tana kallon ta.

Didi ta kalle ta cikin bada umarni ta ce,  Nayla wacece ni a wajan ki?. Nayla a sanyaye ta ce,  Yayata.
 To ki bi umarnina ki tafi Wakin mijinki ki kwana. Nayla kamar zata yi kuka ta ce,  Didi ki yi ha?uri bazan iya ba, shima kuma bazai bari ba. Tsawa zai yi min ko ya wula?antani, bana son hakan bana jin daWi ta faWa ido na cikowa da hawaye.

Didi ta ce,  zai bari, na tabbatar miki bazai miki tsawa ba kuma bazai wula?anta ki ba. In kuma kin je ya yi miki tsawa ko ya wula?anta ki ki dawo mu kwanta tare, amma yanzu ki wuce ki tafi. Nayla ta dawo kusa da Didi ta ce,  Didi ta ya zan iya zuwa? Ni fa ban da Wazu ban taSa shiga Wakin ba wallahi, yanzu ma in ki ka ce min ya tsarin Wakin yake bazan iya faWa ba tunda Wazun ma a ruWe.

Didi ta dafata ta ce,  bazan yi abinda zai cuce ki ba Nayla ke kin sani, dan haka ki tashi ki tafi can ki yi bacci sai da safe. Nayla zata sake magana Didi ta goge mata hawaye ta ce,  kar ki ce komai, ki tashi ki je kawai. Shiru Nayla tayi bata motsa ba tana tunanin wannan chakwakiya da Didi take so ta saka ta a ciki. Maganar da Didi tayi mata ne ya saka ta yi ajiyar zuciya ta ce,  Didi hakan daidai ne kuma?.

Didi ta ce,  Daidai ne.
 Tsoronsa nake ji.
 Babu abinda zai miki, ki je ki gani. Nayla ta rufe ido ta buWe ta furzar da iska ta ce,  Didi ni ko akan tiles ne zan kwanta. Didi tayi dariya ta ce,  kwanan ne baza ki yi a nan ba, ki tashi ki tafi. Didi ta mi?e tsaye ta ce,  mu je na raka ki. Nayla ta mi?e jiki a sanyaye ta ce,  to bara na Wauki hijjab.

Didi ta ce,  ki ajjiye hijjab Win nan, ki tafi a haka me kayan jikinki suka yi?. Nayla ta girgiza kai a tsorace ta ce,  bazan iya ba Didi, ki yi ha?uri. Didi ta murmusa ta ce,  to naji, saka mu je. Nayla ta saka hijjab Win Didi tayi gaba tana binta
a baya ko wayar ta bata Wauka ba saboda ruWani.

A ?ofar Wakin Didi ta tsaya ta ce,  Sai da safe, ban yarda ki kwana a falo ba ciki na ce ki shiga tana faWa ta koma ta barta a wajan tana salati a zuciyarta.

Nayla ta kwashe sama da mintina ashirin a wajan tana tunani, ta rasa abinda zata yi ta shiga ko kar ta shiga? Zuciyarta a raunane take bata so ta shiga ya yi mata tsawa, sannan bata taSa kwana Waki Waya da namiji ba taya zata fara a yau? Yau Win ma kuma da Omar?. Dana sani take yi da ta saka baki Didi ta kwana a gidan, da ta san haka ne da ta langwaSe bata da lafiya ko dan kar ta zo.

Sai da ta yi mintina talatin cif a tsaye sannan ta motsa gaban ?ofar ta kasa kunne wai ko zata ji motsinsa amma shiru babu motsin komai. Ta yi ajiyar zuciya tana karanta duk addu ar da ta zo bakinta, ta murWa handle Win gabanta na faWuwa tana addu ar Allah yasa a kulle Wakin yake. Tana murWawa Wakin ya buWe, gabanta ya faWi matu?a ta taka ta shiga idanunta a kulle ba tare da ta buWe ba.

Omar yana zaune akan stool Win madubi sanye da riga mai hannun single amma ba fara bace dan gabaWaya wannan fuskar zaki ce a jikinta ya buWe baki. Sai wando karami wanda bai zo guiwarsa ba, gabaWaya jikinsa a bayyane yake dan hasken Wakin a kunne yake. Tunda abin nan ya faru ya kasa sukuni, ya rasa me yake damun zuciyarsa, nauyi yake ji a ?irjinsa tunda ya bar gidan har ya dawo.

A hankali ta buWe ido tana kallon Wakin tana fahimtar yadda tsarinsa yake. Sai a sannan ta lura da ya fi nata girma sosai tunda shi sofa cousion Win guda biyu ne masu girma da table ?arami a gaba, sannan funiture Winsa sun fi kyau dan set Waya ne da kayan da yake falo. ?akin a share yake tass babu alamun dauWa a ko kaWan, sai ?hamshin turarensa da Wakin yake yi da alama dai mai Wakin yana gyarawa.

Bata kalli inda madubi ya ke ba hakan ya saka tayi ajiyar zuciya ta ce,  Ashe ma baya nan, ni Didi ta saka ni a matsala ta ya zan iya kwana a Wakin nan? Ta faWa tana zare hijjabin jikinta dan zafi take ji. Garin zare hijjabin hular kanta ta biyo hijjab Win ta ma?ale a ciki.

Shi dai kallon ta yake yi yana mamakin abinda ya kawo ta, tunda ta shigo yake jin ?hamshinta, lokacin da ta cire hijjabin sai ya kasa daina kallonta tun daga gashin kanta har ?afarta da take sanye da room slippers mai kamar safa. ?are mata kallo yake yi cikin jajayen kayan da suka yi mata kyau, sun karSeta duk da basu kama jikinta ba amma surarta ta bayyana a cikin kayan musamman ?irjinta.

Ido ya lumshe jin zuciyarsa na bugawa sosai, ya haWWiyi yawu ya sake buWe ido yana kallon gashin kanta da ta Waure shi a tsakiyar kanta. Ya ji me take cewa yana mamakin kenan Didi ce ta turo ta tazo ta kwana tare dashi, lallai Didi ta raina shi da yawa, sai ya taka mata burki ya ga ta za?e da yawa a lamarinsa.

Kamar ance Nayla ta kalli gefenta ta ganshi a zaune yana kallonta, ta firgita tare da faWin,  Innalillahi!. Hijjab Win ta mayar da sauri jikinta har yana rawa ta ce,  Dama& Dama& ..Didi ce& .dama& .tace& .wai nazo na kwana a nan ta faWa a rarrabe tana kallonsa. Mugun haushin abinda ta aikata yake ji shiyasa bata samu zarafin magana daga gare shi ba. Ya Wauke kai yana cigaba da kaWa ?afarsa as usual.

Nayla ganin haka gabanta ya cigaba da faWuwa ta yi ?asa da kai ta ce,  YaMar Didi ce ta turo ni, na ce bazan zo ba ta ce sai na zo, ka yi ha?uri. Wani iri yake ji a zuciyarsa duk sanda zata faWi sunan nan, bai san me yake ji ba amma bai taSa jin abinda yake ji ba tunda ya zo duniya. Yana jin sunan ya soki zuciyarsa kamar allura, dan wani lokacin har sai ya runtse ido saboda sukar da yake ji, yana jin sunan har cikin jininsa.

Yana jinta tana magana nan ma banza ya yi mata bai tanka ba,amma a zuciyarsa yana tunanin irin matakin da zai Wauka akan Didi.

Tana tsaye yana zaune babu wanda ya sake cewa komai, ita tsoro take ji kar ta zauna tayi laifi shi kuma bazai ce mata komai ba. Ta gaji da tsayuwa tunda ta daWe a tsaye kafin ta shigo shiyasa ?afar ta ta Wan ri?e kaWan.

Tsam ya tashi tsaye da niyar zuwa ya samu Didi ya tako zuwa kusa da inda Nayla take tunda tana kusa da ?ofar Wakin. Kanta na ?asa bata san ya zo inda take ba sai motsisa ta ji, tayi saurin matsawa shi kuma ya ja handle Win ?ofar. Abin mamaki ?ofar a kulle take alamun an kulle su ta waje. Murmushin takaici ya yi yana cize baki dan ya san aikin Didi ne. A bayyane ya ce,  Didi ta gama raina ni. Nayla ta kasa kallonsa tunda ta fahimci ?ananun kaya ne a jikinsa ta kasa kallon koda ina yake tsaye. Tana mamakin kenan Didi kulle su tayi tunda gashi ya ja ?ofar a kulle, ita kanta mamakin Didi take yi balle shi.

Ta gaji da tsayuwar gashi bata son yin laifi daman ta san haushinta yake ji, shi kuma ya koma inda ya tashi ya zauna. Kallon kujerun Wakin tayi ganin ?arama ce ta zaman mutum Waya, duk da tana da faWi amma baza ta iya kwanciya a kai ba. A hankali ta taka ta zauna a kan kujarar ko inda yake ta kasa kallo.

Shi bai ce komai ba itama bata ce komai ba amma ta gaji bacci take ji. Kallon inda yake tayi ta ga idanunsa a kulle suke kamar bai san ma tana Wakin ba. Sai da ta tattaro nutsuwarta sannan ta ce,  YaMar bacci nake ji. A firgice ya kalle ta kamar daman jira yake tayi magana ya ce,  jira ki ke na zama gado ki kwanta!?. Yadda ya yi maganar a fusace ya saka ta kawar da kai dan idanunsa ma sun yi ja. Mi?ewa tayi da ?arfin guiwa ta ?arasa kan gadon tana tunanin kwanciya, a hankali ta zauna kamar mai ciwo kafin tayi salatin annabi ta kwanta ko hijjab Win bata cire ba.

Hasken Wakin ya dame ta, amma tana tsoron kar ta kashe tayi laifi hakan ya saka ta cure hijjabinta Wora akan fuskarta dan ta daina ganin hasken. Yana daga zaune ya kalli inda take yana mamakin wai shine zai kwana Waki Waya da wata mace a rayuwarsa, tunda ya yi hankali bai taSa zaman awa daya da ko wacce mace ba balle kwana a Waki sai ba yau. GabaWaya wani iri yake ji yana ganin kamar akwai raini a cikin lamarin. Duk yana kallon ta har ta kwanta da yadda ta Wora hijjab akan fuskarta duk yana ganin ta.

Shi kansa hasken ya dame shi, hakan ya saka ya mi?e ya kashe ya koma inda ya tashi ya zauna. Nayla jin an kashe hasken ta cire hijjabin tana ajiyar zuciya tana kallo shadow Winsa daga inda take kwance tana ta salati tana fatan bacci ya dau?e ta. A haka bacci ya kwashe ta ba tare da ta ga ya motsa daga inda yake ba.
KRB3P019
Arewabook@nanahaleema11.

Omar yana kallon ta har ta yi bacci a kan idanunsa, ya rasa ta yadda zai fara iya kwnaciya da mace a waje Waya shiyasa ya yi kamar bacci yake yi har ta kwanta tayi bacci. Tashi zaune ya yi sosai yana kallonta ya furzar da iska yana kallon ?ofa yana mamakin wannan ?arfa-?arfa na Didi. Yanzu in fitar gaggawa ta same shi fa? Ta rufe ?ofa ta baya ta bar su a cikin kamar yan prison.

Ajiyar zuciya ya sake yi gabaWaya ?hamshin Nayla ya mamaye Wakin, ?hamshin sai ya bada kala biyu da ?hamshin turarensa da ?hamshin nata turaren, sai hakan ya bada wani ?hamshi mai bala'in daWi da kwnatar da hankali. Shi dai ya san bazai iya kwnaciya da Nayla a waje Waya ba, kuma bai san a inda zai kwanta ba tunda Didi ta rufe ?ofar balle ya ce zai fita zuwa falo ko ya fita daga gidan.

Tashi ya yi ya dawo kan cousion ya zauna, ya Wora ?afarsa akan table ya jingina da kujerar yana lumshe ido. Hoton Naylan ne ya gifta masa a lokacin da ta zame hijjabi ta gashin kanta ya bayyana, ya buWe ido ya kalleta duk da baya ganin ta sosai amma tayi bacci. Tashi ya sake yi ya Wauko waya ya dawo ya zauna ya shiga page Winsu na Instagram ya duba sai ya ga gabaWaya an goge video Nayla kamar yadda ya ce.

Ajiyar zuciya ya yi ya kifa wayar a ?irjinsa yana jin zafi-zafi a ?irjinsa ba tare da ya san dalilin hakan ba. Shi dai ya san bai taSa jin abinda yake ji akan kowa ba sai ita Win, bai san me hakan yake nufi ba, amma yafi danganta hakan da yadda aka bashi ita baya so. Da wannan tunanin ya yi bacci a kan cousion ba tare da ya sani ba.

Haka ya dinga yin baccin yana farkawa saboda ya takura dan shi ya saba kwanciya a waje mai girma. Bai samu wani baccin kirki ba har asuba tayi, ya tashi zaune yana ri?e wuya saboda yadda ya ri?e masa yana Wan juya kansa kaWan. Kallon ta ya yi a lokacin ta motsa itama da alama ta ji kiran sallar a zuciyarta.

Ajiyar zuciya ya yi ya mi?e ya shiga banWaki, yana fitowa ya saka doguwar riga da slippers ya taka zuwa kofar Wakin, yana jan ?ofar yaji ta buWe. Dariya ya yi mai sauti a ransa yana girmama makircin Didi. Har zai fita sai ya kalleta ya ga bata tashi ba sai ya ja ?ofar kawai ya fita.

Da ya dawo bai duba inda Didin ta ke ba Wakin ya shiga kai tsaye ya samu Nayla akan sallaya. Kallon sa ta yi ta ce, "Ina kwana." Maimakon ya amsa sai ya zauna sannan ya ce, "Lafiya." Daga nan ya ja bakinsa ya yi shiru amma yana so ya tambayeta ciwon kan da ta kwana dashi amma izza da aji bazai bashi dama ba. Sai kuma ya sake tashi zai fita ya ake ji a kulle ?ofar.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login