Showing 48001 words to 51000 words out of 332344 words

Chapter 17 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14404

dalilin Omar na yin haka, amma ki tambayi Aisha zata baki labari. Matsayin ki na matarsa Ina ro?onki da ki daidaita wannan gabar da Omar yake yi da mu, shekaru da yawa amma ya kasa manta baya, duk dai ba a kyauta ba. Mun gode da yadda ki ka karSe mu, Allah ya yi miki albarka" ta faWa tana fita.

Tare suka fito da Nayla ta raka su har gate gabaWaya jikinta ya gama yin sanyi. Tana dawowa falon yana fitowa kamar daman jiran shigowarta? yake yi. Kallon ta ya tsaya yana yi ya ce, "waye ya baki iznin barin waWannan su shigo gidan nan? Waye ya faWa miki kowa na zuwa inda nake!?."

Jin yadda yake maganar da tsawa yana buWe idanu sai ya koma mata sak Omar Win gidan Didi mai Wora mata wu?a a wuyanta, ta tsorsta ta Wan ja baya kaWan ta ce, "Cemin suka yi dangin Mamanka ne, kaga....."
"In ki ka sake ki ka ?arasa sai yanke miki baki" ya faWa a fusace yana Waukar ?aramar wu?ar da take kan Apple a ajjiye.

Nayla tayi Wif ganin za a mamaita abinda ya wuce, ya sake wara idanu ya ce, "dan na zo na zauna a nan ba hakan yana nufin zan Wauki ko wanne shirme daga gare ki ba, ki tsaya iya matsayinki, ki tsaya a inda na ajjiye ki kar ki tsallaka inda ban baki izini ba, sannan kar ki sake aikata wannan ganganci kin ji ko!?." Nayla ta zabura jin tsawar har tsakiyar kanta ta ce, "Na ji." Buga gate Win da ake yi ne ya saka ta fita da sauri dan ta gujewa wannan tashin hankalin, tana buWewa tayi ajiyar zuciya ganin Didi.

Ganin ta ruWe ya saka Diid tambayar lafiya amma bata iya bata amsa ba gidan kawai ta kulle suka shiga ciki. Dashi suka fara haWa ido yana tsaye idanunsa sun yi ja sosai, ta kalli Nayla da jikinta yake rawa ta kalli hannunsa ganin ?aramar wu?a sai ta ce, "Omar Lafiya? Me ka ke yi da wu?a a hannu?."

"Ki faWawa ?an uwanki, kar wanda ya sake zuwa gidan nan. indai har ni da nake zaune a gidan nan zan amsa sunan gidan da nake biyan kuWin haya to kar na sake ganin wata ko wani sun zo, in ba haka ba baza a zauna lafiya ba ke kin sani!."

Didi ta ce, "Sai masifa ka ke yi, su waye suka zo?."
"Oho" ya faWa yana cillar da wu?ar ya ce, "ki ja mata kunne, in ba haka ba wata ran zaki zo ki tarar na karya ta gida biyu" ya faWa yana nuna Nayla ya fita daga gidan.

Nayla ta ce, "Wallahi Didi ban san baya so su shigo ba, kuma Don Allah ba?i sun zo zan ce kar su shigo ne?." Didi ta ce, "su waye?."
"Mama Zainab ne." Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Share shi ki zo ki zauna."

Suka zauna tare Didi ta ce, "shegiyar zuciya ce da Omar, baya mantuwa ga shegen ri?o kamar mutanen farko. Abin nan ya wuce, sun nemi yafiya tun shekarun baya amma ya kasa daina kallon su matsayin masu laifi. Ki gode Allah ma dangin Mama ne, inda dangin Baba ne suka zo musmaman matar Kawu, Innalillahi! Ai kaf unguwar nan sai an ji amon muryarsa."

Nayla ta ce, "ikon Allah." Didi ta ce, "Allah ya shirya shi kawai. Kin san me ya faru ai ko?." Nayla ta ce, "Hajja ta taSa bani labari."
"To don Allah Nayla tunda komai ya wuce ba sai ya manta ba? Me ya rasa yanzu a rayuwarsa?."
"Babu, Kuma musulmi da yafiya aka san shi."
"To banda Omar, babu shi a ciki. Ya kasa mantawa tsaf yana zuciyarsa, nayi faWan, nayi nasihar amma a banza."
"Allah ne ya taimake ni kika buga gidan nan, da Ina jin yanka min baki zai yi."

Didi ta ce, "ke ce zaki saka ya yafe musu Nayla." Nayla ta wara idanu ta ce, "ni a suwa Didi?." Didi ta ce, "ke a matarsa." Nayla ta ce, "rufa min asiri, ba da ni ba wallahi." Didi tayi dariya ta ce, "Allah kuwa. Ke ce kaWai maganinsa, kuma ke nake so ki dawo dashi hanya madaidaiciya."
"Hmm Didi kenan, kina magana kamar ni na haife shi."
"Ba ke kika haife shi ba, amma matarsa ce ke."
"Mata ta suna ba."

Didi ta ce, "zata zama ta aikace Nayla, ke dai ki cigaba da ha?uri kawai." Nayla ta yi murmushi ta ce, "na barki a zaune ko ruwa ban baki ba, ga rana ana yi." Didi ta ce, "Kamar wata ba?uwa?. Kuma kin san da bazan zo ba ma wallahi, amma nace bara na shigo, zuwa yamma sai na je gidan su Kawu mu gaisa na yi musu barka da sallah."

Nayla ta ce, "zan raka ki."
Didi ta ce, "to Shikenan, Allah ya kaimu." Nayla ruwa ta kawo mata da lemo kana tsaye, "me zan dafa miki? Kin san ba girki nake yi ba."

Didi bata amsar tambayar ba ta ce, "ni ya tura min kuWi fa Wazu, na ce masa na meye wai na tura miki. Na ce masa kai baka da hannu sai kawai ya kashe wayar." Nayla tayi dariya ta ce, "wai fa advert Win nan da ya gani shine ya tsare ni da ido wai ya saka ni ne, na ce masa bai saka ni ba, na yi ne kawai, shine ya ce ban san ko ke bakya yi masa shishshigi ba sai da izinin sa. Na ce masa nayi ne saboda cigaban kamfanin Yayana wai shi ba yayana bane, keda shi kaWai aka haifa bashi da ?anwa a duniya, dan haka bai ce min yana so ba, kar na sake wannan gangancin."

Didi tayi dariya sosai ta ce, "Omar! Omar!! Allah ka shirya min wannan ?anin nawa." Dariya itama Nayla Win tayi ta amsa da amin suka cigaba da hira cikin nishaWi da walwala.
KRB3P015
Arewabooks@nanahaleema11.


Didi tare suka yini har akayi la sar sannan Nayla ta shirya cikin atampa da tayi mata matu?ar kyau. Ta kalli Didi ta ce,  mu je ko Didi. Didi ta ce,  baki tambayi mai gidan ba. Nayla ta turo baki gaba ta ce,  ya ce duk inda zan je babu ruwansa, ko da wasa kar na ce zan tambaye shi, shiyasa ma bana tambaya. Didi tayi dariya ta ce,  amma yadda ya Waga hankalinsa da azumi da baki dawo ba bai ce miki kar ki sake fita baki faWa masa ba?.

Nayla ta ce,  bai ce ba, cewa ya yi ma to ina ruwansa. Didi tayi dariya ta ce,  Allah ya shirya Omar, tunda ya baki permit mu je. Kin yi daidai ta haka zamu fahimci yanayinsa. Nayla ta yi ?ar dariya bata ce komai ba.

Didi ta ce,  ki ce har yanzu ko abinci baya ci? Har aka gama azumi bai ci abinci a gidan nan ba ko?.
 wallahi Didi bai ci ba, in na yi masa magana akai ma banza yake yi min shiyasa na daina. Ana e gobe sallah dai da yana fama da ciwon kai ya sha tea, shima sha uku kawai ya yi ya ajjiye. Zan iya cewa kofin tea Win shine abu na farko da ya fara amfani dashi a gidan nan.

Didi ta yi dariya bata ce komai ba suka fito tare Nayla ta fito tana dubawa ko zata su Bashir. Sai kuwa taga Tk, ya buWe mata gate Win ta fita da motar suka fita.

Sun sha yawo da Didi har bayan sallar i sha basa nan, haka ya yi mata daWi sosai ko babu komai ta rage kewa. Sai da suka yi sallar i sha a gidan ?an uwa sannan suka taho dan Abdulhamid yana ?ofar gidan Omar yana jiranta. Nayla tayi mamakin dangin su Omar, mutane masu kirki da karamci, gasu duk masu arzu?i dan babu gidan da suka je wanda za a ce gidan talakwa ne, sai dai manya gidaje da madaidaita. A ?ofar gidan suka yi sallama da Didi da al?awarin zata je gidan Didi, Didi bata shiga gidan ba ta shiga motar mijinta suka wuce.

Nayla kuma a waje ta ajjiye motarta, dan ba ita take shiga da ita ba su Bashir ne. Babu wanda ta gani a cikin su hakan ya saka ta shiga ta bar motar a wajen dan ta san zasu zo su shigar mata da ita in suka zo.

Babu jimawa sosai ya shigo, bai kalle ta ba key Win motar ya Wauka ya fita ba jimawa sai ga shi ya kawo mata ta ajjiye. Yanayin fuskarsa ma baza ta bata damar yin magana ba, ko kallonta bai yi ba, a ransa kuwa haushinta yake ji tana take fita tana kaiwa dare ba tare da ya san inda take zuwa ba. Shi kuma bashi da lokacin da zai tambayeta da ya ji da izininwa take fita, sanin bazai iya tambaya ba ya saka ya share ta kawai ya shiga ciki.

Haka zaman na su ya cigaba da tafiya har hutun sallah ya ?are ta koma aiki kamar ko yaushe tun safe sai yamma. A haka ta fara azumin sitta shawwal kamar yadda ta saba kafin wata ya yi nisa take farawa. Su Hajja suna gab da dawowa dan Salma ta sanar da ita a satin zasu dawo haka su Abiy ma.

Ranar laraba da yamma ta dawo daga aiki tana zaune tana danna waya taga kiran Twiny ya shigo, abin ya bata mamaki tana tambayar kanta kenan ta dawo nigeria ko labari. Da zumuWi ta Wauka a nan take sanar da ita ai tana ?ofar gidanta. Da sauri Nayla ta mi?e ta je ta buWe mata tun daga nan suka rungume juna cikin farin ciki suka shiga ciki.

Jidda ta kalli Nayla tace,  Ma sha Allah, matar Omar kin yi kyau kuma duk da har yanzu da wannan shegiyar ramar, Amma wallahi kin fes dake. Nayla ta ce,  Aiki ne fa yake saka ni ramar nan, ga aikin gidan nan yayi min yawa sosai. So nake su Hajja su dawo a kawo min maid Win da zata dinga taimaka min, in yaso ko gidan Hajja sai ta dinga zuwa tana kwana.
 To ke aikin gidan naki ai sai yamma tunda da safe kin fita.

 Daman sai dai ta dinga zuwa da yamma. Jidda ta ce,  Amma duk da haka kin yi kyau, na ji daWi da ki ka cire damuwa ki ka karSi ?addara. Nayla tayi murmushi ta ce,  Hakan ya zama kamar dole ai Twiny. Ya ki ka baro su Mama? Kowa Lafiya?.
 Lafiya kowa ya ke, su ma jibi zasu dawo in sha Allah.

 Allah ya dawo dasu Lafiya.
 Amin. Mama ta ce nan zata fara zuwa ta ga ya yanayin ki yake, Tunda akace an kawo miki harin nan shikenan hankalinta ya kasa kwnaciya, ta ce ko a Abuja suka sauka sai ta siyi ticket ta zo Kano daga na ta wuce a mota

Nayla ta ce,  Allah sarki uwa ta gari, Allah ya dawo dasu Lafiya. Ta amsa da amin tana fito mata da tsaraba Nayla ta ce,  KFC muka yi dake ko Albaik?. Jidda taja tsaki ta ce,  kawai sai na rasa abinda zan kawo miki sai kaza? Kawai ki saka ni dakon kaza? To ban shiryawa haakan ba. Nidai babu abinda na siyo, naga Salma dai ta ce zata siya miki ita Yaya J.

Nayla tayi dariya ta ce,  Ke da baki siyo ba ai kin huta.
 To haka kawai na rasa me zan siyo miki sai fried chicken dan lalacewa? Ba ga KFC Win nan a nigeria ba, mu je ki siya mana.
 Dallah can, tunda dai baki siyo ba kin kyauta. Zaki haWa KFC Win nigeria da ta can ne?.

Jidda tayi mata banza ta mi?a mata ledar ta karSa tana fito abin ciki. Abaya ce rantsatstsiya mai shegen kyau da tsada kalar ba?a, sai wani oil perfume a kwalba mai Wan girma, sai cross slippers, sai kuma misk tahara a babbar tasa. Nayla ta ce,  Kai Twiny wannan abayar ta yi kyau sosai wallahi. Jidda ta ce,  ga kuma turare nan ba, wannan turaren duk ranar da zaki amarce zaki shafa, wannan taurin kan da Tiger yake ji dashi ko lion ne shi duk sai ya sauke shi wallahi. Nayla ta ?yal?yale da dariya mai sauti ta ce,  au ashe ma ranar zata zo kenan?.

Jidda ta harareta cikin jin haushi ta ce,  nufin ki a haka zaki ?are kenan?. Nayla tana dariya ta ce,  ni dai bana wannan tunanin Twiny, ni na san da wa nake tare.

 Ko waye shi sai dain bamu so kama shi ba wallahi, shi Win banza Jidda ta faWa cike da jin haushi. Nayla dai dariya take yi ta buWe misk Win ta ce,  Kamar kin san nawa na barshi a Kaduna, bani dashi a na ko kaWan. Kuma na manta shaf ban siya ba wallahi. Ke dai Allah ya barki da baby, ya fito mana da unborn lafiya.

Ta amsa da amin Nayla ta buWe turaren ta ce,  Akwai ?hamshi kam sosai wallahi.
 Yana da daWi gaskiya, shiyasa bana sakawa na fita nima a gida nake amfani dashi. Nayla ta ce,  mu kam gwara mu shafa mu fita Win, a nan Win amfanin uban me zai min?. Jidda ta ce,  kedai Allah ya ba mu lafiya. Suka yi dariya a tare suka cigaba da hira har aka yi i sha sannan Jidda ta wuce gida.

Ranar juma a su Abiy suka dawo, kamar yadda Mama ta ce Kano Win ta shigo ita da Yaya J. Sai da daddare suka zo gidan Nayla. Da zumuWi ta buWe ?ofar ta rungume Mama tana murna. A falo suka zauna Mama ta bita da kallo bayan sun gaisa ta ce,  Nayla babu wata damuwa dai ko?.

Nayla ta ce,  Babu komai Mama. Mama ta ce,  kar fa ki Soye min damuwarki, in kina ganin baza ki iya faWa min a gaban Jawad ba sai ya bamu waje. Nayla ta yi dariya tana kallon Yaya J ta ce,  babu komai Mama, in akwai zan faWa miki.

Mama ba haka ta so ji ba, bata so ta ji ta ce lafiya lau ko babu komai, damuwa ko tashin hankali kawai take da bu?atar ji daga bakin Nayla. Jin abinda Nayla take faWa sai ta sharebata nuna mata ba ta bata tsarabar da ta siyo mata. Jawad ma ya bata tsaraba harda McDonald fried chicken Win da suka yi da ita, ai kam ta ji daWi sosai sai muryar take yi ta ga babarta da yayanta. Bayan fitar Jawad yana jiran Mama a mota Mama ta kalle ta ta ce,  Nayla zo nan.

Nayla ta dawo kusa da ita ta zauna ta ri?e hannunta ta ce,  Kin tabbatar dai babu matsala?. Nayla ta ce,  babu Mama.
 Kina so ki ce ya karSe ki matsayin matar sa? Har ha??in da yake kansa na aure yana sauke miki ko ya ya?.

Nayla sai ta ji maganar ta yi mata nauyi sosai, ta sunkuyar da kai bata ce komai ba. Mama ta ce,  ba kunya zaki ji ba, faWa min zaki yi, ai ba ajiya aka kawo masa ke ba. Nayla a sanyaye ta ce,  Mama ki yarda babu wata damuwa.
 Baki amsa min ba ai, yana sauke miki ha??in ki da yake kansa?. A ta?aice ma ke da shi kun zama mata da mijin na gaske?. Nayla ta rasa abinda zata ce, ta rasa wacce amsa zata bawa Mama dan wallahi kunya take ji. Baza ta iya ce mata eh ba dan ta san ?arya take yi, sannan bazata iya cewa a a ba saboda kunyar da take ji.

Mama ta ce,  bai faru ba, Ina kallon idanunki na san bai faru ba, kuma ki ce min babu matsala Nayla? Gaskiya zan samu Abiy a raba auren nan kawai. Nayla a sanyaye ta ce,  A a Mama, Abiy har yanzu yana fushi dani, ki bari a kwana biyu ba yanzu ba.
Mama daman abinda so kenan sai ta ce,  ai shikenan. Allah ya kyauta, ki cigaba da ha?uri komai zai wuce.
 Mama ki gaishe da Abiy, Na yi kewar sa sosai, har yanzu bai bani umarnin zuwa Kaduna ba ko?.

 Bai bayar ba Nayla.
 Ki gaishe shi. Bara na kawo sa?o ki kai masa Mama ta faWa tana shigowa ciki da sauri amma ta bita da kallo tana taSe baki. Ba jimawa fito ta bawa Mama sa?on ta karSa tana cewa,  Abiy Wan gatan Nayla, ya gode sosai. Tare suka fito har mota ta raka Mama sannan ta koma ciki zuciyarta cike da kawar ?an gidan su.

" " " " " " " "

Abiy yana zaune ranar asabar da safe shida Jawad suna duba littafi wanda suke rubuta duk abinda ya shafi kasuwancin su musmaman wanda suka bawa kaya. Mama ce ta shigo da sallama hannunta Wauke da abinda Nayla ta bata ta ?araso ta zauna ta ce,  barkan ku da aiki. Suka amsa kafin Mama ta ce,  Abiy ga sa?o jiya Nayla ta ce na baka ta faWa tana ajjiye masa.

BuWewa ya yi ya yi karo da ?ananun cincin irin wanda yake so har take yi masa da tana gidan. Murmushi ya yi yana kallon cincin Win cikin kewarta ya ce,  na gode ya faWa yana rufewa ya cigaba da abinda yake yi.

Mama ta sauke numfashi ta ce,  Abiy haka za a bar Nayla a cikin wannan yanayin da take ciki? Wata biyu da kenan da tarewar ta amma babu cigaba tana nan a rame har yanzu. Dan tana sonsa ai ba hakan yana nufin zamu ?yaleta a halaka ba. Jawad ya kalli Mama jin abinda ta ce, dan shi kam bai ga alamun damuwa a tare da ita ba.

Abiy ya yi shiru bai ce komai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login