Showing 234001 words to 237000 words out of 332344 words

Chapter 79 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14381

shiru bai ce komai ba ta ce,  Ya dai?. Ya Wan sauke ajiyar zuciya sannan ya ce,  ina Marmerh?.
 Bacci take yi, tana Waki. Me ya faru ne?.

 Didi suna son kashe Jidda ya furta ba tare da ya kalle ta ba. Didi ta dafe ?irji ta ce,  innalillahi wa inna ilaihir raji un! Kuma dai? Me ya kuma faruwa?. Bai Soye mata ba ya faWa mata komai har mafarkin da yayi. Ya Wan yi shiru kafin ya ce,  Hankalina ya tashi Didi, ban taSa jin tashin hankali kamar yadda nake ciki a yanzu. Tunda har abin ya kai ga mafarki mai munin wannan na tabbatar da akwai abinda yake shiryawa. Me cikin ya tsarewa ?an ?aura? Meyasa bazai huce haushinsa a kaina ba sai a kan ciki jikinta?.

Didi ta girgiza kai tana jinjina lamarin ta ce,  To kai meyasa ka zubarwa da matarsa ciki?. Ya kalle ta ya ce,  haka kawai sai na zubarwa da matarsa ciki? Ya akayi ma na san tana da ciki harda zan zubar?. Kawai an samu incident ne har cikin ya fita ta dalilina, amma ni a lokacin ko yatsan hannunta ban jiwa ciwo ba.

 Ya akayi ya san Nayla tana da ciki?.
 Abinda ya Waure min kai kenan, na rasa ta inda ya san tana da ciki har yazo Waukar fansa akan cikin ta.
 alamun ana bibiyar duk abinda ka ke yi kenan, ana bibiyarka itama ana bibiyarta. Babu lallai mutum Waya ne, wata?ila akwai masu da yawa Omar.

Omar ya ce,  na sani Didi, na san hakan zai iya faruwa. Ni na san masu bibiyata domin fansa suna da yawa wallahi. Didi ta sauke numfashi ta ce,  illar cutar da wani kenan a rayuwa, da baka aikata ba da hakan bai faru ba.

 Didi tunda Wal?iya ya saka a kashe Jidda nake nadamar rayuwar da nayi a baya, tunda na ga Jidda da ciwo a hannunta nake danasanin abinda na aikata. Meyasa baza su Wauki fansa a kaina ba? Ai ni na aikata ba ita ba, kuma yanzu ina ruwan cikin da yake jikinta da aka tsallako kansa?.

 Illar dabar kenan ai, wannan gabar da son Waukar fansar da take tsakaninku zata iya zuwa har kan jikokinka wallahi, bama cikin Nayla kaWai ba, har jikan da zaka bari a duniya sakayya zata iya faWa masa. Ka kiyayi sakayya Omar, ka kiyayi ha??in wanda ka zalunta ba tare da laifin komai ba. Allah yana yafewa bawansa laifin da ya yi masa duk girmansa, amma laifi tsakanin bawa da bawa Allah baya yafewa, sai dai in Waya ne ya yafewa Waya. Itama matar ?an ?aura yake ko waye ai itama ba ita tayi laifin ba, bata san komai ba balle kuma cikin jikinta da bai zama mutum ba. Ka kwashi yara aka je har gida aka yi mata abinda ya firgita ta har ciki ya zube, daga ?arshe ta rasa ranta. Omar in nace ha??in mutuwar ta a kan ka yake kar ka musa.

Ya girgiza kai ya ce,  A a Didi, babu ha??in ran kowa a kaina, don Allah ki daina faWa. Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce,  abar tausayin ma Nayla ce ba kai ba, ta auri mijin da sakayya da fansa take bibiyar rayuwarsa ta ko ina. Sau biyu ana ?o?arin kashe ta, yau ga na uku ana so a kashe ta har da Wan cikinta. Wannan aure bai amfana mata da komai ba sai tashin hankali, meye ribar wannan auren don girman Allah?. Ta gaba da baya Nayla bata dace da kai ba wallahi.

Omar ya yi shiru bai ce komai ba, Didi ta ce,  yanzu in aka sake cutar da ita da wanne ido zaka kalli mahaifinta? Wancan ya samu labari ya yi shiru bai ce komai ba, ya sake faruwa nan ma bai ce komai ba. Kana tunanin in ya sake faruwa zai yi shiru?. Omar bai ce komai ba ya sake yin shiru yana jinta. Didi ta ce,  Omar domin ceton rayuwarta da rayuwar abinda yake cikinta me zai hana baza ka sake ta ba?.
KRB3P088
Nana haleema

Wani irin kallo yake yi mata mai kama da baki da hankali, ya buWe ido yana sake kallon ta dan ya tabbatar tana cikin hankalin ta kuwa. Didi ganin kallon da yake mata sai ta buWe baki zata yi magana ya dakatar da ita cikin fusata ya ce,  da ina da wani wajen da zan je a bani shawara wallahi bazan zo wajan ki ba, a ko yaushe sai kin Sata min rai akan duk maganar da na kawo miki. Ni ki ke kallo ki ke cewa na saki Jidda? Ni ne zan sake ta?. Anya baza a kai ki asibitin mahaukata a buWe miki file ba? Dan wannan kalaman na ki bai yi kama da aikin mai hankali ba!.

Didi ta Wan yi murmushi dan wallahi dariya ya bata, ta ce,  Ni ba haka nake nufi ba, saboda ceton rayuwarta shiy..! A fusace ya katse ta ya ce,  shiyasa ki ke kallona kina cewa na sake ta? Ko kunyar idona baki ji ba ni ki ke faWawa haka Didi?. Kin ce aurena bai amfane ta da komai ba sai tashin hankali nayi miki shiru ban tanka ba, kince bata dace dani ba shima na share ban ce komai ba. Yanzu kuma idona ki ke kallo ki ke cewa na sake ta? Anya Didi ke jinina ce?.

Bata san lokacin da ta fara dariya mai ?arfi ba, ta kwanta a akan kujera tana dariya dan wallahi dariya ya bata, ko kaWan bata ji haushin kalamansa ba dan inda sabo ta saba. Tsaki taji ya yi, ta san ?arshen abun kuma fita zai yi. Da sauri ta mi?e ta ri?e hannunsa yana niyar fita, ta ce,  Don Allah yi ha?uri, ni ba da wani abun na faWa ba wallahi, bana so a cutar mana da unborn shiyasa na ce haka. Amma ka yi ha?uri bazan sake irin wannan maganar ba, ka dawo ka zauna don Allah.

Hannunsa ya zame ya ce,  bazan zauna ba, dan nazo ki bani shawara ki ka saka ni a gaba kina dariya dan kin mayar dani mahaukaci.
 Naji, ka yi ha?uri mu cigaba da maganar.
 Wallahi bazan zauna ba ya faWa yana Wauke kai. Didi ta ce,  to mu cigaba da maganar a tsaye. Yanzu ya kake ganin za a yi? Wanne mataki za a Wauka akan hakan?.

Banza ya yi mata bai amsa ba, ta ce,  don Allah ka yi ha?uri mu yi magana. Shirun nan bazai amfane mu ba, kar a cutar mana da ita ko abinda yake cikin ta. Omar ya sauke numfashi ya ce,  Meyasa baza su Wauki mataki a kaina ba sai kan Jidda ko abinda yake cikin ta?.

 In aka taSa maka ita sai kafi jin zafi akan a taSa ka, ko me suka yi maka baza ka ji ciwo a ranka ba, zaka fi jin ciwo in aka taSa Nayla ko abinda yake cikin ta. Shiyasa ?an ?auran ya yi jinkirin Waukar fansa, dan yana son ya taSa rayuwarka gaba da baya.

Ya yi shiru bai ce komai, Didi ta ce,  yanzu meye mafita? Zaka je ka samu ?an ?auran ka bashi ha?uri?. Wani kallo ya yi mata mai cike da harara, Didi ta ce,  eh Omar, abinda ya kamata ayi kenan. Ka je ku yi sulhu hakan zai fi, in aka bar maganar nan bamu san abinda zai faru ba.

Ya gyara tsayuwa ya ce,  Didi kai tsaye akwai wanda ya taSa ce miki baki da hankali?. Dariya ta kama Didi, amma gudun kar tayi ya fita sai ta ce,  a a, ba a taSa ba.
 To yau na faWa miki. Na daina tantama, tsaf aka buWe miki file a gidan mahaukata gado zasu baki. Didi ta karyar da kai tana Soye dariya ta ce,  to na gode.

 Dan mai hankali bazai cewa Omar ya je ya nemi sulhu da wani ?aramin alhaki kamar ?an ?aura, ni zan je na nemi sulhu dashi Didi? To Wal?iya da Kb ban je na nemi sulhu dasu ba sai wannan ?aramin abun da bai wuce na taka shi kamar yadda yake taka ?asa ba. Ni bazan je neman sulhu ba, nafi ?arfin neman sulhu.

Didi ta bishi da kallo, ta Wauka yayi sanyi akan Nayla zai iya watsar da girman kai ya je ya nemi sulhu a wuce wajan ashe da saura. Didi ta ce,  ni na rasa yaushe zuciyarka zata yi sanyi Omar, na rasa abinda za a yi maka da zai saka kayi sanyi wallahi.
 Babu, babu abinda zai saka na sakko ?asa Didi. Didi ta ce,  ai shikenan.

 Kawai zan je mu haWu dasu, ayi kare jini biri jini, koni ko su, ko su karni ko na karsu. Abinda nake so dake koda zasu kashe ni, ki tabbatar da Jidda ta kasance cikin ?oshin lafiya, ki tabbatar abinda yake cikin ta ya rayu cikin aminci. In ta haifi namiji ki saka masa sunana, in macece sunanki. Amma ki fara tambayarta, in tana da zaSin suna a saka zaSinta. Sannan ki san duk yadda zaki yi ki tabbatar da Jidda bata auri wani namijin bayan ni ba, ta cigaba da rayuwa a haka har tazo ta same ni mu tashi a aljanna. In ta auri wani bayan ni bazan taSa yin farin ciki ba har abada! Ya faWa so serious yana kallon Didi.

Rauni ya mamaye zuciyar Didi ganin da gaske yake maganar, ta ri?e hannunsa ta ce,  Omar me ka ke faWa haka?.

 Gaskiya nake faWa miki Didi, zan iya sadaukar da raina akan Jidda da abinda yake cikin ta. Marmerh a iya kallo Waya soyayyarta ta cika zuciyata, cikin jikinta kuwa tunda aka ce min an same shi nake jin son ko meye a zuciyata. Da na rasa abinda yake cikinta gwara na sadaukar da raina a huta. Daman ba saboda ni suke wannan abubuwan ba? To in na mutu ba shikenan an huta ba?.

Didi ta fara kuka cikin rauni ta ce,  babu abinda zai same ka, baza ka mutu ba Omar, baza ka mutu yanzu ba in sha Allah. Kuma Omar in ka koma ka Wauki makami dan tsayar da wannan maganar hakan ba masalaha bane, domin wallahi baza su ha?ura ba. Kuma Omar duk Waukakar da ka samu a rayuwarka ka rasa dame zaka sakawa wanda ya yi maka sai ta hanyar cigaba da abinda ka bari!?. In ka yi haka baka godewa Allah akan ni imar da ya yi maka ba, in ka aikata haka wallahi ka butulcewa ni imar Allah, kuma ka bar baya da ?ura, domin baza a taSa daina bibiyar mu ba har abada!. Ka fini sanin illar daba, kai da kanka ka taSa bani labarin wani babban mutum da yayi irin rayuwarku har girmansa, ?arshe har gida aka shiga aka yi masa yankan rago saboda Waukar fansa kawai. Kowa ya san daba haka take, kai zaka aikata laifi amma a kan danginka za a Wauki fansa, matu?ar ka sake komawa ruwa ka gama cutar kan ka da ahlinka. Yadda ka juya mata baya ina so ka sake juya mata baya, ka sauke kai ?asa domin wannan fitinar ta lafa.

Yayi ajiyar zuciya yana shafa goshinsa da yatsunsa kamar yadda ya saba, ya rufe ido ya buWe cikin rashin mafita. Didi ta ce,  ka je ka same su Omar, ba lallai sai ka bada ha?uri ba, ko kuWi ne ka biyasu akan su janye.

 Bazai janye ba, na san halinsa.
 To ku tattara ku bar Kano kai da ita, kana da arzu?in da zaka iya zama a wani garin ba lallai sai nan ba. Ya harare ta ya ce,  kawai ki ce naji tsoro na gudu na bar garin saboda tsoronsu.
 Ba tsoro bane Omar, ja da baya ne.
 Su a wajansu tsoro ne, kuma inaso ki tuna, Omar baya ja da baya.

Didi ta ce,  ni dai bana so ka butulcewa mahaliccinka akan ni imar da ya yi maka, Waukar makami ka je ka ya?e su ba naka bane, Allah ya yi maka suttura bai kamata ka wula?anta kanka ba, Allah ya Waukaka bai kamata ka ?as?antar da kan ka ba. Allah bai duba laifukan da ka yi ba yayi maka abinda baka yi tunani ba, meyasa zata gode masa ta wannan hanyar?. A nutse take maganar hakan ya saka take ratsa shi har zuciyarsa. Ya lumshe ido ya buWe ya ce,  Didi Jidda ake so a kashe fa, abinda yake cikin ta suke so su zubar tun bai zama mutum ba.

 Suna son zubar da cikin jikinta dai ba kashe ta ba, saka maganar da ka yi a ranka shine ya kai ga yin mafarkin za a kasheta. Mafarki kuma ba gaskiya bane Omar. Ka kwantar da hankalin ka, ka je ku yi magana cikin nutsuwa komai zai zama labari.

Yayi shiru bai ce komai ba, Didi ta ce,  Sai ha?uri haka sakayya take akwai ciwo. A haka ma dan kana sallah kana salati, kana sadaka kana taimako shiyasa Allah yake sassauta maka. Abinda nake guje maka kenan tun a baya Omar, babu rabon zaka fahimta sai yanzu. Allah yasa komai ya tsaya daga nan, mu cigaba da neman tuba muna faWawa Allah.

 Astagafirullah! Ya furta a hankali tunawa da ta addacin da suka yi a da. Didi ta sake nutsuwa ta ce,  ka je ka nemi mafita kafin wani abun ya sake Sullowa. Ina Naylan take?.
 Tana gidan Yayarta.
 To ka je ka san abinda zaka ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?yi kafin ta dawo.
 Zan yi Didi.
 Ko ka kira wannan dpo da ku ke shiri dashi ya shiga maganar, ko iyaka ya yi maka da ?an ?auran ai an rage.
 Na gaji da saka hukuma a lamarina Didi, da kaina zan Wauki mataki.
 Ha?uri zaka yi da Waukar matakin nan, dole a saka hukuma a ciki matu?ar kana son zaman matarka da Wan ka lafiya.

Ya sauke numfashi ya kalle ta ya ce,  Koda za a kashe ni ki tuna da abinda na faWa miki dai, ni jikina yana bani gwara naje su yi yadda suke so dani a ku huta da wannan tashin hankalin. A baya in naga mutum ya zubar da makamansa ya bada ha?uri saboda danginsa ina Waukar hakan a matsayin tsoro, kuma ina ganinsa a matsayin wanda ya bada maza. Ashe abinda ake ji kenan& gwara na je ayi ta ta ?are indai zaku zauna lafiya. Didi ta girgiza kai ta ce,  baza ka mutu ba in sha Allah, mutuwarka ba mafita ba ce. Ya kake so mu yi in baka nan? Ni da nake fatan na bar duniya Marmreh tana da kai kuma ka dinga faWar haka? don Allah ka daina, bana so.

Ya lumshe ido ya kalle ta sai yaga tana hawaye, yayi murmushi ya ce,  wai ke irin mai sona Win nan ko? Bakya so na mutu na bar ki. Ta goge ido ta ce,  eh ka Wauka hakan ne, sai na riga ka barin duniya in sha Allah. Na fi so na mutu na barwa Marmerh uba kamar ka, yallaSai mahaifinta, kai kuma ubanta. Yayi ?ar ?aramar dariya da son kawar mata da damuwa ya ce,  To ki mutu Win mana, ai ba Jidda ce zata mutu ba balle na damu ya faWa yana taSe baki.

Didi tayi dariya sosai ta ce,  Nima mijina yana sona, baya so na barshi. Kuma na janye maganata, kaje ka mutu ka ji Omar. Kuma wannan ?aunar da ake mana rawar kai a kanta nice silarta, ko an?i ko anso Aisha ce silar wannan soyayyar.

 Kin ci ?arya kin kwana da yunwa, wannan soyayyar haWin Allah ce, ko da Aisha ko babu Allah ya yi nufin ?ullata.
 Ko mutuwa tana da sila, faWa min waye silar?.

Yayi murmushi ya ce,  Anji kin zama sila, in kin isa ki raba ?aunar.
 Aikin banza, kamar ba kaine ka dinga masifa ba, kana ihu kana cewa ni bana so, ai bance ina sonta, kuma bazan sota ba. Didi in ke kika halicce ni sai ki saka min sonta, wallahi zan yanke ala?a da ita ta faWa cikin kwaikwayon muryarsa tana dariya.

Dariya yayi mai sauti kamar yadda take dariya, ya girgiza kai ya ce,  ni kika yiwa gori ko? Shikenan zan rama. Ta yi dariya ganin ta kawar masa da damuwar kan fuskarsa sai taji daWi. Ya kalle ta ya ce,  Jidda bata san maganar nan ba, kar ki faWa mata, bana so ta damu.

 Daman bai kamata ta sani ba, tsaf tsoro zai saka mu rasa unborn. Ya girgiza kai bai ce komai ba, ta matso ta Wan yi masa side hug ta ce,  Ka je kayi abinda ya kamata, amma kar ka bar baya da ?ura don Allah.

Ya girgiza kai ya ce,  to meye na shige min jiki? Sai kin saka matata taji hakan a ranta? Kamar fa cin amanarta ne. Didi ta Wago tana kallonsa taga ba murmushi yake yi ba alamun da gaske yake, sai ta ce,  ka faWawa matar ta ka, kafin ta shige maka jikin ni na shige. Kuma ka faWa mata ni Win nan dai babu abinda ban maka ba, tun daga kan wanka& . Bai bari ta ?arasa ba ya rungume ta yana murmushi ya ce,  zan rama wannan gorin Didi, ki bini bashi ya faWa yana raba kansa da ita ya fita yana jin damuwarsa ta ragu sosai. Didi ta biyo bayansa sai da ta ga ya tafi sannan ta dawo tana murmushi da fatan Allah yasa ya daidaita dasu komai ya wuce.
KRB3P089
Nana haleema.

Sai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login