Showing 297001 words to 300000 words out of 332344 words

Chapter 100 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14406

da zuba daga idanunsa.
KRB3P116

A wannan yanayi bacci ya Wauke su dukka su biyun, basu tashi farkawa ba sai lokacin sallar la'asar. Nayla ta kalli fuskarsa da ta koma ja, idanunsa sun kumbura, gashi ya rame, gashin fuskarsa ya sake taruwa. Kallo Waya zaka yi masa ka san baya cikin hayyacinsa.

Nayla ta saka hannu tana shafa fuskarsa da take wuyanta har lokacin. A hankali ya buWe jajayen idanunsa ya kalle ta ta ce, "ana kiran sallah." Kai ya Waga bai ce komai ba, ta mi?e tsaye sai tayi kamar zata faWi ya ri?o hannunta da niyar ri?eta amma sai ta faWa kansa dan bashi da ?arfin iya ri?eta. Mi?ewa tayi daga jikinsa ta ce, "kazo ka yi alwala."

Hannunsa ta ri?e ya mi?e suka yi alwala suka yi sallar la'asar ya koma ya jingina da bango ya yi shiru baya cewa komai.

Nayla ta kalle shi cikim tsananin tausayi ta ce, "addu'a zaka dinga yi mata, wannan tunanin ba shine mafita ba." Ajiyar zuciya ya yi mai nauyi ya furzar da iska waje ya ce, "Ina Marmerh?." Nayla ta ce, "suna wajan Umma." Mi?ewa tsaye ya yi, ta mi?e itama ya ce, "zan je na ganta."

Hannunsa ta ri?e ta ce, "mu je tare." Tare suka fito har zuwa falon Nayla, suka samu Marmerh tana ta tsalle-tsalle tana yiwa Musliha wasa. Rauni ya sake mamaye zuciyar Omar, hawaye ya suka cika masa idanu. Marmerh ta juyo ta kalle sa sai gabansa ya faWi, rana ta farko da ya amince Marmerh da Didi take kama. Marmerh tana ganinsa ta yi dariya ta tawo a guje ta faWa jikinsa ta ce, "Daddy!." ?aukarta ya yi a kafaWarsa yana kallon fuskarta cikin ?auna da tausayinta da yake ji.

Marmerh ta ce, "Daddy, Ummi zani." Omar ya rufe ido ya buWe a raunane ya ce, "Marmerh Ummi ta rasu" Nayla ta ce, "Haba YaMar, ya zaka faWa mata haka kai tsaye? Duk da bata san mutuwa ba amma bai kamata...." Kallon Nayla ya yi sai bata ?arasa faWa ba, ya ce, "?arya ki ke so na yi mata? Na ce mata Mamanta tana da rai zata dawo in anjima?." Nayla ta yi shiru bata ce komai ba ya ce, "bazan iya saka mata rai akan abinda bazan iya bata shi ba har abada, gwara na faWa mata gaskiya."

Umma Saroot ta kalle su cikin rauni ta ce, "Ga abinci Omar, zauna ku ci don Allah." Ya Wago ido ya kalle ta, maganarsu ta ?arshe da Didi tazo zuciyarsa, ya lumshe ido ya buWe ya sake yin ajiyar zuciya ya kalli Umman kamar zai yi magana sai ya fasa. Umma ta matso ta ce, "Ku zauna don Allah." Nayla ta jawo hannunsa suka zauna, ta Wauki Musliha amma ba ita take so ta Wauke ta ba, shi take mi?awa hannu.

Ya karSe ta itama ya haWasu su biyu a jikinsa yana kallonsu. Umma ta zuba musu abinci Nayla ta karSa tana juyawa cokali bata ci ba shi kam bai ma karSa ba. Umma ta ce, "Omar." A hankali ya kalle ta ta ce, "ka ci abinci don Allah." Ajiyar zuciya ya yi ya karSa ya fara ci a hankali ba dan yana jin daWi ba, ko rabi bai ci ba ya ajjiye.

Kan Marmerh yake shafawa a hankali yana cewa, "Zan kula da rayuwarki, bazan taSa bari ki yi kukan rashin mahaifiya ba Marmerh. Zan sadaukar da duk abinda nake dashi dan na zauna dake kawai, zan miki gata a duniya, zan baki duk abinda ki ke so, bazan bari rayuwarki ta wula?anta ba, bazan bari ki san ba ni ne na haifeki ba Marmerh!. Zan tabbatar da kin samu nagarta a duniya, zan baki gatan da koda Didi tana da rai iya abinda zata yi miki kenan, bazan bari maraici ya taSa rayuwarki kamar yadda ya taSa ni ba, zan zama gatanki gaba da baya Marmerh, zan sadaukar da duk abinda nake dashi dan inganta rayuwarki! Ya faWa hawaye masu zafi suna sakkowa daga idonsa.

Sai Marmerh ta saka hannu tana goge masa ido, ya yi murmushi tare da sumbatarta a goshi, ya sumbaci Musliha da take kallonsa ya ce, "Zan kula da rayuwar ku gabaWaya in sha Allah, Allah ya bani aron ran da zan baku rayuwa mai kyau, Allah ya bani aron ran da zan kula da rayuwarku. In kuma nima na bi Didi kafin na samar muku da rayuwa mai kyau Jidda tana nan" ya faWa yana kallon Nayla. Suna haWa ido ta fashe da kuka ta kwantar da kai a kafaWarsa tana kuka. Umma Saroot ma kuka take yi gabaWaya ba su lura da Mama Zainab da Aisha da Baba Adamu a tsaye ba.

Mama Zainab ta ce, "Omar ku daina kuka, addu a." A hankali ya Wago ido ya kalle ta ya ce, "baza mu daina kuka ba, har abada!." Baba Adamu ya dafa shi ta baya ya juya ya kalle shi ya ce, "Sai ha?uri Omar. Ka daure ka cinye wannan jarabawar, kar ka sare lokaci guda. Allah ya ji?an Aisha ya gafarta mata, halinta na gari ya bita, Allah ya sa zaman kabari ya fi mata zaman duniya daWi."

"Amin& .amin ya Allah" ya furta yana lumshe ido tare da ajiyar zuciya. Yana ji ashe haka ake jin daWi in aka yiwa wanda ka rasa addu a?.

Marmerh ya kalla da take ta tsokanar Musliha tana yi mata wasa. Omar ajjiye Marmerh ya yi ya ajjiye Musliha ya mi?e tsaye Baba Adamu ya ce, "ina zaka je?."
Omar ya ce, "ba nisa zana yi ba, zan dawo yanzu."
"Amma baka da lafiyar da zaka iya fita kai kaWai."
"Zan iya, bazan jima ba zan dawo."

Mama Zainab ta ce, "A a Omar, kar ka fita wani abun ya same ka." Ya yi murmushi yana kallonsu yana jin wani iri a zuciyarsa, Didi da Nayla ne kaWai masu damuwa dashi, yau ssi ga dangin mahaifiyarsa suna tsoron kar ya fita wani abun ya same shi. Ya lumshe ido ya ce, "kuma tsoron kar nima na mutu ko? Suka kalle shi gabaWaya cikin rauni, ya girgiza kai ya ce,  Kar ku damu, Allah zai bani aron rai har sai na inganta rayuwar Marmerh" ya faWa yana fita daga falon. Nayla suka dinga bawa ha?uri ita dai jinsu take yi amma da ta tuna wani abun sai kuka.

Omar kuwa saboda ganganci da kansa ya ja mota, kai tsaye ma?abarta ya wuce ya je kabarin Didi ziyara. Addu'a yake mata yana kuka yana ji kamar ya tone kabarin ya fito da ita. Ya fi awa Waya a gaban kabarin sannan ya tashi ya shiga mota ya jima a zaune kafin ya tafi. Tafiya yake yana tunanin ya bar Didi a can shi kuma gashi a cikin mota yana tafiya, Didi bata duniya shi kuma yana duniya, sai ya ji kamar bai kyauta mata ba. Hawaye yake gogewa yana tafiya ya wuce gidan Didi.

A ?ofar gidanta ya ajjiye motar ya tsaya yana ?arewa gidan kallo. Jikinsa ya shafa yana nemn wayarsa, sai ya tuna bashi da waya bai ma san inda wayar take ba gashi yana son magana da AbdulHamid, kuma bazai iya shiga cikin gidan ba. Ana haka sai ga AbdulHamid ya fito Omar ya zuba masa ido, shi kansa AbdulHamid Win ya rame sosai kana kallonsa ka san yana cikin yanayi na damuwa. Omar ya sauke glass a sanyaye ya ce, "Mijin Didi."

AbdulHamid ya kalli Omar sai ya yi murmushi duk da gabansa ya faWi, Omar ya fito daga motar yana kallonsa AbdulHamdi ya ?araso inda Omar yake. Hannu Omar ya bashi suka gaisa ya ji jikin Omar zafi zau ya ce, "Omar baka da lafiya me ya fito da kai?." Omar ya yi ajiyar zuciya ya ce, "na jima a nan ina jiranka, bani da waya balle na kira ka, kuma bazan iya shiga gidan nan ba."

AbdulHamid ya yi murmushi ya ce, "Allah ya gafartawa Aisha."
"Amin ya Rabbi. Yanzu ma naje kabarinta na gaishe ta, amma ban ji ta amsa kamar ko yaushe ba. Tana cewa lafiya lau Alhaji Omar, da tana da rai da yanzu ta ce Omar me ya same ka, mu tafi asibiti" Omar ya yi murmushi hawaye na sake taruwa a idanunsa ya ce, "Amma yanzu ta tafi ta barni, ta bar duniya ni kuma ta bar a cikinta ko tausayin bata ji ba. Ko ta ya rayuwa zata yi min daWi bata tare dani oho, bata yi wannan tunanin ba ta mutu ta bar ni.

Sai kalamansa suka karyawa AbdulHamid zuciya ya goge ido ya ce, "Mutuwa bata bari wani dan wani ai Omar, dan ka rasa wani ba hakan yana nufin ka rasa farin ciki ba ne. Omar ya goge idanu ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Alfarma nazo nema a wajanka, ban sani ba ko zaka iya yi min."
"Ko wacce irin alfarma ce zan yi maka Omar, ka faWi komai da yake zuciyarka. Yadda Aisha zata yi maka duk abinda ka ke so nima zan yi Omar.

Omar ya girgiza ya ce, "Marmerh....! Marmerh nake so ka bar min ita ta dawo hannuna da zama. Na san abu ne mai wahala a gareka amma ka duba raunin da nake ciki na rashin Yayata, na san kai matarka rasa ni kuwa duniyata na rasa gabaWaya. Ka san itace komai nawa, ka san bani da kowa sai Didi. Zaman Marmerh tare dani zai Wan rage min wani abu kaWan daga cikin kewarta. Ka amince don Allah ka bani ita!."

AbdulHamid ya yi ajiyar zuciya kafin ya yi magana Omar ya ce, "Don Allah kar ka ce a a, nayi maka alqawarin zan bata tarbiyya mai kyau, zan inganta mata rayuwarta ba dan kai baza ka iya ba. Ina so na nuna mata ?aunar da baza ta yi maraicin uwa ba, kuma ba dan kai baza ka iya ba. Ka taimaka min don Allah!." AbdulHamid ya kalli Omar yaga gabaWaya ya canja, ya yi sanyi da rauni kamar bashi ba, gashi ya rame matu?a. Ya ce, "Shikenan Omar, na baka ri?on Marmerh."

Omar ya yi ajiyar zuciya ya kalle shi ya ce, "na gode, na gode sosai." Ya yi murmushi ya ce, "babu komai, na san zaka kula da rayuwarta sosai, Allah ya baka ikon kula da ita."
"Amin..amin& Na gode sosai."
"Sai batun gadon yayarka, na fara tartara abinda na san ta mallaka domin a sauke mata nauyi."

Omar ya ce, "ka yi duk abinda ya kamata." AbdulHamid ya ce, "in sha Allah, Ka koma gida baka da lafiya." Omar ya Waga kai ya shiga mota ya tafi. AbdulHamid ya bishi da kallo cikin tausayi, ya jima bai ga Wan uwan da ya fita daga hankalinsa saboda mutuwar yayarsa ba sai Omar.
P117

? ? ?? Omar bai shiga gida ba sai da ya yi sallar magriba, a harabar gidan nan suka haWu da su Bashir suna jiran sa. Ganinsa duk suka taho suka gaishe shi ya amsa suna sake yi masa gaisuwa. Ya kalli Bashir da ya kasance shine manager, shine mai kula da komai in baya nan ya ce, "Bashir ka cigaba da kula da komai, duk abinda kaga ya dace ayi, in ya zama dole na sani sai ka kira ni." Bashir ya amsa a sanyaye, bai taSa ganin Tiger a cikin wannna yanayi ba, sai ya bashi tausayi ya wuce su ya shiga ciki.

Da Umma Saroot suka haWu, tana tsaye da hijjabi ta juya baya tana magana da masu aikin gidan magana. Kallonsa ta yi a sanyaye ta ce, "Omar ka dawo? Ya jikin?." Ya girgiza kai ya ce, "naji sau?i sosai. Fita zaki yi?." Tsayawa tayi tana kallonsa, sai ta yi saurin kawar da mamakinta ta ce, "Gida zan koma Omar, tunda ka samu lafiya."

"Meyasa zaki tafi? Kafin ta bashi amsa ya ce,  ko an Sata miki rai?. Ta girgiza kai ta ce,  Babu abinda aka yi min Omar, kawai zan koma ne. Omar ya ce,  Ki zauna don Allah" ya faWa a sanyaye yana kallon ta. Zata yi magana ya ce, "don Allah!."

Sanyi da daWi ya mamaye zuciyarta tayi murmushi ta ce, "To Omar, zan zauna zuwa wani lokaci."
"na gode Umma!" ya faWa yana wuce ta ya hau sama. Murmushin farin ciki take yi ta Wauki waya tana kiran ?an uwan tana basu labarin abinda Oamar ya yi mata.

Bai iya kuma fita ba a Waki ya yi sallar i'sha, Nayla ta kawo masa abinci har cikin Wakin ta zauna a kusa dashi ta ce, "ka ci abinci." Ya kalle ta ya ce, "har yanzu ?irjina bai daina nauyin nan ba, da na zubar da hawaye ya ragu amma akwai saura."
"Sai a hankali ai zai daina, ka cigaba da addu'a. Ga wayarka Wazu Baba ya bani bayan fitar ka." KarSa ya yi ya ajjiye a gefe.

Nayla ta ce, "ka ci abincin." Da kanta ta bashi ya Wan ci kaWan ya ce ya ishe shi, bata matsa masa sai ya cinye ba ta bashi magani ya sha. Wuyanta ya taSa ya ce, "kema baki da lafiya, kin rame sosai."
"Na samu sau?i, rashin ?arfin jiki ne kawai da bani dashi." Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Na je gidan Didi."

Ta kalle shi ya Waga kai ya ce, "Gidanta na gaskiya da gidanta na duniya, na kai mata ziyara kabarinta na gaisheta amma banga murmushinta ba, kuma ban ji sautin muryarta ba. Na yi mata addu'a ina kuma fatan addu ar ta iske ta."

Nayla ido ya ciko da hawaye ta ce, "amma baka faWa min mun je tare ba?." Ya kalle ta cikin sanyi ya ce, "Zaki iya zuwa?."

"Na taSa raka Abiy kabarin Ummana amma an jima sosai, shima yana zuwa ziyara duk ranar juma'a har yanzu. Nima zan je na yiwa Didi addu'a, in zaka je ka dinga faWa min." Ya ri?e fuskarta ya share mata hawaye ya ce, "in sha Allah zan faWa miki." Nayla ta bi fuskarsa da ta koma ?ar ?arama da kallo ta ce, "ka tuna maganar Didi ta ?arshe?." Ya Waga kai alamun eh ta ce, "ka cika mata burinta don Allah, ka yi abinda zata yi farin ciki a cikin kabarinta."

Ya ce, "Zan yi Jidda! Wallahi zan yi!. Zan ri?e kowa kamar yadda take so, zan bar komai ya wuce bazan sake tuna komai ba. Zan ri?e su kamar iyayena, zan nemi shawararsu da albarkarsu da komai, zan kuma nemi su yafe min, zan cika birin Didi in sha Allah!. Da ace na san mutuwa zata yi da na bar komai ya wuce tun tana duniya, da ace na san zata mutu bazan ?i amincewa da abinda take faWa ba, da zan yi tun tana da rai ko dan na faranta mata rai. Haushin kaina nake ji da ban bar komai ya wuce tun tana raye ba, da ace nayi abinda take so da zan ga fuskar ta da farin tunda abinda take buri kenan. Amma yanzu ko na yi bazan ga hakan akan fuskarta ba, meyasa ban bari ya wuce tun tana da rai ba?.

Nayla ta ce, "Ko yanzu zata yi farin ciki, kai baza ka gani ba amma na tabbatar zata yi. Yin abinda take so shine cikar ?aunar da ka ke yi mata, kuma zata tanadi kyakykyawan murmushin da zata yi maka a aljanna, kuna haWa ido zata yi murmushi kyakyawan ha?oranta su bayyana." A ?irjinta ya kifa kansa ya sauke ajiyar zuciya hawaye na zuba a idanunsa. Kansa take shafawa a hankali da ya cika da gashi ta ce, "Ka cigaba da zubar da hawaye a duk lokacin da suka zo, kar ka dakatar dasu, zubarsu shine zai sassauta maka nauyin da ka ke ji."

Bai ce komai ba yana kwance a jikinta itama bata ce komai ba. Ya mi?e zaune ya goge idonsa ya ce, "na rasa iyayena Jidda, amma ban san haka zafi da Wacin mutuwa yake ba sai yanzu. Ban san haka ake ji ba sai a wannan lokacin. Ni na san bazan sake yin farin ciki ba har abada, zan zauna zaman jiran lokacin mutuwa yazo, dan rayuwa babu Didi baza ta yi min daWi ba.

"Na rasa mahaifiyata nima YaMar, amma ban san Wacin mutuwa ba sai yanzu" ta faWa tana kallonsa. Ta ce,  ka daina cewa baza ka sake farin ciki ba, Allah ne yake bada farin ciki da akasinsa, rashin Didi bazai hana ka farin ciki ba, tunda ba itace take bayarwa ba Allah ne. FaWar wannan kalmar bai dace ba, in kana faWar hakan kamar baka karSi ?addara ba kenan. Allah ne ya halicci Didi ya baka aronta, yanzu kuma ta koma gare shi, daman tashi ce ba taka ba.

Ya girgiza kai yana suke numfashi ya ce, "Didi ta yi min komai a duniya, ta hana kanta ta bani, ta ?i ci ta bani, ta ?i sha ta bani, ta yi wahala dani, itace nemana har police station, itace kawai mai damuwa da na ci ko ban ci ba, ita kaWai ce mai shiga damuwa da damuwata, itace kaWai mai yin jinya da rashin lafiyata Jidda. Ta sadaukar da komai nata saboda da ni, kullum tunaninta wacce hanya zata bi dan ingnata min rayuwata, ko yaushe cikin tausayina take, bata so ta ga na yi fushi balle na kasance cikin Sacin raiii!. Ashe iyakacin rayuwar da Allah ya tanadar mata kenan, ashe raunin da take cewa tana so ta gansa a fuskata raunin mutuwarta ce, ashe lokacin da take magana akan barin komai ya wuce na ahlina mutuwar ta ce sila! Ya ja numfashi ya sauke ya ce,  Allah ka ji?an wannan baiwa ta ka, Allah ka karSi shahadarta, halin ta na gari ya bita."

"Amin ya hayyu ya qayyu" Nayla ta faWa a sanyaye.

Ya ce, "Jidda na yanke hukunci ba tare da izininki ba, na je wajan mijin Didi na ro?e sa ya bani ri?on Marmerh ya kuma bani. Ban nemi shawararki ba kafin na aikata, bana so Marmerh ta bar hannuna ne shiyasa. Allah yasa ban takura miki ba."

Nayla ta Wan yi murmushi ta ce, "Didi tawa ce fa YaMar, ko bana auren ka wallahil azim


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login