Showing 252001 words to 255000 words out of 332344 words

Chapter 85 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14377

ruwa rana da kai kafin ka amince. Shiyasa mu ka haWa baki da YallaSai aka karSi kuWin, kuWin farko kuma dasu aka haWa aka yiwa Nayla kayan lefen. KuWi na biyu kuma kana turawa wanda muka ce maka shine mai gidan ya dawowa da YallaSai su, yanzu haka suna hannuna. Na zaSi na faWa maka yanzu ne dan na san yanzu baza ka yi wani abun mara kyau ba, kuma ya kamata ka sani ko dan ka saka alkhairi da alkhairi."

Ajiyar zuciya ya yi cikin takaici ya ce, "daman a gidansa nake kwana nake tashi?."

"?warai Omar, a gidan Kawu ka ke rayuwa da matarka." Ya yi ajiyar zuciya ya buWe takardar yana kallo kafin ya ninke ya ajjiye a gefe cikin wani yanayi na jin haushi da ?unar rai, da zai iya da ya jawo kwanakin da ya yi a gidan ya goge. Didi ta ce, "Akwai wata gaskiyar da na kuma Soye maka lokacin aurena. Tsakani da Allah ba Hajja ce tayi min kayan Waki ba kamar yadda na ce maka, Baba Adamu ne."

Ya zuba mata ido yana kallon ta ta ce, "na ce maka Hajja ce saboda kana ganin girmanta zaka iya amincewa da ita akan Baba Adamu. Shima kuma ya ce kar na bari ka sani, matsayinsa na yayan mahaifiyata shine zai min kayan Waki. Na faWa maka yanzu saboda ka saka alkhairi da alkhairi."

Ya taSe baki ya ce, "Sai da aka gama munafurta ta sannan zaki faWa min?."
"Taoronka ake ji Omar, tsoron hargaginka nake yi shiyasa duk ban faWa maka ba. Amma a yanzu na san kana jin su a zuciyarka, zaka iya amincewa da komai shiyasa. Kuma ina jin tsoron cigaba da ajjiye sirrin, gwara ka sani dan ka saka musu kaima."

?auke kai ya yi bai ce komai ba sai kuma ya ce, "to na ji. Amma kin san da na san gidansa ne wallahi bazan zauna ba."
"Sanin hakan ya saka na Soye maka, na kuma ce bazan faWa maka ba sai gidan ya yi maka amfani." Girgiza kai ya yi bai ce komai ba kafin ya kalli takardar ya ce, "to me zan yi da gidan yanzu kuma? Ki Wauka ki mayar masa na gode."

Ta yi dariya ta ce, "Gida dai ya rufa maka asiri, kafin ka mallaki wannan Win a shi ka zauna. In kuma zaka mayar masa ai ka san gidansa,
sai ka je ka mayar masa" ta faWa tana mi?ewa tsaye ta ce, "ni zan wuce, Allah ya sa albarka a gidan nan, ya tabbatar da alkhairi." Nayla ce ta amsa da amin ta rakata har waje ta shiga mota AbdulHamid ya ja suka tafi.

? ? ? Nayla da ta dawo bata same shi a ?asa ba amma ya bar takardun gidan a wajan, ta Wauke ta hau saman inda yake. Yana ganin ta ya mi?o mata hannu, ta ri?e hannunsa ya zaunar da ita a kusa dashi ya ce, "ki daina yawan yawon nan mana." Fuskarsa babu walwala ko kaWan, ta san abinda Didi ta faWa yake taSa zuciyarsa tunda mai hali baya fasa halinsa. Ta yi mamaki ma da bai balbale Didi da masifa ba. Nayla ta kalli Wakin da suke ciki, duk da ita ta tsara komai na Wakin amma ya burgeta sosai. Ga hotonsa shida ita da suka Wauka a maldives an yi illegin, ga nasa da Didi shima an kafa. Nayla ta ce, "Baka mamaki ace yau mu ne a wannan gidan kuma mallakinka?." Ya kalle ta ya ce, "ikon Allah ne ai Jidda, rayuwa na tafiya a hankali, komai yana zuwa mataki-mataki kamar mafarki."

"Gaskiya ne, Allah ya cigaba da dafa mana a cikin lamarin mu."
"Amin ya rabbi. Ramadan mai zuwa a wannan gidan zaki tashe ni sallar tahajjud" ya faWa yana ?ar dariya yana kallon ta. Murmushi ta yi ta ce, "eh mana, a gidan nan zaka ce ai ba kabarin mu Waya ba" ta faWa cikin kwaikwayon yadda ya yi maganar wancan lokacin. Tare suka yi murmushi ganin ya saki rai ba kamar Wazu ba sai ta ji daWi dan itama tana so ya shirya da familynsa.?

Omar ya ce, "taso mu je ki yi bacci ki huta, ni na san kin gaji sosai." Nayla ta mi?e bayan ya tashi ta ce, "wallahi na gaji kam, sai ka taimaka min da tausa."
"An gama" ya faWa yana ri?r hannunta suka kwanta.

? ?? Watan ramadan za a shiga, yana so su je umrah amma kuma saboda cikin Nayla ya tsufa dole ya ha?ura amma ya biyawa Didi da mijinta da Marmerh su zasu je. Ko da ya faWawa Nayla ta ce hakan ya yi sosai ya ce mata in sha Allah a shekarar sau uku Didi zata je Saudia har aikin hajji.

? Cigaba ake ta samu a fannin kasuwanci, dan zuwa lokacin inda aka mayar dashi kamar company ana aikin takalman an ?ara girmansa har babban office Omar yake dashi a ciki mai kyau na saukar Saki. Yanzu ya ma daina yin aikin gabaWaya yara ne suke yi, tunda an zamanantar da abin injina ne suke yin komai sai dai abinda ba za a rasa ba.

?? A cikin azumin Nayla tana video call da Didi ya shigo, bayan ta kashe ta kalle shi zata yi magana sai ya ce, "Yaushe ne aka ce haihuwarki?." Nayla ta ce, "ko yau zan iya haihuwa, a yadda aka ce."
"Mace suka ce ko?."
"Eh."
"In kika haifi mace wanne suna zaki saka mata?." Ta kalle shi ta ce, "zaka saka mata dai ko?." Ya ce, "to wanne ki ke so?." Nayla ta ce, "Duk wanda ka ke so, ni bani da zaSi."

Ya girgiza kai ya ce, "a'a, sai kin faWa." Nayla ta yi murmushi ta ce, "Sunan Didi, tunda Didi ta haifa mana Marmerh sai mu haifi mai sunanta." Ya kalle ta ya yi murmushin jin daWi a zuciyarsa ya ce, "Allah yana gani in mallakar da ki ka yi min har abinda yake zuciyata ki ka fara gani." Dariya ta yi ta ce, "to waye ya sani?." Ya ce, "Daman ina so na ji ra'ayinki ne amma daman ni sunanta nake so na saka, Ban sani ba ko kina son saka sunan mahaifiyarki shiyasa na baki dama."

Nayla ta ce, "ni bani da wannan ra'ayin gaskiya, ban sani ba ko nan gaba zan saka." Ya kalle ta yana taSe ya ce, "kin cika iyayi ne ai." Ta yi dariya ta ce, "na ji, duk da ban kai ka ba." A washe garin ranar da yamma gab da za a sha ruwa Nayla ta haifi kyakykyawar ?arta mace a asibitin da take zuwa ganin likita.
KRB3P096
Nana haleema.

Nayla ta sha wahala wajan haihuwa, hakan ya saka aka yi mata allurar bacci dan ta huta. Omar ya kasa nutsuwa sai kai kawo ya ke yi, gashi ya kasa kiran kowa, bai ma san wanda zai yiwa wayar ba. Omar a asibiti ya sha ruwa, shi dai ya san da aka yi kira ya sha ruwa kawai, bayan nan ya kasa komai. ?akin da Nayla take bacci ya shiga yana kallon ta tana kwance tana bacci, ga babyn ta na kwance a kan baby bed idanunta a buWe tana ta mutsu-mutsu.

Zubawa Babyn ido ya yi yana kallonta, wai ?arsa ce wacce ya haifa shima, in ban da Allah waye zai maka haka?. Kamar yadda ya ji ?aunar Marmerh lokaci Waya tana shiga zuciyarsa haka yake jin ?aunarta na ratsa zuciyarsa. Yana so ya dau?e ta amma yana jin tsoro kar ta faWi, sai ya du?a ya shafa fuskarta tare da sumbatarta. Murmushi ya yi yana kallon ta ko ?iftawa idanunsa basa yi saboda ?aunar yarinyar da yake ji a zuciyarsa. Farin ciki yake ji shima yanzu ya zama uba, soyayyarta da ?aunarta ratsa zuciyarsa take yi sosai.

"Rouhii!." Nayla ta furta a hankali dan tunda ya shigo ta farka tana kallonsa yana kallon Babyn yana shafata. Juyowa ya yi ya kalle ta yaga murmushi take yi, sai dai ta rame a fuskarta, kuma kana kallon ta zaka san bata da lafiya.

A hankali ya taka zuwa inda take kwance, yana zuwa ta mi?e zaune, yana daga tsaye ya rungume ta a jikinsa yana sauke ajiyar zuciya. Kuka take yi a hankali, ya zauna yana mayar da kanta ?irjinsa cikin sanyin murya da rauni ta ce, "Rouhii haihuwa da wahala, Allah ya ji?an iyayenmu Rouhii, Allah ya saka musu da alkhairi." Bayan ta yake shafawa a hankali bai ce komai ba, dan likitar da ta karSi haihuwar ta faWa masa ta sha wahala sosai.

Ji yake shima kamar ya zubar da hawaye, ga farin cikin samun Wiya ga kuma tausayin abar ?aunarsa. Tana jikinsa a kwance yana shafa bayanta tana sauke numfashi, ya sumbaci goshinta ya mayar da ido ya lumshe bai ce komai ba itama bata sake magana ba. ?ofar Wakin aka Wan yi knocking, bai sake ta ba ya juyo yana kallin ?ofar midwife ta shigo da sallama ta ce, "Sannu Maman Baby."

Nayla ta goge idanunta ta ce, "Yauwa sister"
"Ya jikin na ki?."
"Da sau?i."
"Me ki ke ji yanzu?."
"Ciwon kai."

Ta ce, "zan ga bp Winki." Omar ya bata waje ta auna bp Nayla sannan ta ce, "Bp ki ya hau shine silar ciwon kan, anya baccin nan ya ishe ki?." Nayla ta ce, "nayi bacci iya yadda zan iya."
"Okay ya kamata ki sake yin bacci kam, yanzu ki ci abinci zuwa anjima sai ki kwanta ki huta. Zan faWawa Dr abinda yace zan sanar dake." Nayla ta Waga kai ta fita ya dawo kusa da ita ya ri?e hannunta.

Nayla ta kalle shi a raunane ta ce, "Wai jinina ya?i sauka." Ya kalle ta yana shafa fuskarta a hankali, cikin son kwantar mata da hankali ya ce, "zai sauka in sha Allah." Shiru tayi bata ce komai ba, ya Wago fuskarta yana kallon idanunta, ya ri?e fuskarta da hannayensa, ta Wan lumshe ido ta ce, "Rouhi hannunka sanyi" ta faWa tana ri?e hannun nasa tana shafa shi a fuskarta.

Peckimg Winta ya yi a goshi yana kallon idanunta da suka yi kama da na marasa lafiya. Ya gyara mata hular kanta ya ce, "ki kwantar da hankalin ki, zai sauka." Ta Waga kai alamun to, ya sake pecking Winta a kumatu yana kallon ta. Tashi ya yi ya jawo gadon babyn ya kalli Nayla da take kallon Babyn ya ce, "Kin ga kyautar da Allah ya yi mana ko Ashiq?."

Nayla a raunane ta ce, "A lokacin da baby take gab da fitowa daga jikina, na rasa hankalina Rouhi, ina jin kamar na mutu kamar ina da rai, na kasa gane a raye nake ko kuma a mace. Ciwon haihuwa ciwo ne wanda duk mai kwatance bazai iya kwatanta shi ba Rouhi" ta Wora hannunta akan fuskar babyn ta ce, "Amma lokacin da ta fito aka zaro ta aka Wora min ita a ?irjina, sai na ji wani farin ciki, na ji soyayyarta na mamaye ko ina na jikina. Rouhi ba a banza uwa take son abinda ta haifa ba, ita kaWai ta san ta yadda ta same shi. Wallahi na daina ganin laifin son da mahaifiya take yiwa ?a?anta, ko bata yi niyar nuna soyayyar ba sai ta nuna" ta faWa hawaye na gangaro mata tunawa da mahaifiyarta.

Ta dawo da hannunta fuskarsa tana shafawa a hankali ta ce, "Nayla ce ta haihu yau YaMar, ina ganin abin kamar a mafarki, gani nake kamar zan farka na ganni a gidan Abiyna. Ina ma mahifaiyata tana da rai da na ninka biyayyar da nake yi mata sau babu adadi, domin yau na WanWana abinda ta ji a lokacin da ta haife ni." Hannunta da yake fuskarsa ya ri?e ya sumbaci hannun, ya shafa fuskarta yana share mata hawaye ya ce, "Allah ya ji?ansu yasa suna aljanna."
"Amin Rouhi, amin ya rabbi."

"Ki gode Allah da ya yi nufin kina daga cikin wanda ya yiwa ni'imar haihuwa Ashiq, ki gode masa." Nayla ta ce, "Alhamdu lillah! Alhamdu lillah!!." Murmushi ya yi ya ce, "Na rasa da wacce kalma zan yi amfani na nuna miki farin cikin da nake ciki a yanzu. Kallo Waya na yiwa ?armu soyayyarta ta gama mamaye ko ina a zuciyata, nima ji nake kamar a mafarki wai ni Omar ne yau nake da ?ar da dole a gaban sunanta a saka Omar. Abin mamaki yake bani, amma in na tuna ikon Allah sai na ji sanyi a zuciyata. Tunda Allah ya bani ke nake ganin canji da yawa a cikin rayuwata, yau ni kika haifawa wannan kyakykyawar yarinya a matsayin ?ata. Na gode Ashiq!."

Murmushi tayi ta shafa kansa, ta lumshe ido ta buWe taga ita dai yake kallo ta ce, "Ni ai ko ban ce ba ka san ina sonka, na kusa mutuwa saboda haihuwar ?arka" ta faWa tana mayar da fuskarta kalar tausayi. Dariya suka yi a hankali shida ita ya kalli Babyn ya ce, "ina so na Wauke ta ina tsoron kar ta faWi."

Nayla ta mi?a hannu ta Waukota ta ri?eta a ?irjinta tana kallon ta kafin ta kalle shi ta sake kallon ta ta ce, "Tabarakallah ma sha Allah! ?ar tamu ta Wauko suffar kamannin mahaifinta, gata nan kyakykyawa kamar babanta. Allah ya sa kar kamanninta su canja, so nake ta zauna da kamannin YaMar Wina." Ya yi murmushin farin cikin da yake ji yama ratsa zuciyarsa.

"Assalamu alaikum!" Aka faWa daga bakin ?ofa suka amsa aka shigo. Dr ne ya shigo ya ?araso ciki ya mi?awa Omar hannu suka gaisa ya ce, "An samu ?aruwa, Allah ya raya." Ya amsa da amin ya kalli Nayla ya ce, "Madam ya jiki? Nurse ta ce har yanzu bp ki bai sauka ba, da alama a asibiti zaki yi bikin sallah." Nayla ta ce, "Kaina na ciwo har yanzu."
"Saboda jinin naki da bai sauka ba ne, hutu ya kamata ki samu ban da hayaniya, ki yi bacci sosai."

Nayla ta ce, "To."
"Amma akwai maganin da za a baki shima zai taimaka miki in sha Allah, sannan ki ci abinci mai ?arin jini."
"Na gode" ta furta tana kallon ?arta. Daga nan ya fita daga Wakin.

Omar ya ce, "Na sanar da Abiy, amma bani da number Mama da na faWa mata" ya faWa yana kallon ta tunawa da kalamanta na kwanakin baya. Nayla bata kalle shi ba ta ce, "bani wayar na kirata." Nayla ta karSi wayarsa ta saka number Mama Sa'adatu ta sanar da ita. Ta saka number Twiny dan ta haddace ta faWa mata, Salma kuwa ta san tunda Abiy ya sani zai faWawa Jawad, Jawad kuma zai faWa mata.

Nayla ta kalle shi bayan ta gama wayar ta ce, "Ka kuwa sha ruwa? Na ji ana zancen gobe sallah." Ya kalle ta ya ce, "na sha ruwa mana Ashiq, amma bayan shi na kasa cin komai." Ta kalle shi a Wan firgice ta ce, "baka ci abinci ba? Rouhi azumi fa ka yi."

Ya zuba mata idanu yana yawo da ?wayar idanunsa a kanta ya ce, "Kina kwance zan iya cin wani abu? Wallahi na manta azumi nake yi sai da naga ana ta shan ruwa sannan na tuna ashe na yi azumi. Bani da nutsuwa Ashiq, sai da ki ka farka sannan hankalina ya kwanta." Ajiyar zuciya ta yi ta ce, "to yanzu ka je ka ci abinci."

"A Ina?." Sai ta kalle shi ta yi ajiyar zuciya tunawa da bashi da kowa tunda Didi bata nan, Nayla ta ce, "to tea ka haWa mana ai ka iya, don Allah kar ka zauna da yunwa ka ga babu lallai mu tafi gida yau tunda sun ce bp na bai sauka ba." Omar ya yi ajiyar zuciya yana kallon ta ko kifta ido baya yi amma bai ce komai ba.

"Rouhii."
"Ashiq."
"Ka je ka ci abinci, ni na samu sau?i."
"Zan ci, amma sai kin nutsu yanzu ki ka gama kuka fa."
"Ai na daina, kuma na tabbatar yanzu Mama zata zo."
"To ki jira ta zo sai na je, bani Yayata na Wauketa" ya faWa yana mi?a mata hannu alamun ta bashi babyn.? Bashi ita ta yi ya ri?eta yana kallon fuskar yarinyar, zuciyarsa sai ta karye ya ji rauni yana mamaye sa, sai ya ji ina ma shima mahaifiyarsa tana da rai, da yau ta ga abinda Omar Winta ya haifa da zata yi farin ciki sosai.

Ajiyar zuciya ta ga ya yi ya kalle ta ya ce, "Da wanne suna zaki kirata? Ko Aisha Winta zaki ce?." Ta girgiza kai ta ce, "Sunan Didin zan faWa kai tsaye babu girmamawa? A'a bazan iya ba. Zan kirata da Musliha."

Ya Waga gira sama ya ce, "Meye kuma Musliha? Bazan yarda a sakawa ?ata sunan wata dabbar ba." Murmushi ta yi ta kalle shi ta ce, "ba sunan dabba bane Rouhi. Musliha yana nufin Righteous, good doer, reformer. Sunan larabawa ne irin ku." TaSe baki ya yi ya ce, "Ni dai Didi zan ce, babu wani Musliha da zan ce."

Ta yi murmushi kaWan kawai bata ce komai ba dan kanta nauyi yake mata. Ganin ta yi shiru sai ya kalle ta ya ga ta Wan kawar da kai gefe ya ce, "Ashiq ya dai?." Nayla ta kalle shi kamar zata yi kuka ta ce, "kaina ne ya yi nauyi sosai Rouhi, har bana son motsawa."
"Subahanallah! To sun ce ki ci abinci ai, kuma baki ci ba, Wauketa a hannuna na samo miki abinci...Ko kuma barta bara na ajjiye ta da kaina, ki yi addu'a kar na yar miki da ita."

Murmushi ta yi kawai bata ce komai, ya ajjiye ta akan gadon ya kalle ta ya ce, "itama yunwa take ji Ashiq." Nayla ta yi ajiyar zuciya bata ce komai ba. Matsowa ya yi ya dafa kanta, cikin tausayawa ya ce, "Sannu Jidda, bara na samo miki abinda zaki ci." Zai motsa ta ri?e hannunsa ta ce, "ina zaka je? Kaima baka ci komai ba."
"Kin fi ni bu?atar cin abincin Jidda, haihuwa ki ka yi fa."

"Kaima azumi ka yi, gwara ni daman tun safe bana azumin, na kuma ci abinci, amma kai fa?."
"Sai kin samu lafiya zan nutsu Jidda, ki bari na samo miki, na san baza su rasa entry a wajan nan ba, Ina zuwa." Ta sake ri?e shi tana langwaSewa ta ce, "A'a Rouhi, in ka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login