Showing 3001 words to 6000 words out of 332344 words

Chapter 2 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14368

kowa ba kuma bai yi magana ba. Didi ta mi?e ta bi bayansa da sauri. Duk fitowa suka yi aka saka Nayla a motar Daddy zuwa gidanta da yake bayan layin gidan Hajja.

Masoyan Omar anya zai yarda ya zauna da Nayla kuwa?>?#?>?#?>?#?>?#?
KRB3P002
Arewabooks@nanahaleema11.

Omar a zafafe ya buWe gidan ya shiga ciki, ya cillar da hular kansa ya tattare rigar itama ya cire ya jefar dan ji yake kamar wuta ce a cikin rigar. ?ofar falon ce kawai ta bashi haushi, ya saka ?afa ya dake ta ta Surma ciki ya saka hannu yana dukan kansa cikin rashin sanin abinda zai yi. FaWar Sacin ransa Sata baki ne, shi kaWai ya san irin abinda yake ji a zuciyarsa, shi kaWai ya san irin tiririn da zuciyarsa take yi masa saboda abinda aka aikata masa.

A lokacin Didi ta shigo gidan ta fara karo da hularsa tana yin gaba ta ga rigar da ya cire ya cillar, ta kalli kayan sannan ta kalle shi sai zagawa yake yi alamun ya rasa abinda zai yi.

Yana jin motsinta ya jiyo ya kalle ta ya ce,  aka haWa baki da ke, aka haWa baki da ke tare da wanda basa ?aunta aka Waura min aure ba tare da izinina ba, aka aurar dani ba tare da na ce Inaso ba. Ni na faWa miki aure nake so? Na faWa miki Ina son aure ne Didi!?. Yadda ya faWi maganar da tsawa wallahi sai da gabanta ya faWi, ita burinta a yanzu ta saka ya je gidan amarya.

Didi ta ce,  ai bazan yi abinda zan cutar da kai ba Omar, duk abinda zai zamar maka alkhairi shi nake nema maka a rayuwa. Kai ya ke girgizawa ya kalli idanunta da nasa idanun da suka yi ja sosai ya ce,  ji nake a zuciyata meyasa ma ban amince na warware auren nan ba? Didi dan ina girmama ki sai ki dinga yi kin dole? Ba fa haifata ki ka yi ba. Dan na amince na rabu da ke ai ba uwata ba ce ba, meyasa ma na saurare ki har na amsawa iyayenta na karSi auren?.

Jin yadda kalaman sa suke fita ta san ya rasa control ne, ransa a Sace yake sosai. Ta yi ajiyar zuciya ta ce,  ka tsaya ka saurare& . Dukan ?ofar ya sake yi ya ce,  bazan saurare ki ba! Bazan saurare ki Didi, na gama sauraren ki akan wannan maganar!.

Sai da gaban Didi ya faWi ta firgita, bata taSa ganinsa a Sacin rai kamar na yau, ko akan abinda ya faru da Narma bata ga ya shiga wannan yanayi ba. Ta Wan ja da baya kar ya maketa ta ce,  Omar Ina sonka, bazan yi maka abinda zai cutar da mai ba. Ban saka ka karSi auren nan saboda na Sata maka ba, na saka ka karSa ne saboda& ..

Wata irin zabura yayi ya zo daf da ita ya ce,  saboda ki faranta min? Kina so ki ce kin saka karSa ne saboda ki faran ta min rai Didi? Ya girgiza kai ya ce,  Auren nan bazai taSa faranta min ta rai, kin haWa kan ki da mi?iyina a duniya kin aurar dani kamar wani ?ar tsanar roba. Yanzu zasu dinga ji a zuciyarsu sun zama kamar dole a rayuwata saboda su suka karSi aurena. Kuma wai kin san maganar amma ki ka yi min shiru, har ki ke cemin kar na baki kunya ashe akan wannan ne. Wallahil azim baki kyauta min ba, in na ce bana jin haushin ki ?arya nake yi, in ba dan ke Win ba ce wallahi ko wacece yanzu tana gadon asibiti in ma ban zama silar barinta duniya ba. Amma kema Win ma ki yi baya-baya a yanzu, yadda nake jin zuciyata wallahi zan iya sha?e ki.

Didi bata taSa jin tsoronsa ya shiga ranta kamar yau ba, yadda yake hayayya?o mata lamarin ya firgita ta sosai. Ta dake bata nuna masa ba, ta ri?o hannunsa ta ce,  Ka tsaya ka saurare ni. Yanzu ka Wauka ni ce a matsayin Nayla, aka aurawa wani ni kamar yadda aka aura maka, zaka ji daWi ace sake ni daga Waura aure da kwana bakwai kawai?.

 Gwara ace auren ya mutu yanzu akan ace ya jima. Ai wallahi in kece sai an raba auren, babu wani a duniya da zai aurar dake ba da sanina ba kuma na amince ki cigaba da aurensa. To in ma wai kina yi min misali da kan ki ne dan ki saka min wani tunani ki daina, dan kina sake tunzura ni ya faWa tana janye hannu ta daga jikinsa dan wallahi haushi take bashi.

 Yarinyar nan itace wacce ta shiga ta fita aka karSo ka daga wajan Sen, ba dan ita ba da wata?ila har yanzu kana can a hannunsu. Wanne irin karamci ne mahaifinta bai yi mana ba da muka je? Wanne irin tarba ce bamu samu daga gare shi ba ehe?. Da aka zo aurena a gidan kakarta aka yi komai, daga ?arshe ma kakarta ce tayi min kayan Waki. Meyasa zamu saka musu ta hanyar sakin ?arsu Omar?. Kana da halin da zaka ri?eta a yanzu, in da Omar Win baya ne da bashi da aikin yi nima wallahi bazan amince ba, saboda na san baza ka iya ri?e aure ba, amma Omar Win yanzu daban ya ke da na dah.

 Ka ji matsalar, har an fara yi min gorin ba ni ne nayi miki kayan Waki ba wata bare ce a gefe. Inda ni nayi ai baza ki kalle ni kina faWa min wannan har ki kafa hujja dashi ba. Kuma da ki ke zancen ita ta shiga ta fita aka karSo ni daga Abuja ni na saka ta? Na je na ce tayi min ne Didi?.

 Ba kai ka ro?a ba ni na ro?a, dan haka in na ro?a abu kamar ka ro?a ne. Banza ya yi mata ya juya mata baya yana jan numfashi. Didi ta ce,  Auren nan itama ba a son ranta ya faru ba, babu wanda ya san dalilin mahaifinta na aura mata kai a ?aramin lokaci, Meyasa baza ka fahimta ba?.

Jiyowa ya yi yana kallon ta ya ce,  meye ma sunan garin su?.
 Kaduna.
 Daga Kaduna kawai ya Wauko ?afa ya zo Kano, da kuma yazo Kanon sai ya rasa inda zai je sai gida waWancan munafukan mutanen nan, kuma kaf ?a?an da suke dasu ya rasa da wa za a Waurawa ?arsa aure sai da ni. FaWa min in ba shirya abin nan aka yi ba me aka yi? Haka kawai zuciyarsa zata faWa masa ya aura mata Omar ne?, Na san ?arsa ne?, Ko na taSa zuwa gidan su nace Ina sonta?, Ko kuma magana mai ?arfi ta taSa shiga tsakanina da ita ne?. Amsa min Didi.

Didi ta ce,  ?addarar aurenku ce ta kawo hakan, kuma shi yayi haka ne saboda dalilinsa wanda bamu sani ba, wata?ila hukunci ya ke yiwa ?arsa.

Ya wara hannaye tare da harWe su a ?irji y ce,  Ni kuma gani mai ba?in halin duniya wanda dani kaWai za a haWata ya zama mummunan hukunci a rayuwarta ko Didi?. Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce,  mun gama maganar nan da kai, Zaka ri?e aurenta babu saki koda mahaifinta ne ya ce ka sake ta kar ka saketa, ka ri?eta a hankali komai zai canja.

 Hmmm! Shine abinda ya ce kenan yana kawar da kansa gefe cikin matu?ar takaici. Didi ta ce,  Yanzu ka Wauko rigar ka da ka jefar, ka saka hular ka kazo mu je gidan da zaku tare kai da amar& .. kallon da ya yi mata shine ya hanata ?arasawa. Ya ce,  ?arasa mana Didi, Ina jinki.
 Omar Yayarka ce ni fa, ka dinga sanin irin abinda zaka yi min.
 Ai ina gab da daina kallon ki matsayin yayar tawa, dan babu abinda zaki sake saka ni nayi kuma a yanzu.

Didi a raunane ta ce,  ni dai don girman Allah ka saka kayanka mu je gidan da aka kai amaryarka, don Allah ka zo mu je kar ka ce min baza ka je ba.
 Au ni ne ma zan bita wani gida ba ma ita zata zo ba ko?. To bara kiji, na rantse da girman Allah baza ni ba, gwara na yi miki kankat ki ji, wallahi babu inda zan je.

Ajiyar zuciya Didi tayi cikin damuwa, tunda har ya rantse ta san bazai je ba wallahi sai ta shiga damuwa fiye da wacce take ciki. Ta kalle shi ta ce,  shikenan, naji baza ka je yanzu ba, amma in anjima sai mu je zan zauna har lokacin mu je tare. Kallon banza yayi mata dan bazai amsa ba, ya share ta ya cigaba da abinda yake yi.

 Omar in baka je yau ba babu daWi, amarya ce fa Omar, amarya fa. Tunda ka rantse ka ce baza kaje yanzu ba, zan zauna na jiraka har zuwa anjima sai mu je ta sake faWa kamar zata yi kuka dan damuwar Omar tsaf zata sakata hawaye

Bar mata wajan ma ya yi alamun bata bu?atar amsa, har zai gota ya juyo ya ce,  naji ana batun wani gwajin jini, Ina so ki sani babu wanda ya isa ya saka ayi min wani gwaji, gwara ki faWa musu kar azo ace za a Wauki jinina, dan wallahi sai na cakawa yaron da aka turo allurar yana faWa ya shige Waki ya barta a wajan a tsaye cikin rashin sanin abinda zata yi.

Didi cikin tsananin damuwa ta ce,  Ya Allah ka kawo min mafita, rigimar Omar yawa gareta. Wayarta taji tana ?ara ta duba ta ga AbdulHamid ne ta san yana waje yana jiranta. Numfashi ta fesar ta fita daga gidan ba tare da ta Wauki wayar ba.

A mota ta same shi ta shiga ta zauna tana sauke numfashi. Ya kalle ta ya ga yanayinta babu daWi ya ce,  Ya dai?.
Sai da ta yi ajiyar zuciya ta ce,  Omar gab yake da sakawa jinina ya hau YallaSai, ka ga masifar da yake zazzaga min kamar shine gaba ni?. Ya yi murmushi ya ce,  Ai dole yayi masifa fa, aure irin wannan baka shirya ba ai dole yaga kamar ba a kyauta masa ba.

 Yanzu maganar da nake maka ya rantse da Allah bazai je gidan amaryar ba, kuma daman na san bazai yi min alfarma biyu a yau ba. Na farko na tilasta masa ya furta ya amince da auren a gaban iyayenta, tunda har ya amsa musu ni kaina na san bazan iya ta?wara shi ya je gidan ba a yanzu, sai kuma wani lokaci. Gashi suna zancen gwajin jinin da ake yi na aure, ya ce na faWa musu aka turo wani ya Webi jininsa sai ya chaka masa allurar.

Dariya sosai AbdulHamid ya yi ya ce,  Kai Omar yana da bin dariya wallahi.
 Dariya ma ya baka?.
 Dariya ya bani mana. Amma yanzu ya za ki yi? Ya kamata ace yaje gidan amaryar tunda har ya amince da auren.

 Ya ce wai ba ma ita zata biyo shi ba shine zai bita? Ashe ba za a je ba. AbdulHamid ya murmusa ya ce,  Wannan amarya dai taga ta kanta, irin wannan miji mai zafin zuciya da zafin kai irin Omar zama dashi ai sai mai ha?uri. Ga kuma yadda auren ya zo yana gani kamar an bashi ita sadaka, sai dai mu yi fatan Allah ya sa ya ri?eta hannu biyu, amma zata sha wahalarsa na wani lokaci.

Didi ta ce,  wallahi tausayi take bani, sannan kunyar iyayenta nake ji. In ba ?addara ba wallahi tafi ?arfin Omar nesa ba kusa ba, yanzu haka aikin gwamnati take yi duk da dukiyar da mahaifinta yake da ita. Ga kyau masha Allah kamar ita tayi kanta. Shi ba abin farin cikinsa bane ya tsinci dami a kala? In aurota zai yi ina ya ga abinda zai kashe ya aureta?. AbdulHamid ya ce,  Ki bar zuciya da abinda take so, haka ki bar zuciya da abinda bata so. Ita tana sonsa, shi kuma baya sonta, kowa shi kaWai ya san abinda yake ji a ransa.

 Shiyasa take baki tausayi, inda ace bata sonsa da kaina zan saka ya saketa kawai a warware auren, amma tana sonsa sosai tana burin mallakarsa a matsayin mijinta. Shiyasa na?i bashi damar sakinta, ba dan na ba?anta masa nayi hakan ba sai dan saboda soyayyar da take yi masa. An ce ?iyayyar namiji tafi ta mace zafi, har gwara ace itace bata so akan ace shine baya so. Aka yi rashin sa a namijin ma irin Omar! Karkataccen mutum mai shegen ri?on tsiya. Tunda nayi masa faWa a gabanta yake jin haushinta, ashe itace matarsa dukkan mu bamu sani ba. Wallahi lamarin Omar yana damuna sosai.

Ya yi ajiyar zuciya ya ce,  kar ki damu, ki tayi masa addu a komai zai zama daidai. Kuma zancen ?iyayyar namiji duk zance ne kawai wuyarta dai ya fara sonta, daga lokacin da Allah ya saka masa sonta a zuciyarsa wallahi duk wannan wahalar da yake bata sai ta fanshe cikin ruwan sanyi. Ke ai kin fini sanin komai, kin san halin ku na mata da lagon maza da ku ka haddace a kan ku. Ki yi masa addu a kawai, in yaso gobe sai na dawo dake mu kai shi gidan amaryar. Yanzu ita da wa zata kwana?.

 To bana ce ba, amma muje gidan yanzu nayi magana da ita, gwara na faWa mata gaskiya kawai kar na Soye mata ai ta san halin Omar Win.
 Eh ki faWa mata, amma kar ki yi amfani da kalaman da zata ji babu daWi. Ki yi magana yadda zata fahimta, in yaso ko gida zamu wuce da ita ta kwana sai mu tafi, in yaso goben in kika rarrashi Damisar sai mu dawo.

Didi ta ce,  Damisar gaske, in ji Hajja tace carbin ?wai janka sai mai nutsuwa, to shi Omar mai nutsuwar ma hargitsa shi yake yi. Murmushi yayi ya ja motar zuwa ?ofar gidan dan babu nisa sosai, in da ?afa ne yafi nisa, in a mota ne gidan babu wahalar zuwa.

A ?ofar gidan ya ajjiye motar tare da kashe motar, Didi ta kalli gidan tana sauke numfashi. Gate Win gidan fari ne mai Waukar ido, ?ofar gidan da haske sosai gidan ya yi kyau kana gani kasan sabo ne. Wajan bashi da jama a sosai duk da Waya unguwar ne amma wajan gidan su Didi ya fi mutane akan wajan gidan Nayla. BuWe motar Didi tayi ta shiga gidan zuciyarta sam babu daWi.

Gida yana da wajan ajjiye miota guda Waya sai hanya mai girma wacce za siya ajjiye babura har gida biyu. Kana ganin gidan ka san sabo ne ba a jima da gama shi ba, komai sai Waukar idanu yake, ga wasu flowers da suka fara tasawa daga gefe an zagaye su anyi musu ado da ?ananun fitila a ciki. Sai ka hau steps guda biyar wanda aka zagaye su da staircase silver, ga chandelier light da ta haske ?ofar falon mai kyau.

Falon ta buWe ta shiga, yana girma amma ba sosai can ba sai dai ya yi kyau matu?a, kai kana ganin falon kasan kuWi da masu kuWi ne suka haWa shi. Ya sha kujeru na alfarma, ga 85 inchs plasma an Worata akan tv stand mai kyau da girma, ga turkish carpet da ya mamaye tsakiyar falon an Wora masa center table a kai. Daga can gefe ga dining room an saka dining table mai guda shida, ya sha adon show glass cabinet, an saka plates, mugs da glass cups. Kusa da dining Win fridge ne babba mai tsaho da girma. Daga can ?arshen falon an saka cabinet Win da aka yi ado turaren wuta da humra, an yi ado da fitila a ciki sai kawowa suke suna Waukewa. Didi da yake ta san gidan bata tsaya ?are masa kallo ba kai tsaye Waya ?aramin falon ta shiga.

Shi da yake bashi da girma kujerun sa basu kai waWancan girma ba, shima akwai tv da carpert komai ya fito tsaf gidan ?an gayu.

A zaune ta tarar da Nayla da Salma da kuma Jidda suna ta rarrashin Nayla da take zubar da hawaye. Sallamar Didi ya saka suka kalle ta tare da amsawa, ta zauna kusa da Nayla ta dafata ta ce,  Nayla har yanzu kukan ne? Jikinki da zafi, Salma ki yi mata allura.

Salma ta ce,  na yi mata, sai tayi bacci zata ji daWi.
 Sannu kin ji Nayla, Allah ya ?ara miki lafiya. Kiyi ha?uri kin ji?. Hawaye ya sakko daga idanunta ta share hawayen tana numfashi.

Didi ta kalli Salma da take kallon ta itama, kafin Didi ta ce wani abu Salma ta ce,  Ina angon? Ya ?i zuwa ko?. Didi ta sauke ajiyar zuciya ta ce,  A a yanzu zai ?araso shiyasa nazo, kin san hali basai na faWa ba, zuma ne sai da wuta. Salma ta murmusa kawai bata ce komai ba. Nayla jin zaizo sai ta mi?e kawai ta shiga bedroom bata ce komai ba.

Didi ganin ta shiga ciki ya saka Didi ta sauke murya ?asa ta ce,  Tsakani da Allah Omar bazai zo yau ba, ya ce ya karSi auren a yau bazai kuma yin wani abun a yau ba. Salma kin dai san halinsa kema, ni Win ma ba barina yayi ba. Na faWi haka ne akwai saboda bata da lafiya, kar na faWi abinda na faWa miki taji babu daWi a zuciyarta. Yanzu ya za a yi? Ko zata bi ni mu je gidana ta kwana? Kin ga ai babu daWi a ce ta koma gidan Hajja ko gidan Daddy ko?.

Jidda cikin damuwa ta ce,  gaskiya babu, ko mu tafi gidana ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login