Showing 258001 words to 261000 words out of 332344 words

Chapter 87 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

14893

tana rawa matu?a saboda kawai an yabi ?afarki. Yau fuskarki da surarki ake yabo..." ya faWa yana watsa hannayensa cikin tsananin kishi da Sacin rai.

"Har wanWanda ba sa jin hausa abokan kasuwancina sun kira ni suna cewa sun ga matata. Hankalinki ya kwanta an ganki ko Nayla!? To ta shi ki tashi ki bani waje!." Nayla ta kalle shi da sauri jin da sunan da ya kirata, zata iya irga sau nawa ya kira ta da Nayla, dan baya faWa kwata-kwata. Kuma ta san baya taSa ce mata Nayla sai in ta Sata masa rai, a lokacin ne yake mantawa da Jidda ko Ashiq ya kirata da sunanta.

A raunane ta ce, "wallahi Rouhi ban ce ayi posting ba, na san laifina ne da ban yi magana na ce kar ayi ba, amma ban san zasu yi ba."
Kamar zai dake ta ya yo kanta da faWa a hargitse ya ce, "Amma kin san babu ta yadda za a yi ayi mana hoto nida ke ace baza a yi posting ba ko!? Likers suke nema, kuma matu?ar aka Woraki dole a samu likers har da comments. Meyasa baki wannan tunanin ba!?" Ya faWa a fusace yana zare mata idanu waje.

? ?? Sak ya koma mata Tiger, kallon Tiger take masa lokacin da ya Wora mata wu?a a wuyanta yana zare mata ido, kallon tiger take masa wanda ta ganshi da jini kaca-kaca a jikinsa. Jikinta ya yi sanyi sosai, a hankali ta sake cewa, "na yi kuskure ka yi ha?uri, amma yanzu na yi mata magana zata goge in sha Allah." Ya kalle ta cikin hararar da ta saka ta yin shiru, ya yi ?wafa tare da jan tsaki ya girgiza kai bai ce komai ba.

? ?? Nayla ta duba wayarta ta nuna masa ta ce, "ka gani har ta goge ma." Ya Harare ta da jajayen idanunsa ya ce, "Ko ki matsar da wayar nan daga kusa dani ko na fasata, kuma wallahi in na fasa bazan siyi wata ba, kema kuma baza ki siya ba, na kuma ce wallahi." Nayla ta janye wayar ta ajjiye a gefenta, ya bita da kallon up and down ya ce, "Dan ta goge mutane nawa ne suke dashi? Mutane nawa ne suka saka su ma? Ko duk zaki bi su ki ce su goge ne?."

? ? ? Yadda ya kafe ta da ido shine ya saka ta sauke ido ?asa bata ce komai ba. Yaja dogon tsaki ya ce, "Kawai kin riga kin cuce ni, kin yi min abinda bana ra'ayi kuma bana so. Duniya gabaWaya a kan hotonki take magana, ni ba banza ba ne da zan ji alfahari dan wani ya yabi matata ba......" ya Wauke ido daga kanta, kafin ya sake kallon ta ta ce, Ki ta shi ki bani waje na ce ko!?."

Nayla zata yi magana cikin tsawa ya ce, "in kika yi min magana sai na fasa miki baki, ki bar wajan nan ko na nuna miki asalin waye ni!." A hankali ta mi?e ta bar falon bata ce komai ba, ya yi tsaki ya Wauki wayarsa ya shiga TikTok, bai yi seconds biyar yana scrolling ba ya yi karo da video sa shida Nayla da kuma Musliha.

Kishi da haushi suka sake kama shi ya furzar da iska ya cillar da wayar. A haka ya kwanta cikin takaici da Sacin rai, in dai zai farka sai ya duba wayarsa, amma baya jimawa yana scrolling zai ga ga abinda baya so, ?arshe kashe wayar ya yi cikin ba?in ciki da takaici.

? ? ? ? ? ? " " " " " " " "

Cikin wanda suka ga video Nayla da Omar harda Narma, Narma ta ruWe ta saka hotunan a gaba tana kuka. Dad da yake zaune a kusa da ita ya ri?e hannunta ya ce, "Haba Narma meye haka kuma? Baki yarda da abinda nace miki bane ba wai?."

Narma ta ce, "Dad kalli matar shi, kalli yadda yake farin ciki kana gani ka san yana sonta. Dad ni ce baya so, Dad bazai aure ni ba, shikenan mutuwa zan yi." Ta faWa cikin kuka mai tsanani. Mum ta kalle ta cikin tausayi ta dafata ta tace, "ki yi ha?uri Daughter, kin ga saboda ke mu ka zo Kano dan a same shi a yi magana, in kina wannan kukan sai ki saka mu ga kamar har yanzu kina ganin bamu kyauta miki ba."

Dad ya ri?e hannunta ya ce, "Zan je na same shi da kaina nayi masa magana, na tabbatar zai amince ya aure ki tunda yana sonki yana ?aunarki, na tabbatar zai amince ya aure ki in sha Allah, so don't be nervous." Ta kwantar da kanta a kan kafaWar Dad ta ce, "Dad da gaske zai amince?." Dad ya ce, "zai amince ya aureki, I promise you zan san yadda zanyi ya amince ya aure ki daughter. Kar ki damu ki kwantar da hankalinki."

? Ta goge idanunta tana cigaba da kallon hoton Nayla da Omar zuciyarta na bugawa sosai. Hankalinta ya gama tashi gani take yi bazai amince ya aure ta ba tunda yana da matarsa mai kyau gashi har ta haihu.

? ? ?? Washe gari da safe Dad da Mum suna zaune suna breakfast Narma ta fito taja kujerar dining ta zauna, Dad ya kalle ta kafin ya yi magana ta ce, "Morning Dad." Dad ya ce, "Ya ki ka tashi Daughter?."
"Fine" ta faWa tana haWa tea tana sha bata sake cewa komai ba. Dad ya ce, "nayi waya an tabbatar min da yanzu yana office, in na fita zan je na haWu dashi."

Narma ta Waga kai kawai bata ce komai ba. Mum ta ce, "ki kwantar da hankalinki dear, komai zai zama daidai." Kai ta Waga bata ce komai ba ta mi?e da mug Win hannunta ta hau sama.

Mum ta kalle shi a raunane ta ce, "Dear anya yaron nan zai amince da auren Narma?."
"Zai amince in sha Allah, kar ka damu in sha Allah zai amince. In bai amince ba ya zamu yi da Narma? Ai sai ta samu heart attack." Mum ta yi tagumi ta ce, "wallahi na damu sosai, bana son wani abu ya samu Narma wallahi."

"Saboda ita zan je na same shi amma bayan haka ke kin san bazan je ba, amma zan je saboda mu san abinda zai faru, Na san bazai ?i amincewa ba tunda yana sonta. Kuma a matsayin da yake dashi yanzu abin alfaharinsa ne ace yana da inlaw kamar ni." Mum ta girgiza kai ta ce, "to ba dole ma ya amince ba, ai dole ya amince ya aureta ko baya so." Shiru ya yi ya girgiza kai bai ce komai ba ya mi?e ya fita.

? ? ?? Omar da safe koda ya tashi shiryawa ya yi ya fito falo ya tarar an ajjiye masa kayan breakfast. Zama ya yi yana ci, a lokacin Nayla ta shigo da sallama hannunta Wauke da Musliha. Sallamar ya amsa ya kalle ta ya watsar kamar bai ganta ba, ya mi?a mata hannu alamun ta bashi ?arsa. Ba musu ta bashi Musliha, sai ya yi murmushi yana kallonta domin kuwa Allah ya zuba baiwar kyau a fuskar Musliha. Nayla ta ce, "Ina kwana."


Kallonta ya yi ya Wauke kai a da?ile ya ce, "Lafiya." Daga nan ya yi shiru bai ce komai ba. Nayla ta ce, "YaMar har yanzu fushi ka ke yi?." Bai kula ta ba ya gama abinda yake yi, ya sumbaci goshin Musliha ya mi?e tsaye ya zo inda take ya ajjiye mata ita a jikita, ya kalle ta suka haWa ido na wani lokaci kafin ya janye idonsa ya Wauki key na mota ya sauka daga saman.

Ajiyar zuciya ta yi tana binsa da kallo ta ce, "na shiga uku kuma fa ai, shi bai san ayi abu ya wuce ba, yayi ta fushi kenan kamar tsohon arne. Zai yi ya gama ya dawo ya same ni." Tashi ta yi ta shiga nata falon dan bata san abinda zata yi masa ba kuma.

? ? Omar ko da yaje a haWaWWen sabo office Winsa na karSar manyan ba?i ya zauna, office Win yana da girma sosai, Wauke da kujeru set Waya masu kyau da kuma kujeru na zaman office. Da awards da ya samu a jere akan wani dogon table, ga hotonsa da manyan mutanen nigeria da wajenta.

? ? Babu abinda babu a office Win, tv, dispenser, fridge, kettle ta dafa tea, microwive da komai na amfani akwai. Buga ?ofar aka yi ya ce a shigo, aka shigo da sallama ya kalli yaronsa alamun ?arin bayani ya ce, "Boss akwai wani babban mutum da ya zo nemanka." Omar ya Wan yi jim kafin ya ce, "Waye?."
"Kamar Wan siyasa ne."
"Ya jira ni ina zuwa, ina wani aiki yanzu." Yarom ya amsa ya fita.

Ya samu Sen a zaune ya ce, "Boss ya ce ka jira shi yana zuwa." Da mamaki yake kallon yaron ya ce, "ka faWa waye ya zo nemansa?."
"na sanka ne da zan faWa masa waye?."
"Ka koma ka ce masa Sen Sagir ne yazo."
"Umarninsa nake bi ba naka ba, in kai shugaban ?asa ne ba sanata ba abinda yace shi zan yi" ya faWa yana wucewa ya bashi waje. Sen cike da ?unar rai ya bi yaron da kallo, sai yanzu yake dana sanin rashin tahowa da escort, da tare suke dasu babu abinda zai hana bai saka an yiwa yaron dukan tsiya ba.

? ? ?? Sen ya gama zuwa wuya, sama da mintina talatin yana jiran Omar bai ce ya shigo ba. Sai wuci yake shi kaWai yana ?wafa, Allah ya taimaka wajan ba public waje bane da ya shiga uku da jin kunya. Narma kaWai yake hange a idanunsa, in ba dan haka ba da yanzu ya saka an tashi wajan, amma ita yake tunawa shiyasa yake yin sanyi. Bashir ne ya zo wucewa ya ga babban mutum kamar Sen yana jiran Boss Winsu. Ya bishi da kallon mamaki, bai yi magana ba ya shiga wajan Omar. A tsaye ya samu Omar yana Waukar wayarsa da key da alama fita zai yi. Bash ya ce, "Tiger kana da ba?o a waje."

Omar ya Wan dafe kai ya ce, "na manta, ka ce ya shigo" sai ya kalli agogo ya ce, "duk da dai sauri nake yi." Bashir bai faWa masa waye ba ya Wauki abinda ya kawo shi wajan Omar Win ya fita.
P099

? ? ? Da sallama aka shigo ya Wago tare da amsawa idanunsa suka haWu da na Sen Sagir. Omar ya gyara zama yana kallonsa da matu?ar mamaki amma bai ce komai ba, ya ?araso ya zauna yana kallon Omar kamar yadda yake kallonsa, Hannu ya mi?awa Omar alamunsu gaisa, ba musu Omar ya bashi hannu suka gaisa. Yangance Sen ya ce, "Ya aiki? Ka barni ina jira for more than 40mints." Omar ya ce, "Alhamdu lillah.... Ban san da zuwan ka ba, so dole zaka jira na gama abinda nake yi." Sen ya yi ajiyar zuciya, bai bari maganar ta yi tasiri a ransa ba, Narma kaWai yake gani hakan ya saka ya ce, "Tiger nazo tun daga Abuja kawai saboda na ganka."

Omar ya Wan taSe baki ya ce, "zaSe ya kusa ko? Kamar saura ?an kwanaki kaWan na ji ana cewa ko?." Sen ya kalli Omar suka haWa ido sai Omar ya ce, "Yanzu ba wancan tiger Win da ka sani ba bane, wannan Tigers Footwear ne. In ma kana neman wanda zasu yi maka aiki kamar yadda ka saba zaka iya zuwa bakin titi suna nan suna zaman jiran zuwanka, in maganar da ta kawo ka kenan ina da ba?in da zan yi" Omar ya faWa yana cigaba da duba abinda yake gabansa.

Sen ya daure ya ce, "Ba wannan maganar ce ta kawo ni ba."
"Ina jinka, but don't waste my time, ina da ba?i suna jirana."
"Omar na zo ne akan batun Narma." Da sauri Omar ya kalle shi kana ya ce, "Driver take nema ne?."

Sen ya kalli Omar jin ba?ar magana yake faWa masa a fakaice, amma saboda Narma da halin da take ciki sai ya kawar da maganar Omar ya ce, "Omar wannan ya wuce ya kamata ka manta komai ya wuce. Narma ta shiga damuwa a kanka, tana matu?ar sonka, in ta rasa ka zata shiga damuwa sosai. Please Omar ka amince ka karSi auren Narma, this the first time da nake ro?on wani a rayuwata, i beg you for that, ka amince ka auri Narma in ba haka ba zata iya samun matsala."

Omar ya zuba masa ido yana kallonsa cikin mamaki da al'ajabi, wato yanzu ya zama mutum kenan, tunda da ya ce kallon dabba yake masa, ya ce ma gwara dabba akansa. Yanzu ya tashi daga jahili kenan ya dawo mai ilimi tunda gashi a zaune a cikin office Winsa yana kallonsa yana faWa masa ya auri ?arsa, yanzu ya tashi daga wanda bai zai kaiwani mataki a rayuwarsa ba ya dawo mai matsayi a idon sanata. Soyayyar da ake i?irarin yayi asiri yanzu ta dawo ta gaskiya tunda gashi ana cewa ya aure ta. Omar ya dinga binsa da kallo yana tuna abinda ya faru a baya, hakan ya saka ya zuba masa ido kawai yana kallonsa. In ba dan ma yana so ya nuna masa banbancin da da yanzu shi ya isa ya iya haWa ido dashi?.

Sen ba tare da jin nauyi ba ya ce, "Gab take da kamuwa da heart attack Omar, ka amince da ita ka aureta zata zama matarka ta biyu, dan ta zo a sencond wife Winka ba wani abun damuwa ba ne."

Omar ya girgiza kai cikin dubun mamaki, ya yi wani irin murmushi na rainin hankali ya kalle shi ya ce, "Sen Sagir Sani Shatima, yau kaine ka ke neman alfarma a wajan Omar? Ka manta waye Omar ne a wajanka?."

Sen ya ce, "ka ji na ce komai ya wuce ai, ni dai burina ka amince ka auri Narma please ." Omar ya jingina da kujerar office yana Wan motsawa a hankali tana juya shi kaWan-kaWan ya ce, "to abin ne yake bani mamaki, ka manta kace dabba ta fi ni wajan ka? Ka manta kace ko a mai gadin gidanka bazan zo ba balle sirikin ka?. To ya aka yi aka haihu a ragaya? Ko dai Satan kai ka yi kazo wajena? Dan na san ba ni Omar Win ka ke nema ba."

Sen ya yi shiru bai ce komai ba Omar ya ce, "Wannan Omar Win ba shi da ilimin da zai auri ?arka, ?arka tana matakin masters ko? ?arka tana juya kuWin masu yawa ko? ?arka tafi ?arfina sai dai na zo a mai gadinta ko?. Ina so ka tuna? wannan Omar Win fa ko takardun secondary bashi dasu har gobe, kai da kan ka ka ce baka Waukar mutum aiki a gidanka sai yana da takardar digree ko masters, to ya aka yi ka ke so ka bawa ?arka jalihin mutum irin Omar?."

Sen ya ce, "Please Omar! Abinda ya faru ya riga ya wuce, ka manta mu kalli abinda yake present a yanzu."

Omar ya sake yin murmushi ya ce, "Shine nake mamaki ai Sen Sagir, ta ya zaka amince ka bawa ?arka wanda babu matakin rayuwar da zai iya kai wa?. Ka ce wanda ba shi da ilimi babu inda yake zuwa sai dai rayuwarsa ta ?are a kan titi kuna cigaba da amfani da rayuwarsu wajan gina ta ku rayuwar da ta ?a?anku. Shine amfanin mu kawai a wajanku, ya aka yi ka zo kana son irin wannan namijin ya auri ?arka?."

Sen ya yi ajiyar zuciya yayi ya ce, "Omar ka daina wannan maganar, yanzu magana ake ta ceton rayuwar yarinyata, tana sonka, tana ?aunarka, tana so ya rayu dakai a matsayin mijinta. Na amince ka aure ta ko dan ceton rayuwarta." Omar ya yi murmushi yana kallonsa yana girgiza kai cike da mamakin Wan adam ya ce, "Senator Sagir Sani Shatima kenan...." ya sake yin ?ar dariya ta rsinin hankali ya ce, "tambayarka nake so na yi." Ya kalle shi alamun ina ji, Omar ya ce, "waye ni?." Sen ya ce, "Omar mana."
"Ina nufin waye ni..Kai ba Senator ba ne? So nake ka faWa min ni waye kamar yadda ka faWa min a wancan lokacin."

Sen ya ce, "Omar ne kai, C.E.O Exclusive Footwear." Omar ya yi murmushi yana girgiza kai? ya ce, "A'a, Tiger ne wannan, Wan daba, Wan shaye-shaye, mara aikin yi, wanda yayarsa take Waukar Wawainiyar rayuwarsa saboda ya gaza. Mara ilimi ne, jahili, wanda ya yiwa ?arka asiri, wanda bazai je ko ina a rayuwa ba, Ko ba haka ka ce ba?."

Sen ya yi shiru bai ce komai. Omar ya ce, "Haba Sen, yanzu shi ka ke so kace zaka aurawa ?arka? Ko dai ka yi Satan hanya ne kana neman wani Omar Win ba ni ba?." Nan ma ya yi shiru bai ce komai ba. Omar ya Waure fuska sosai, ya canja daga lokacin fara'a ya dawo lokacin rashin mutumci ya ce, "Alhaji Sagir zan ce ko Malam Sagi..?"

Ya sake girgiza kai ya ce, "ina so ka sani ba lallai sai kana da ilimin boko zaka kai wani mataki a rayuwarka ba, meye ilimin bokon....? Turanci ko?. Ina so ka sani akwai masu Digree da masters Win da ka ke ta?ama dashi a ?ar?ashina a cikin wajan nan, ni da ka ke kallo bani da ilimi ni ne nake biyansu albashi a duk wata. Ni Win dai da kake kallo matsayin wanda ba zai je ko ina a rayuwa ba ni ne dai na kai matakin da kai baka je shi ba. Ba kai kaWai ka taSa yin senator a Nigeria ba, amma ni ni ne kaWai akan matakin babu wanda ya taSa kaiwa a kaf africa ba nigeria kaWai ba, duk wanda zai samu matsayin da na samu a yanzu a bayana yake, ko babu komai sai an ce ai Omar ne ya fara kafin wannan. Ko a iya haka Allah ya bar ni Alhamdu lillah, ya gama yi min komai a rayuwa, balle kullum sake cigaba nake yi."

Omar ya Wan yi murmushi ya nuna shi da ya yatsa ya ce, "Dama ba nace ka kasance a raye ba?


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login