Showing 285001 words to 288000 words out of 332344 words

Chapter 96 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

30872

zauna tana kuka mai taSa zuciya. Didi duk bata ji daWin abinda yake faruwa ba, tausayin Nayla take ji dan wannan shine ga mari ga tsinka jaka. Ta daure ta ce, "To Omar iya wannan tsawar da ka ke yi mata ma ai cikin sai ya zube da kansa, ka nutsu mana, ka san dole zata ji babu daWi, kwata-kwata Musliha watan ta nawa da za a ce tana da ciki?."

Ya kalli Didi ya ce, "in ma bata yi wata Waya ba bai dame ni ba, ai tun farko na faWa mata ko wata Waya ne Musliha bata yi ba ta samu wani cikin ina maraba dashi, amma dan rainin hankali cikina zata ce zata zubar? Dan shirme da zalla rashin hankali Wan da Allah ya bani zata salwantar min?. Hmmmm! wallahi da ta yi wannan gangancin da baza ta sake marmarin tuna ta zubar da ciki ba a rayuwarta. Ta zubar min da ciki!" Ya maimaita yana kallon Nayla.

? ? ? Sai kuma ya kalli Didi a fusace kafin yayi magana ta ce, "Ka nutsu mana, ka yi addu'ar Allah ya inganta shi mana,? sai masifa ka ke yi. Baka da tabbacin cikin zai rayu har ya zo duniya, wannan tayar da jijiyoyin wuyan da ka ke yi akai wata?ila Allah bai nufa za a haife shi ba. Ka cika kawo matsala wallahi, har yanzu ka kasa tsayawa ka fahimci abu kafin hukunci."

Kallon ta yake yi har ta gama magana fuska a haWe cikin kaushin murya ya ce, "Babu abinda zai samu cikina, zai inganta ya zo duniya kamar yadda Musliha ta zo duniya. Ki daina yi min fatan cikina bazai inganta ba, bana son wannan mugun bakin" ya faWa yana harararta.

Sai kuma ya ja tsaki yana kallon Didin ya ce, "Da ke ake haWa biki za a kashe min Wana ko? Da ke ake so a munafurce ni a zubar min da ciki ko Didi?. Har wani cemin ki ke yi wai in bazai zo duniya ba da yake kun ?ulla munafurci dake da ita. To wallahi in har ku ka zubar min da cikin nan daga ke har ita sai nayi shara'a da ku, kuma a inda kuka zubar dashi sai kun je kun kwaso shi kun dawo min da kayana. Allah ya hore min, zan iya rainon yara Wari koda ba nawa ba ne."

? ?? Didi kallon mamaki take masa jin wai sai ya yi shari'a dasu, ko wajan wanne al?alin zai kai su oho masa. Har yanzu halinsa yana nan, fusata da masifa. Takawa yake yi zai bar wajan ya juyo ya sake kallon su ya ce, "Ina maimaita mu ku, aka sake aka yi wannan gangancin wallahi....sai bai ?arasa ba ya girgiza kai ya ce, "dukkan ku kun san bana rantsuwa na karya, kun san sauran" ya faWa yana Waukar Musliha da take ta mi?a masa hannu ya hau sama a fusace.

Nayla ta kwanta a jikin Didi tana kuka sosai ta ce, "Ni fa sai na zubar da cikin nan Didi." Didi tana shafa bayanta ta ce, "Ki yi ha?uri Nayla, ki daina kuka. Ki bar zancen zubar da cikin nan tunda mijinki baya so."
"Kar ya so mana, ?ar?ari in na zubar ya sake ni, shine ?arshen hukuncin da zai yi min. Saki ai ba a kaina aka fara ba, mata nawa ake saki a kullum?. Tunda ba Waukar raina zai yi ba ai shikenan, ni sai na zubar bazan sake haihuwa yanzu ba" ta faWa a fusace.

Didi ta yi dariya jin abinda ta ce, ta san Sacin rai ne ya saka take faWar haka. Didi ta ce, "ki yi ha?uri ki daina faWar haka, zubar da cikin da ba na halak ba ma haramun ne balle cikin halak wanda aka samar dashi ta hanyar aure. Meye laifin cikin? Laifi ai na Omar ne ba shi ba. A kansa zaki huce ba akan cikin da Allah ya baki ba.? Don Allah ki bar batun zubar da cikin nan, ki yi ha?uri ki saka a ranki Allah ya yi zuwan abinda yake cikin ki duniya shiyasa hakan ya faru. Ki kwantar da hankalinki, Allah zai baki ikon rainonsa ki haihu lafiya."

? ? ? Nayla dai bata ce komai ba sai hawaye da take yi, wai wata bakwai da haihuwarta ace tana da wani cikin, ita ko shekara biyu bayan haihuwa ta ga mutum ya sake haihuwa sai ta ga kamar bai san ciwon kansa ba. Amma ita gashi ko shekara Waya ba a yi ba ta kwaso wani cikin, gabaWaya haushin cikin ya mamaye mata zuciya, Omar kuwa ji take kamar ta je ta dinga dukansa har sai ta wuce takaicinta akansa.

"Ki daina kuka Nayla, ki daina kuka bana so na ji kina kuka. Sannan don Allah kar ki zubar da cikin nan, kar ki biyewa zuciya ki aikata aikin dana sani." Nayla ta sassauta kuka tana jan numfashi cikin rauni. Rarrashinta Didi ta dinga yi har ta daina kuka, ta Wauko mata ruwa ta bata ta sha tana cigaba da bata baki har ta ga hankalinta ya Wan kwanta sannan Didi ta wuce gida. Amma ita kanta ta tausayawa Nayla sosai.
P111

Nayla haka ta kwana biyu bata kula Omar shima baya kulata, ta saka ?in cikin a zuciyarta hakan ya saka ta fara rama saboda damuwa. Sai kuma cikin ya zo mata da laulayi ba irin na Musliha ba, tafara amai ga zazzaSi da ciwon kai. Har lokacin haushinta yake ji itama haka, ba ya ma haWuwa da ita saboda takaici, itama bata zuwa inda yake. In ya tuna ta ce zata zubar masa da ciki sai ya ji haushin duniya ya ishe shi, sai ya ga wacce irin ?iyayya take yi masa da zata zubar masa da ciki? Duk ?aunarta da yake yi da wannan zata saka masa.

? ?? Yau ma Nayla na jikin sink tana amai kanta ya yi bala'in nauyi, Musliha kuma tana gefe tana kuka tana bu?atar uwarta Wauketa amma Nayla bata da wannan ?arfin. Dawowa ta yi ta kwanta a kan carpet tana juya kai ga sanyin da take ji. BuWe ?ofar aka yi, Nayla ta san? mai aikinta ce ta ce, "Salima zo ki Wauketa ki bata cerelec, sannan ki taimaka min da ruwa na sha kaina zai cire."

Omar ganin yanayin da take ciki sai jikinsa ya yi sanyi, tausayinta ya kama shi matu?a, ya tuna wayar da suka gama da Didi take sanar dashi cikin ya zo mata da laulayi sosai.

Nayla jin bata yi magana ba sai ta ce, "Salima kuka take yi ki Wauketa, bazan iya Waukarta ba. Sanyi nake ji, ki Wauko duvet a Waki ki rufe ni." Omar ya sake jin tausayinta ya ratsa shi, ya buWe bedroom Winta ya Wauko duvet mai nauyi da laushi ya rufa mata, ta ja shi har fuskarta ta rufe tana rawar sanyi.

?aukar Musliha ya yi da take kuka har lokacin ya kwantar da ita a jikinsa yana rarrashinta. Nayla jin har lokacin Musliha bata yi shiru ba sai ta mi?e zaune da?yar ta ce, "bani ita Salima, in ban Wauketa ba bazata daina kuka ba" ta faWa tana dafe kai hawaye na sakkowa daga idanunta. Rauni ya ji ya mamaye masa zuciya, tausayinta da haushin share ta da ya yi kwana biyu ya cika masa zuciya.

Ganin tana mi?o hannu alamun a bata Musliha sai ya kasa bata, ganin yanayin da take ciki kuma ta kasa share ?arta da take kuka sai ya sake jin rauni sosai a zuciyarsa, duk fushin da yake da ita ya kau daga zuciyarsa.? A tausashe ya ce, "Ki kwanta, zan bata da kaina." Jin muryar Omar ta Wago idanunta da suka koma jajaye suka haWa ido, hawaye ya sake sakko mata cikin rauni ta ce, "Tana ta kuka, yunwa take ji sosai, ka bata cerelac ko na je na bata."

"Zan bata, ki kwanta ki huta. Sannu" ya furta cikin tausayi yana kallonta. Komawa ta yi ta kwanta shi kuma ya tashi zuwa kan table Win Wakin, a nan ya ga duk abinda yake bu?ata da zai haWa mata kamar yadda ya saba, da kansa ya haWa mata ya zauna yana bata sai dai duk ya Sata kayan jikinsa itama jikinta haka. Tana gama sha ta sha ruwa sai kuma ta fara kuka tana kiran Mummy.

? ? Nayla ta fara bacci kenan ta ji ihunta tana kiran sunanta, ya kalle ta ya ga ta buWe ido a wahale ta ce, "bani ita."

"A'a Jidda, baki da lafiya ki bar ni da ita."
"Bazata daina kuka ba, in tana kukan bazan iya baccin ba, ka bani ita kawai." Ajiyar zuciya ya yi ya ?arasa inda take ya ajjiye mata Musliha. Hannunsa ya kai wuyanta ya taSa ya ji zafi sosai ya ce, "Jidda jikinki da zafi, tashi mu je asibiti." Nayla ta ce, "zai sauka, haka yake yi min kullum, zuwa nan da magriba zai daina."
"Haka zaki zauna da ciwo? Ki tashi mu je."
"Bana son tashi, kaina cirewa zai yi."
"To sai na Wauke ki."
"Ka bari kawai, zai daina haka nake yi kullum."

Tashi ya yi ya je ya canja kayansa ya dawo da ruwa da towel ya zauna a kusa da ita, ganin Musliha tayi bacci a kusa da ita sai ya Wauketa ya kwantar akan baby bed Winta da yake falon, ya dawo ya mi?ar da ita ya kwantar a jikinsa ya zuge zip Winta rigarta ya buWe ta baya. Cire mata rigar yayi gabaWaya ya ajjiye ya fara goge mata jikinta da ruwan sanyi.

? ?? Ajiyar zuciya ta yi jin sanyi na ratsa ta ya shafa mata ruwan a fuska, ta kifa kanta a ?irjinsa tana jan numfashi da?yar. Sai da ya ji zafin jikin nata ya ragu sannan ya saka hannu yana shafa bayanta a hankali cikin tsananin tausayinta. A hankali ya furta, "me zaki ci....Uhum?." Nayla ta girgiza kai ta ce, "babu."
"Ki tuna, me ki ke so a kawo miki?."
"Kunun gyaWa nake so da kilishi."

Omar ya ce, "bara na je na saka ayi kawo miki." Ta ri?e shi a jikinta ta ce, "Kar ka tashi, ina jin sau?in jikina a haka."
"Zan faWawa Salima ta yi miki kunun ne, shi kuma kilishin zan saka a kawo miki."
"Bana so ka tashi, ka zauna."
"To Sannu, ki yi ha?uri ki yafe min. Ban yi niyar saka ki a wannan yanayi ba." Bata iya magana ba ya cigaba da shafa bayanta a hankali, tausayi take bashi amma ko kaWan baya ji a zuciyarsa zai iya ba da goyan baya a zubar da cikin nan.

? ?? A hankali ya ji tayi bacci a jikinsa, ya yi murmushi yana kallon ta tare da kissing Winta a forehead yana shafa kumatunta a hankali.
"Ki yi ha?uri Jidda" ya sake faWa yana shafa kanta a hankali. ?aukarta ya yi ya kai ta Waki ya kwantar da ita ya rufeta ya rage mata ac. A falon ya zauna saboda kar Musliha ta tashi ta yi kuka ta tashe ta. Har aka yi sallar i'sha bacci take yi zuwa lokacin Musliha ta farka tana wajansa. Sai takwas ya sake shiga Wakin da Musliha a hannunsa, ta mi?awa Nayla hannu tana kiran Mummy.

? ?? Murmushi Nayla ta yi idar da sallar ta kenan ta ce, "Musliha!." KarSarta tayi ta rungume ta a jikinta tana shafa kanta ita kuma tana ta dariya. Fita ta ga ya yi bai jima ba ya dawo da tray a hannunsa ya zauna akan gadon ya ajjiye tray a tsakiya ya ce, "ga abinda ki ka ce kina so."

Nayla ta kalli kunun gyaWar ta yamutsa fuska ta Wauke kai ta ce, "ka Wauke, bana son ?hamshinsa ko kaWan." Da mamaki ta ce, "ke ki ka ce kina so."
"Ya fita daga raina wallahi, gwara dai kilishin,
Ka fita dashi kar ya saka ni amai." Bai musa ba ya tashi ya fitar dashi falo ya dawo, ya zauna kusa da ita ya fara bata kilishin a baki tana ci. Kilishin ya yi mata daWi sosai dan yana da yaji ita kuma yajin ne ke mata daWi.

? ? Ta ci da yawa sosai, ya bata ruwa ta sha ya Wauke tray Win daga tsakiyarsu ya ajjiye a gefe, Musliha tana tsaye a bayansa ta Wafe masa wuyan tana yi masa wasa.

? ? Hannun Nayla ya ri?e sai ta zame ta mi?e da sauri zuwa banWaki, da sauri ya bi bayanta ya ga gabaWaya kilishin da ta ci ya dawo har ta hanci. Ta gigice saboda yaji, hankalinsa ya tashi ya bata ruwa ta sha ya ri?ota suka dawo Waki ya zaunar da ita ya ce, "Abinda ki ka ci ya dawo, zaki kuma ci?." Ta ce, "Haka nake fama, komai na ci sai ya dawo."
"To ki kuma ci."
"Ko na ci zai dawo."
"Kuma ba ki faWa min mun je asibiti ba?."

Ta kalle shi ta ce, "fushi ka ke yi dani ai, kuma ko mun je asibiti babu abinda zasu iya yi min, laulayi ne kawai." Ya ri?o hannunta duka biyun kafin ya Wora hannu Waya akan fuskarta ya ce,"Amma lokacin Musliha ba haka ki ka yi ba, zan iya irga sau nawa na ga kin yi amai, bakya zazzaSi kuma bakya ciwon kai." Ta kalle shi da jajayen idanunta ta ce, "Wannan ya canja, Mama ta ce daman haka abun yake."

? ? ? Ya Wago fuskarta da ta sunkuyar yana kallon idanunta tana karanto tausayinta da yake kan fuskarsa sosai, ta kuma san ya yi rauni duk fushin da yake yi da ita ya kau daga zuciyarsa. A hankali ya kai bakinsa goshin ta ya yi kissing ya sake ri?e hannayenta ya ce, "Allah ya baki lafiya."
"Amin."

"Jidda!." Ta Wago ido ta kalle shi ya ce, "Ki yi ha?uri." Bata ce komai ba ya kuma cewa, "Kwana biyu na share ki, raina ne ya Saci akan batun zubar da ciki nan amma kina raina, kema kin san bazan iya ?yaleki ba. Ban san haka ki ke fama da ciwo ba Jidda, da na sani da na kasance a gefenki a ko yaushe, amma ki yi ha?uri!" Ya faWa a tausahse a hankali yana murza yatsun hannunta.

Nayla ta yi ajiyar zuciya ta ce, "ni daman wannan wahalar nake gudu shiyasa na ce zan zubar, kuma ga kula da Musliha. Bata yarda da su Salima balle su Wauke ta, daga ni sai kai take yarda dasu, kuma kai ba zama ka ke yi ko yaushe ba."
"Shiyasa na ce ki ha?uri Ashiq, tabbas kina shan wahala ga tsananin ciwo ga kula da ita, ki yafe min don Allah, ina ji kamar ban miki adalci ba. Na yi miki cikin da yake baki wahala kuma na shareki, sannan ga ?ata da ki ke kula da ita."

Ta Wago ido tana kallonsa ya ce, "Eh duka laifina ne, da sai na san hanyar da zan bi na yi miki irin wancan cikin mara wahala." Jin abinda ya ce sai ta yi murmushi wanda bata shirya ba, ganin ta yi murmushi sai ya samu damar cigaba da yi mata wayo, ya le?a fuskarta ya ce, "Da gaske nake, duk laifina ne." Ya dawo gabanta ya sauke guiwarsa a ?asa ya dafa guiwarta, Musliha tana daga bayanta a tsaye tana wasa da yarin kunnen Nayla.

"Sai ki faWa min tun farko baki son ciki mai wahala sai a san hanyar da za a bi, duk da cikin Musliha share ni ake yi amma gwara hakan akan ace kina zama cikin wannan ciwon. Jidda bana so na ganki cikin koda yanayin Sacin rai ne balle ciwo, Wazu da na ji zafi a jikinki ?iris ya rage ban yi hawaye ba. Ina yi miki soyayya ta har abada, inda na san hakan zai faru da ranar da za a samun cikin nan ba a yi gaggawa ba, wata?ila gaggawar ce ta kawo wannan wahalar."

Murmushi ta kuma yi bata ce komai ba. Ya ce, "Amma fa na ji haushi da ki ke zancen zaki zubar min da ciki, ba ke kaWai ba har Didi da ta biye miki ko kula ta na daina yi, ban da Wazu da ta kira ni tun ranar bana yi mata magana. Kashe min Wana fa zaki yi, kin san wahalar da na sha kafin na samar dashi kuma ki ce zaki zubar?. Raina ya baci matu?a, na fara tunanin ko dai kin daina sona ne shiyasa bakya son Wana?."

Nayla zata yi magana ya Wora hannunsa akan leSenta ya Wan bude ido kaWan ya ce, "Shiiii! ki jira na gama. Duk uzurinki akan cikin nan ban karSa ba, ko meye bai kamata ace ki furta zaki zubar dashi ba. ?ana ne fa, ko da sati Waya da haihuwar Musliha aka sake samunsa ban yi tunanin zaki ce zaki zubar ba, wasu nema suke yi basu samu ba, Allah ya bani kuma ni sai na wula?anta?. Jidda ko ba ta hanyar aure aka samu cikin nan ba banyi tunanin zaki ce zaki zubar ba, balle cikin na halak ne."

Yatsansa ya Wauke daga kan bakinta sai ta ce, "Nifa ban ce zan zubar saboda wani dalili ba, kana ganin yadda Musliha take shan wahala saboda rashin kula da ita da bana yi. Kuma ga cikin yana bani wahala, haka nake fama da wannan ciwo duk yamma da asuba, kaima ka daina kula ni balle na samu ko sannu ka ce min na ji daWi. Ga exams zan fara next week, ta ya zan iya da wannan yanayin ni kaWai?."

Zai yi magana ta ce, "kar ka ce min ni na saka kaina karatu, da izininka nake yi da baka amince ba bazan yi ba. Yanzu ka ga an ce dole na yaye Musliha saboda ina da ?aramin ciki, kana ganin nayi mata adalci? Wata bakwai kawai a duniya ace an yayeta?. Twiny ta jima da haihuwa, amma ko ciki bata dashi, ni na kasa faWa musu ina da ciki wallahi."

"Saboda cikin ba na halak bane?."
"A'a, ina yawan cika baki akan irin wannan haihuwar tun kafin na yi aure. Wata bakwai bama shekara ba, cikin ya yi wuri wallahi."
"Sai Allah ya haWa ki da miji mai so kuma jarumi, jamuri daga waje jarumi daga ciki. Ai ba aikin ko wanne namiji bane zai iya samar da wani cikin bayan haihuwa da wata bakwai ba, sai wanda Allah ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login