Showing 306001 words to 309000 words out of 332344 words

Chapter 103 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14407

mu aljanun daban suke, ba irin aljanun da aka sani bane."

"Kuma sun tashi Win, har tsoro na dinga ji kar maganganun aljanun ka su tashi ?a?ana" ta faWa tana ?ar dariya tana kallonsa. Ya cize lips Winsa na ?asa ya ce, "babu laifi in sun ji, gwara su tabbatar da babarsu tana sakawa babansu ya haukace. Shiyasa na ce miki laifin ki ne."

Cikin muryar shagwaSa ta ce, "Oh laifina ne ma?" Ta faWa tana kallon idanunsa, ya Waga gira yana kallon bakin ta ya ce, "laifin waye?."
"Naka ne, tunda duk tare zamu zauce Win, a tare aljanun na mu suka tashi." Ya Wage gira guda biyu sama ba tare da ya sauke su ?asa ba ya ce, "Ni ban kama ?afarki ba ai ?an mata."

Girarsa take shafawa a hankali, murya a ?asa ta ce, "Nima ban kama ?afar ka ba Wan samari, kai kana ganin nice a gaba, ni kuma ina ganin kaine gaba. Kowa ya ri?e nasa. Abinda na sani kawai mijina daban ya ke, shiyasa nake addu'ar kasancewa dashi ni kaWai har abada" ta faWa tana bashi light kiss a girarsa tare da sanya harsheta ta Wan sosa ta kaWan. Ya lumshe ido ya buWe ya kalle ta ya ce, "Yanzu sai ki ce min asuba ta kusa, amma kina ?o?arin ki saka wannan gashin naki ya ?ara shan ruwa."

"In ya sha ruwan ma zai bushe." Ya Wan buWe ido ya ce, "da gaske?." Ta Waga gira tana kallonsa ya langwaSar da kai ya ce, "Yau na zama Wan gatan Jidda." Ta shagwaSe fuska tana kallonsa ta ce, "Daman kai Wan gatan ta ne." Zuba mata ido ya yi yana kallo cikin ?aramin hasken Wakin, ya ri?e hannunta yana murzawa a hankali kafin labari ya sake canja salo.

Suna fitowa daga wanka aka yi kiran farko na asuba, Nayla bacci take ji sosai, idanunta har lumshewa yake yi, ta kalle shi ganin ya shimfiWa sallaya ta ce, "Bazan iya sallah ba, bacci nake ji sosai Rouhi." Ya bata light kiss a goshi ya ce, "ki huta kafin ayi kiran asuba, zan ro?a miki duk abinda ki ke so. Me zan ro?a miki?."

"Rayuwa dani kaWai, babu wata macen." Ya yi murmushi ya ce, "an gama, ki huta kafin ayi sallah." Kwanciya tayi ya gyara mata gashin kanta ya sake yi mata kiss a kumatu yana ji kamar ya mayar da ita cikinsa saboda so. Shi kansa a gajiye yake kuma baccin yake ji, amma yana da bu?ata da yawa a wajan Allah dole ya daure ya tayar da sallah.

Ana kiran sallar asuba ya tashe ta ya ce, "Jidda! Jiddana!." Ta buWe ido a hankali ta kalle shi ta ce, "Rouhii bacci!."
"Na sani, tashi ki yi alwala mu yi sallah sai mu kwanta, tashi kin ji?." ?in tashi ta yi tana shagwaSa, ganin zata Sata masa lokaci ya Wauketa ya shigar da ita banWakin ya ajjiye ta a gefen bathtub ya ce, "Ki yi alwala Jidda, za a tayar da sallah."

Kai ta Waga ya fito yana jiranta, ba jimawa ta fito ta saka doguwar riga ta saka hijjabi aka tayar da sallah suka bi masallaci suka tayar su ma. Ana idarwa ta kalle shi da idanunta a lumshe ta ce, "Good Morning Rouhi." Ya matso kusa da ita ya ce, "Good morning zam zam." Bacci ne a kanta bazata iya bashi amsar sunan da ya kira ta dashi ba, ta zare hijjabinta kalli su Marmerh ta ce, "Ka dawo dasu nan." Ya kwanta a kan gadon ya ce, "bar su a can" ya faWa yana janta jikinsa bacci mai daWi ya kwashesu.

Kukan Marmerh da Musliha ne ya tashe su gabaWaya, Nayla ta mi?e zaune kanta ya yi nauyi sosai saboda bacci, ta kalle shi ta ga ya ?arasa ya kwaso su dukansu ya bata Musliha ta fara bata laban. Laban Win shima ya bawa Marmerh dan ya san yunwa take ji ta sha ta fara wasa. Musliha ma tana ?oshi ta fara kalle-kalle tana kallon babanta tana dariya alamun babu batun bacci.

Nayla ta kalle shi kamar zata yi kuka ta ce, "Bacci Rouhiiii." Ya matso kusa da ita ya ce, "Kwanta ki huta, zan fita dasu har sai kin tashi."
"Amma kaima baccin ka ke ji."
"Zan yi anjima, amma ki huta yanzu." Ta kwanta ya rufeta ya shiga banWaki, bai jima ba ya fito ya Wauki baby pusher Winsu ya saka su suka fita daga Wakin.

Nayla sai azahar ta farka har lokacin basu dawo ba, ta yi wanka ta shirya a lokacin ta ji ana kiran sallah. A Waki ta yi sallar dan ta san in ta fita babu lallai ta samu elevetor tunda lokacin sallah ne a cike yake zuwa. Jim kaWan da idar da sallah suka dawo, ta kalle shi kamar yadda yake kallonta, barinsu ya yi a cikin pusher Win ya ?araso inda take, ta Wora hananyenta a kafaWarsa ta ce, "Sannu da zuwa."

Goshinsu ya haWe waje Waya idanunsa a lumshe, a hankali ya fara kissing Winta cikin salo na soyayya, bai jima baya dakata ya kalli idanunta ta ya ce, "kin gama baccin?." Ta Waga masa gira kafin ta ce, "amma fa da saura, sallah ce ta tashe ni."
"Ki sake komawa, zan sake fita da yaranki har sai kin tashi."
"Kaima fa na san baccin ka ke ji ko?."
"In kika yi kamar na yi ne, ki yi mana bacci."

Ta yatsine fuska ta ce, "Yunwa nake ji." Ya raba kansa da ita ya Wauki leda a bayan pusher ya ce, "Na taho miki da abinci zuma, gashi ki ci."
"Kai fa?."
"Mun ci na mu, ni dasu mun ?oshi. Murmushi ta yi ta karSa ta buWe ta ci abincin, bayan ta gama ta ajjiye ragowar ta dawo kusa dashi da yake tare dasu Marmerh sai turmurmusa masa jiki suke yi da tsalle-tsalle.

Nayla ta ?araso ta bawa Marmerh wayarta dan tayi game, ta Wauke Musliha daga jikinsa ta ce, "Sai tsalle-tsalle ku ke yi masa a jiki, ba ku san ya gaji bane? Ba ku san...." Sai ta daina kallon Musliha ta kalle shi kamar yadda yake kallonta ta ce, "Ba ku san ya ?arar da ?arfinsa akan Mummynku ba..? Ku bar shi ya huta, ya gaji sosai." A yadda ta ?arashe maganar ya saka shi bata light kiss a bakinta ya ce, "Zumata."

"Da asuba ka ce zam zam, yanzu ka ce zuma. Wanne yafi dacewa dani?."
"Kuma sunayenki ne, zaki amsa sunan zuma, zaki amsa sunan zam zam. Zam zam ya fi komai daWi da magani, kema kuma magani ce a gare ni mai matu?at tasiri. Zuma kuma za?inta mai daWi ne da kuma magani, musamman pure zuma wacce ba a yi mata mix da komai ba, asalin yadda Allah ya yi za?inta kamar irin ta ?asar nan. Haka za?inki yake daga Allah Jidda, mai saka Omar zaucewa da fita daga cikin hankalinsa..." ya marairaice fuska yana sake yin ?asa da murya ya ce, "Zumata, Don Allah ko bayan na mutu kar ki yi wani auren kin ji? Bazan taSa farin ciki a cikin kabarina ba, zan kasance cikin halin ?unci da kishi." Bakinsa ta yiwa kiss ta ce, "Tare zamu mutu in sha Allah."

Ya yi ajiyar zuciya yana murmushi ya ce, "Da na rasa Didi na Wauka na gama samun farin ciki a duniya, na yanke rai da cigaba da rayuwa, na ji dama nima na mutu na huta. Duniyar tayi min zafi, komai ba yayi min daWi, komai ya tsaya cak, ina jin kamar an canja ni. Ina ji kamar gatana ta tafi, ina ji kamar farin cikina ta bar duniya, ina ji kamar rayuwata ta lalace tunda babu ita...." Ya ri?e fuskarta da hannu biyu, yana shafa kumatunta da yatsa Waya ya ce, "Amma a jiya kin saka min ?aunar cigaba da rayuwa, kin saka min ?aunar cigaba da kasancewa da ke, kin saka min ?aunar cigaba da rayuwa har nan da shekara Wari. Ina so na rayu da ke Jidda, ina so na cigaba da kasancewa dake kodan na cigaba zuwa inda naje a jiya, ina so na rayu dake ki cigaba da nuna min soyayya da ?auna kamar dai jiya!...."

Nayla tayi murmushi jin abinda ya ce, ta bishi da kallo kafin ya ce, "Allah ya nuna min ikonsa, ya nuna min ko babu Didi zan cigaba da samun farin ciki a rayuwata, rashinta bazai hana ni cimma farin cikin da yake jirana. Shiyasa Allah ya shigo min dake rayuwata, ashe kece zaki maye gurbin dangina gabaWaya. Huh Allah gwanin hikima da iya tsara komai ga bawansa, baya barin wani dan wani yaji daWi, domin kuwa koda ya bari Win shi yake bayar da jin daWi ya kuma bayar da akasinsa. Kasantuwar wanda ka ke so a tare da kai ba shine dawwamar farin ciki ba, a ko yaushe cikin jiran ikonsa ka ke."

Nayla ta ce, "Wanda ya rasa uwa da uba a lokaci Waya ma yana cigaba da farin ciki a rayuwar, indai ya mi?a lamarinsa ga Allah zai yaye masa dukkan damuwa ya kuma bashi farin cikin da bai samu a lokacin da suke da rai ba. Kamar yadda kace, zaman wani a duniya baya zama silar dawwamar farin cikin wani."

Ya girgiza kai cike da gamsuwa ya ce, "Haka ne Jidda. Allah ya cigaba da bamu ikon karSar ?addara, Allah ya bamu ikon mi?a masa lamarin mu gabaWaya. Amma gaskiya ina kewar Didi sosai, ban taSa jin kewar wata halitta kamar yadda nake kewarta ba, in na tuna bata duniya bana sani lokacin da hawaye yake zubowa daga idanuna. A kullum dana farka daga bacci itace take fara zuwa zuciyata, dana rufe idona fuskar Didi zan fara gani. Amma wanda ya fini sonta ya karSe ta, daman aro ya bani ita, kuma yanzu ta koma gare shi. Ina ji a jikina tana cikin rahamar Allah." Nayla tayi murmushi ta ce, "in sha Allah."

Omar ya zuba mata ido yana kallo bai ce komai ba, da suka haWa ido sai ya Waga mata gira yana lumshe idanunsa. Murmushi bata ce komai ba shima bai ce sai kallonta da yake yi.

"Our yesterday night is memorable!" Ta faWa a hankali tana shafa gashin fuskarsa. Lumshe ido ya yi yana kallonta ya ce, "ni na rasa ma ne zance miki akan daren jiya." Fuskarta ta haWe da tashi ta ce, "Ka bar sa a ranka kawai." Kallon bakinta yake yi kafin ya fara kissing Winta.

Sun manta da yara a ajjiye, sai da Marmerh ta fara kiran sunanta sannan ta zame kanta ta kalle su ta kalle sa ta ce, "Honeymoon mu ke yi ne ko childmoon?." Dariya ya yi ya ja kumatunta ya ce, "Lokacin su ne, tafiya ta gaba dole mu dire su a gida, bazai yu irin haka ta dinga faruwa ba. Murmushi ta yi tana hargitsa gashin girarsa, ta hargitsa kuma ta mayar ta gyara. Sai kuma ta mi?e ta shiga banWaki ta Wauko sabon brush na hotel Win ta buWe ta dawo kan cinyarsa ta zauna ta fara gyara masa gira.

Tajeta take yi ta??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????na bi a hankali tana kwantar da ita, bayan ta gama da gira, ta dawo tana taje gashin fuskarsa tana kwantar dashi a hankali. Shi dai kallon ta kawai yake yi yana ji ina ma ace su kaWai ne a duniyar nan, ai da ya nuna mata ?aunar da bai nuna mata yanzu ba.

Sai da ta gama gyaran gashin ta ce, "kalli kanka, baka yi kyau ba?." Ta faWa tana nuna masa mirror, ya kalle ta ya ce, "indai na yi miki kyau shkenan."
"Ka yi min."
"Case close" ya faWa yana kallon ta yana murmushi kamar yadda take murmushi.
P121

Nayla ta bi ?afarsa da kallo, ta ri?o abinda yake Waukar hankalinta a ?afarsa tana kallonsa ba tare da ta saki ba ta ce, "wai shi wannan meye fa'idarsa ne? Tun kafin na aureka na san dashi a ?afarka, meye amfaninsa?." Ya yi murmushi tare da jan hancinta ya ce, "mallaka ce, bani shi akayi akace indai yana ?afata zan mallake zuciyar zumata."

Nayla cike da shagwaSa ta ce, "Ai tun kafin ka san zumar ta ka yana ?afarka, tun kana hararata kana cewa ta ?auracewa ganin ka." Omar ya yi dariya mai sauti, ya ri?e kumatunta da hannu biyu ya ce, "bakya mantuwa Jidda." Itama murmushi ta ke yi ta ce, "Ya za a yi na manta? Ni ka kalla ka ce ina yi maka korar shaiWanu."

Dariya yayi sosai harda tafa hannu, ya Wan murza goshinsa kamar ko yaushe yana binta da kallon ?asan ido ya ce, "ke ko...." sai bai ?arasa ba ya girgiza kai yana murmushi. Nayla ta ce, "haka ne mana, ko ba haka aka yi ba?." Ya yi pecking Winta a goshi ya ce, "Haka ne Jiddana."
"To faWa min fa'idarsa" ta faWa tana jan abin ?afar tana kallonsa. Omar ya ce, "kin san wanda ya yi rayuwa irin tawa ana bashi maganin tsari, har da maganin da makami bazai shiga jikinsa ba. A lokacin da nake tsaka da rashin ji wani mai maganin gargajiya ya bani su, harda na hannu da na ?ugu dana wuya. Wai in na saka zan gagari kowa, babu wanda ?arfen da zai iya ratsa jikina. Hmmm kin san meye?."

Ta girgiza kai alamun a'a, ya taSe baki ya ce, "duk ?arya ce, dasu a jikina aka ji min ?aton ciwo a bayana. Dan tabon ya baje ne da na nuna miki, haka suka bar Yayata da jinya. Ai kuwa da na samu lafiya shima mai maganin sai da ya yi jinya, sannan na saka aka kwashe jarin maganin aka watsar a kwata." Yadda ya ?arashe maganar ya bawa Nayla dariya, ta dinga dariya babu ?a??autawa tana kallonsa. Shima dariyar yake yi ya ce, "shiyasa duk na tattara na zubar, kuma tun daga ranar babu wanda ya isa yazo inda nake yace ga maganin wani abun, dan in har kazo kai ne zaka je neman maganin ciwon da zaka koma dashi."

Nayla ta tsayar da dariyar ta ce, "kaima ban da abinda Rouhii, wanne magani ne zai hana shigar makami jikinka?."
"Akwai fa Jidda, wanda suka mayar da hankali akan abin su sun samu. Ni kam watsarwa nayi, daman Didi sai da ta faWa min duk na ?arya ne amma na?i ji" ya ?arasa faWa yana girgiza kai tare da murmushi.

"Daman wanda ya?i ji ai bazai ?i gani ba.
"Na gani kam, amma shima mai maganin ya gani ai. Ya ji a jikinsa sannan ya rasa jarinsa."
"To ya aka yi ka bar na ?afar?."
"Yana burge ni ne kawai, na bar shi dan burgewa ba dan rigakafin makami ba." Nayla ta sake yim dariya ta ce, "ai kam yana yi maka kyau sosai, sai ka koma kamar Wan india. Kasan suma haka suke saka ba?in abu a ?afarsu, wai maganin baki."

Murmushi ya yi sannan ya ce, "shiyasa nake so na ganshi a ?afarki, adonsa yana yi miki kyau." Nayla ta kalli ?afarta taga wanda ta Waura tun a nigeria yana nan, ta kalle shi ta ce, "kaima yana yi maka kyau Baby Rouhii." Murmushi ya yi sosai jin sunan da ta faWa, ya sake pecking Winta a goshinta tare da ri?o hannunta.

Suna wannan hidimar aka yi kiran sallar la'asar, basu fita masallaci ba a Waki suka yi sallah, sai sallar magriba sannan suka fita. Kamar jiya rabuwa suka yi sai tara na dare sannan ta dawo, ta fito daga wanka kenan ya shigo. Yaransa suka fara murnar ganinsa ya ?arasa ciki yana bawa ko wacce KitKat Win da ya siyo musu sai da ya gama dasu ya kalle ta.

"Abinci fa?" Ya faWa yana kafe ta da idanu saboda daga ita sai towel. Zama tayi akan stool ta Wora ?afa kan Waya ta ce, "Na ci shawarma, I'm okay. Zamu je yawo ne?."

Ya girgiza kai alamun a'a, ya zauna kusa da ita ya ce, "Nifa danasani nake yi, ji nake ina ma wata ?asar muka je ba nan ba." Nayla ta waro ido ta ce, "Madinan?."
"To ai nan garin ibada ne Ashiq, tsakani da Allah ki faWa min wacce ibada mu ke yi nida ke? Ina fitowa daga rauda Allah Allah nake yi na dawo wajanki. Kamata ya yi ina cikin masallaci yanzu ina karatun alkur'ani ina yiwa wanda na rasa addu'a, amma kin ganni a nan ina kallon ki."

Dariya ya bata sosai ta yi dariya ta ce, "Sai mu mayar da hankali akan ibadar yanzu." Ya girgiza kai ya ce, "ibada sai da nutsuwa, ni kuma kin saka na fita daga nutsuwata wallahi. Sai da nayi da gaske na kawar da tunaninki kafin na tayar da sallah." Murmushi ta yi tana kallonsa ta ce, "to yanzu ya za a yi?."

"Haka zamu cigaba da zama, ai hakan ma ibada mu ke yi." Ta yi dariya kaWan ta kalli su Marmerh da suke ya cin lays cheese ta kalle shi bata ce komai ba.

"Wai yaran nan baza su yi bacci ba? Ni na gaji da jira wallahi. Babu wani maganin bacci da zan Wura musu su kwana su yini suna bacci?." Dariya Nayla ta dinga yi harda ri?e ciki dan ya bata dariya sosai, ya harareta ya ce, "Dariya na baki?." Ta cigaba da dariya ta ce, "Allah ka bani dariya, haka kawai sai ka basu maganin bacci?."

"Baccin shine ya kamace su ai." Dariya ta take yi sosai ganin ya mi?e ya Wauke su duka ya kwantar dasu akan extra bed Win da ya saka aka saka musu, ya dinga rarrashinsu a lallai sai sun yi bacci. Marmerh dai tayi baccin amma Musliha babu alama, ?yaleta ya yi a kwance ya dawo wajan Nayla ya ce, "I have gift for you." Murmushi ta yi ta ce, "da gaske?." Ya Waga kai ya juyar da ita tana kallon mirror ya ce,"rufe idonki." Ba musu ta rufe idon, ya Wauko ?aramar cover a aljihunsa ya buWe ya Wauko necklace mai kyau siriri ya saka mata ya rufe hook Win.

"BuWe ki gani." Ba musu ta buWe idon tana kallon sar?ar a madubi, ta Wora hannunta a kai ganin sa?ar mai kyau ?ar siririya sai sunanta da yake a jikin sar?ar. Jidda, shine abinda ya zama gaban sar?ar. Receipt Win ta ya mi?a mata ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login