Showing 21001 words to 24000 words out of 332344 words

Chapter 8 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14371

duk abinda zaka yi sai dai kayi amma baka isa ka yi min komai ba, I am not your slive baka isa ka cigaba da wula?anta ni ba. Dan ka ga nayi shiru na jure kana ganin tsoronka nake ji? Don t forget, I m a lawyer, na san right Wina ina da ikon ?in yin duk abinda ya saSani da ra ayina. Ina ?yaleka ne kawai saboda ko meye ya faru su Dad ne dalili, amma yanzu na daina. Zan dawo asalin Narma da ka sani, na daina Waukar rainin hankalin da ka ke yi min ina ?yaleka. Zan bar America zan koma Nigeria in ka isa ka hana ni ta faWa tana barin a wajan ta shiga Waki.

Dariya ya yi yana shafa fuskarsa a bayyane ya ce,  ai ban gaji dake ba Narma, barinki America ai ba yanzu ba dai lokacin da na ga dama. Mu zuba mu gani ya faWa yana cigaba da cin abincin sa yana murmushi, domin kuwa shi kansa ya tabbatar da ba son Narma yake yi ba akwai sha awar take bashi. Kafin ya samu abinda yake sha awa a tare da ita sai ya Wauka so ne, amma yanzu da ya samu ya tabbatar da sha awarta yake yi babu soyayyarta ko kaWan a zuciyarsa, kuma bai ga laifin kansa ba, dan duk abinda ya faru itace silar faruwarsa.
KRB3P007
ArewaBooks@nanahaleema11

Zaman Nayla da Omar babu cigaba sai ci baya, dan Omar bai ma cika zama a gidan ba, in kuma ya kwana to kafin ta tashi ya bar gidan wani lokacin bazai dawo ba sai tayi bacci. Ba kasafai ta cika ganinsa ba, dan in ya fita bai cika dawowa ba sai dare, sai dai in akwai abinda ya manta ko abinda zai yi shine yake dawowa. Ko da zasu haWu bazai ce mata komai ba itama tunda ya yi mata warning shikenan ta daina yi masa magana. Ta gaji da kula shi yana shareta ko ya harareta wani lokacin harda tsaki, ga tsoronsa da take ji shiyasa tunda ya hanata kula shi ta hanu har aka shiga watan ramadan.

Yau an kai azumin ramadan na uku kenan, kuma ya yi daidai da kwana goma sha bakwai da tarewar Nayla a gidan Omar.

Tana nan kamar yadda ta ke, bata mayar da jikinta ba kuma bata rame ba. Tana nan kamar yadda aka kawo ta da ?ar rama da kuma damuwa. Dan zaman shirun ma damunta yake yi, sai dai ta danna waya ta gaji, ta yi karatu ta gaji, ta yi bacci ta gashi abinda take yi kenan a gidan. GabaWaya zaman damunta yake yi shiyasa bata da walwala ko kaWan.

Tana zaune a falo sun gama waya da Twiny da take ?asar saudia ta je umrar azumi. Wayar ta ce tayi ?ara ganin sunana Yaya J sai ta Wauka da hanzari tana murmushi. Kafin ta yi magana ya ce,  Ina gate Win gidanki. Kamar an yiwa Nayla albishir da aljanna, ta mi?e da sauri ta saka hijjabi ta fita ta buWe gate Win ya shigo yana kallonta da murmushi.

 Yaya J ta faWa tana rungume shi cike da murnar ganin Wan gidansu. Dariya ya yi ya ce,  Nayla kin kasa girma har yanzu, ke fa matar aure ce ya faWa yana rabata da jikinsa amma ta ri?e hannunsa gam tana kwantar da kanta a kafaWarsa.
 Sannu da zuwa Yaya J.
 Yauwa Nayla. Hannunta na cikin nasa suka ?arasa falon ta zauna shima ya zauna ya ce,  parlour gidan nan na ki ya yi kyau Nayla, ya burge ni. Nayla tayi dariya ta ce,  Ina yini Yaya J.
 Lafiya lau Nayla, ya ibada?.
 Alhamdu lillah Yaya J. Ya hanya?.

Jawad ya ce,  Alhamdu lillah. Da yake tun jiya ina Kano ba yau na shigo ba. Nayla ta ce,  shine ba ka zo ba tun jiyan?. Ya murmusa ya ce,  gashi ai na zo yanzu.
 Yanzu mu ka gama waya da Twiny.
 Eh, ita kwanan ta biyar da tafiya ma ai ko?. Nayla ta Waga kai alamun eh Jawad ya ce,  Abiy fa? Kun yi waya?. Nayla a sanyaye ta ce,  na kira shi na yi masa Allah ya kiyaye, yanzu ma ma san sun sauka ko?.

Jawad ya ce,  Da yake Egypt airline suka hau kin san yana da wahalar sha ani, sai sun yi transite Nayla tayi ajiyar zuciya ta ce,  Allah ya kiyaye. Ya bita da kallon tausayi a zuciyarsa, amma a bayyane ya ce,  Amin Nayla.

Ya ciro takarda daga aljihun ya ce,  Ga takardar canjin wajan aikinki, na saka wata abokiyar aikin ki tayi komai da komai. Yanzu ki yi signing a wannan takardar zan bayar a kai can Kaduna Win, gobe in Allah ya nuna mana sai ki je branch Win da yake kusa da gidan governor ki kai wannan takardar ki yi signing shikenan.

Nayla farin ciki ya mamaye mata zuciya, ko babu komai zata rabu da zaman kaWaicin da yake damunta wani lokacin. Biro ya bata da kansa ta saka hannu ya karSa ya ce,  zan bayar a kai can Kaduna Win, wannan kuma sai ki tafi da ita goben. Ta karSi wacce yake mi?o mata ta ce,  To Yaya J, na gode sosai. Na ji daWi wallahi.

Murmushi ya yi ya ce,  zan cire miki hanci keda kin gode Win ai. Ga key Win motar ki da nayi alqawari, gata can a waje an zo miki da ita, akwai laptop Winki da iPad Winki a ciki. Akwai kayan ki da Mama ta bani da dai abubuwan ma dai suna cikin motar. Nayla ta Wauki key Win da ya ajjiye kusa da ita cikin tsananin farin ciki ta ce,  na gode Yaya J Tana faWa sai kuma ta fara hawaye.

Jawad ya yi tsaki ya ce,  Allah zan yi tafiyata, ya zaki dinga yi min kuka kuma?. Ta goge idanunta ta ce,  To Yaya J na daina ta faWa tana goge idanunta.
 Babu abinda ki ke so?.
 Babu komai.
 In kawai ko meye ki faWa min. Kuma aikin gidan nan bai yi miki yawa ba kuwa?. Nayla ta ce,  za a kawo min house maid daga Kaduna, sai Mama ta dawo. Jawad ya ce,  meyasa sai Mama ta dawo? Yanzu aikin baya yi miki yawa?.

Ta ce,  Ina iyawa.
 Kin tabbatar?.
 Eh Yaya j.
 Gaskiya ki yi magana ko gidan Hajja ne a kawo miki housemaid, har wani aiki ki ka iya da zaki iya gyara gidan nan?. Bayan wannan falon akwai wani, sannan ga bedrooms. Gaskiya ki yiwa Hajja magana ko wacce zata dinga zuwa tana taya ki ta koma ne ki samu. Nayla ta Waga kai ta ce,  To Ya J. Kuma kaga gwara ma ta gidan Hajjan, damaan ni bana son mai kwana.


Jawad ya ce,  haka dai ya kamata. Yanzu abinda zai faru zan tashi na wuce, kin san ?arfe uku zai tashi, yanzu ga Waya da rabi har tayi ina da sauran awa Waya da rabi. Zan je gida a kai ni airport ya faWa yana mi?ewa tsaye. Nayla ta ce,  Yaya J Allah ya kiyaye hanya. Su Hajja ma gobe da zafe zasu tafi.

Yayi dariya ya ce,  kawai ki ce saura ke kaWai a nigeria kowa ya gudu ya barki. Dariya tayi ta ce,  Yaya J in zaka dawo fried chicken Win McDonald nake so, na bawa Twiny sa?on Albaik, na baka na McDonald, Salma kuma zan bata na KFC.

Dariya sosai ya ce,  Duk ke kaWai? Kuma ki rasa abinsa za a siyo miki sai soyayyiyar kaza?. Nayla ta ce,  ita nake son ci. Tare suka fito shi da ita suna hira har ?ofar gidan, ta buWe sabuwar motar ?irar glk ta Wauki laptop Winta da iPad Winta. Ya kalle ta ya ce,  To Nayla na tafi, ki cigaba da addu a ya faWa yana shiga mota ta Waga masa hannu ya tafi.

Gidan ta koma cike da kewa ta saka laptop Winta a chaji ta dawo ta yi sallar azahar sannan ta Wauki alkur ani ta fara karantawa. Gate taji ana bugawa abin ya bata mamaki, ta hijjabi saka ta fito tana tambayar waye. Muryar Bashir yaron Omar taji hakan ya saka ta buWe ya ce,  Antyn mu barka da rana. Damisa ne ya aiko ni na kawo wannan kayan gidan nan. Nayal ta ce,  to shigo. Ya ibada?.
 Alhamdu lillah. Ta bashi hanya ya shiga ta rufe gate Winta koma ciki.

Kaya ne da yawa a leda babba ya ajjiye yana kallon falon ganin da haske sosai sai ya ce,  Antyn mu zan iya yiwa kayan nan hoto a nan? Naga da haske sosai, in ban yi ba yanzu in anjima zan saka a nemo ni. Nayla tayi dariya kaWan ta ce,  kayi mana, babu komai.
 Godiya nake ya faWa yana fito da takalman daga ledar. Nayla hannu ta saka ta Wauki takalmi guda Waya na mace ta ce,  kai amma takalmin nan ya yi kyau sosai, kuma da gaske aikin kune wannan? Da hannu aka yi shi?.

Bashir ya ce,  ?warai kuwa Antyn mu. Wannan boss ne da kansa ya yi shiyasa ya ce na kawo shi nan sai na shago sun ?are za a fitar da su. Tun safe aiki mu keyi har yanzu. Nayla ta ce,  Gaskiya ya burge ni sosai ma ta faWa tana shafa logon takalmin wanda aka rubuta Tiger da wani style mai kyau da kuma yanayin jikin Damisar.

Nayla ta kalli wayar da ya Wauko zai yi hoton ta ce,  ko na ara maka wayata kayi hoton da ita? ta faWa tana mi?a masa wayarta. KarSa ya yi ya ce,  Godiya mu ke Antyn mu, ga iPhone 16 ai iPhone 13 baza tayi ba. Hotuna yake yiwa takalman tana kallon dan ya iya Waukar hoton sosai. Ya jima yana yi tunda suna da yawa sannan ya gama. Nayla a ?afarta ta saka takalmin yayi mata bala in kyau kasancewar jikinsa baki ne sai ya haska ?afarta sosai.

Wayar da ya mi?a mata ta karSa kawai sai ta yiwa ?afarta ta hoto ta tsaya tana kallo domin hoton ya yi kyau sosai. Bashir ya ce,  Antyn mu ayi min airdrop. Ba musu ta buWe ta tura masa hotunan suka je har wanda ta Wauki ?afarta bata san ta tura ba. Kallon hoton ya yi ya kalleta ya ce,  Antyn mu amma hoton nan ya yi kyau sosai. Zamu iya posting Winsa? Ya faWa yana haska mata hoton.

Nayla ta ce,  ban ma san na tura maka ba, amma babu damuwa zaka iya.
 Daman muna son a dinga sakawa ana Wauka a ?afar mace, to Boss Win ne shi ba wasu mata ya sani ba balle a dinga biya ana yi. Na mazan ma daman da ?afarsa ake Wauka shima kuma sai ya ga dama, in ya ga dama ya saka a Wauka in bai ga dama ba ba za a Wauka ba. Amma wannan kam ya yi kyau.

Nayla ta ce,  kuma nawa ku ke siyarwa?. Bashir ya ce,  ya danganta gaskiya, bamu cika siyar da guda Waya ba, an fi siyan kwali ko guda sha biyu. Nayla ta ce,  ya kamata ace kuna siyar da pieces saboda ga sallah ?arama nan zata zo akwai wanda zasu siya sosai. Bashir ya ce,  Gaskiya ne, amma da yake muna kaiwa kasuwa da shaguna bamu cika siyar da Waya ba. Amma zamu fara in sha Allah.

Nayla tavce,  nima ina da shop a Kaduna, ina so a haWa min masu kyau ku bawa driver da ya ke muku aiki ya kai can na tabbatar da za a siyar. Bashir ya ce,  To Antyn ku duk sanda ki ka shirya.

 Ai gobe nake so a tura, ka haWa package mai kyau na maza da mata da na yara, zan yi waya a karSa dan na tabbatar bazai kai sallah ba ya kare. Bashir ya ce,  za a yi hakan.

 Meye sunan platforms handle Win ku ke posting?. Sunan page Win ya faWa mata sannan ya ce,  duk da sunan kWa amfani, ig, x, facebook har da TikTok ma. Nayla ta ce,  zan taya ku advert in sha Allah. Ka bani number ka saboda kayan da za akai gobe. Bai yi musu ba ya bata number sa ta yi saving ta kira shi shimaya yi saving sannan ta ce,  Amma kun taSa kai advert gidan tv ko radio haka?.

Bashir ya ce,  gaskiya ba mu taSa ba.
 Ya kamata ace an kai saboda manyan mutane su gani. Ga sallah zata zo in aka yi talla yanzu abinda zai wuce yadda ake tunani. Gobe in fita zan shiga arewa24 zan ji ya tsarin sun yake, yadda muka yi dasu zan sanar dakai. Za a yi tallah a kwanakin nan koda guda biyu ne.

 An gama Antyn mu, hakan ma tunani ne mai kyaun. Nayla ta ce,  tunda ka ce wannan kayan shi ne ya ce ka kawo, Ina son guda Waya yanzu ka kawo min daga shop Win amma irin wannan nake so ta faWa tana nuna irin wanda ta saka a ?afarta.

Bashir ya ce,  ai kawai Antyn mu ki Wauka a nan, babu irin waWannan a shago. Yin su aka yi kuma ya ce ba yanzu za a fitar dasu ba. Nayla ta girgiza kai ta ce,  to na gode. Yadda mu ka yi zan yi maka waya sai a shirya wajan in zasu zo Waukar video. Amma bana son Boos Win na ku ya sani. Ya yi dariya ya ce,  babu damuwa Antyn mu, duk da dai kwana biyu yana zama sosai a shagon amma zan san abinda zan yi. Nayla ta amsa ta ce,  don Allah zaka iya shigo min da farar mota da take wajen gidan nan?.

Bashir ya ce,  zan iya. Ta bashi key Wn ta ce,  na gode. KarSa ya yi ya fita ba jimawa ta ji ya shigo da ita sannan ya dawo ya bata key Win tayi masa godiya shi kuma ya fita.

Kallon takalma ta zauna yi sai kuma ta dinga sakawa tana yin hoto da video a ?afarta, ko wanne kala sai da ta saka tayi hoto kuma sosai hoton yake yin kyau a ?afarta. Kai da ka kalli ?afar ka san tana shan predicure saboda yadda farcen ?afar yayi haske sosai, ga wani kyau da ?afar tayi musamman in ta saka takalmin. Shiru tayi tana kallon takalmin ta tabbatar colleagues Winta zasu siyi takalman sosai, kuma tana da friends da cousins yadda takalman suka yi kyau da wuri za a siye su.

Ajiyar zuciya tayi tunawa da ?an gidan su gabaWaya suna saudia, ita kanta ta manta rabon da tayi ?aramar sallah a Nigeria, ta manta yaushe rabon da ta yi azumi a Nigeria, ko lokacin da take makaranta ajjiye karatun take yi tayi tafiyarta indai ba jarabawa zata yi ba, da yake Allah ya aiko mata da ?addararta gashi yanzu tana yi. Ajiyar zuciya tayi tana jira dare ya yi ta je ta yiwa su Hajja sallama dan tunda ta shigo gidan bata taSa fita ba sai yanzu da ta raka Yaya J.

A wajan ta bar takalman amma ta Wauki guda Waya kamar yadda Bashir ya ce, zuciyarta na ta rawa akan Waukar kar ta je tayi laifi, a haka dai ta daure ta Wauka. Bayan sallar la asar ta rasa abinda zata yi, gashi dai tana cikin ?an first ramadan with habibi amma ita first ramadan with habibiya ne ba habibi ba, dan shi ba ma shan ruwan gidan yake yi ba balle ya ci wani abu, bata taSa ganin ya buWe fridge ya Wauki ruwa ba, sai dai ya shigo dashi a hannunsa. Shiyasa ma bata taSa tunanin yin girki ba, dan ta san in tayi ma asara zata yi shiyasa bata wannan gangancin.

Tea kawai ta dafa ta zuba a flakas, bayan ta gama ta ji tana sha awar soya ?osai ta wanke wake tana wakewa tana cewa,  Kayan abincin nan sun yi yawa, gwara na yiwa Didi magana a bayar in ba haka ba zasu lalace. Iya ni kaWai nake ci ya zanyi dasu? Ko drink Win nan ma har ya yi expire ban shanye ba. Daga haka ta gama ta markaWa ta saka a fridge dan sai anjima zata soya.

Sai da yamma tayi sosai sannan ta soya, bayan ta gama tayi alwala ta hau kan sallaya tana faWawa Allah bu?atarta har aka sha ruwa. Ruwa ta sha sannan tayi sallah ta fito ta sha tea da ?osanta sannan ta yi wanka ta zauna tana jira ayi sallah i sha.

A lokacin ya shigo da sallama kamar ko yaushe, ta amsa bai kalle ta ba ya kalli kayan da suke wajan ya Wauka ya shiga dasu Waki ba tare da ya ce mata komai ba. Bai jima ba ya dawo falon ya Wauki ruwa ya sha ya zauna yana duba waya. Nayla gabanta faWuwa yake yi ganin ya zauna a falo bayan ya san tana zaune, sannan ga ruwa da ta ga ya Wauka yana sha a karo na farko da taga hakan tunda ta suka tare a gidan.

Kallon sa take yi tana jin kamar bata kyautawa yadda ko gaisuwa bata haWa su, sannan kuma gashi ana azumi ko babu komai in ta ce masa an sha ruwa lafiya zata samu lada. Tunawa da batun komawarta aiki da kuma zancen son zuwa gidan Hajja ya saka ta daure ta gyara zama bata ce komai ba.

Waya ya fara amsawa kamar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login