Showing 24001 words to 27000 words out of 332344 words

Chapter 9 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14379

baya son magana kafin taji yayi tsaki ya kashe wayar. Nayla ta haWWiye yawu tana mamakin izzar wannan bawan Allah, da?yar ta ce,  Yaya Omar an sha ruwa lafiya?. Da?yar ta iya faWar maganar saboda yadda zuciyarta take bugawa, kwana biyu da bata bata gashi ba sai ya yi mata kyau sosai, duk da ya Wan rame amma ya ?ara yin haske gashin kansa da na fuskarsa ya sake taruwa kuma ya yi ba?i sosai.

Yaya Omar Win da ta ce shine ya saka shi lumshe ido a hankali, bai san meyasa yake jin wani iri ba a duk lokacin da tace masa Yaya, itace kawai take ce masa Yaya bayan ita babu wata halitta a duniya da take kiransa da wannan suna. Bashi da ?anne mata ko maza balle yaji hakan daga bakinsu, shiyasa in ta faWa sai gabansa ya faWi. Ganin bai mata magana ba sai ma rufe ido da ya yi ya saka Nayla ta ce,  Gobe su Hajja zasu tafi umrah, Ina so in an idar da sallar tarawee na je nayi mayi sallama. Sannan kuma gobe zan koma aiki.

Kamar bai ji ta ba haka yayi, nan kuwa yana jin duk abinda take cewa, bai san meyasa yake jin wani abuna zuciyarsa ba indai zata kasance tana kusa dashi. Ya san kawai saboda ba ya sonta ne shiyasa yake jin hakan. Tashi ya yi zaune sosai yama kallonta bayan ya haWe yatsunsa waje Waya kamar zai yi magana sai kuma ya fasa ya Wauke kai.

Nayla gabaWaya ji take ta gama muzanta a wajan, tayi masa magana ya yi mata banza bayan ya ji. Idonta ya ciko da hawaye saboda wula?ancin da ya yi mata ya daki zuciyarta, bata taSa jin haushin abinda yake mata kamar na lokacin ba. Gata gashi tayi masa magana ya shareta bayan ta san ya ji tunda har niyar bata amsa ya yi ya fasa.

Hawaye ya zubo mata akan fuskarta sai ta mi?e zata bar wajan cikin sanyi jiki da sagewar guiwa. Cikin muryarsa ta ko yashe ta ji ya ce,  tsaya!.

Cak ta tsaya bata zauna ba ya ce,  ai na faWa miki babu ruwanki da lamarina babu ruwana da lamarin ki. Dan zaki je wani gida ina ruwana? Ki je duk inda zaki je babu abinda ya dame ni, in duniyar zaki bari Allah ya kiyaye hanya bai damu Omar ba. Ki daina takura min da magana, bana son a shiga harkata in dai ba ni na shiga harkar mutum ba. In kina yi min haka zaki yi dana sani wata ran. Nayla hawaye ya sakko mata, murya na rawa ta ce,  to, na gode tana faWa tayi ciki da sauri tana kuka.

Da kallo ya bita ya ja tsaki tare da taSe bakinsa. Samun kansa ya yi da sake kallon inda ta bi ya ja numfashi kawai sai ya tashi ya bar gidan gabaWaya.

Nayla kuwa kuka ta ci sosai, tausayin kanta take ji da rayuwarta, kenan ita a haka rayuwarta zata ?are? A haka rayuwarta zata zauna babu wani cigaba kenan? Laifinta ne dan an bashi ita ba tare da ya sani ba? Laifin ta ne dan zanen ?addarar su ya zo a haka? Meyasa yake yi mata haka bayan ita matarsa ce?. Kuka take yi sosai tana jin zuviyarta na yi mata matu?ar zafi, babban abin haushin kuma tana matu?at sonsa har yanzu, duk abinda yake yi mata bai saka sonsa ya fita daga zuciyarta ba, Wazu da ta ganshi ji take kamar ta zauna kusa dashi ta dinga shafa gashin da yake fuskarsa saboda tsananin burgewa da kuma shau?in so da take masa amma babu dama. Bata da wannan damar kuma bata tunanin zata samu irin damar har abada.

Kiran sallar i sha da aka yi ya saka ta tashi ta goge fuskarta, ba jimawa aka tayar da sallah ta bi jam i har aka yi tarawi aka idar. Lokacin tara na dare ta kusa, da yake ta san daren azumi ne ba a rasa jama a a kan hanya sai ta saka hijjabi da cross slippers ta Wauki wayarta ta fito falon. Sai kuma ta tsaya tana tunanin ya kamata ace ta fita kuwa?. _Shi ya baki dama ai, ya ce ki je duk inda zaki je, ki yi tafiyar ki kawai._ da wannan tunani ta Wauki key Win gidan ta kulle gate Win ta nufi gidan Hajja tana takawa a hankali iskar bayan sallar i sha ta watan azumi na ratsa jikinta.
KRB3P008

Nayla kusan Sata tayi a hanya da?yar ta kai kanta gidan Hajja ta tura gate Win ta shiga da sallama. Daga falon aka amsa mata ta shiga. Ihun da Salma tayi ne ya bata matu?ar kunya sai ta rufe ido da hannayenta tana dariya. Salma ta ce,  Amarya!. Nayla bata buWe fuska ba kuma bata amsa ba ta zauna akan kujera. Salma ta fara ?o?arin buWe mata fuska tana cewa,  ka ga wata gulma, yau kunyar mu ki ke ji?. BuWe fuska ta yi suka haWa ido da Hajja da take kallon ta tana murmushi. Hajja ta ce,  Hauwa u ke ce tafe da daren nan?.

Nayla ta ce,  Hajja Ina yini.
 Lafiya lau Hauwa u, kin sha ruwa lafiya?.
 Lafiya lau Hajja. Ya ibada?.
 Alhamdu lillah. Ya mijin na ki?. Nayla sai ta sunkuyar da kai ba tare da ta bata amsa ba dan bata san ma ne zata ce ba. Bata ma kula da Didi a zaune ba sai ji tayi ta ce,  baki amsa tambayar ba, aka ce ya bauWaWWen mijin na ki?. Kallon Didi tayi ta ce,  kai Didi! Ai ban ganki ba, Ina yini.

Didi tayi murmushi ta ce,  lafiya lau Amarya, an sha ruwa lafiya?.
 Lafiya lau, Ashe kin zo?.
 Na zo yiwa Hajja sallama. Nima yanzu na shigo.

Nayla tayi murmushi tana wasa da hannunta gabaWaya jinta take yi kamar ba?uwa a gidan Hajjan. Kallon Salma tayi ta ce,  Su Abiy ma sun tafi, Wazu Yaya J yazo ya kawo min mota shima na san yanzu ya kusa sauka. Salma ta ce,  ai bana kina Nigeria, ki bani sa?on abinda ki ke so ta faWa cike da tsokana.

Murmushi tayi kawai bata ce komai ba ta kalli Hajja ta ce,  Hajja an gama haWa kayan ne?. Hajja ta yi murmushi ta ce,  na gama Hauwa u. Wai daga yin azumi uku ne naga har kin rame Hauwa u?. Nayla ta wara ido ta ce,  Hajja yanzu har kin ga na rame? Hijjab ne fa a jikina. Hajja ta ce,  Nayla ai ba jiya na san ki ba. Murmushi kawai tayi bata ce komai ba ta kalli Didi da take kallon ta tace,  Didi gobe zan koma aiki.

Didi ta ce,  anyi miki transfer zuwa nan Win kenan?.

 Eh, shine abinda Yaya J ya kawo min Wazu.
 Hakan yana da kyau, Allah ya taimaka ya bada nasara. Amma zaki sha wahala ga azumi ga aiki.
 Amin Didi. Akwai wahala kam sosai. Hajja ta ce,  Ina mijin naki? Shi bazai zo ya gaishe ni ba ko? Lallai Ummaru, zamu gamu dashi. Murmushi kawai tayi bata furta komai ba dan bata san ne zata cewa Hajjan ba.

Warmers ta gani a ajjiye a gaban Didi sai ta tashi ta ce,  meye a ciki? In akwai abin daWi na ci. BuWewa take yi ganin duk abincin bai mata ba sai ta Wan yi tsaki ta ce,  bai yi min ba ma. Didi ta yi dariya ta ce,  ke da ki ke amarya daman ta ya abincin tsohuwa zai burge ki?. Hajja ta ce,  faWa mata dai. Nayla bata ce komai ba sai murmushi da ta yi kawai.

Didi ce ta mi?e tsaye ta ce,  Ina zuwa ta faWa tana fita daga falon. Hajja ta kalli Nayla da kulawa ta ce,  Hauwa u matso kusa dani. Nayla ta matsa kusa da Hajja ta ri?e hannunta ta ce,  Anya kina jin daWin zaman auren nan? Ni ban ga canji ko kaWan a tare dake ba, sai rama da naga kin yi har a fuskarki. Nayla tayi ajiyar zuciya ta ce,  Babu komai Hajja, kawai tun ramar baya ce har yanzu ban koma yadda nake ba, amma babu komai.

Hajja ta ce,  kar ki yi min ?arya fa Nayla, ni idona ba haka yake gani ba. Nayla ta ce,  Hajiya Hajja ba ?arya nayi miki ba gaskiya na faWa miki. Babu komai, kawai ki taya ni addu a Allah yasa Abiy ya daina fushi dani. Hajja ta ce,  ba fushi yake yi dake ba in sha Allah, Kar ki damu da wannan. Salma ta ce,  Yaushe rabon da ki yi azumi kuwa a Nigeria?. Nayla ta ce,  nima bana ce ba Salma, amma an jima gaskiya.

Hajja ta ce,  wannnan zaman da zata yi ai yafi ta je saudia, ga aure ga ibadar azumi. Ladan da zata samu Allah ne ya sani. Nayla murmushi kawai tayi amma bata ce komai ba dan ita tasan babu wani ladan aure da zata samu.

Hajja ce ta tashi ta shiga Waki Nayla ta koma kusa da Salma ta ce,  Salma don Allah kar ki manta dani a addu a, ko yaushe da kin fara addu a nazo zuciyarki. Ban san me yake damuna ba, amma ko me zai yi min bana jin haushinsa, har gobe ina son shi ta faWa murya na rawa tana ri?e hannun Salma. Salma ta Wora hannunta akan nata ta ce,  kar ki yi kuka mana, ni ban san meyasa hawaye bayabyi miki wahala ba, in Hajja ta fito taga kina kika ai sai a samu matsala. Addu a zan yi miki in sha Allah Nayla, wallahi zan miki addu a kamar ke ki ka je da kan ki, ba dan kar nayi ?arya ba da nace zan yi miki addu ar da ko ke kika je baza ki yiwa kanki kamar ta ba. In sha Allah kafin ramadan Win nan ya fita sai komai bani ya warware.

Ta goge ido ta ce,  Allah ya sa Salma. Salma ta ce,  Amin. Wai babu wani cigaba a zaman nan na ku?.

 Hmm ko magana bata haWa ni dashi, yau ma da nace masa zan zo wajan Hajja gobe kuma zan je aiki cewa ya yi in ma duniyar zan bari ina ruwansa, sannan kar na sake shiga sabgarsa.
 Amma Omar Win nan bashi da mutunci wallahi, dan ya samu ma mace kamar ki tana zaune dashi matsayin matarsa kuma tana sonsa shine zai dinga yi mana wula?ancin da ya ga dama?. Bar ni dashi, addu ar mallaka zan miki, in sha Allah sai kin juya shi kamar waina
Dariya Nayla tayi sosai harda dukan Salma ta ce,  Allah ya shirya ki, wai addu ar mallaka. Wallahi kin bani dariya.

A lokacin Hajja ta dawo sai Salma itama tayi dariya kawai suka tafa bata ce komai ba ganin Hajja.

Didi kuwa lokacin da ta fita gidan su ta kalla ta ga ?ofa a buWe da alama Omar yana ciki. Bata shiga ba sai ta kira shi a waya yana Wauka ta ce,  kana gida ne?. Katse kiran tayi alamun an bata amsa ta nufi gidan.

A zaune ta same shi yana shan tea gefe ga slices bread guda biyu, sai kankana da apple da banana da suke ajjiye suma. Didi ta bishi da kallo shima ya kalle ta ya ce,  Kwana biyu ana yawan ganin ki, kin sha ruwa lafiya?.
 Lafiya lau. Da yake na zo yiwa Hajja sallama ne gobe zasu tafi umra.
 Okay ya amsa a ta?aice yana cigaba da shan tea Winsa hankali kwance.

Didi ta ce,  ba dai sai yanzu ka ke cin abinci ba?.
 Yanzu na ke ci.
 Baka ci a gidanka ba ne?. Ya kalle ta da mamaki jin ta kira gidansa ya ce,  gidana kuma? Ina da gida ne?.
 Gidan da matarka take ciki fa?.
 Oh! gidan haya zaki ce ai ba gidana ba.
 To gidan haya! ta faWa a a fusace dan ya fara fusatata akan zancen gidan hayar nan. Omar ya sha tea a hankali kafin ya ce,  bana ci, a gidan mu nake ci. Didi ta kalle shi cikin matu?ar takaicin halinsa ta ce,  meye amfanin matar ka?.

Ya Wora ?afa kan Waya yana kallonta ya ce,  Amfaninta zama a gidan da aka kama hayar dan ita mana. Didi ta tausasa murya ta ce,  Omar! Wai me yake damun ka don Allah? Abincin ma baka ci kenan? Wannan wacce irin Wabi a ka Waukarwa kanka?. Wallahi na tabbatar Nayla baza ta ?i dafa abinci ta baka ba, kenan wula?anci ka ke yi mata baka ci ko?.

Ya kalli Didi ya ce,  ni ban yiwa kowa wula?alanci ba, to har wacece ita da zan tsaya na saurareta balle wula?anci ya biyo baya? Wanda ya isa ai shi ake wula?antawa. Abinci ne bazan ci ba daman dan ita aka kai ko? To sai ta dafa ta ci kayanta ai ba ni na kai mata ba.

Didi ji take kamar ta zabga masa mari saboda takaici kawai yake Wura mata a zuciyarta, ta danne fushinta tana girgiza kai ta ce,  Omar na faWa maka abincin da aka kaita dashi daga gidan su al adar hausawa ce ba wani abun ba, gara ake kiranta, kuma yawancin hausawa masu kuWi da sarauta duk haka suke yi, ba an kai maka gara dan ka gaza bane ka fahimta mana.

Omar bai ce komai ba shayinsa yake sha hankali kwance dan maganar ba shigarsa take yi ba. Didi ta sake kallonsa ta ce,  Omar ha??in yarinyar nan zai bibiye ka fa.

Ya ajjiye kofin shayin ya kalle ta ya ce,  ni ban ce ha??ina zai bibiya ta ba sai ita za a ce ha??inta zai bibiye ni? Dole aka yi min babu yadda zan yi na karSa na amince har nake kwana gida Waya da ita. Ban taSa kwana a gida Waya da ko wacce mace ba in ba ke ba sai ita, iya rashin sakewar da bana samu shima shiga ha??ina ne. Meyasa ko yaushe ki ke maimaita min ha??inta a kaina ni bakya tuna nawa?. Ba fa sonta nake yi ba, dole aka yi min na zauna dan babu yadda zan yi. GabaWaya kin canja alaka, kamar itace jininki bani ba, ko yaushe cikin tausasa harshe ki ke a kanta. Ni ga banza bare ko tani bakya yi, ko tausayina bakya yi sai ita tunda ga ?ar diamond ya faWa yana taSe baki yana kallonta

Didi ta ce,  ko kana sonta ko baka sonta matar ka ce, kuma kula da ita dole ne a kan ka. Zancen na canja alaka a kanka ai dole na canja Omar, ita duk abinda nace mata tana yi kai kuwa fa? Sai na sha wahala na Waga murya sannan zaka iya sauraron abinda zan ce maka. Ina tunasar da kai ha??inta ne ba dan na zaSeta na barka ba, yarinyar bata da damuwa ko kaWan, inda zaka sauke wannan banzan girman kan naka zaka ji daWin zama da ita fiye da kowa.

TaSe baki ya yi bai kula ta ba ya Wauke ido daga kallon ta. Didi ta ce,  Ta ce min gobe zata koma aiki, ka sani?.
A fusace ya juyo ya ce,  Sai na sani? Ta tafi lahira ma ina ruwan Omar?.
 Kai fa mijinta ne, ta ya zaka ce sai ka sani?.
 To ni a wajena ba sai na sani ba, duk inda zata je ta je bai dame ni ba. Zama nake yi kawai ba dan Ina so ba sai dan saboda ke, ana yi min abinda bai yi min ba bazan sake komawa gidan ba. Ganin yarinyar ma takaici yake bani balle ta buWe baki ta yi magana, wa adina nake jira ya cika in na bar gidan wallahil azim ko me zaki ce Didi bazan komai ba.

Didi ta dafe kai bata san ya zata yiwa Omar ba wallahi, caja mata kai yake yi a ko yaushe da matsalolinsa na yau da kullum. Ta daure ta ce,  to ka tashi mu je ka yiwa Hajja sallama zata tafi umra gobe. Kallon up and down ya yi mata yana Waga gira sama ya ce,  a dangin wa zan je yi mata sallama?.

 Matsayinta na babba wacce nake kallo matsayin uwa kuma kakata. Sannan matsayin kakar matarka!. Yayi murmushin rainin hankali ya ce,  Da kin tsaya a iya na farkon sai na je, amma tunda ki ka faWi na biyun babu inda zan je.
 Wallahil azim sai ka je ta faWa a fusace tana kallon sa.

Kallon ta yake yi jin har ta rantse, ya Waure fuska yana binta da harara ya ce,  Dan fa na karya miki rantsuwa ba wani abun bane a wajena Didi, ki daina ganin kina yi min dole ina ?yalewa wallahi an kusa zuwa gaSar da zan kasa jurewa. Ba fa haifata ki ka yi ba wasu shekaru kawai ki ka bani, amma yadda ki ke bani umarni ko uwar da ta haife ni sai haka. Komai kan ki tsaye ki ke cewa wallahi sai na yi, nayi abubuwa da yawa a baya wanda ki ka ce, an kusa zuwa gaSar da wallahi bazan yi ba!.

Didi ta harWe hannu a ?irji ta ce,  kawai ka ce ka kusa daina ganin girmana da darajata.
Ya gir???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?giza kai ya ce,  Ni ban ce haka ba, amma dolen da ki ke saka ni ne na kusa daina jurewa wallahi. Gwara na ma faWa miki na kusa daina


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login