Showing 165001 words to 168000 words out of 332344 words

Chapter 56 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14369

gefensa. Shiru ta yi bata ce komai ba kafin ta sauke numfashi ta ce, "YaMar ka yi ha?uri da abinda Mama ta yi maka Wazu don Allah, ban san meyasa Mama ta ce haka ba, amma don Allah ka yi ha?uri."

Idanunsa ya Wago ya kalle ta, Nayla ganin idanunsa sun yi ja ta san ransa a Sace yake sai ta ji babu daWi, ta san Mama ce kawo wannan Sacin ran ba tare da ta san dalilinta na yin haka ba. Cikin sha?ewar murya Omar ya ce, "kin ji na yi magana ne?."

A sanyaye ta ce, "A'a ban ji ba."
"To meye na bani ha?uri? A cikin kalamanta akwai kuskure ne?..." Nayla ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, Omar ya ce, "Duk abinda ta ce gaskiya ne, ban cancanci zama dake ba, kuma sona ki ke yi ba."

Nayla ta girgiza kai a raunane ta ce, "Allah ina sonka, wallahi ina sonka sosai." Ya girgiza kai shima yana kallon ta ya ce, "Wazu ma kin faWa da kan ki Jidda, Wazu da bakin ki kin faWa bakya sona. Dah na yi tunanin zamu iya rayuwa ko da bakya sona saboda ni ina sonki, ban Wauka abin yayi girman haka ba."

Nayla ta ruWe tana girgiza kai ta ce, "Wallahil azim in sonka, ina sonka YaMar, ina ?aunarka. Na so ka tun kafin ka soni, na so ka tun daga ranar da ka fara yin murmushi a kan idanuna, na sonka son da ban san adadinsa ba, na so ka son da ban san yawansa ba, kuma har gobe ina sonka. Allah shine shaidata, Jidda da Salma sune shaida, saboda kai nake zuwa Kano, saboda kawai na ganka YaMar!" Ta faWa tana kuka sosai.

?ago ido ya yi yana kallon ta, ganin yadda take kuka sai ya share mata hawaye da hannunsa, kafin ya yi magana ta ce, "Ko lokacin auren mu ni na aureka ne saboda ina so, duk abinda ya dinga faruwa a gidan nan ban taSa jin na daina sonka ba. Ko wacce rana, ko wanne awa, ko wanne minti, ko wanne second, ban taSa jin na daina sonka ba, sonka ko yaushe ?aruwa yake a zuciyata. Wallahi kalaman Mama ba haka bane, itama ta san ina sonka tamkar raina, ina sonka sosai, akan sonka zan iya mutuwa YaMar, ka yarda dani, kar kalaman Mama su yi tasiri a zuciyarka don Allah!. Itama ban dalilinta na faWar haka ba, amma itace mai goya min baya akan auren mu. Wata?ila tana gwada ka ne dan ta tabbatar kana sona ko baka sona. Amma ka yi ha?uri, kar ka ri?e maganar da ta faWa a ranka. Mamana ce, tana son duk abinda nake so, ta san ina sonka, itama kuma tana sonka!."

Lokaci guda duk wani Sacin rai da yake damun zuciyarsa ya ji gabaWaya ya gushe, ya zuba mata ido yana kallonta, bai gaji da jin yadda take furta tana sonsa ba shiyasa bai ce mata komai ba ya yi shiru yana jira ta cigaba da magana.

Nayla ta tsagaita kukan da take yi ta ce, "ban taSa cewa bana jin daWin zama da kai ba, ban san a ina? Mama ta samo kalaman nan ba, amma ka yi ha?uri wata?ila wani abun ne ya Sata mata rai, dan Mama itace mutum na farko da ta fara bani goyan baya akan aurenka. Uwata ce, haihuwata ce kawai Mama bata yi ba, amma duk wani farin cikin da Wa yake samu wajan mahaifiya Mama ta bani shi. Ganina da ta ke yi ina yawan shiga damuwa a kanka ta amince ta jure Sacin ran Abiy saboda farin cikina. Ka yi ha?uri, kuma ka daina cewa bana sonka, na so ka tun kafin ka so ni, na tabbatar ina yi maka son da baka yi min shi....."

Akan laSSanta ya Wora yatsansa yana kallon cikin idanunta yana hango zallar gaskiya a kalamanta. Ya zuba mata ido yana kallon idanunta da suka canja launi zuwa jajaye saboda kuka, ya lumshe ido ya buWe.

Cikin sanyin murya ya ce, "Shiii! Kar na sake ji kin faWi kalmar kina yi min son da bana yi miki. Kin san adadin son da nake miki kuwa Jidda? Kin san yadda zuciyata take bugawa akanki a ko wanne lokaci?. Hmmm! Da kin sani da baki ce haka ba, son da ki ke min bai taka kara ya karya ba akan wanda nake yi miki, kar ki yi saSo wajan faWar wannan kalmar......babban zunubi ne Jidda!" Ya ?arasa faWa muryarsa a can ?asa yana kallon idonta tare da buWe idonsa a cikin nata.

Nayla ta ja numfashi tana kallonsa ta ce, "Na yi ciwo ta sanadin son da nake maka, na kwanta a asibiti saboda tunaninka. Ina ganin ina wahalar da kaina ne saboda na san bazaka so ni ba, sannan a lokacin kana son Narma baza ka taSa kallona ba, sannan kuma ka tsane ni kana jin haushina. Tunanin hakan shine yake haifar min da ciwon da ?an gidanmu suka kasa gane kaina. Lokacin da ka ke a Abuja na kusa yin accident da mota saboda damuwata a wanne hali ka ke ciki, duk yadda zan faWa maka how much you means to me you will never understand wallahi, abu Waya na sani....wallahi ina sonka!" Ta faWa murya na rawa sosai, bakinta sai kar kar kar yake yi saboda rawar da yake yi.

Bakinsa ya Wora akan nata, ya Wan yi kissing kaWan kafin ya cire yana kallon ta ya zuba mata ido yana kallon ta tana hawaye. Nayla ta ja numfashi jin bai yi magana ba sai take tunanin har lokacin kalaman Mama basu bar zuciyarsa ba. A sanyaye ta ce, "Zan iya sadaukar da komai saboda kai YaMar....a kan sonka zan iya mutuwa Rouhii!."

Da zafin nama ya rungumeta, ta shiga jikinsa sosai ta matse shi a jikinta tana ji kamar za a ?wace mata shi. Jikinta har rawa yake yi ta rasa yadda zata sarrafa shi a jikinta, tana ji kamar runguma bata yi mata ba, ji take kamar ba a jikinsa take ba.

Sai da ta Wauki lokaci a jikinsa tana sauke nunfashi sannan ya ce, "Ni zuwan Mama ma ya yi min amfani, ko babu komai na ji sirrin zuciyar matata, ki faWawa Mama gobe ta dawo, ta dawo ta ga son da Omar yake yiwa ?arta, zata tabbatar da Omar yana son Nayla soyayyar da zata sakata farin ciki da alfahari" ya furta idanunsa lumshe yana jin yadda ta ri?e shi sosai, shima sai ya ri?eta da kyau yana jin buguwar zuciyarta a ?irjinsa. Bata motsa ba sai lumshe ido da tayi tana sake gyara kwanciya a jikinsa.

Murya a ?asan ma?ogwaro ya ce, "Wai tsananin ?auna ce in aka cewa mutum za a iya mutuwa a kan son da ake masa?..." ta ji ya tambaya amma bata amsa ba dan nutsuwa take so ta lalubowa kanta.

Ya yi ?ar dariya sannan ya Wagota daga jikinsa, ya ri?e fuskarta yana kallon idanunta ya ce, "To Jidda in ki ka mutu akan son da ki ke yi min ta ya soyayyar zata amfane mu bayan bakya nan?, kin tafi kin bar ni, wata?ila na yi rayuwa da wata sai abin tuna ki ya zo sannan zan tuna duk da tsananin son da ki ke yi min. A ganina ba mutuwarki nake da bu?ata soyayyata ta yi miki ba, zan fi bu?atar ingantacciyar rayuwarki, mu rayu a inuwa Waya, mu yi hira, mu yi faWa, mu shirya, mu ci abinci tare, mu je duk inda mu ke so tare, mu haifi yara, mu basu tarbiyya a tare da ke. Na baki farin ciki na hana ki ba?in ciki, na mayar dake gimbiya wacce ta fi sarauniya iya sarauta, na soki, na mayar dake aljannata kuma duniyata. Yin hakan tare dani shine ?arshen tanadin ?auna da soyayya a gare ni da samun ta tare dake Jidda! Hakan ne zai amfane mu ni da ke amma ba ta hanyar rasa ki ba Jidda....."

"Ya Wan numfashi mai Waukar hankali, ya lumshe ido ya buWe akan idanunta ya ce, "Cikar ?aunar da nake miki ba mutuwa ba ce Ashiq, tanadar miki da lokacina da kuma soyayyata a gare ki shine cikar soyayyar da nake miki, na sadaukar miki da kaina da rayuwata shine asalin abinda ake kira ?auna. Mu inganta rayuwar mu dan morar juna shine soyayya ba mutuwa ba. Mutuwa ai sau?i ne da ita ta, in Allah ya yi nufinta kamar a buWe ido a rufe ne har an gama. Amma rayuwa itace mai wahala, itace zaka tashi yau ka kuma tashi gobe, ba tare da ka san me zai faru da kai ba. Inganta rayuwarki da baki farin ciki shine asalin ?auna Ashiq, in ki ka mutu kuma wa zan bawa Jiddana!?" Ya ?arasa faWa yana kallon idanunta tare da murmushi kamar yadda take kallon kallonsa tunda ya fara magana.

Kalamansa sun gama kashe ta, ta zuba masa ido tana kallo dan ita bata Wauka haka ya iya kalamai masu kyau da saka farin ciki ba sai da suka fara rayuwar farin ciki dashi. Tana yabawa da hikimar da take cikin kalamansa sosai, tana yabawa da azancin da yake dashi musamman a kalaman yanzun nan. Duk da maganar ta sa sai ya ga dama, kalaman sun gama tafiya da ita bata san ta sake komawa jikinsa ta kwanta ba.

"I love you so much YaMar!." Ya lumshe idanunsa ya furta, "I love you Jidda!. Oh ashe fa ni bahaushe ne, ina sonki Jida!" ya faWa yana sake mayar da ita jikinsa tana murmushi jin abinda ya ce.

?? "Kar na sake ji kin ce zaki iya mutuwa akan son da ki ke min, ki ce zaki iya rayuwa dani akan son da ki ke yi min Jidda. Kuma ina so ki san ba ke kika fara sona ba ni na fara sonki, na fara sonki tun a ranar da na kuSutar dake daga hannun waWannan ?an iskan, a lokacin naji abinda ban taSa ji ba a zuciyata, amma bazan fahimta ba saboda ina ji da tantiranci da ?uruciya. Na yi dakon sonki na sama da shekara goma, na rayu da sonki, zan kuma mutu dashi, zan tashi dashi. Ina so na mori soyayyarki har a aljanna Ashiq. A cikin son da nake miki kaWan ki ka Wauka kina yi min, kamar a saka ?aramin cokali ne a Webi shinkafa a cikin buhunta. Baki san yadda Allah ya saka min ke a zuciyata ba ne shiyasa ki ke tunanin na ki ya fi nawa. Hmmm! Na ki bai wuce ruwa a kan farcen jariri ba."

Murmushi take yi cikin farin ciki da jin daWi da kuma walwala. Ta kasa Soye farin cikinta kamar yadda ya kasa Soye nasa sai murmushi suke yiwa junansu.

?? Omar ya Wan sassauta ri?on da ya yi mata, ya saka hannu aljanu ya Wauko wata ?ar ?aramar jaka ya buWe jakar ya fito da red colour ring cover ya buWe, zoben gold ne a ciki, ya Wauko ya kama yatsanta na kusa da na ?arshe ya saka mata. Kiss ya yiwa hannun nata yana murza yatsan kaWan ya ce, "komai aka baki kyau yake yi miki Ashiq,? ya haska hannunki sosai, sai na rasa gane ke ce kike yi masa kyau ko shi yake miki kyau?......" ya faWa yana kallonta. Gira ya Waga mata ya ce, "Kyautar farko daga wajan mijinki kuma masoyinki Omar, ina fatan zaki so ta har cikin ranki"

Nayla ta kalli zoben tana shafa shi, bashi da girma sosai amma a ido ka san yana da tsada dan nauyinsa zai kai four to five grams. Nayla ta kalle shi with full of surprise ta ce, "YaMar gold ne fa." Ya Waga mata gira ya ce, "Ko diamond ki ke so? In shi kike so sai na siyar da duk abinda na mallaka ka samo miki shi. Duk abinda na rasa na san zan iya sake samunsa, amma ke in na rasa ki na rasa kenan Ashiq!."

Dariyar farin ciki ta yi tana kallon zoben ta kalle shi, ta ri?e fuskarsa ta yi masa kiss a goshi with full of excitement ta ce, "Na gode.....na gode YaMar!. Na ji daWin kyautar nan ta ka sosai, na gode Allah ya saka maka da alkhairi ya bar mu tare, Allah ya cigaba da shiga lamarinka, ya Waukaka ka je inda baka yi tunanin zuwa ba."

Ya Wan harare ta kana ya ce, "Amin, amma godiyar ki cire ta. Ni ya kamata na gode miki Jidda. Kin zauna dani duk da kin fi ?arfin zama da ni Win, kin jure duk abinda nake yi miki a zaman mu na farko saboda ni Win kawai. Daga ?arshe kin mallaka min zuciyarki, ki ka ?ara min da kyautar jikinki. Na kasance mutum na farko da ya fara mallakarsu a duniya, ni ne wanda ki ka fara so, kuma ni ne wanda ki ka fara bawa jikinki. Jidda in ban gode miki ba me zan yi?..." ya faWa yana murmushi yana kallon ta. Blushing Nayla take yi ta kasa magana, ya Wora hannunsa a lips Winta yana shafawa ya ce, "Ni ya kamata na ce miki na gode ba ke zaki faWa ba."

Yana kallon yadda take murmushi ta kasa magana saboda farin cikin da take ciki, abinda yake buri kenan, fatansa ya samar mata farin cikin da ko a gidansu bata same shi ba, yana so ya yi mata gatan da ake cewa ta bari a gida ta dawo wahala, yana so ya saka farin cikin da kowa zai shaida tayi aure, ta auri wanda take so yake sonta. Ganin tana murmushi sai ya ji a ransa burinsa ya fara cika kenan.

Ya tausasa murya ya Wago da fuskarta ya ce, "Zaki jure zama dani? Ina da faWa Jidda, ina da zafi, ina da saurin fushi, ina da, ina da, ina da Win da yawa. Ki jure zama dani a duk yanayin da na samu kaina, kin san kaWan daga cikin halina Jidda. Dan kaWan zance ba duka ki ka sani ba, a cikin kashi goma na halina Waya zuwa biyu kawai ki ka sani, takwas zuwa tara suna jiranki. Ban ce bazan Sata miki rai ba, na san zai faru, amma in sha Allah farin cikin da zan baki zai ninka Sacin ran da zan saka ki." Nayla tana kallon idanunsa ta ce, "ni zan jure zama da kai a ko wanne hali a ko wanne yanayi, kai nake so ni kawai."

Bakinta ya shafa a hankali ya ce, "bakin nan ya iya faWar kai nake so, sai ka ce son wani auki ne dashi." Ta turo bakin gaba har lokacin yana ri?e dashi ya yi murmushi ya ce, "ShagwaSSiya kawai." Nayla ta ce, "ShagwaSaSSen Didi kawai." Dariya ya yi mai sauti ya ce, "Sai da ki ka ce Didi na tuna, ko ya jikin Marmerh ban sani ba."

Nayla ta yi murmushi ta ce, "Kana son Marmerh da yawa ko?." Ya yi ?asa da murya? ya ce, "Sosai Ashiq, ban taSa jin abinda a kallon farko ya shiga raina kamar ta ba, ana haifarta na kalle ta na ji tana shiga zuciyata sosai. Ina son Marmerh Jidda, amma duk son da nake mata na fi sonki a kanta."? Dariya tayi mai sauti cikin nishaWi ta ce, "ai matsayinta daban nawa daban my Love."
"YaMar!" Ya faWa yana Waga mata gira. Ta ce, "YaMar!." Lumshe ido ya yi ya buWe ya ce, "Da wata gurSatacciyar R Win ki."

? ? Bata ce komai ba sai murmushi da take yi, ya kalle ta ya ga ta kalle shi ta Wauke kai, ya matso sosai kusa da ita ya sanya bakinsa a cikin nata ya fara kissing a hankali. Lumshe ido dukkan su suka yi cikin tsananin farin ciki da shau?in junansu. Tsadaddiyar ?auna ya shiga nunawa Nayla, ya baje mata abinda yake zuciyarsa, yana sake tabbatar mata da ita Win dai yake so, lokaci kaWan ya mantar da Nayla a duniyar da take ciki, ta tabbatar ta sake tabbatarwa babu wata a zuciyar Omar sai ita Win kawai, ta tabbatar da son da yake mata daga rabbil azzati yake. Tuni suka manta da Mama balle kalamanta.

Byee masoya=?)?>?y?>?p?
KRB3P060
Nanahaleema.

Washe gari ma kulawa sabuwa ya sake buWewa Nayla, ya shagwaSata har girki a ranar shi ya yi mata, tana zaune a falo yazo ya yi feeding Winta baya cewa komai sai kallon idanunta, ita kuma kallon shine yake bata kunya. Tunda ta yi wanka ya hanata saka kaya, daga ita sai bathrobe wacce iyakacinta cinya, gabaWaya jikinta a buWe yake a Warere take saboda kunya.

Bayan sun kammala cin abincin Bashir ya kira shi a waya, sai a lokacin ya Wauka ya saka a speaker Bashir ya ce, "Boss barka da safiya." Omar ya ce, "kun tashi lafiya? Ya aiki?."
"Lafiya lau Boss, Daman akan kuWin nan da za a turo ne, kayan nan sun kusa ?arasowa." Omar ya ce, "yanzu zan tura."

"Godiya mu ke Tiger. Amma muna bu?atar ganin ka a company, akwai aikin da za a yi, mun kasa yi yadda ya kamata." Ajiyar zuciya Omar ya yi ya Wora hannunsa a cinyar Nayla yana zagayawa da yatsunsa a hankali ya ce, "zan shigo zuwa anjima" ya faWa yana katse kiran.

Bai kalli fuskarta ba cinyarta yake kallo yana sake zagawa da yatsansa a hankali, kallon fuskarta ya yi ya ga idanunta a kulle, sai ya mi?e tsaye ya shiga Waki ba jimawa ya dawo ya zauna yana duba littafin da yake rubuce-rubuce. Nayla ta kalli cikin littafin ta ga lissafi ne gabaWaya a ciki, da wanda aka bawa kaya da wanda za a bawa da wanda zasu bada kuWi. Nayla ta ce, "YaMar kana da good hand writing, wannan rubutu mai kyau kamar computer?." Murmushi ya yi kawai kafin ya ce, "Wauki wayata ki yi min transfer kafin na manta."

Mamaki ya bata jin wai ta Wauki wayarsa tayi transfer, daman akwai mazan da suke bawa matansu wannan damar ta sanin sirrin asusun su?. Bata tsaya dogon tunani ba ta Wauki wayar danna ta buWe alamun babu security a kai. Ta kalle shi ta ce, "wanne application ne?."

"First bank" ya bata amsa ba tare da ya kalle ta ba. Ta buWe mobile app Win ta mi?a


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login