Showing 273001 words to 276000 words out of 332344 words

Chapter 92 - KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

30 Nov 2025

30866

"Ni zan wuce gida Nayla, don Allah kar ki bar komai ya dame ki." Ta yi murmushi ta ce, "Babu komai Didi."

"Ya tafi da Marmerh, ki karSo min ita." Nayla ta amsa ta karSi Musliha ta bawa mai kula da ita sannan ta hau sama ta shiga Wakin Omar. A kwance taga Marmerh a kan gado, ta Wauko ta bata ce komai ba ta sakko ta kawo mata ita har mota, Didi ta shiga motar ta ja ta tafi.

Didi ana tafiya Nayla ta Waure fuska, ta juya ya koma gidan ta hau sama kai tsaye inda ta ganshi ta wuce. Har zata shiga Wakin nasa sai kuma ta fasa dan haushinsa taji sosai, ta Wauka zai faWa mata akan maganar Narma Abiy ya kira shi, kuma da ta tambaya sai ya ce zai faWa kuma bai faWa ba ya cigaba da harkarsa, hakan sai ya Sata mata rai, sai ta ga babu amfanin ta yi masa maganar kawai ta share shi.v
KRB3P105

Narma haka suka koma gida cikin yanayi mara daWi, Mum tana ganin shigarsu ta mi?e ta ri?o Narma ta kwantar da ita a jikinta suka samu waje suka zauna Mum ta ce, "Safna ina ku ka je ne haka? Ina ta kiran ku babu wanda ya Wauki wayata." Safna ta ce, "Gidan Omar mu ka je." Mum ta ce, "What? Gidansa kuma?."

"Eh Mum, can muka je muka same shi."
"To ya aka yi?." Safna ta taSe baki ta ce, "Kusan ya wula?anta mu zan ce, wata tsawa da ya yiwa Narma sai da gabana ya faWi wallahi. Amma a haka Narma kuka take yi tana so ya saurareta amma ya?i, idonta ya kalla ya ce baya sonta ba zai aure ta ba, ta daina wahalar da kanta a akansa, shi in ya yi gaba baya dawowa baya."

Ajiyar zuciya Mum ta yi, a lokacin Dad ya shigo falon ya ji abinda Safna ta ce ya zauna Mum ta ce, "To ya Narma? Me ta ce?" Ta faWa tana taSa wuyan Narma tana jin body temperature ta. Safna ta ce, "Ni tunda muka taho nan bata ce komai ba, amma kuma dai bata kuka, wani lokacin ta kan yi murmushi kawai."

Dad ya kalli Narma ya ce, "Narma kin gani da idonki, kuma kin ji duk abinda mu ka yi dashi ko? Har baban matarsa na samu ya yi masa magana amma bai yi aiki ba." Ta kalli Dad ta ce, "Da ka amince min tun farko da haka bai faru ba Dad...." Ta ja numfashi ta ce, "amma shikenan na yarda ?addarata ce kamar yadda Yayarsa ta ce, zan yi ha?uri, in kuma ha?urin ya zama ajalina shikenan."

Mum da tashin hankali ta ce, "Akan Omar sai ki mutu?."
"Yes Mum, ina son shi son da ban taSa yiwa wata halitta a duniya ba, ina ?aunarsa matu?ar ?auna." Safna ta ce, "Baza ki mutu ba Bestie, baza ki mutu ba, zaki cigaba da rayuwa kamar kowa, zaki samu wanda zai kula da ke. Ki daina faWar wannan kalmar babu daWin ji."

Narma ta kalli Dad ta ce, "Dad zan shiga Saudia, ina so naje nayi addu'a sosai. Bazan iya cigaba da zama a Nigeria ina ganin Faruk ba, zan tafi can ko zan samu nutsuwa." Dad ya ce, "Shikenan." Bata jira me zai ce ba ta wuce Waki Safna ta bi bayanta.

Dad ya kalli Mum ya ce, "Wai wannan yaron da na raina shine yake wahalar min da zuciyar yarinya haka, abin haushi abin takaici da Sacin rai. Saboda shi mu kazo Kano gashi zuwan bai yi amafanin komai ba, sai Sacin rai da ya ?ara mana, Na yi dana sanin saninsa a cikin rayuwata gabaWaya. Ban taSa kasa yiwa ?a?an abinda suke so ba sai a kansa, a kansa na Waukar mata al?awari kuma na kasa cikawa. Komai suke so ina samar musu dashi, amma na gaza bata Omar."

Mum tayi shiru kafin ta yi ajiyar zuciya ta ce, "amma tabbas nayi darasin rayuwa Dear. Duk yadda mutum ya ke kar ka wula?anta shi dan baka san ya zai zama nan gaba ba, Ban yi tunanin Wan daban yaron nan zai iya zuwa wani matakin rayuwar ba, balle har ya kai ga mun nemi alfarma a wajansa ya kasa yi mana ba. Kuma wai alfarmar ma ta auren ?armu, ban Wauka zai aikata hakan ba. Tabbas Allah ya nuna mana ba komai ka ke nema ka samu ba, duk ta?amarka akan duk abinda suke so kana samar musu dashi Allah ya nuna mana shi yake baka iko. Wannan da bai nufa ba gashi bai faru ba." Dad ya yi shiru bai ce komai ba, amma ya san tabbas abinda ta faWa haka ne, tsaki ya yi ya tashi ya shiga ciki yana tunani da tausayin ?arsa.


? ? ?? Nayla haka ta kwana biyu tana Sata rai, yana lura da ita ya kuma san dalilin fushin, a ganinsa meye na fushi tunda a gabanta ya yanke hukunci, ta kuma san bazai canja magana ba meye zata wahalar da kanta tana fushi kamar wacce aka yiwa laifi. Haka suke rayuwa kafin ya fito ta ajjiye masa breakfast ta bar falon, kafin ya dawo daga office ta ajjiye masa abinci, baya sake ganin ta sai ya yi da gaske.

A ranar lahadi da yamma ya shiga falonta wanda bai cika shiga ba saboda ba?in da ake yawan yi, sannan ga wacce take zaune da ita shi baya sakewa a waje in akwai ba?uwar fuska. Kukan Musliha yaji daga cikin Wakin Nayla, kai tsaye Wakin ya wuce ya buWe sai ya ganta tana sallah. ?arasawa ya yi ya Wauki Musliha ya fita daga Wakin ba tare da ya yi magana ba. Da faWuwar gaba Nayla ta idar da sallar, Allah ya sani bata so ya ganta tana sallah ba, shiyasa take rufe Wakin in zata yi sallah, yau ma tautsayi ne ya saka ta bar ?ofar a buWe.

A sanyaye ta mi?e tsaye ta zare hijjabin daman riga da wando ne a jikinta ?an kanti, rigar tana da tsaho har guiwa amma bata da kauri, wando kuma black jeans ne, ta saka hula ba?a sai shigar ta karSe ta kamar ba wacce take jego ba. Fita tayi zuwa falonsa, ta same shi da Musliha a zaune har lokacin tana ta kuka. Zama tayi a gefensa ya bita da kallo dan shigarta ta Wauki hankalisa sosai, ta Wauki Musliha a jikinsa, ta buWe maSallan gaban rigarta ta fara shayar da Musliha.

Shi dai ido kawai ya zuba mata yana kallonta cikin burgewa, rainon ma kyau yake ma musamman a lokacin da take shayar da ita, sai ya ji kamar ya Wauketa ya saka a Waki yana ta kallonsu. Nayla bata kalle shi ba dan ita tsoro take ji bata so ya yi mata maganar ta fara sallah, shi kuma kyaun da tayi ne yake Waukar hankalinsa, ga wani haske da ta sake yi sai ?hamshi take zubawa mai daWi shiyasa ya kafa mata ido kawai yana kallonta.

Shi ya katse shirun ya ce, "Gobe zamu kai ta passport, ina tunanin zamu yi tafiya a kwanakin nan." Nayla ba tare da ta kalle shi ba ta ce, "to." Daga nan tayi shiru bata sake cewa komai ba.? Gumin da Musliha take yi a goshinta ta saka hannu tana goge mata har lokacin shayar da ita take yi bata cire ba. Bacci ta yi a jikinta, ta cire ta ta mayar da maSallan ta rufe, ta gyarata a jikinta tana gyara mata hular kanta.

Shiru ya sake ratsa tsakaninsu, kamar ta yi masa maganar Narma amma sai ta fasa, ta gama gyara Musliha har lokacin bata kalle shi ba. Shi kuma kallon ta yake yi yana murmushi a zuciyarsa, wai kishi take yi kuma take fushi dashi, ita a wajanta haka take kishin ana share miji kuma ana fushi dashi. Bayyana murmushin nasa ya yi har ta ji sautinsa, sai a lokacin ta Wago suka haWa taga sai murmushin yake yi, sai ta yi tunanin ko sallar da ya ga ta fara ne ya saka yake murmushi, dan ta san halin kayanta, tsaf ganinta tana sallah zai saka shi murmusawa dan an daWe ba a haWu ba. Gabanta ya faWi sosai dan ita bata shirya koma masa ba.

Bata iya cewa komai ba shima kuma bai ce ba, dan shi bai ga laifin da ya yi mata da take share sa ba. ?o?arin mi?ewa ta ke yi zata bar wajan, ya daure ya ce, "Ina zaki je?." Nayla ta kalle shi ta ce, "Waki zan je."

"Kar ki tashi, ki zauna" ya faWa cikin bada umarni yana kallon ta. Fasa tashin tayi tare da yin ajiyar zuciya, sai ta sake bashi dariya ya sake yin murmushi ya ce, "Hajiya Jidda manya mata! Ranki ya daWe gimbiyar mata, sarauniya mai mulki a duniyar Omar" ya furta yana murmushi.

Bata kalle shi ba wasa take yi da hannunta, ya sake yin murmushi ya ce, "Dole sai kin saka na yi magana ne? Ni ban ga dalilin wannan fushin ba, laifin me nayi miki?." Ta kalle shi a ?ufule ta ce, "Sai yau zaka tambayi me ka yi min? Kwana nawa da yi min laifin sai share ni ka ke yi irin baka damu da ni ba balle fushina?."

Dariyar da ya ke Soyewa ta bayyana ya ce, "Jidda ni ban yi miki laifi ba, haka kawai ki Wauki fushi dani ki ka sakawa a zuciyarki, shiyasa na baki hutu ki yi fushin ki gama sai mu yi magana." Ta kalle shi tana harararsa ta gefen ido ta ce, "baka damu ma da fushin nawa ba tunda har hutu ka bani ko?." Ya juyo yana kallon ta sosai ya ce, "na damu mana, kema kin san na damu sosai." Ta kawar da kai gefe, ya saka hannu ya juyo da fuskarta yana ri?e da fuskar amma bai yi magana ba.

Murmushi ya sake yi dan wallahi dariya take bashi ya ce, "Yanzu meye kuma? Uhum....ina jinki." Ya faWa yana kallonta. Ta kalle shi ta ce, "misali a zo har cikin gidan nan a zauna a gabanka ana cewa ana sona za a aure ni, zaka ji daWi?." Ya Wan gimtse fuska kaWan ya ce, "Kina matar tawa za a ce ana sonki?."

Sai kuwa ya tunzurata, cikin fusata ta ce, "Nima ai kana mijin nawa aka zo aka ce ana sonka, gashi nan har ka haWe fuska saboda baka ji daWin maganata ba, abinda ka ji a ranka a yanzu nima shi na ji kuma ka share ni. Nima fa ina da kishin nan, amma a komai sai ka nuna kamar ka fini sanin mahimmacin kishi, yadda ka ke ji a kaina haka haka nake ji a kanka!."

Shi dai kallon ta yake yi ganin yadda take yi masa masifa kamar zata zane shi, bai ce komai ba har ta kai ?arshe. Sai da ta saka full stop sannan ya ce, "Kina jin kishina Jidda, amma asalin kishi ni nake yinsa ba je Jidda, a cikin kashi goma baki Wauki kashi Waya daga cikin kishinki da Allah ya Wora min. Ke fa ni kaWai Allah ya halitta miki a duniya, ni kuwa Allah ya halatta min mata har guda huWu, zuciyarki ni kaWai zan zauna a cikinta, ni kuwa....." a fusace ta katse shi ta ce, "mata dubu zasu zauna a cikin taka zuciyar ko? Zaka iya saka son mata dubu a zuciyarka ko!?" Ta faWa cikin masifa tana kallon sa.

Murmushi ya yi mai sauti yana girgiza kai ya ce, "Tuba nake ranki ya daWe, ni ba haka nace ba."
"To me ka ce? Me ka ke nufi da abinda ka ce? Kenan ni ban cancanci nayi kishi ba sai kai? Kaine ne ka cancanci ka yi kishin matarka, kaine mai kishi ni kuma banza ce wacce bata kishin mijinta. Wai har Abiy ya kira ka akan maganar nan amma ka kasa faWa min, inda nice nayi kwatankwacin abinda kayi min da kaf garin nan sai an ji kan mu. Amma ni da ka yi min share ni ma kayi ka daina shiga harkata, saboda kaine kawai mai kishi a duniya ni bani dashi!."

Ya saka hannu ya shafa gashin fuskarta yana wani murmushi mai Waukar hankali ya kalle ta, ganin yadda ta gimtse fuska ya sake bashi dariya ya ce, "na so na faWa miki batun zuwa wajan Abiy mantawa nayi. Sannan ita bana kawo batunta a raina, mahifinta ma da yaje ya same ni mantawa nayi da batun gabaWaya shiyasa ma ban faWa miki ba. Kuma da ta zo gidan nan Jidda ni na kawo ta? Ni ban ce tazo ba ai, kuma a gabanki tazo ban san ya akayi tasan gidan nan ba, kuma da ta zo me nace mata huh....!?."

Kawar da kai tayi gefe tana Waure fuska, ya saka hannu ya juyo da fuskarta ya ce, "FaWa min mana, me nace mata?." Bata ce komai ba ya ce, "Jidda bani da ra'ayin ?ara aure a rayuwata, bani da ra'ayin yin aure balle har nayi tunanin zan iya aurenta. Maganar sona da take yi kuma ai mun yi magana dake tun a baya, bana da bu?atar maimaita miki wannan maganar. Kuma ni ban Wauka zaki yi fushi haka ba, kin san halina, kin san abinda zan yi, kin san wanda bazan yi ba. Kuma na faWa miki komai a kanta tun farkon zamana dake, ban Wauka dan tazo gidan nan zai dame ki ba, amma sai ki ka yi fushi ki ka daina kula ni" ya ?arasa maganar cikin karayar murya yana kallon ta.g
P106

Nayla ta kawar da kai kafin ta sake kallon sa ta ce, "Meyasa komai ka ke faWa min baka mantawa, amma batun Narma shi kaWai ka ke mantawa baka faWa min ba?."
"Kema gashi kin faWa, bana manta duk wani abu mai mahimmaci na rayuwata, komai da ya faru nake sanar dake. Amma ita saboda rashin mahimmacinta ne shiyasa nake mantawa Jidda."
"Uhum."
"Baki yarda ba?."

Ta kawar da kai gefe bata ce komai ba, ya zuba mata ido yana kallon ta ganin ta?i sakin fuska alamun akwai sauran damuwa a ranta. Kallon da yake aika mata dashi ne ya fara shiga zuciyarta yana yawo a jininta, ta sauke numfashi bata ce komai ba kuma ta?i yarda ta kalle shi. Can ?asan ma?ogwaronsa ya ce, "Jidda!."

Nayla ta kalle shi fuska babu walwala ta ce, "To ba kai bane ka ke share ni..? Kai ta hararata, kuma ka san ni bana son ganin idonka in kana harara ko ranka a Sace. Kuma ai ka san dole zan yi kishi ko yaya ne tunda kai mijina ne, amma ka yi min banza ko kula ni baka yi. Ka fara daina sona kawai, yanzu Musliha ka ke so ba ni ba."

"Yanzu harararki da nayi shine matsalar?..." ya yi shiru yana kallon ta har lokacin fuskarta a Waure. Ya ce, "To Jidda Allah ya baki ha?uri, shikenan ko?."

Bata kalle???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? shi ba ta sake kawar da kai tana goge idanu ya ce, "ko ba shikenan ba?."
"Shi kishin da nake ji nayi ya ya dashi?."
"Ki cigaba da jin kishin a zuciyarki, wannan halak ne dole ki yi kishi dani." Bata kalle shi ba kuma fuskarta a haWe har lokacin bata yi dariya. Ya ce, "C'mon Ashiq, ki yi murmushi na gani."

Bata yi murmushin ba ta ce, "ba wani murmushi da zan yi, ka daina sona gabaWaya, Musliha ka ke so yanzu bani ba." Ajiyar zuciya yayi yana kallonta, wannan rigimar ta ta kaWai ya san yana iya jura a duniya, ba ya so aje gaba a dawo, amma in tana rigima sai aci awa Waya ana maimaita abu Waya.

Ya ce, "Ina son Aisha baki yi ?arya ba, amma son da nake miki daban wanda nake mata daban. Ke fa kece rayuwata Ashiq, daga ke babu wata, daga ke ba ?ari, kece dai duniyar Omar, aljannarsa, kuma matarsa. Babu ta yadda za a yi Aisha ta fiki a wajena. Ita soyayyar uba da ?a nake yi mata, ke kuwa fa...? Soyayyar da nake yi miki ta tara komai a cikin ta Jidda." Turo baki tayi gaba, sai tayi murmushi tana ?ifta idanu. Murmushi shima ya yi ya ce, "Sai da ki ka wahalar dani zaki murmushin? Shikenan na gode. Yanzu fushin dai ya wuce ko?."

Bata yi magana ba ya Wauke Musliha daga jikinta ya kwantar da ita a gefensa, ya ri?o hannunta ta taso gabaWaya ya zaunar da ita a jikinsa ya zagayo da hanunsa ?ugunta ita kuma ta sa?alo wuyansa da hannunta tana kallonsa kamar yadda yake kallon ta.

"kin bar fushin ko Ashiq Wina?" Ya faWa yana kai hancinsa wuyanta yana shakar ?hamshinta wanda ya ke kashe masa jiki. Yadda yayi maganar a hankali itama sai ta ce, "A'a, ban gama ba."
"To me zan yi miki?" Ya faWa yana Salle maSallan gaban rigarta tare da kifa kansa a wajan yana jan numfashi a hankali.

"Ka yi min wa?a." ?ago kai ya yi ya kalle ta, dariya ta so kubce mata ganin yadda ya Wago da sauri, amma ta daure ta ce, "Ni dai ita nake so."

Ya Waga girarsa sama ya ce, "ban iya wa?a ba Jidda." Nayla da shagwaSa ta ce,"Uhum uhum! Allah ni wa?a nake so, kuma kai nake so ka yi min wa?ar, in ba haka ba bazan ha?ura ba." Wani irin shock ya ji kamar jan wutar lantarki a ?wa?walwarsa, hakan ya saka shi ri?o kanta da sauri ya haWe bakinsu waje Waya ya hanata yin magana yana tunanin ko wacce wa?a ya iya da zai yi mata oho.

Nayla ta raba fuskarta da tasa tana yi masa kallon shagwaSa ta ce, "ni dai ka yi min wa?a, Allah in baka yi min wa?a ba na daina kula ka."
"Jidda bana jin wa?a."
"Allah sai ka yi min wa?a, in baka yi ba bazan daina fushi ba."

Ajiyar zuciya ya yi yana binta da kallo, ya Wan yi shiru yana tunawa da wata da wa?a da yake yawan ji a tiktok, kuma ta yi masa daWi saboda sunan Jidda da ake faWa har yake cewa zai rera mata.

Gyaran


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login